Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 45

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Washe gari amakare suka farka agida Sardauna yay sallah. bayan sunyi sallah. suka koma bacci, sai karfe tara Sardauna ya farka Nisha na manne dashi cikinta ya shafa” baby good morning ya janyeta ya sabko daga saman gadon ya shiga bedroom yai wanka ya fito agagauce ya shirya cikin wata dakekiyar shadda ganila maron colour yayi kyau sosai yana gyara gashinsa Nisha ta farka da sauri ta Mike ta sabko ta shiga, bathroom agagauce tayi wanka ta fito daure da towel Sardauna har ya fita sai kamshinsa ke tashi ad’akin ahaka ta fito ta nufi bedroom d’inta ta shirya agagauce ta murza, mai ta saka Riga da siket na atamfa ta fesa, turare ta fito ta nufi kan dining yana zaune yana waya cikin nutsuwa yana kurbar tea ” wow my Dr kayi kyau sosai ta fada tana zama kusansa ta kwanto jikinsa ta dora hannunta saman fuskarshi”sweetheart? kallonta yay” OK gani nan yanzu amma sai na biya gida thanks bye. ya tsinke Kiran ya kalleta yana had’e face”meye zaki wani zo kina shasha fani. kara shiga jikinsa tayi ta marerece ta kamo fuskarsa, tana hawaye”my Dr kayi hakuri bana iya jure fushinka muje kayi bazan sake rakiba kaji mijina? murmushi yay ya rungumeta” to naji yi shiru amma banaso nima da sauri ta kame bakinsa tana tsotsa idanu ya zuba mata har tagaji ta saki tana dariya kai ya girgiza ya dauki tea d’insa yana kurba” maza tashi kici kazarki babyna najin yunwa janye jikinta tayi tana kallonsa”to ka hakura? ” eh maza ci na hakura ta janyo kular ta bude ta zubi soyayen dankali da cinyar kaza ta faraci sauri sauri idanu ya zuba mata yanzu yanacewa taci ahankali zata fara kuka Dole ya samata idanu dan yasan laifin babynsa ne tea ta hada,

tanasha mik’ewa yay”my Nisha na tafi ba rakiya tsaye ta Mike ta dauki guntun namanta ta biyoshi” my Dr dan Allah inason tafiya gidan zainab nagano baby abin mutuwa bai bari najeba kallonta yay to ahaka zaki da kazar? ” bari NASA aleda”Oya yi maza ki shirya da sauri taje ta zube namanta aleda ta wanke hannunta ta saka hijabi. ta dauki yar karamar jaka tasa ledar namanta ta leka kitchen Rabia na aiki tace”Rabia ina kwana na fita sai nadawo? ” to hajiya Allah kiyaye. ” Amin ta fice har ya fita sai a habar gida ta iskeshi ya fito da mota ta bude ta shiga yaja suka tafi dama get abude megadi na tsaye suka gaisa Sardauna ya fice yana hawa saman titi ya fara gudu sosai ya kalli Nisha yai murmushi “wai Nisha naman ne kika dauko ajaka? kanta ta dora kirjinshi tana dariya” eh wlh my Dr bai sake magana ba ya maida hankalinsa kan driving taname surutu jinsa shiru ta gane miskilancinsa ya motsa shiru tayi ta rungume abunta tana kallonsa idan sun hada idanu ya daga mata gira tayi murmushi har ya kaita kofar gidan zainab tunda unguwa dayace da gidansu daddy saide ba layi dayaba yana parking yace”Oya jeki”Ya Faisal mushiga kaga, baby mana? ” my Neesher na makara ai na ganshi kuma yau zatazo gida wanka kema rashin hakurine kije kawai murmushi tayi ta masa kiss shima ya mata ta bude motar ta fito ta rufe masa lofar yaja ya tafi

get tura ta shiga gidan da Hadeem suka hadu zai shiga mota suka gaisa yace”ai kuwa suma yanzune zasu gida an hada komai. ” masha Allah bari na shiga da gudu tayi ciki parlon ta shigo da sallama taci karo da ummarta zasu fito tana rungume da d’an zainab zainab ta kalleta” Aunty Nisha rungumeta Nisha tayi” zainab wlh nazata bazaki zo wanka ba yau har kwana tara. Hauwa tace” saketa ana jiranmu muje gida sai kuyi surutun. sakinta Nisha tayi suka fito gun motar suka nufa ya bude musu suka shiga ya rufe yaja suka tafi, Sardauna na zuwa akofar gidansu yay parking ya fito ya shiga gidan suna gaisawa da ma’aikatan gidan part d’insu ghaisha ya shiga parlon ya shigo da sallah ghaisha na zaune da su minata da ummi har da zee baby tana kwance jikin ummi jin muryashi ta Mike da gudu tayi kansa tana kuka Dole ya ware mata hannayensa ta fada jikinsa tana kuka rungumeta yay yana sabke ajiyar zuciya” my bugun Numfashi kiyi hakuri nima shinake. cikin shashekar kuka tace”my babyna ina sonki” wlh nima ina miki son so my baby zainabata yi shiru bari kukan shiru tayi tana sabke ajiyar zuciya ta lafe a jikinsa yana buga bayanta baki daya iyayansu suka zuba musu idanu ghaisha tayi tagumi tausayinsu ya cika mata zuciya tuwusai da yake kunsan mutananmu Na Niger basu gani su kyale sai sun fadi gaskiya tace” oh ni tuwusai naga abunda ya gagareni agaskiya Faisal Dole zakaja da baya har zainab ta gama takaba tunda batada iddah bakin kwana arba’in ne wlh son da kukewa, junanku yayi yawa,da abarku kuna irin runguma haka dan banzan yaro kace zaka bada aurenta da wani kaiko ka kwana a ina. munafuki wlh sonta yakeyi Allah sarki mahbeer rabone ya kasheka ta fashe da kuka, murmushi yayi ya janye zee daga jikinsa ya kamo hannunta sukazo gun tuwusai ya zauna ya rungumeta”yi hakuri bari kukan ni bakomai tsakanina da ita shakuwa ce minata tace” kaci gidanku Sardauna ja’irin yaro saida ya, lallaba tuwusai tayi shiru ya saketa yaje ya gaida ummi tace” ina Aisha? ” tana gidan zainab gun ghaisha ya nufa ya gaidata dukansa tayi” Autana bakada, kunya fah murmushi ya mata kiss yaja hannun zee, suka nufi kan dining yaga ledar maganin a ajiye kai

ya girgiza ya zaunar da ita ya hada mata tea ” bugun Numfashina kinki yarda kowa ya baki abunci sai abin sonki ko da idanu ta tsareshi kanta ya rike ya shiga bata tea d’in abaki tanasha har ta shanye ya zuba soyayen dankali da kwai yana bata abaki tanaci tana rike da hannunsa daya har yagama bata ya ballo magani ya bata tasha ta tsora masa idanu tace” my babyna, murmushi ya sakar mata” na’am my baby jikinsa, ta fada tayi masa kiss akumatu ta matsa ta dora bakinta akunnensa tana hura masa iska ta zura harshenta tana lasar kunnensa da sauri ya janyeta, yai kicin kincin da fuska yana hararata zata fara kuka ya buga mata tsawa” shiru karkimun kuka shiru tayi tana zaro idanu tausayi ta bashi ya mikar da ita tsaye”Oya baby muje ki kwanta hannunta ya kama suka nufi bedroom suna shiga ya kwantar da ita ya zauna kusanta ya dora kanta a cinyarsa yana mata waka me dadi da larabci duk batasan me yake fadiba dariya take ta rike hannunsa gam tana dariya tana kiransa”my babyna ina sonki har maganin ya ratsata jikinta ya saki tayi shiru tasa, yatsarsa bakinta tana tsotsa sai bacci har yatsar ta kufce mata tana sabke numfashi ahankali murmushi yasaki ya dauke kanta ya dora saman matashi ya tofa mata Addu’a ya lulubeta ya Mike ya fito su Nisha ya isko sai zuba take tanaga Sardauna tayi shiru dan taji haushinsa ganin daga inda ya fito gun umma Hauwa ya nufa ya gaisheta ya kalli Nisha yace”tashi na maidaki gida? ” dan Allah yaya kayi hakuri sai zuwa dare wani mugun kallo ya watsa mata Dole ta Mike zainab tayi dariya ya kalleta “ke dan kin haihu shine bazaki gaida niba ai ko maijidda ni zata girmama ba keba. gunsa zainab ta nufa ta rungumesa”yayana yi hakuri wlh inada niya ina kwana? ” banaso saida na roka sakeni ni dariya tayi ta sakeshi ta amso mahbeer karami ta kawo masa ya amsa ya zubama yaron idanu yaga sak kamarsa daya da mahbeer kwalla ta taru idanun Sardauna ya rungume yaron yana tofa masa Adu’a ya bata ta masa itama hawayen takeyi haka kawai ghaisha ta fashe da kuka tana kallonsu umma taje ta rungumeta tana bata baki Sardauna gunta ya nufa shima ya rungumeta ya fara kuka kowa yanaga haka baki daya parlon ya kaure da kuka dama su tuwusai akusa ake sai aka mama daddah ta shigo ta fara musu fada daket daddah da Hauwa da ummi Raiyan suka lallashesu Nisha kuka take sosai ganin mijinta nayi zainab kowa yayi shiru kinyi shiru tayi saida Sardauna yazo ya rungumeta ya lallasheta yasa taba danta nono tukun tayi shiru yace da Nisha su tafi ta dauki Jakarta tayi musu sallama suka tafi, suna fita ya bude mata mota ta shiga ya daga ya shiga

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button