HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Amma yanzu” Saida ya tab’e baki yana girgiza kanshi snn yace “bani da wacce na tsana nakejin kamar na shake na kashe ko Zan huta da bak’in ciki sai ke. ”

Zaro ido tayi tana kallonshi hawaye har sun fara wanke mata fiska, a ranta take cewa “abin har yakai ga kisa? Lallai yanzu ba k’aramin kiyayya Bobbo yake min ba.”

Cikin Kuka tace “Bobbo dan Allah ka gafarceni, idan bazaka iya zama dani ba, kada mu bawa kanmu wahala, ni daga nanma ko gida bazan koma ba, balle ayi tunanin sake dawo maka dani, Zan yi nesa dakai ta yadda bazaka kuma ganina ba balle ranka ya rika baci.”
Ta k’arashe maganar cikin matsanancin Kuka.

“Really, zaki iya nesa dani Ashe. ”
Ya tambaya yana kallonta.

Gyad’a kai ta shigayi kamar kadangaruwa. “Zan iya Indai hakan zai kawo maka kwanciyar hankali. ”

Jikinshi ne yayi sanyi, a zuciyarshi yake Tunani, yanzu Maisa Zata iya yin nisa dashi kamar yadda tace, idan Zata iya shikam bazai iya ba, gwara suyi ta zama a hakan.

Kallonta yayi yaga har yanzu kukan take amma k’asa k’asa.
Zama yazo yayi tare da hard’e k’afa yana fuskantarta, ji yake kamar ya yi hugging d’inta ya rarrasheta amma wancan muguwar zuciyar tashi tana hana shi aikata hakan.

Basarwa yayi da cewa “Well, niba dogon surutu nazo muyi dake ba, na zo ne dan na gindaya miki sharrud’an zama a gidana. ”

Na farko, kinsan bana son kazanta, ko kad’an kika kuskura naga datti a gidannan ranki zai b’aci .
Dan naji labarin, babu abinda kika iya na aikin gida sai shashanci, har wani cemin ake min ke yarinya ce tsabar ke shagwababbiya ce.

Na biyu ban yarda da yawan fita ba kuma bazan lamunci a shigo min da k’ato gidana ba.

Idan zaki dafa abinci ki dafa dadai cikinki banda ni, dan bazan ci jagwalgwalo ba.

Idan kina bukatar wani abu, zaki iya tambaya, ko Meye shi.

Lastly wnn ‘yan iskan sutura da kike sakawa, bana son ganinki dasu dan nan ba gidan ‘yan iska bane.

Idan kunne yaji……..

Yana gama fad’ar haka ya tashi yayi ficewarshi ya barta da tunani.

Duk abinda ya lissafa tasan Zata jure ta yi, amma banda sutura, dan takurar zaiyi yawa.
ita kad’ai cikin gida ace ta takura kanta tayi ta saka manyan kaya, wnn ne kawai za’a samu matsala.

Haka zamansu ya kasance kullum da kalar bak’ar maganar da yake yab’a mata.
Ayyukan gida kuwa tun tana yi jikinta na mata ciwo har wahala yabi jikinta, ga gida ba k’arami ba. Kuma babu mai taimako.

A haka yan uwansu suke zuwa su sameta kullum cikin aiki ba hutu, har wasu suka fara magana akan hakan.

A cikin hakanne kawu khamis yaji labari yayi tattaki yazo har gidan Kabeer dan ya ganewa idanun sa abun da yake faruwa.

Da fatan baku manta abinda zuwan kawu ya jawowa Rumaisa ba.

*Mu koma labari.*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*16*.

Tana fitowa daga toilet, ta had’a Zufa tayi sharkaf, tana gaisawa da mutane be amma Sam hankalinta baya jikinta.

Ba abinda yafi d’aga mata hankali sai da taji Mamma tana cewa,” Maisa kam bata San Amminta tazo bane?”

Da sauri ta fara dube dube tana neman ta inda Ammin tata take.

Kakaro fara’ar dole tayi, tana nuna farin cikin ganin Ammin.

Sai lokacin ta gane taruwar ‘yan uwansu a gidan bazai rasa nasaba da zuwan Ammin ba . Relief ta d’an fara ji yana shiganta.

Bata ida tunaninta ba, Faisal autan Abba babba ya zo yace mata ana Kiran ta a falon Abba babba.

Cikin sanyin jiki ta tashi taje. tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ganin haka ne yasa Mamma ta tashi ta bita a baya.

Saida aka bata izini snn ta shiga falon.

Kawunanta ne da pendonayenta dankam a cikin falon.

Wani sauti cikinta ya bada, kamar ta zura a guje take ji.
Ta waiga ta Kalli bayanta taga Mamma na biye da ita, hakan ya d’an bata kwarin gwiwar isa gurin da suke zaune.

Gaishesu tayi d’aya bayan d’aya, snn tayi k’asa da kanta.

Kurr kawu ya kure ta da ido yana mai jin takaicin yadda ya ganta kamar bata cikin hayyacinta.

Iyakacin Su iyayen ne kawai babu Yara a cikinsu sai Kabeer da Rumaisa.

Da Addu’a aka fara snn Abba babba ya fara magana kamar haka:.

“Kabeer, Babanka Hamisu ya kawo mana karar ka, akan kana wulakanta Rumasa’u.
Duk da dai bamu san laifin da ta yi maka ba, amma abin bai mana dad’i ba, shi yasa muka kira taron gaggawa, sbd musan wani irin zama kukeyi,gani ga sauran iyayenka.”

Babu abinda Baban Kabeer yakeyi sai zabgawa Kabeer harara, Shiko Kabeer ya Duk’ar da kanshi, tun ganin farko bai kuma yarda sun had’a ido da Babbanashi ba.

“Bismillah, muna sauraronka. ”
Cewar Abba babba.

Kanshi a kasa yace “Babu abinda tayi min. ”

A kufule Babanshi yace “Tsabar cin zali ne kawai kake zalintarta? Ko kuma…..

Dakatar da shi Abba babba yayi ta hanyar d’aga mishi hanu. Ya sake maida dubanshi ga Kabeer.

“Ina jinka, babu abinda take maka auran ne baka so, ko itace bakaso?”

Girgiza kanshi kawai yayi ba tare da ya yi magana ba.

“Idan baya sonta ,ai ba dole ba sai ya sawwake mata ba.”
Cewar kawu Yana huci, ji yake kamar ya makure Kabeer ko zai samu sassaucin abinda yake ji.

Shima Kabeer cikin jin haushin Baffan nasa ya ce “Ba Zan rabu da Maisa ba, sai dai….. ”

K’asa ya sake yi dakai yana jin nauyin maganar da yake so yafad’a.

“Sai dai me? “Abba babba ya tambaya.

“Abba, ku gafarceni, amma inason aja wa Baffa kunne kada ya kuma zuwa gida na, Wlh banaso na sake ganinshi kusa da Maisa……

Maman Maisa da hankalinta ya gaza Kwanciya da wnn meeting da akeyi ba a gayyaceta ba, ga kuma sauran yan uwanta a ciki, ga gudan jininta.
Sulalewa tayi ta nufi falon, tana isa K’ofar taji Abba babba na cewa.
“Bamu fahimceka ba Kabeer, mu iyayenka ne bakaso muje gidanka ko yaya?

Kad’a kanshi yayi ba tare da ya d’ago ba yace “Baffa khamis ne bana so yaje gidana, sbd yana so ya kashemin aure. ”

Hayayyako mishi kawu yayi “Kaji d’an iskan yaro, ni d’in ne zan kashe maka auren, bayan wulakanta matarka da kikeyi, ka kiyayeni Kabeer, Zan b’alla ka in b’alla banza wallahi. ”

Gaba d’aya jikin baban Kabeer ya gama mutuwa ,zuciyar shi ta fara halarto mishi da wani bahagon Tunani.

Suko matan har sun fara zagin Kabeer, a ganin Su raini ne irin na d’an yau, idan ba haka ba mutumin da Maisa ta girma a hanunsa, ya zamo kamar mahaifinsa, ya nuna mata dukkan gatan,yace bayaso yaje inda take.

Abba babba ne ya dakatar dasu daga surutan da sukeyi har sun fara d’aga murya.dan shi ma ya fiskanci kamar akwai matsala mai girma dan shi a iya saninshi bai San Kabeer da rashin Kunya ba balle kuma ga iyayensa.

A nitse yace “Kabeer, kada ka kuskura ka mana wasa da zumuncin mu, ba’a tab’a irin haka a wnn family ba kuma a kanka baza’a Fara ba, so nake a yanzu ka fad’a min dalilinka na muzgunawa yarinyar nan da kuma dalilin cewa kada Baffanka ya kuma zuwa gidanka. ” ya k’arasa maganar a zafafe.

“Abba, duk dalilan Maisa ta sansu ,zata kuma yi bayani da bakinta. ”

A harzuke kawu ya Mike “Kaga, bamu son iskanci, kai aka tambaya ba Maisa ba sbda haka Kai muke jira ka bada amsa d’an iskan yaro mara mutunci, wanda bai San girman na gaba dashi ba. ”

Tafasa zuciyar Kabeer yakeyi sbd jin irin tijarar da kawu yake mishi, ita ko Maisa cewa take a ranta inama da Zata iya b’acewa daga gurin da tabbas za’a neme ta a rasa.

Bata ida tunaninta ba taji Kabeer yana cewa “Maisa, a yau, a wnn guri, a yanzu a gaban kowa nake so ki fad’i wa ya miki ciki………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button