HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

 

*Turkashi.????????*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

 

♣♣♣

*Dedicated to my other half.
*Nafeesat Abdussalam (Mrs Bashir Bello.)*

*17*.

Wani irin tsinkewar zuciya da fad’uwar gaba Mmn Rumaisa ta tsinci kanta ciki, kamar yadda ya kasance Maisa.

Sauran wad’anda basu san da labarin cikin bama maganar tazo musu a bazata, ciki, a cikin familynsu, babbar magana.

Tunani Maisa ta shiga yi lokacin da tayi accident tana kwance a hospital bed .

Shigowa Kabeer yayi fiskarshi a murtuke kamar bai tab’a dariya ba, sosae yanayin fiskar shi ya tsorata ta dan bata tab’a ganin shi cikin wnn yanayi ba.

Idan ba idontane ya gane mata ba daidai ba kamar ma Kuka yayi dan idonshi yayi ja sosae.

“Tashi ki zauna. “Yace da ita.
Ba musu ta mik’e ta zauna.

“Zan tambayeki, wallahi idan kikayi min karya ,kinga wnn?”
Ya fito da wani ruwan magani yana nuna mata.
“Kasheki xanyi dashi kuma in kashe kaina , kina jina?”

Kai ta gyad’a tana kallonshi a tsorace.
“Ya akayi kika samu ciki, ubanwa ya miki shi?”

“Ciki? ”
Ta fad’a gami da zaro ido.

“Kada ki ce min baki sani ba, nasan kin san dashi.”

Wani irin juyawa taji d’akin yake mata, take taji jiri na d’ibanta daga zaune.
ita da mutuwar ma tayi a yanzu zai fiye mata akan wnn ritsata da Bobbonta yayi, kuma abun takaice babu wanda ya gano cikin sai shi.
Amma zancen ya kasheta da hanunshi kam bata taso ba.

Katse mata tunanin taji Kabeer yayi da cewa “Ba zaki fad’a ba kenan? ”
Binsu Abba babba tayi da Kallo ta maida kallonta kan Kabeer ya galla mata muguwar hararar da yasata Duk’ar da Kai ba tare da ta shirya ba.

Tunowa tayi da alk’awarin da ta d’aukar mishi, lokacin da ta sanar da shi uban cikin.
Da ta nemi yi mishi k’arin bayani yayi saurin dakatar da ita da cewa “Ba nason jin komai daga gareki a yanzu, alk’awari d’aya nakeso ki d’aukar min. ”

Cikin sauri ta d’aga Kai.
“Duk lokacin da na bukaci ki bayyana wanda ya miki ciki, zaki fad’a ko da a gaban wayene. ”
“gyad’a mishi kai tayi.

“Da baki zaki yi min magana ba da kai ba munafuka, kinyi alk’awarin? ”

Da sauri ta ce “Nayi. ”

“Rumasa’u. ”

Abba babba ya dawo da ita daga kogin tunanin da ta afka.

“Kinyi shiru, ke muke saurare?”

“Kawu ne. ”

Tace bayan ta sunkuyar da kanta jikinta kuma sai b’ari yakeyi.

Difff gurin yayi, kowa ya zuba mata ido kamar Suna jiran k’arin bayani.

“Wani kawun? ”

“Kawu khamis. ”
Tace cikin rawar murya.

Salati kowa ya d’auka banda kawu da ya kafe Kabeer da ido kamar ya cinyeshi d’anye .

Cikin kid’ima Baban Kabeer yace “Garin ya haka ta faru, me yasa baki sanar mana ba tun da farko. ”

A sanyaye tace “Cewa yayi zai kashe Bobbo idan na fitar da maganar. ”
Salati aka kuma d’auka, masu inna lillahi, suna yi, masu, Hasbunallahu ,suna yi, masu Subhanallah Suna fad’a duk dai addu’ar da ta fito daga bakinsu yi sukeyi, dan ba shock suka ji ba.

Kabeer kallon Rumaisa ya shigayi da mamaki, wai dan shi ta bari aka lalata mata rayuwa.

Bai Ankara ba yaji an mishi mummunar shaqa.
Kawu ne ya shaqeshi yana surfa mishi zagi “Shege tsinanne, nasan wnn duk munafurcin ka ne, kai ka shirya wnn munafurcin. ”

Cikin azama da b’acin rai Abba babba ya d’auke shi da wata lafiyayyar Mari, ni da nake labe saida na dafe kumatuna.

“Sakar min wuyan d’a khamis tun ban baka mamaki ba,
Kaiconka khamis Kayi asara, ‘yar cikinka?ka b’ata mana sunan Zuri’a.”
Shi yasa yarinyar nan tayi Yunkurin guduwa har sau biyu, da yake Kai munafuki ne, Ka taramu ka mana k’aryar cewa wani ne yake hure mata kunne, ko tsoron Allah babu, kasa muka takurata muka sata zama a gidan ka ka cuci yarinya a banza, ka zalince ta. ”

Ya k’arashe maganarshi da kukan bak’in ciki.

“Ba shakka biri yayi kama da mutum. ”
Abinda Baban Kabeer yake ta maimaitawa kenan yana karkad’a k’afa.

Kowa a wajen jikinsa yayi sanyi zuciyar su baki Kirin.

Niko nace, yo dama me kuke tsammani, wnn irin Mulki da Maisa take zubawa a gidan kawu na banza ne?
Ina Kuka tab’a ganin namiji kad’ai yayi tarbiyar ‘ya mace ba tare da mace ‘yar uwarta ba.
Wnn shak’uwa tasu ta banza ce,?
Wa yafi qarfin sharrin shaid’an ,sai wadda Allah ya tsare.
Allah kasa mu fi qarfin zuqatanmu.

Da k’arfi Kabeer ya fincike daga rikon da kawu ya mishi da su biyu ne kawai a gurin shima babu abinda zai hana ya shakeshi har sai yaji Kamshin lahira.

Fad’uwar da suka ji daga k’ofar falon ne yasa su duka maida hankalinsu wajen.
Maman Rumaisa ce ta yanke jiki ta fad’i tsabar yadda maganar ta kad’a ta.

Kusan a tare duka sukayo kanta,
Maisa dake rusa Kuka tun d’azu, ta sake k’ara k’arfin kukan ta tana kiran Amminta.

Kabeer ne yasa hanu ya……
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W..

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*18*.

Ciccib’eta ya fita da ita, sauran suka rufa mishi baya.
Da mamaki mutanen cikin gidan suke binsu da Kallo, har suka fice.
Adda binta tayi saurin binsu tana tambaya, ina duk hankulansu sunyi nisa, babu wanda ya kula ta cikinsu, da gudu ta juyo Zata shiga gida sukayi karo da Maisa.

Rik’e Maisa tayi tana tambayar abunda ya faru, Maisa ba magana sai kuka.

“ya salam .”tace snn ta kuma cewa “Maisa me ya sami goggo? Kabeer ya sakeki ko?”

Dan ita a tunaninta Kabeer ya saki Maisa ne yasa mmnta shiga wnn hali.
A ranta take cewa “Ba dole ba kwata kwata ma auren wata nawa ne har an rabu, dole goggo ta shiga damuwa. ”

Fad’awa jikinta Maisa tayi tana mai ci gaba da kukanta.
A sanyaye tace “Kiyi hakuri Maisa, Allah yasa hakan alkhairi ne, Allah ya ba goggo lafiya. Amma Kabeer bashi da mutunci Wlh. ”

Da sauri ta shiga girgiza kai “Ba laifinshi bane Adda, laifi na ne. ”

“Ke dalla tafi can wani irin laifinki, duk zaman hakurin da kikayi dashi ya rasa sakayyar da zai miki sai ta saki. ”

“Adda, Bobbo bai Sakeni bafa.”
Ta fad’a cikin Kuka.
“Ha’a, to me ya farune wai fad’a min man Maisa. ”

“Ammi na, zanje na ga halin da take ciki. ”

“Yanzu ina kikasan suka nufa da ita. ”

“Adda, bazai wuci asibitin su Bobbo bane.”

“Jirani mu tafi tare. ”

Ko da suka isa basu sha wahalar nema ba dan kusan rabin familyn duk suna wajen har da wad’anda basu je gidan Abba babba bama sun ji labarin ciwon Dadda.

Kowa ka gani hankalinshi tashe sai jajanta zancen ake tayi, wad’anda basu san abunda ya faru ba sai Tambaya sukeyi.

Sun d’auki lokaci mai tsawo kafin aka samu ta farfad’o dan mata kam har sun fara Kuka, mazan ne, suke ta kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu tana raye da yardar ubangiji kuma zata samu lafiya.

Tare suka fito shi da wani doctor dukansu share gumi sukeyi, mutanen gurin kaff suka zuba musu ido Suna jiran su karaso Su musu bayanin halin da take ciki.

************
Gida kawu ya koma, cikin tashin hankalin da bazai misaltu ba, sosae yake jin haushin Kabeer dan shine silar tonuwar asirinshi, snn a tuñaninshi Kabeer shi ya jawowa ‘yar uwarshi ciwo.

So yake ya bisu asibitin amma Yana tsoron abinda bin nasu zai jawo.
Dan yasan yanzu kowa yasan abunda ya aikata, kuma sun gaskata hakan tunda daga bakin uwar gayyar maganar ta fito, kenan ba damar musu.

A b’angare d’aya na zuciyarshi kuma har yau har yanzunnan yana jin bak’in cikin raba shi da Maisa da akayi, sbd har yanzu shaid’an bai bar kawata mishi Maisa ba, har yau k’aunarta da sha’awarta Suna nan manne cikin zuciyarshi shi yasa ka bai ji zafin tona mishi asiri da tayi ba, duk laifin Kabeer ya daurawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button