HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Cikin Jimami tace “Nikam Hindu da gaskene ya khamis shi ya wa Maisa ciki?”

Zaro ido matar kawu tayi kamar zasu zazzago su fad’o k’asa.

Dakyar ta iya bud’ar bakinta tace “Ke zali ina Kika jiyo wnn labari. ”

Zali da ta tsorata da yanayin matar kawu sai ta waske da cewa, “Share kawai jita jita ne irin na mutane muma ji mukayi. ”
Tana gama fad’ar haka ta fara k’okarin barin wajen.

Da sauri matar kawu ta riko”Dan Allah zo kimin bayani yadda zan fahimta, to ko shi yasa yaki zuwa duba ta ya turo ni.”

“Ba dole ya turoki ba an mishi k’azafin da yafi qarfin shi. Wai Maisa dai ‘yar da ya fifita akan ‘ya’yanshi ake mishi k’azafin shi ya lalata ta. ”
Zali ta k’arasa maganar kamar zata yi Kuka dan itama abun ya dameta, kuma tsakaninta da Allah tana tantamar cewa kawu ne ya aikata gani take abin kamar shiri ne amma ba damar ta furta tunda sauran yayyunta sun yarda da maganar.

Da dai matar kawu bata samu takamemmen abinda takeson ji ba sai ta kyaleta.

Komawa sukayi suka zauna a inda sauran ‘yan uwansu suke.

Mamma da mamar Kabeer ne suka Iso da Manya manyan kulolin abinci dan Mamma ta koma gida dan kawo Abincin data nan suka had’u da mamar Kabeer da tazo yiwa Dadda Sannu da zuwa bata samesu ba taji labarin sune asibiti Zata fita kenan Mamma kuma ta shigo.
Nan tace mata ta jirata tad’aukowa mutane abinci shine suka zo tare.

Bayan sun shiga sun duba ta, sun fito, tun kan Su koma inda sauran suke matar kawu tayi saurin zuwa ta tare su daga hanya idonta ya rufe, ba abinda takeson ji sai gaskiyar al’amari.

 

08161594233
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

Wnn shafin nakine Kakus.
*Amina Saleh Muri.*
Allah ya barmu tare.

*20*.

Tana isa ta sake Gaishesu tare da musu ya mai jiki.
“Mamma wai nikam Maisan ce da kanta ta fad’i maganar nan. ”
Ta fad’a da son bugar cikin Mamman.

Cikin takaicin abinda ya faru Mamma tace “Ita ta fad’i sai akayi yaya?”

Duk da fad’uwar gaban da taji bai hanata cewa “Abinne da mamaki Mamma, wai Maisa tace Kawunta da kanshi ya lalatata. ”

Shek’ek’e Mamma ta kalleta “Meye abun mamaki a wajen,mutum da halinsa ,ko ba akan irin hakan Kuka tab’a rikici ba har kika koma gidan ku, ba kama shi kikayi da me miki aikiba.

“In ko hakane mutumin nan ya cika cikakken munafuki, shine harda Koran yara a gida harda Amir fa yace yana zargi tsabar ya raina min hankali. ”
Cewar matar kawu cikin b’acin rai.

“Kemafa da laifinki Hindu, ta yaya za’a baki rikon ‘ya baza ki jata jiki ba, baki san matsalarta balle ki bata shawara, baki saki jiki da ita balle tayi tunanin tunkarar ki da damuwarta, baki damu kisa hankali a kanta ba balle ki fahimci wani canji a tattare da ita, ke sunan kuna gida guda ne kawai, shin Tsakaninki da Allah idan ‘yarki ce ko ‘yar uwarki zaki mata haka?”

Sosae jikin matar kawu yayi sanyi,a sanyaye tace “Tabbas nasan yana da wnn hali amma ban tab’a tsammani hakan zai iya faruwa tsakaninshi da Maisa ko don yadda yake mutunta Dadda. “inji matar kawu.

“Sharrin shaid’an dana zuciyar fa,ke kike tare da su kinfi kowa sanin kusancin dake tsakaninsu, abinda ya faru ya riga ya faru sai Allah ya kiyaye gaba, ita kuma uwar yarinya Allah ya bata lafiya da hakuri. Ke kuma sai ki dage da yiwa mijinki addu’a dan al’amarin shi kam sai addu’a, tunda ko kwanakin da kika kwanta rashin lafiya ma ‘yar aikinki na yanzu ita tace min khamis yace mata ciwonki na gulma ne, me ya kaishi wnn maganar da ‘yar aiki.
Mamma tace, ga dukkan alamu sosae take jin haushin matar kawun.

“Allah ya shirya, Mmn Kabeer tace tana jinjina abin a ranta, mamakin kokari da kuma kwarewar kawu wajen munafurci dan bazata manta lokacin da ya d’aga musu hankali akan wai Kabeer zai lalata mishi Maisa.

*************
Sai bayan sallar isha suka shiga asibitin dan saida ya kuma ritsata taci abinci snn suka fito.

Mamma da Mmn Kabeer kawai suka samu a asibitin sauran duk sun tafi.

Lokacin da suka shiga idonta a bud’e, Kabeer ya fara gaisheta, dakai ta amsa snn Maisa ma ta gaisheta.
Rintse idanunta tayi ba tare da amsawa Maisan gaisuwar da tayi mata ba.

Kukane ya taho mata hakan yasa ta toshe bakinta da hanu ta fita daga gurin a guje.
Da sauri Kabeer yabi bayanta yana kira.

Sai da yayi da gaske ya samu ya Cafkota ,Kuka ta sake fashewa da shi tana cewa “na shiga ukuna, banga amfanin rayuwata ba, tunda na zamo silar sa masoyana cikin damuwa. ”

Sosae take Kuka tana surutai har maganar ya daina fita sai sautin kukan.
Jin kukan yake yi har cikin ranshi.
Riko hanunta yayi har cikin office d’inshi .
“Maisa nace kukan ya isa haka, ko sai kema kin kwanta ciwonne?”
Ya fad’a yana zaunar da ita kan kujera.

Cogewa tayi taki ta zauna tana ci gaba da kukanta.
Hanun shi ya hard’e a kirjinshi yana kallon ta tare da tunanin abinda zai yi tabar kukan.

Sai ganinta yayi ta durkushe a wajen tana Kuka mai cin rai cikin kukan take cewa Allah ya dauki ranta ta huta.

“Subhanallah. “yace da sauri.
“Me haka Maisa, kina da hankali kuwa?kin tab’a ganin inda mutum ya mutu kwananshi basu K’are ba?
Ashe shi yasa da Baffa yace miki zai kasheni kika biye mishi Kuka tabka rashin hankali?
Mutum mai cikakken imani bai kamata wnn kalma ta Zan kashe ta bashi tsoro ba, Indai ya riga yayi imanin Allah ke rayawa da kashewa. ”

D’agowa tayi ta kalleshi “Bobbo ya zanyi,? Kai kana fushi dani Ammi na ma haka, Allah yasan yawan wad’anda suke jin haushina cikin family dan nice ta farko da ta fara b’ata mata Suna.
Ya zanyi ta k’arashe cikin Kuka kamar zata shid’e.

D’agota yayi ya rungume ta yana d’an bubbuga bayanta a hankali.
“Neman gafarar Allah shine babba dan ta namu mai sauk’i ne.
In don tani kam na yafe miki Allah ya yafe mana. Dama zafin Kishine ne yake sa nakeyi nake b’ata miki rai, ki rikemin amanar kanki, ki kaucewa duk wani abinda zai sake kawo irin Wannan matsala, wallahi ina kishinki sosae Maisa har bansan yadda zan rika controlling kaina ba, ki kiyaye dan Allah. ”

Itakam sai gyad’a kai takeyi, ko ba komai ta samu sauki tawani b’angaren, tunda Bobbonta ya yafe mata.

“Ina fatar kema zaki yafe Min musguna miki da nayi tayi. ”
Kai ta kuma gyad’a wa tana jin relief na shiganta .

“ita kuma Ammi ki bata lokaci komai zai daidaita.taji abinda bata zata ba dole abin ya buge ta. ”

Kankameshi tayi tana sauke ajiyar zuciya “Na gode Bobbo, na gode. ”
Take ta maimaitawa.

“Ya isa haka, zauna ki huta, kukan ya isa haka. ”
Ya fad’a yana sake ajiyeta kan kujera. ”

Sai pass 11 suka bar asibitin har zuwa lokacin Maisa bata samu tayi magana da mamanta ba.

************
Komawar matar kawu gida ta tarar dashi yana zaune a kofar gida kamar jiranta yakeyi.
Tana isowa yana cewa “ya jikinnata.

Wani Kallo ta Watsa mishi tayi wucewarta.
Sai a snn ya tuna wautar da yayi na tura ta asibiti, daga kallon da ta mishi ya tabbatar da taji komai.

Bin hanyar da tabi da Kallo yayi snn yayi Kwafa..

 

*Gaisuwa da fatan alkhairi gareku masoya, kabeer da Maisa sun gaisheku.*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*

 

♣♣♣

Dedicated to my sisters.
*Hajiya (Mmn Affan)*
*Ummi*
*Hameeda*
*Zahra*
*Shafa*
Allah ya barmin ku k’annena.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button