Zee Baby Book 1 Page 42
*????????42*
….cikin sassarfa ya karaso gareta ya riketa ya mannata jikinsa yana buga bayanta” zainab ki tsaya mana kukan me kike babu inda zani shiru tayi ta kwanta kirjinshi ta d’ago da kanta tana kallonsa murmushi ya sakar mata” my kanwas murmushi ta sakar masa hawaye nabin kumcinta cikin sanyin murya tace”my kanwas lumsassun idanunsa ya zuba mata zuciyarsa na wata irin bugawa ya tallabo kanta hawaye yacika masa idanu ya lakuto. hawayen fuskarta ya lasa” my zainab meyasa zakimun haka me haka yake nufi menene ya faru dake please idan wasane kike ki dainamun kinji murmushi ta Saki ta zuba masa manyan idanunta ta beka hannuta ta shafo hawayen fuskarsa ta lashe ta rike fuskarsa ta maimaita abunda ya fada mata da sauri ya Mike ya cire mata na’uran da ya jona mata ya zaunar da ita ya juya ya nufi gun wata na’ura aikuwa ta fashe da kuka da Sauri ya dawo ya ware mata hannunwasa tazo gareshi Sam batasan
hakanba Dole yazo ya Sanya hawansa ya dauketa kamar baby ya rungumeta ” to yi shiru kallonsa take tana shashekar kuka tace”my Kanwas” Na’am my Kanwas please kimun rai kibar kukan ahaka tana jikinsa ya nufi gun Na’uran ya kunna ya dawo bakin gadon ya kwantar da ita harzata fara kuka taga ya zauna tayi shiru jona mata Na’urorin wayarsa ya dauka ya kira Daddy bugo daya ya daga da sallama “assalamu alaikum Dr Allah yasa muji alkhairi”Daddy” please kuzo yanzu hospital harda momyna da ummi duk kuzo kuga hukuncin Allah ya sake sabka akanmu Allah yasake Dora mana wata jarabtar arikice daddy yace” Sardauna meke faruwane? ” Daddy sai kunzo kitt ya tsinke kiran ya kwantar da zee da ta tsareshi da idanu ya shiga duba lafiyarta, su Daddy sunzo suna waje saida ya kwashe awa daya cur ko ina na jikinsa rawa yakeyi sai sunayen Allah yake kira ya cire abun da ya jona akunnesa dabas ya zauna ya cire mata na’uran ya zuba mata idanu kukanma ya kasa Nabeel ne ya kirasa awaya su Daddy sun matsu suga zainab yace ya kawosu, kofar aka turo da sallama ya amsa ghaisha da ummi da gudu sukayi gun zee ai tana daga kwance taga mutane na nufota akidime ta Mike zaune ta fashe da kuka ta fada jikin Sardauna tana karkarwa ta boye kanta acikin kirjinshi
tana kiransa” my kanwas rungumeta yayi yana buga bayanta ya Kara boyeta jikinsa sosai tamkar cinyeta zasuyi hankalinsa atashe yace” baby yi shiru bari kukan lafewa tayi jikinsa ta rikeshi gam tayi shiru ta lumshe idanunta ya kalli su daddy ” wlh Daddy akwai babbar Matsala batasan kowa ba fah ayanzu sai ni sabode tayi losing memory ta mance kowa da komai nata na baya sai Wanda za’a koya mata yanzu da ita da Wanda aka Haifa yau basuda banbanci Nima abinda yasa ta yarda dani saboda tana bude idanunta nita fara gani ita atunaninta babu kowa cikin duniya sai mu biyu daddy yace “innahlillahi wa’innailaihi Raji’un Allah mun gode maka kuma mun amshi jarabawar da kake bamu ummi Raiyan fashewa tayi da kuka ghaisha ta rungumeta”kiyi hakuri Raiyan zata samu sauki da yarda Allah kinsan bawa baya wuce kaddarasa Daddy yace”Raiyan don Allah kiyi hakuri zata warke insha Allah daddy yazo bakin gadon ya zauna “Dr yanzu yaya za’ayi fitar da ita za’ayi k’asar waje ko yayane?” Daddy zata warke insha Allah akwai maganin da zan dorata akai da yarda Allah lokacin da yaso zata dawo haiyacinta koda yaushene babu yau babu gobe ghaisha taja hannun ummi Raiyan ta zaunar da ita saman kujera ta nufi gun Sardauna ta dafa kafadunsa”Dr Sardauna yanzu ya zamuyi momy ta saba damu ta yarda murika koya mata abubuwa? Daddy yace tashin hankalin kenan, ai
Sardauna ya furzar da iskar bakinsa ya kalli zainab da tayi luf ajikinsa idanunta arufe ta rikeshi gam kamar zai gudu murmushin karfin hali yayi”Daddy muje gida yanzu sai nasamu nayi Mata yan dabaru ta yarda da ummi saboda ta Rika koya Mata abubuwa idan yaso zan kasance ina bata abunci da magani mu dage dayi mata Addu’a zata warke Dr Nabeel yace” Dr ayanzu yarinyarnan bazata iya rayuwa da kowaba sai dakai saboda kaika dai take gani mutum Dan uwanta Sardauna ya kalli Dr Nabeel “Dr kaje ka dubo mun irin magugunan da ya dace mu dorata akai ka kawomun kai Nabeel ya d’aga ya fice ghaisha kukan tausayin zeey ne ya kufce mata Sardauna yace”momy kiyi hakuri Adfu’a zaku mata ba kuka ba janyeta Sardauna yayi daga jikinsa ta bude idanunta ta saka masa kuka”baby tare zamu yi hakuri sabkota yayi daga saman gadon ya shidota k’asa ya rike hannuta boyewa tayi abayansa tana rike da rigarsa daddy yace”Allahu Akbar
Allah ya baki lafiya Sardauna yace”Amin ya kwashe wayoyinsa ya kalli iyayan nasa” Daddy mutafi gida asamu tayi wanka taci abunci mik’ewa sukayi Sardauna yana rike da hannuta ya rigasu fita waje zainab na rike da rigarsa har suka fito yana jiran Nabeel kafarta ya kalla ba takalmi ya cire na kafarsa ” baby bari nasamiki nawa sakarmun Riga idanu ta zuba masa dan bata gane me yake fadiba ahankali ya cire hannunta daga rigarsa ya sunkuya gabanta ya kamo hannuta ya dora akafadarsa ta rike tana dariya ya kamo santaleliyar kafarta fara tas tamkar ta jarirai dan taushi ya saka mata takalminsa sun mata yawa sosai murmushi yayi ya Mike tsaye ya dagota dariya tayi ta fada saman faffadan kirjinshi tace”my kanwas? rungumeta yayi”Na’am my kanwas kallonsa take tana murmushi shima kallonta yake baima San iyayansu sun fito ba da kallo suka bisu daddy ya jinjina kansa yanajin dadin yada Sardauna yake kula da zeey Dr Nabeel ne ya ISO
da leda ya hado Wanda suka samu dafa kafadar Sardauna yai “Dr gasu kallon Nabeel yayi ya beka hannu ya amshi maganin”OK zan duba idan mun isa gida thanks Dr murmushi Nabeel yayi” ai munatare uban gidanmu kai Sardauna ya girgiza ya kalli daddy” my dady mu tafi ya janye zainab ya kama hannunta ummi Raiyan hawaye ya cika mata idanu yau gata ga zainaba amma batasan taba Sardauna yace” dady kuje gamunan zansa takalmi a Office “to sai kunzo Dr hannuta yaja suka nufi Office d’insa ya ciro makullai ya
bude yana rike da hannunta suka shiga idanu take zarowa tana kallon ko ina na Office d’in sakin hannuta yayi yaje yasa takalmi da gudu ta biyoshi ta rungumeshi ta baya tace “my kanwas” Ya Salam ya fada yana juyo da ita gabansa ya rike kafadunta ya zuba mata tsumammun idanunsa”baby babu inda zani takalmi zansa kai ta langwabe tana turo baki sakinta yayi ya kama hannunta sukaje yasa, takalmin ya riko hannuta suka fito ya rufe Office d’in suka fito tana rike dashi gam har gurin mota ya bude ya zaunar da ita agaba ya rufe da ya zagaya ya shiga idanunta har sun tara kwalla yana zama ta kifa kanta saman cinyarsa ta fashe da kuka tana kiransa”my kanwas”Ya
Allah gani gareka baby ya zanyi Dole fah zamu rabu tunda ba guri dayaba zamu rinka kwana dake ba please ki daure kisaba da rashina ah irin wannan lokacin jikinsa ya janyota yana bubbuga bayanta yakai bakinsa kunnenta” yi shiru baby nine nataba Habibty shiru bazan sake barinki ba ina tare dake baccine zai rika rabamu lafewa tayi jikinsa tanajin dadin maganar da yake mata akunnenta ta lumshe idanunta ta kamo hannunsa ta rike cikin nata gam jin tayi shiru yayi murmushi ya janye bakinsa ya gyara mata kwanciya jikinsa ya tashi motar ya nufo bakin get horn yai aka bude masa get ya fice ana ta daga masa hannu driving yake cikin nutsuwa zuciyarsa babu dadi damuwa tayi masa yawa ga zainab cikin halin da take ayanzu tana bukatar kulawarsa hannusa da ta rike janye ya dora saman kanta ya shafi gashinta” my baby kanwas kara shigewa jikinsa ta d’ago da kanta tana lumshe masa idanu muryata can k’asa tace”my baby kanwas kallota yayi ya daga mata