HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

A zuciyarshi ji yake inama da aure tsakaninsu da Maisa da babu abinda zai hana shi aurenta.

????wnn irin bala’in da me yayi kama.
Allah ka tsare mu da sharrin shaid’an kasa Mufi qarfin zuqatanmu.

Gaza hakura yayi ya d’au wayarsa ya fara dialing numbers d’insu d’aya bayan d’aya, abin da takaici babu wadda ya d’auka a cikinsu.
Dan Suna can hankali a tashe duk wanda yaji wayarshi tayi ringing idan yaga shine sai yaja tsaki yayi ignoring. Sbd dukansu zafinshi suke ji.

Haka yayi tayi har ya gaji gashi hankalinshi ya gaza Kwanciya, so yake yaji halin da take ciki.

“Hindu. “Ya kwala wa matarshi kira da karfi kamar muryarshi zai tsage.
A guje ta Iso tana amsawa da jin yadda muryarshi take babu alamar Rahama a cikinta, duk a tsorace take, tana tunanin yau kuma da wanne ya shigo.
Gashi dama tasan tayi mishi laifi dan yace taje ta Marabci Daddanshi, har ta amsa zata je, yana fita ta kama harkokinta tana mitar, tunda ya hanata zuwa wajen danginta ita ma babu gurin d’an uwanshi da Zata kuma zuwa har sai ya gaji ya barta ta fara zuwa wajen nata.

Fiska a had’e shi nan baya so ta raina shi.
“Shirya kije ki duba min Dadda a specialist hospital, idan kin isa kuma immediately ki kirani ki gaya min halin da take ciki. ”

“Dadda bata da lafiya ne?”
Ta tambaya tana nuna alamun tausayawa.

A masifance yace “Ban sani ba Hindu, kin tab’a ganin inda lafiya yakai mutum asibiti, malama idan zaki je ki tafi kawai idan baza kije ba kuma ki sanar da ni. ”

Har itama zata mayar mishi da martani akan baza taje ba d’in sai kuma wani tunani ya fad’o mata ta fara tambayar kanta.
“Me yasa shi bazai je ya dubo ta da kanshi ba?

Cikin sauri ta tashi tana cewa a ranta koma menene idan naje Zan ji.

Har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo da baya.
“wani ward take?”

“kar ki dameni Hindu ban sani ba. ”

Tab’e baki tayi ta tafi ta kama shiri sauri sauri ta gama tazo ta tsaya a kofar falon shi, kallonta yayi zaiyi magana ta rigarshi da cewa “Transport. ”
‘yar karamar tsaki yayi kafin ya zura hanu a aljihu ya ciro dari biyar ya jefa mata.

Isa tayi ta d’auka a ranta take cewa “Masifaffe kawai. ”
Ta fice.

***********

Gurin mazan d’ayan doctor ya nufa Shiko Kabeer ya k’arasa wajen matan, dukansu suka yo ca akanshi Suna tambayar ya take dadai Isowar matar kawu wajen.

“Alhamdulillah da sauki, sai dai BPn tane ya hau sosae yanzu bacci take, insha Allah Zata samu lafiya. ”

Ya fad’a fiskarshi ba walwala snn kuma yana binsu da Kallo d’aya bayan d’aya.

Akan Adda binta ya Tsaida idon shi, da idon yake tambayarta Maisa.
Ganin bata fahimceshi ba ya mata da hanu.

Waige waige ta fara yi alamar neman Maisar da mamaki d’auke a fiskarta dan ita duk tunaninta Suna tare da ita.

Gefe ya koma ta bishi a baya.
“Kabeer tare fa muka zo da ita, d’azu dazunnan ma na gama bata baki dan Kuka take tayi tunda muka zo. To ina ta shiga,?ko ta koma gida ne? ”

Duk ta jera tambayoyin a kid’ime.

Shiru yayi kamar yana tuna wani abu sai yace mata “ina zuwa bari inje masallaci. ”
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

 

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

This page is yours .
*Jamila U.Nyaja.(Mmn Al-Mustafa.)*
Allah ya bar zumunci.

*19*.

Sosae yayiwa goggonshi addu’ar samun lafiya, bayan yayi sallah, snn ya k’ara da neman zaman lafiya tsakaninshi da Maisa da kuma addu’ar Allah ya sanyaya mishi zafin da yakeji game da ita.

Kamo hanya yayi dan dawowa cikin asibitin yana mai fatan Allah ya sa ya samu Maisa agun Su Adda binta.

Idonshi ne ya sauk’a a kanta tana zaune a kasan wata bishiya ta gefen masallacin, kanta a kasa ta k’urawa k’asa ido ko kiftawa bata yi.

A tsanake ya isa wajenta, har ya isa bata d’ago ba balle ta nuna tasan da mutum a gurin.
Dafata yayi ta d’ago ta kalleshi, Suna had’a ido tayi saurin Kawar da nata.

Saida ya tsorata ganin yadda idanun ta suka kumbura suka yi Ja da alamun Kuka tayi ba kad’an ba.
Ta gurin da ta maida fiskarta ya koma tasake Juyawa d’aya b’arin ,wasu Sabbin hawaye suna sake fitowa daga idanunta.

D’agota yayi ya mik’ar da ita, gaba d’aya ta saki ba ka’rfi a jikinta, dama jirine yasata zaman gurin bayan tayi sallah.

Hawayen ya shiga d’auke mata da yatsunshi, snn ya kamo hanun yana kallon cikin idonta.
“Kinyi sallah? ”
Tambayar da yayi mata kenan.

Kai kawai ta gyad’a mishi. Ba tare da Shima ya sake magana ba ya fara tafiya still yana rike da hanunta, hakan yasa ta kama binshi kamar rakumi da akala.

Har suka isa wajen babu wanda ya kuma cewa uffan a cikinsu, ba tare da ya Kalli kowa ba ya jata suka wuce inda aka kwantar da Mmn Maisa.
Binsu da Kallo mutanen wajen dukkansu a sanyaye suke sun zama abin tausayi.

Har bakin gadon ya isar da ita snn ya saki hanunta ya jawo kujera kusa da ita ya mata nuni da ta zauna.

Kurr ta k’urawa mamanta ido tana tunanin duk a kanta mmnta ta shiga wnn hali.
Tana kallon mamanta shi kuma yana kallonta.

Wa yaga kallon mai Kallo.

Tun tana kokarin mayar da kwallar da suke shirin zubo mata har suka yi nasarar zubowan.
Sosae take kukan bak’in ciki halin da ta shiga ta kuma jefa mahaifiyarta ciki.

Ji yake kamar ya tayata kukan dan dai shi namiji ne bai kamata ya dad’a karya mata zuciya ba.

Ba tare da yayi mata magana ba ya sake d’agota ya jata suka fita daga d’akin.

Direct gurin motarshi ya nufa da ita, saida ya bud’e mata ta shiga snn Shima ya zagaya ya shiga.

“Maisa.”Ya kira sunanta cikin dakusasshiyar murya, bata amsa ba amma ta d’an Tsagaita kukan da takeyi.
“Kalleni nan. ”
Ya kuma ce mata.

A hankali ta d’ago tana kallonshi hawayen kuma basu daina tsere kan fiskarta ba.

Handkerchief yasa yana goge mata hawayen.
“kukan kike so nima nayi ? ”

Ya tambaya still yana goge mata hawaye.
Girgiza kai tayi alamar A’a.
“To ya isa haka Kiyi hakuri ki bar kukan haka nan, da wanne kikeso muji da ciwon goggo ko kuma da wanda kikeso ki jawo mana yanzu. ”

Shiru tayi tana kallon hanunshi dake rike da hand k. D’in.

“Nasan kina jin yunwa muje kici abinci ko? ”

Girgiza kai tayi snn cikin disasshiyar murya tace “Bana jin yunwa, Zan zauna gurin Ammi na. ”

K’ara d’aure fiska yayi yace “Idan kinga kin dawo wajenta kinci kin koshi ne.”

Shiru tayi dan bata da ta cewa.
Saida ya biya ya musu take away snn suka wuce gida.
Kusan d’uren Abincin ya mata duk da shi d’in ma ba dad’in Abincin yake ji ba.
Da lallami da fad’a haka suka yi ta fama har ya samu taci ta koshi.

Tana gama ci ta mik’e “Bobbo na koshi mu koma to. ”

Girgiza kanshi yayi “Sai kinyi wanka, in fact ma sai muyi sallar maghrib zamu koma, dan naga alamar ciwo kike so ki kirawa kanki.

Babu yadda ta iya haka ta shiga d’akinta da niyyar Wankan kamar yadda yace.

************

Bayan matar kawu ta kirashi ta sanar da shi abinda Kabeer ya fad’a game da Mmn Maisa, sai ta fara tunanin yadda zatayi tambaya taji musabbabin ciwon.

Ta d’an d’auki lokaci tana jira taji ko wani zaiyi k’arin bayani yadda Zata fahimta amma shiru ,hakan yasa ta kamo hanun kanwarshi d’aya ta mata alamun zasuyi magana.

Saida suka keb’e gefe matar kawu ta tambayeta musabbabin ciwon tunda dai tasan ance tazo kuma lafiya qlau.

D’an jimm Kanwar tayi tana tunanin kamar kada ta fad’i gaskiya sai kuma ta tuna watakil matar kawun ma ta sani tunda cikin gidanta abin ya faru, ta iya yiyuwa shi yasa ta dage sai Maisa ta bar mata gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button