HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Ba tare da b’ata lokaci ba suka je Jigawa wajen dangin mahaifin Rumaisa.
Sun samu tarba na karamci da mutunci.

Cikin mutunta juna suka gama komai na neman aure, basu ja lokaci mai tsawo ba suka sa watanni biyu masu zuwa.

Kayan lefe ma saidai Kabeer yaji labari ankai .

Sai da aka kai lefe, Mamma ta kirashi, akan tana da magana dashi.
Sam baiso haka ba amma babu yadda iya, dan yana mutuntata ba kad’an ba, ganin mahaifiya yake mata.

Ada ko wani bayan Kwana biyu yake zuwa gaisheta, amma tunda Rumaisa ta koma gidan ya daina zuwa, ko ya kama hanyar zuwa yana karya Kwana da Zata Sada shi da gidan ya ke jin matsanancin fad’uwar gaba, wadda yake tilasta mishi komawa babu shiri.

Daurewa yayi ya je gidan domin amsa Kiran Mamma.
Bayan ya gaisheta cikin girmamawa ta amsa cikin kulawa, shiru ya d’an biyo baya.

Nisawa tayi tace, “Kabeer. ”

“Na’am Mamma. ”
Yace ba tare da ya d’ago ba, dan jikinshi na bashi ko ya Akayi wnn kira yana da alak’a da Rumaisa………
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

 

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie “Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

Wannan shafi nakine dan jin dad’in ki *Saudat Muhammad.* Fasaha online writers grp.

*14*.

“Da farko abinda Zan ce maka shine, Kayi hakuri, ka k’ara akan wanda kake dashi.
Ko ba’a fad’a min ba nasan baka ji dad’in hukuncin da iyayenka suka yanke akanka na auren Maisa ba.
Ka sawa ranka cewa haka Allah ya kaddara maka, idan ka yarda da kaddara sai Kayi hakuri kayiwa iyayenka biyayya sai Kaga abin ya zamo maka alkhairi.
Kai mai ilimi ne, ko ban tsaya fad’a maka ba kasan cewa mai cikakken imani shi ke yarda da kaddara, Walau mai kyau ko akasin haka.fatana dai shine Allah ya baka ikon cika burin iyayenka na ganin Rumaisa ta samu farin ciki da rufin asiri, wanda kuma ta wajen ka suke fatan hakan. ”

“Bayan haka, sai kayi hakuri da halayen Rumaisa dan har yanzu yarinya ce. ”

A ranshi yace “Yarinya indeed. ”

Haka dai tayi ta bashi shawarwari da kwad’aita mishi falalar biyayyar da zai wa iyayenshi, har yaji zuciyarshi tayi sanyi.

Har ya tashi zai tafi, ta tambayeshi, bazaiga Rumaisar bane?
Sosa kanshi yayi cikin jin kunya ya ke tambayar ina take.

D’akin ta ta nuna mishi.
Tana cikin d’akinta taci Kwalliyar ta da dressing nata na fama. Body hug da trouser.
Taje sumarta take yi ta rabashi gida biyu, ta gama taje b’ari d’aya tanayin d’ayan b’arin taji muryar da baza ta tab’a mancewa ba a rayuwarta, muryar da ko cikin bacci taji zata gane maishi ,muryar da take kewa,da muradin jinsu a dodon kunnuwanta, muryar da take jin yafi ko wane murya dad’i. Yana Sallama kamar baison yi .

Wuff ta mike ta tsaya tana raba ido, kirjinta sai bugawa takeyi, tana fatar Allah yasa da gaske Bobbonta ne yazo gareta ba mafarki take ba.

Sallama yayi a karo na uku, snn ta amsa muryar ta yana shaking.
Wani abu yaji yana masa yawo a jiki, ba shakka yasan yayi missing wnn golden voice d’in.

“In shigo? ”

Yace a dakile. Ba tare da ya san lokacin da maganar ta fito daga bakinshi ba.

“Bismillah tace tana jawo gyale domin rufe jikinta.

A hankali ya d’aga labule ya kutsa kanshi cikin d’akin.
Wani sassanyar kamshi ne ya Marabci hancinshi har yasashi lumshe idanunshi.

Bud’esu yayi ya sauk’e su kan fiskar ta, da ta Kara mishi kyau.
Kallon juna suka tsaya yi ,ji suke kamar sun d’ebi shekaru basu ga juna ba.
Shiru d’akin yayi kamar babu mai rai a ciki, sun jima Suna kallon juna kafin daga bisani ta katse shirun da cewa.

“Sannu da zuwa Bobbo. ”

Sai a snn hankalinshi ya dawo jikinshi.
Saurin kawar dakai yayi ba tare da ya amsa mata Sannun da ta mishi ba.

Sallaya ta d’auka ta shimfida mishi tare da mishi Bismillah. Kallonta ya kumayi ya Kalli sallayar snn ya Tab’e baki, a ranshi kuma cewa ya ke, ” dube ta kamar wata mutuniyar kirki. ”

K’asa tayi da Kanta ganin yadda lokaci guda ya canza fiska, yana wani yatsina kamar yaga abin kyama.

“Waya ce miki zama nazoyi cikin wnn kazamin d’akin naki,
Idan zuciyarki tana raya miki cewa son ganinki ne ya shigo dani nan gara ta dena, dan banga abin gani Anan ba.
Da yake kuma kin cika cikakkiyar ‘yar iska shine kikasa wad’annan kaya a cikin gidan mutane, ko wani d’an iska ma ya ganki a haka ko.
Kuma dan rashin sanin ciwon kai shine da nace in shigo kika wani ce Bismillah kamar dama jira a shigon kikeyi, haka kenan kike barin ko wani Gardi yana shigo miki d’aki kina sanye da irin wad’annan sutura ko kunya babu sbd rashin kamun Kai.
Kai nidai Su Abba sun gama dani da suka rasa wacce zasu aura min duk yawan matan garinnan saike Maisa. ”
Ya k’arasa maganar yana nunata da yatsa tare da yi mata kallon kaskanci.

Durkushewa tayi a gun ta fashe da kukan bak’in ciki ,ji take kamar ta hadiyi rai ta mutu akan irin munanan kalaman da Bobbonta yake jifanta dasu.

Cikin sauri ya fice daga d’akin, dan bazai juri jin kukan ba. Har yana tuntub’e .

Sai da taci kukanta ta koshi snn ta mik’e taje ta wanko fiskarta tare da d’auro Alwala, dan nemawa kanta sassauci a gurin Allah Ta’ala.

A hanyarsa ta komawa gida yake zancen zuci,”Allah ne ya taimakeni da ba’a ce za’a bawa wani ke ba Maisa da bansan yadda rayuwata Zata kasance ba.
Sajenshi ya shafa yace “I really love you Baby Maisa. ”

Sai can kuma yaja tsaki, shi Sam ya rasa yadda zaiyi da wnn b’acin rai da yake zuwa mishi duk lokacin da ya tuno ta,” Allah ka kawo min sauk’i. ”

Ya ce a fili.

Tun daga ranar basu kuma had’uwa ba sai lokacin bikin su.
Sun yi kokarin ganin Sun b’oye duk wata damuwa da suke ciki a gaban Jama’a, sbd da haka har akayi bikin aka gama babu wanda ya fiskanci akwai wata matsala.

Lafiya akayi biki aka gama, aka kai amarya gidan angon ta dake anguwar Millennium suite….

Har kawaye suka watse ba’a ga idon ango ba sai abokanshi, haka suka bar amarya ita kad’ai cikin katon gidanta.
Tsoro duk ya isheta,tun tana Kuka har idanun suka bushe daga baya bacci yayi awon gaba da ita.

Tun da tazo gidan yau Kwana biyu bata sashi a ido ba, bata da masaniya akan gidan take Kwana ko kuwa, ita dai sunanta matar gida, kuma amarya.

 

*Toh ko wani irin zamane Bobbo Kabeer zasuyi da Amarya Baby Maisa.*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

 

*Wannan shafin nakune masoyan Zumuntar zamani duk inda kuke, na gode da k’aunarku gareni.*
*15*.

A ranar da ta cika Kwana uku da safe tana kwance kan sallaya dan tun da ta idar da sallar Asubah bata tashi ba.

Sai ji tayi an turo k’ofa.
A razane ta tashi tana kallonshi dan jin da wanne ya shigo dan itakam yanzu halayenshi tsoro suke bata kamar ba Bobbonta da ta sani mai sonta da k’aunarta ba.

Murmushi ya sakar mata, wanda ya saukar mata da kasala.
kasa maida mishi martani tayi dan tasan yanzu ya dizga ta ba damuwarshi bane.

“Baby Maisa Amaryar Bobbonta. ”
Taji yace still bai bar murmushin ba. Ita dai nata ido, tana jira taga k’arshen rainin hankalinshi.

“Well, kina ta murna kin zama matar Bobbo ko? ”
Ya fad’a yana d’age girarshi d’aya.

Sai kuma ya girgiza kai yace “Saidai ni kuma akasin hakanne dan ina cikin bakin cikin had’a mu da akayi, hakan ya sani zazzafar zazzabi, duk sbd aurenki da nayi.

Kin cuce ni Maisa, kin kuma cuci kanki.
A da ,bani da wacce nake k’auna da so da kuma burin ta zamo uwar ‘ya’yana kamarki Rumaisa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button