HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Snn idan taje hutu Jigawa kuma mamanta bata damu da tasa ‘yar tata a gaba dan ta gano matsalarta ba, sai tasata tayi ta zaga dangi ‘yan uwan babanta, dan Ita a tunaninta Rumaisa tana samun kula da tarbiya yadda ya kamata, Shima Baban ta hankalinshi kwance dan gani yake ‘yarshi bata da wata matsala, dan ba alamun hakan tattare da ita.

Sauk’in abunma Kabeer ya tsaya tsayin daka akan karatunta da haka zata taso ba sanin addini sosae, tunda malamin da kawu ya d’auko yake mata lesson a gida ma ya koreshi yace Shima bai yarda da shi ba.

Kewar Kabeer take sosae kamar tayi yaya, amma ganinshi ya gagareta, ko ta kirashi a waya kuma baya d’auka, kullum cikin zullumi da tuñaninshi take.
Gashi ba damar fita dan kwata kwata an hana ta fita ko kofar gida.

**********
Kabeer kam gaba D’aya ya koma wani iri, so yake lallai sai ya yakice Maisa daga zuciyarsa amma abin ya faskara. Wani irin zafi da rad’ad’i yake ji a zuciyarshi du lokacin da ya tuna da halin da ta jefa kanta ciki.

Duk iya kokarinshi, har da Addu’a ya ke had’awa Allah ya cire mishi Maisa a zuciyar shi, all to no avail ………..

Kawu ko ba karamar matsala ya shiga ba sanadiyyar barin ta gidan, ya zamto ko bak’i yayi, suna hira kallonsu yake kawai amma hankalinshi baya garesu.
Ko wani gurin yaje sai an gane yana cikin damuwa.

Gaba d’aya ya daina ma d’an uwanshi baban Kabeer magana, ko ya mishi baya amsawa.

Halin da matar kawu khamis ta shiga baya fad’uwa, dan gaba d’aya gidan ya zama kamar gidan makoki, duk yadda taso su daidaita da kawu ya ki saurararta.
Ba abinda yafi d’aga mata hankali irin yadda ya maida ita matar kulle ka’rfi da yaji, kwata kwata ya hana ta fita, ba damar taje gurin ‘yan uwanta, ko gidansu ya hanata zuwa.
Tun tana tunanin abin na d’an lokaci ne har taga dai abin da gaske ne.

Kuka tayishi har ta gode Allah, har ciwo ta kwanta, yace ciwon na gulma ne ba maganin da zai sayo mata.

Kannenshi mata biyu wanda suke ciki d’aya ne suka zo gidan, suke tambayar basu ga Maisa ba .

Nan ta kwashe komai ta sanar dasu.
Salati suka shiga yi dukansu biyu kafin d’aya daga cikin su tace anya Dadda ta bar yaya Khamisu banza kuwa.

D’ayar tace, “Kuma fa da gaskiyarki, haka kawai bazai shiga damuwa dan an d’auketa daga gidanshiba, saidai in asiri ta mishi.

Subhanallah wato ma ba cikin da tayi ne ya damesu ba, damuwar d’an uwansu ya damesu.

Nan sukayi ta surutansu Suna cewa ya kamata ace Sun fahimci hakan tun farko dan gatan yayi yawa ko yaranshi basu samu gatan da suka samu ba, .

Har cewa suke idan ba asiri ba me yasa ba ya kulawa da ‘yayansu Su da suka fito ciki d’aya.

Yanzu ai da tabar gidan zasu gane inma wani irin munafurcin suke kullawa asirin Su zai Tonu.

Har D’ayar tana cewa idan ‘yar riko yake nema a cikin nasu yaran zasu bashi.
haka sukayi ta maganganu marasa dad’i akan Maisa da mamanta, kamar ba yan uwan da suke bala’in son juna da nunawa juna kulawa ba.

Musamman taje ta sameshi, yana ganinta had’e girar sama data k’asa.

Magana ta fara yi mishi a sanyaye kan Indan barin Rumaisa Gidanne ya ke damunshi haka, yaje ya dau d’aya daga cikin yaran kannenshi mata, ko kuma ita ta d’auko a yaran yan uwanta.

Hayayyako mata yayi kamar zai dake ta yana cewa babu wata shegiyar da za’a kawo mishi gida, kada ma ta kuma kawo mishi wnn zancen banzan.
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

 

*Fasaha Online Writers.*

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*13*.

Wata uku curr tayi a gidan ba tare da taje ko ina ba, tun abin na damunta dan ta saba da yawo har ta hakura.

Sosai take istigfari, tana me kaskantar da kai wurin ubangiji mahaliccin sammai da kassai.

Kawu kuwa duk lokacin da ya kira ta, ta d’auka bata iya yin magana mai tsawo dashi idan tayi kokari ta gaisheshi, daganan yayi ta surutanshi shi d’aya wani lokacin ta sa mishi Kuka, daga yaji tana Kuka kuma sai ya shiga rarrashi dan kukan ta ba k’aramin tab’a mishi zuciya yake yi ba.

Mamma kuma bata daina sata a hanya duk abinda tasan ya kamata ta sani, tana iya kokarinta wajen ganin ta koya mata.
Koda mamanta tazo daga Jigawa babu wanda ya sanar da ita abinda ya faru saidai tayi mamakin ganin Rumaisa a gidan Abba babba maimakon gidan kawu.

Da ta tambayi Mamma, sai ce mata tayi, sun fahimci kawu ya sangarta Maisa da yawa shi yasa suka d’auko ta idan ba haka sukayi ba haka zata ta zama ba tare da ta iya komai ba, dan can matar kawun bata koya mata komai.

Bata kawo komai a ranta ba, ta yarda da maganar Mamma dan itama shaidace akan irin shagwab’a Rumaisa da kawu yayi, ko Yaushe tazo sai tayi ta mata fad’a akan irin zaman da sukeyi da matar kawu, ita komai sai kawu ,matar da ya dace Su shaqu ta koya mata as abubuwa na mata, sam dukansu biyu sunki, ita matar kawu Tana jin haushin Rumaisa, Itako Rumaisa Tana biyewa kawu.
Shi yasa Maman Rumaisa take ganin wnn hukunci da suka yanke daidai ne.

Lokacin da tazo komawa Jigawa babu abinda ya canza na daga alkhairan da yake mata, wnn al’adar Su ce duk wacce tazo daga wani gari cikin yan uwansu idan Zata koma, kowa a cikinsu zai mata alkhairi dadai gwargwadon iyawanshi, kawu kuwa dama ya saba kyautatawar da yakeyiwa yayarshi wato mman Rumaisa ta daban ce, haka ma wnn Karon har yafi na kullum, har ta koma basu bari ta fahimci akwai wata matsala ba .

Gidan kawu yanzu ya gama watsewa dan duk yaran yan uwanshi samari da suke zama a gidan da masu zuwa su kwana biyu su tafi duk ya koresu daga gidan, yace a cikin su lallai baza’a rasa wanda ya lalata rayuwar Maisa ba, zargi harda d’an cikinshi akan Rumaisa.
Saida Maman matarshi tace za’a jisu a kotu idan ya kuma d’aurawa jikanta sharri, tukuna ya bar maganar .

Bayan komawar Dadda( Mmn Rumaisa) da wata guda, Baban Kabeer ya kirashi.
Saida ya mishi nasiha mai shiga jiki ya gama d’aure shi da jijiyoyin jikinshi snn ya sanar da shi kudurinshi nason had’a shi aure da Rumaisa, dan shi tsakani da Allah tausayi suke bashi daga Rumaisar har Kabeer, sbd ya tabbatar akwai k’auna mai ka’rfi tsakanin su, saidai shi yanzu Kabeer d’in abinda ya faru yasa ya fita harkarta, amma fa duk wanda yasan shi idan ya kalleshi da kyau yasan yana cikin damuwa duk da kokarin b’oyewar
da yakeyi.
Ta b’angaren Rumaisa ma ya fahimci abin haka yake dan ko Yaushe yaje gidan Abba babba sai ta tambayeshi labarin Bobbonta, hakan yasashi yin wnn shawara har ya sanar da mai Mahaifiyar Kabeer d’in, Tare da nuna mata amfanin yin hakan, da yake ita mai fahimta ce, kuma bata da Matsala yasa ta amince ba tare da nuna wata damuwa ba.

K’arfin hali Kabeer yayi ya nuna wa mahaifinshi ya amince.
Albarka yayi ta sa mishi kafin ya sallameshi.

Fita yayi ya koma d’akinshi yanaji zuciyarshi Tana mishi zafi, gaba d’aya fitar ma ta fice mishi a Kai.

Wani irin ciwo yake ji zuciyarshi nayi, bugawa takeyi kamar zata fito ,wani abu yaji ya tokare mishi mak’oshi, har wani d’aci d’aci yakeji.

Ba wai bayason Maisa bane, a’a, takaici da bak’in cikin abinda ya faru ne ya gagara barin zuciyarshi, ko a yanzu akace Maisa Zata auri wani bashi ba, yasan dole ya shiga damuwa, amma yanzu da aka ce shi zai aureta sai yaje jin ya shiga tashin hankali.

Ko da ya samu mahaifiyar shi da maganar, hakuri da ban baki ya samu daga gareta, k’arshe ta bishi da nasiha wanda ya sanyaya mishi jiki da zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button