Zee Baby Book 1 Page 46

Nisha kanta fashewa tayi da kuka ta Mike taje ta rungume zee, itako dariya take musu ta ture nisha ta koma gurin ummin ta kwanta jikinta ummin kanta kuka takeyi zee ta goge mata hawayen fuskarta ” ummi kirawomun my babyna kinji yau bangansa ba ko yatafi gun mijina mahbeer baki ta rufe mata tana girgiza kai” baby bari fadin haka.ayanzu Sardauna shine garkuwarki bazai miki Nisan da mahbeer ya mikiba rungumeta ummi tayi tana buga bayanta zee ko dariya take tana kwaikwayon maganar ummi wlh kowaye indai yanada imani sai zee baby ta bashi tausayi umma Hauwa ta Mike ta Kara waya a kunneta ta nufi kofar kitchen daddy ta kira bugo daya daga” Haba Yaya wai me kuke jira da safe Baku daura auranba zainab tana bukatar kulawar Sardauna wlh babu Wanda baiyi kuka ba yanzu a parlon nan. “Hauwa kiyi hakuri abinda yasa mun barine sai anjima amasallaci bayan sallah juma’a insha Allahu. ” yauwa to Allah yasanya Alheri ta kashe wayar, bangaran Sardauna kuwa bacci yayi sosai sai karfe sha biyu da rabi ya tashi ya kira nisha ta hado masa tea ya shiga wanka agurguje ya fito ya goge jikinsa ya shafa mai ya mayar da wata d’anyar shadda gizna blue colour sai kamshi yake Nisha ce ta shigo da tea ahannunta wayoyinsa ya kwashe suka fito parlo ya zauna ta zauna kusansa ta jingina da jikinsa” wow my Dr kayi kyau sosai murmushi yayi yaja hancinta tea din ta fara bashi yanasha har ya shanye ya kalli tsadaddan agogon hannunsa karfe daya saura minti biyar janyeta yayi” Oya muje na kusa makara dariya tayi suka fito ya rufe kofar ya nufi gun rumfar motoci takunsa yake cike da izza da jarumta gwanin burgewa sai baza kamshi yakeyi Neesha ta bishi da idanu tana murmushi tana tsaye get din su ghaisha saida ya shiga mota ya nufo get ya kalleta hannu ya daga mata itama ta daga masa ta aika masa kiss megadi ya bude masa get ya fice shima ya rufe ya fice zuwa masallaci Nisha dariya tayi ta shige cikin gida lokacin da Sardauna ya isa masallacin kofar sauro cike yake dam motocin su daddy ya gani amma gun babu inda zai ajiye tashi wani gurin ya nema ya ajiye motarsa ya dauko darduma ya fito ya rufe motarsa ya nufi masallacin acike yake Dole ya zauna awaje ya jira afara sallah Dan gani yake su nawajan sunfi naciki yawa, su daddy suna ciki da mutanan sa liman na isowa aka fara huduba Ana gamawa aka tada sallah masha Allah Al’ummah ba’acewa komai Ana gamawa akayi sanarwa akwai daurin aure Sardauna zai Mike jin haka ya tsaya
yasa musu albarka ya zauna can ciki kuwa kawu Saminu ne ya nemawa dansa Faisal auran zainab Daddy ya bashi Ana take kawu saminu ya ciro dubu dari biyu kash ya bayar Sadaki da huhun goransa guda uku ya ajiye daddy ya amshi kudin ya waribdubu Hamsin ya bashi sauran yace” albarkar aure mukeso ba kudiba Dole Saminu ya amshi sauran sadakin yabawa Nuhu ya rike maitmran karfe yaji dadin hakan nan babban liman da kansa da sauran malamai da alwalin ango da na amarya aka daura Auran Faisal da zainab Akan sadaki nera dubu Hamsin nan mai sanarwa ya fara cewa” jama’a ku amsa fatiha an daura auran Faisal Da Zainabu Abu mai tagwayen suna Akan Sadaki nera dubu hamsin lakadan ba ajalan ba tazama shi yazama ita karaf akunen Sardauna saboda lasifikace ake maganar da ita zuwat ya Mike tsaye jikinsa yana rawa liman suka musu Addu’ar Allah yabasu zaman lafiya daddy yasake bara addu’a akayi musu nan aka shiga Rabo goro da kudi huhun guda daddy yaba liman da kudi nera dubu Hamsin jama’a sai albarka suke samusu saida mutane suka rarage su daddy suka fito Sardauna na hango su daddy ya nufo gunsu daddy ya hangoshi ya tsaya yana murmushi” masha Allah Dr Sardauna ango dariya sukayi yana isowa ya fada jikin daddy ya Saki kuka tamkar karamin yaro jikinsa sai rawa yake daddy yace” haba Faisal jarumin jarumai ya kuma yau kake kuka kaida zakayi farin ciki momy Allah yayi tazama mallakinka fatana ka kulamun da ita ka rikemun ita Amana Allah ya dubomu ya bata lafiya kwana biyu abun nata duk ya rikice amma ba komai mun barma Allah ikonsa yi shiru Dr namu wani kukan ya Saki ya rungume daddy gam Dan ya tunamasa da mahbeer” daddy meyasa kuka auramun matar yayana ni danace zan zabar mata miji nagari murmushi daddy yayi yana buga bayansa “kaikuma kayi yaya da sonta kabar maganar aduk duniya ayanzu babu Wanda zan iyabama zainaba kulawa ta musamman ba kosawa idan ba kaiba Nuhu yazo yana murmushi yace”ai zainab dakai tafi cancanta Saminu yace” yanzu sai mutafi gida Faisal ka ajiye hankalinka D’ana mairan karfe yace ja’iri yanaso kissa murmushi Nuhu yayi ya kama hannusa Kawu Saminu yarakasu har gun motar Sardauna ya bude ya shiga Saminu yace”my son kayi tuki cikin nutsuwa kaji kansa
ya d’aga Nuhu ya rufe masa kofa Sardauna yayima motar key yaja ya tafi daddy sai murmushi yakeyi suka shiga mota suka tafi. acikin Nutsuwa Sardauna yake driving yarasa wani irin yanayi yake ciki farin ciki ko akasin haka sigari ya dauka ya kunna ya fara bata hayaki baki da hanci kai tsaye hospital ya nufa saboda yau bai lekaba akwai yaron da zai duba jiya da tunaninsa ya kwana, can gida kuwa bayan an dawo daga sallahr juma’ah suka Mike kowa yaje yayi sallah, zaune suke saman dinning su maijidda sai kwasar gara ake ummi tayi tayi da zee taci abunci taki ta kafa, musu kuka sai babynta yazo yau bata ganshi ba ko ya mutune duk ta fitinesu. Neesha tace” kiyi hakuri zaizo ai ghaisha tace” momy zo ga wayata ki kirayi mijinki da kanki nasan zuwa yanzu an daura auran da Sauri Neesha ta kalli gashi dariya zee tayi ta Mike taje gun ghaisha ta zauna ta amshi wayar su daddy ne suka shigo da sallama Hauwa ta Mike”Dan uwa ya da fatan an daura murmushi daddy yayi Nuhu ya bata goro farare tas ba kadan ba cikin farin ciki Hauwa tace Alhmdllh Saminu yace”Alhmdllh tazama matarsa fatanmu Allah yabata lafiya cikin farin ciki suka gabaki dayansu suka ajiye spoons sukace amin suka Mike zainab ta rungume zee maijidda tace Allah ya baki lafiya maryama tace” zainab Amaryar Sardauna Nisha uwar gida ghaisha farin ciki ya hanata magana Nisha har wata zufa take keto mata tayi ta maza ta goge tana murmushi ta nufi gun zee ta rungumeta” Alhmdllh my dear zan rikeki Amana Allah yabaki lafiya yau kin zama matar babynki ko? ta fadi tana murmushi kallonta zee tayi tana murmushi ” ke ni matar mahbeer ce ba babyna ba maijidda tace” ai an daura muku aure dashi jikinta ta janye ta nufi gun daddy tana dariya” daddy wai babyna munyi aure yo mahbeer din fa hannunta ya kama idanunsa ya ciko da kwalla yace” momy kinci abunci dariya tayi” daddy wlh bazanci ba sai my babyna yazo yabani abaki wayarsa ya ciro daga aljihu ya lalubo number Sardauna bugo biyu ya d’aga yabawa zainab” amshi momy yi masa magana maza yazo ya baki abunci amsa tayi ta Kara akunne ashagwab’e tace”my babyna kazo kabani abunci nasha magani tun d’azu nake kuka ko me yace mata tayi dariya tana tsalle tace”????????yeeee mijina kazo yanzu wayar ta bekama daddy tana ta murmushi ta nufi bedroom da gudu da idanu suka bita cike da tausayinta su daddy kan dining suka nufa ghaisha ta bisu ta hada musu abunci ummi yawan surutun zainab ya fara damunta dannewa takeyi sai take ganin yar tata kamar ta haukacene Neesha fakar idanun motane tayi tabi bayan zainab bedroom tana shiga zee na fitowa da ledar magani ahannunta shiyasa sukayi Karo Nisha ta mayar da ita ciki ta rufo kofar “my dear don Allah ki saurareni. zee ta bita da kallo tace” meye ne ni gun babyna zani riketa Nisha tayi ta fashe da kuka zee ta kalleta…………… ????