Zee Baby Book 1 Page 42
gira ya maida hankalinsa kan driving ta maida kanta kirjinshi ta lumshe idanunta Nisha ta kirasa,har sau biyu bai dagaba ahaka har suka ISO gida horn yayi aka bude masa get ya shige da motar nan tskiyar harabar gidan yai parking ya kashe motar,
ya dagota”My Baby Kanwas Oya mushiga ciki murmushi tayi ta dora hannunta saman dogon karan hancinsa tanaja kai ya girgiza ya janyeta jikinsa ya bude motar ya fito da ita shima ya fito ya zagayo ya kama hannuta da ido takebin gidan har suka shiga parlon da sallama hafeeza ta taresu da gudu zata riko zee tayi tsale ta makale Sardauna tana ihu. janyeta yayi ya nufi gun ummi ya zauna zee na daga gefe tana makale dashi sai wani irin kallo takema su Najib da su minata da Tuwusai Sardauna yace” ummi kuje ki gwada mata wanka da sallah da sauran abubuwa agyara mata gashinta kufito ina jiranku na bata abunci da magani sai natafi mik’ewa ummi tayi Sardauna ya mikar da zeey tsaye”baby kuje agyaraki tsaresa tayi da idanu tsaye ya Mike ya kama hannunta yajata har kofar d’aki yaba ummi ita fur taki tafiya ta fara kuka daurewa yayi ya had’e fuska ya daka mata tsawa wuce maza ku tafi nace cikin rawar jiki ta labe bayan ummi tana kiransa”my baby kanwas kai ya kauda”ummi kuje ki nuna mata ya fada yana juyawa ya
dawo kan kujera ya zauna kusan ghaisha ya kwantar da kansa kafadarta ya lumshe idanunsa zee ko Dole tabi ummi suka shiga da ta rike mata hannu fizgewa tayi suna shiga ta shiga bathroom ta hada ruwan zafi tazo tajata tana tirjewa harda kuka tana Kiran my kanwas haka tajata ummin kanta hawaye take daket ta cire mata kayan jikinta ta nasata cikin ruwan gumin tana zuba mata ruwan har kanta da kanta tayi mata wanka har dukanta take amma saida ta wanke tas har gashinta bayan ta gama mata ummi ta tube ta kunna shower ta dauki soso da sabulu tana wanka zee ta fito itama ta tsaya gaban shower ta amshi soson tayi duk yada ummi tayi tana murmushi towel ummi ta d’aura itama ta d’aura ummi tayi Alwalla zee ma tayi suka fito tana karda gashinta tana dariya gaban dressing mirror ta janyota ta tsane mata gashinta ta shafa mata man gashi ta dauré mata da Ribbon yada ummin tayi abaya mai kyau ummi ta dauko mata ta bata ummi ta dauko tasaka itama ta saka tayane mata kanta da mayafin abayar
Darduma ta shimfida itama zee tazo ta tsaya gaban ummin tana kallon tana turo baki tace”my kanwas ta fada tana nuna kofar daki janyota tayi suka kalli alkiblah ummin ta tayar da kabarar sallah duk abinda ummin tayi cikin hukuncin Allah shi zee takeyi sukayi sallah isha’i bangaran Sardauna ghaisha ta shafi kansa”Auta kayi hakuri kafara cin abunci ansan mutuwa da ciwo amma babu yada muka iya daddy yace”Faisal ka dauré muyi ta wakali mu amshi kaddara kaga yada Allah ya sake jarabamu ta fannin zainab minata ta share hawaye tace”wlh ina tausayinta sosai baiwar Allah sai abinda aka koya mata Sardauna jinsu kawai yake dan basu fishi shiga damuwaba dauriya yake ga rashin d’an uwansa na ragargazar zuciyarsa ghaisha ya kalla”momyna kanshi ta kuma shafawa”Na’am Autana me kakeso? ” babu komai ya fada yana murmushin karfin hali” zakasha coffee? su ummi ne suka fito zee tasha abaya mai kyau da mayafi da gudu tayi kan Sardauna fuska ya had’e ganin yada yayi yasa ta karasa anutse ta zauna kusansa tana kallonsa ta matsa ta kwantar da kanta kafadarsa”my baby kanwas daddy kallonsu kawai yakeyi janyeta yayi ya Mike ya kama hannuta ya dauki ledar maganin
ya nufi kan dining.kujera yaja ya zaunar da ita ya dauki plate ya zuba mata abunci jalof d’in shinkaface taji busashen kifi shi ba ciba yake amma Dole ya zuba ya zauna ya dauki spoon ya ya tsakuro yakai bakinsa murmushi tayi ta dauki spoon d’in ta tsakuri abuncin takai bakinta tana kallonsa kai ya daga mata” Oya baby ci sake daukowa tayi tanaci ganin tanaci ya ajiye spoon din hannusa itama ta ajiyewa tai” baby kici mana kafada ta makale tana kallonsa dauka yayi ya tsakuro yana bata da kansa tako amsa tanaci ta matsa ta kwanta jikinsa ahaka ya bata abuncin har ta koshi ya bude robar ruwa ya dago kanta ya kafa mata robar ta rika sha saida yaga ta dan sha mai yawa ya barta ledar maganin ya bude ya duduba ya b’aballosu ya tallabo kanta ya zuba mata cikin baki ya dauki robar ruwan ya kafa mata abaki tasha saida ya tabbatar ta shanye ya ajiye ya rungumeta yana shafa kanta sanin maganin yanzu zai fara aiki don bayaso tayi kuka idan zai tafi d’ago da kanta tayi tana kallonsa hannuta saman dogon hancinsa tana Ja tana murmushi gira ya daga mata yana hura mata iskar bakinsa yana shafa lallausan gashinta suna kallon junansu idanu ta lumshe yada yake hura mata iskar bakinsa ta kara rikeshi gam. ganin alamun bacci sun fara baiyana ya mikar da ita ya dauki ledar maganin ya riko hannuta sai lumshewa take ya ratso ta parlon suka shige dakin ummi ya kwantar da ita ya zauna yana shafa kanta kin kwanciya tayi ta tashi ta kwanta cinyarsa barinta yayi yana buga bayanta ko 5 minute batayi ba tayi bacci ya kwantar da ita ya rankwafa ya sakar mata kiss saman lips d’inta da
goshinta ya shafi fuskarta”my zeener da sonki zan mutu wlh ina mugu mugun sonki da kaunarki amma babu damar zama dake tabbas nasan sai sonki ya kasheni zuwa GABA zuciyata inada yakinin zata buga akanki nayi miki alkawalin tsayawa na kula da rayuwarki har Allah ya baki lfy ki warke na zaba miki miji nagari ki aura rungumeta yayi yana wani irin sabke ajiyar zuciya”my zainba i love you kece bugun numfashina ina sonki sonki kasheni zaiyi nan GABA kadan sosai ya rungumeta da karfi yana sabke Numfashi da karfi saida ta motsa tana kiran “my kanwas tana rungumeshi “Na’am bugun numfashina janye jikinsa yayi ya tofa mata Addu’a yaja blanket ya lulubeta
Ya Mike ya fice daga d’akin ya fito parlo Daddy yace “Allah ya biyaka Sardauna yace”Ameen daddy yayima iyayansa sallama ya tafi hafeeza ta Mike ta nufi dakin tana hawaye tuwusai tace”bawan Allah wlh dauriya yake yaron yanada damuwa ghaisha ta share hawaye tace”ai Dole rabuwa da dan uwa rabuwa ta har abadan ga el uwasa cikin mawuyacin hali ummi tace “khadijah hakuri zamuyi mu amshi kaddara daddy yace” mutumin da Allah baya jarabarsa ai ba mutum bane yayi kuka da kansa minata tace” niko Abdulmutallab inada magana amma bari naga Daddah tukun da mai ran karfe? kai ya jinjina” to Allah ya kaimu goben saboda dare yayi kowa ya Mike ya nemi makwancinsa ummi tana shiga tayi shirin kwanciya kafin karfe biyu ta tashi sallah ta kalli hafeeza da ta rungume zainab hawaye ya bushe kan fuskarta har bacci ya dauketa saman gadon ta hauro ta kwanta gefen guda ta rungume zee tana shafa kanta tana tofa mata Addu’a” hafeeza yau jikin el uwa akayi bacci Allah sarki ta fada tana goge hawaye tana tunanin yaranta da iyayanta kullum burinta mahaifinta da mahaifiyarta su dawo gareta da ‘ya’yanta ahaka har bacci ya dauketa Asubah ta gari,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sardauna lokacin da ya isa gida Nisha tana parlo tana jiransa hankalinta atashe sai sunturi take ta kasa, zaune takasa tsaye ta hada cikin kayan bacci farare tas Riga da wando knocking taji anyi da gudu nufi kofar ta murza key ta bude yana sayo kafa ta fada jikinsa ta fashe da kuka ta rungumeshi”my heartbeat ina kashiga ina kiranka baka dauka rungumeta yai yana buga bayanta yakai bakinsa kunnenta”My Neesher Sorry ki yafemun naga kiranki banida nutsuwane yi shiru bari kuka my Neesher ina cikin koshin lfy kinji matata shiru tayi ta kara shiga jikinsa tana sabke ajiyar zuciya daukarta yayi cak” muje ki kwanta ya babyna? fuskarsa ta shafa ta sakar masa kiss ” my Dr inajin sonka kamar zai kasheni ta fada tana lasar fuskarsa “no maman babyna muna tare insha Allah inason zama dake ya fada yana shiga bedroom d’insa da ita saman makeken royal bed d’insa ya zaunar da ita ya lakaci hancinta”Nessher Dr kinci kaza ko naje na kawo miki? ” naci sai da safe “gud ya fada yana cire kayansa bathroom ya shiga ya santalo wanka ya fito daure da towel yana goge jikinsa ya murza maiyuka masu kamshi Nisha ta dauko masa kayan bacci masu kyau ta saka masa yana kallonta bayan ta saka masa ta dauko turarensa mai masifar kamshi ta fesa masa” thanks my Neesher murmushi tayi kwanciya sukayi ya kashe wutar dakin ya janyota jikinsa ya lulubesu ya dora hannusa saman cikinta yana shafawa” my Dr? ” my Neesher Oya muyi bacci ya fada yana kara shigar da ita jikinsa dan sam bashida nutsuwar da zai iya Saduwa da ita lamo tayi jikinsa hannunta saman fuskara tana shafawa” Dr ina sonka sosai kanta ya tallabo ya sakar mata kiss ya lalubo bakinta yana tsotsa yana shashafata jikinta ta sakar masa tana lumlumshewa har ya rikitata bacci ya dauketa bakinsa ya zare anata ya rumgumeta yana tofesu da Addu’a bai jimaba bacci shima ya daukesa ransa babu dadi sam baya cikin kwanciyar hankali jarumata kawai yake saboda shi Mutumne mai dakiya da tawakali Asubah ta gari Sardauna and Nisha…………✍????