HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

 

*21*.

Zama yayi a gun na d’an lokaci kafin ya tashi ya shiga yana wani cin magani.

“Ke ana miki magana kina wani share mutane, nace ya jikin Daddan?”

Kallonshi tayi a d’age snn tace “Marar kunya dai baiji dad’in rayuwarshi ba. ”

Kamewa yayi “To to, na gane, rashin kunya dai kikeso ki min yanzu, ki kiyayi ranar da zaki shiga hanuna dai. ”

Ya fad’a yana tafiya.
Shima kanshi abun ya kashe mishi jiki, sai yanzu ya fara jin Kunyar abun, yanzu da wani ido zai Kalli Dadda.

Washegari ma tun safe yace ayi breakfast da ‘yan asibiti.
Bata kula shi ba ya gaji da tsayuwa ya tafi.
Sai can bayan yaran Sun tafi makaranta ya kuma dawowa.
“Wai nikam Hindu baza kije asibitin bane? ”
Dama Kiri’s take jira, ai kuwa ta Kankance ido ta fara Watsa bayani.
“Dakata malam, Bafa ni na saka d’irkawa ‘yar mutane ciki ba, ka jawa uwarta damuwa snn ni kazo kana damuna. ”

“Abinda zaki ce kenan? ”

“Eh, an fad’a ko karya aka maka baka yin bane? ”

“Tsiyata daku kenan ku mata daga kunji magana sai ku hau Kai ku zauna ba tare da bincike ba. ”

katse shi tayi da cewa “Ku kuma mazan idan aka barku sai ku rainawa mutane wayo ba, idan ba haka bane ka Musa mana, an daiyi abin kunya.
Maisan Kawu Maisan Kawu Ashe kawu da abu a kasa. ”

“Ki kiyaye ni Hindu, ina raga miki dan yarannane fa.”
Ya fad’a yana kifkifta ido.

“Kada ka raga min Abban Amir, Kayi duk abinda Kaga dama, babu abinda zaka b’oyemini yanzu babu kuma barazanar da zakayi tayi tasiri a kaina. Kaje mana da kanka ka dubata in dai kana da gaskiya. ”
Ta K’arasa maganar tana murgud’a mishi baki.

Fuu ya wuce kamar zai yi abin Kirki, sai naga kawu kam ya taka birki a kofar gida.

Kan dakali ya zauna ya buga tagumi yana ta shawara a ranshi ko ya shafawa idonshi toka ne yaje ya duba ta.

Sai ya Mike kamar zai tafi sai kuma ya fasa. Yadda zai had’a ido da Dadda yake tunani.gaba d’aya jikinshi ya gama yin sanyi, sai yau yake nadamar abinda ya aikata.

Da ya koma tunanin yadda yabi yaci zarafin baiwar Allah Maisa kuma gaba d’aya sai yaji ya tsani kanshi tausayinta duk ya cika shi.

Tabbas yasan ya cuce ta ba kad’an ba Ammafa duk sai a yau yasan da haka.
Bai Ankara ba yaji hayawe na d’iga daga idanunshi.

Sosae ya shiga nadamar abinda ya aikata,Tunani yakeyi yanzu idan yaranshi Sun San da maganar nan yaya zasu d’auke shi.

Niko nace daga baya kenan.

yanzu babban damuwar shi yadda zai iya had’a ido da Daddan shi wnn kuma ya zama dole tunda yana da niyyar neman gafarar ta.

Wani tunani yayi, da sauri ya tashi, gidan Abba babba ya nufa,
Ko daga tarban da ya mishi da mummunar Kallo ya ishe shi amsa.

Da kyar ma ya amsa gaisuwar shi, daga yayi ta zuba yana bada hakuri da cewa a nema mishi gafarar Dadda.

Nan ne Abba babba ya hayayyako mishi “Khamis kada ka raina min hankali mana, lokacin da kake aikata abinda ka ga dama ka nemi shawarata, tunda ka fitsare kafafunka, nasan itama Daddar taka ba kunyarta zaka ji ba, saboda haka Kayi duk abinda zaka yi kada ka had’a dani cikin al amuran ka, babu ruwana da kai. ”

Babu yadda ya iya jiki a sanyaye ya bar gurin yana tunanin mafita, baiyi tunanin zuwa wajen Baban Kabeer ba tunda ya daina mishi magana, amma ya kudurta a ranshi zai fara mishi magana yasan bazai ki amsawa ba tunda dama can shine mai bakin halin.

*************

A b’angaren Maisa kuwa duk iya kokarinshi na gani ta kwantar da hankalinta taki Sam, dan muddin Amminta bata mata magana tasan haka zata dawwama cikin bak’in ciki.

Ganin haka yasa Kabeer ya samu Mamma da maganar, itama ta lura da hakan amma tayi wa Mmn Maisa Uzuri dan tasan dole taji ba dad’i akan abinda ya faru. Saidai tace mishi zatayi mata maganar.

ita kuwa Mmn Rumaisa duk lokacin da taganta abinne yake zame mata Sabo sai taji kamar a lokacin take jin mummunar maganar .

Shi yasa take rufe idanunta idan ta ganta, amma a can kasan zuciyarta tausayin Maisar take ji, dan tasan tabbas an cuce ta, ga dukkan alamu kuma bata samu kwanciyar hankali a gidan aurenta ba.

A tausashe Mamma ta mata magana tana nuna mata illar fushinta ga Rumaisar.

Sai da tayi da gaske snn Ammi ta fara kula Maisa saidai ko Yaushe ta tuna tana jawa kawu Allah ya isa.

Bata tab’a tsammanin yadda suka riki zumuncin su akwai wanda zai iya cutar wani cikinsu ba, sai gashi kawu ya wa ‘yarta tabon da bazai tab’a gogewa ba.

Kabeer yana iya bakin kokarinshi ganin ya kyautatawa Rumaisa wadda hatta Mmn Rumaisa saida ta fahimci hakan, shi yasa tad’an samu kwanciyar hankali.

Kullum Rumaisa take zuwa ta wuni a asibiti ,sai dare suke komawa tare da Kabeer.

Kwanan Mmn Maisa shida a asibiti aka sallameta, tana komawa gida tace Zata koma Jigawa Dakyar Abba babba ya matsa mata ta k’ara kwanaki.

Koda kawu ya nemi Iso gurinta cewa tayi bata son ganinshi ,babu wanda ya ga laifinta dan ya cancanci fiye da haka ma.

An sami sabanin raayi cikin Familyn dan wasu Sun yarda da abinda aka ce kawu ya aikata yayin da wasu suke ganin k’azafi kawai aka mishi.

Ba ma kamar wad’anda suka fito ciki d’aya cewa suke saida Dadda da Maisa suka gama morar kawu snn suka mishi muguwar sakayya.
Zali kanwarshi har cewa tayi zata mayarda ‘yarta Fauziya gidan kawu dan huce haushi.

Kafin ta koma Jigawa saida ta kira Kabeer da Maisa tace mishi tana son tasan Ra’ayin shi game da Maisa, Indai yasan takura kanshi zaiyi ya rabu da ita kawai Zata koma da ita Jigawa.
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

 

♣♣♣

Wannan nakine maqociyar kirki.
*Khadija ( Mmn Buhari.)*

Allah ya barmu tare.
*22*.

 

Ce mata yayi, ba takura, yana son matarshi, komai kuma ya wuce.
Har cikin zuciyarta taji dad’i bazata so auren Maisa ya mutu ba bare har abinda ya faru yaje kunnen dangin mahaifin ta.

Nasiha sosae tayi musu mai shiga jiki.

*************

Fitowa Baban Kabeer yayi cikin shirin tafiya sallar Juma’a, sai ganin kawu yayi tsaye kofar gidanshi.

Da mamaki ya bishi da kallo, ko kafin yace wani abu sai gani yayi kawu ya Mika mishi hanu, yana kuma yi mishi Sallama.
Mika mishi hanun yayi shims tare da amsa sallamar.

“Bismillah “.kawu yace mishi yana bud’e motarshi, dan Baban Kabeer ya shiga kamar dai yadda suka saba tafiya masallacin tare.

D’an jim yayi kamar bazai shiga ba
Me kuma ya tuna, sai kawai ya shiga.

Hira sukeyi jefi jefi, Sun gagara sakin jiki da juna,sun zama kamar wasu bak’i, har suka je suka dawo ba wata sakewar kirki kamar ba yan uwan juna ba.

Saida suka zo rabuwa kawu yace “Yaushe Dadda zata koma. ”

“Ta koma. “Baban Kabeer ya fad’a a takaice yayi gaba.

Jinjina kai kawu yayi yana tunanin shi kenan yanzu Zumuntar Su ta lalace.

Niko nace wa ya jawo ????

Har gida Abba babba yazo ya samu matar kawu ya bata hakuri tare da shawarar ta rufawa mijinta asiri Su zauna lafiya ta kuma rufa maganar kada yaranshi suji.

Dansu yaran ba kanana bane Sun girma suma, Babban ya gama sec. School.

Sai na biyu da yake ss2
Shi kuwa na uku ss3
Sai auta Farida Jss 3.

Shima kawun ya Sauko daga borin Kunyar da ya hau, nan ya lallaba matarshi suka zauna lafiya.
Amma fa yanzu Sam bata yarda dashi dan mugun sa mishi ido tayi.
More especially kan mai mata aiki.

*************

Kabeer da Maisa yanzu zama suke yi na mutunta juna, suna zaune lafiya ba maijin kansu, saidai itama yasa mata dokar zuwa gidan kawu, ko gidansu zata je tare suke zuwa, da yake itama haushin kawun takeji ko kallon gidanshi batayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button