HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Dad’i Adda binta take ji idan suka je gidanta ko taje gidansu ta gansu Suna wasa da dariya ,kwarai abin yake mata dad’i.

Har mai Shara da wanke wanke Kabeer ya nemawa Maisa idan ta gama aikinta ta koma gida, girki da gyaran dakunansu kawai Maisa keyi yanzu.

Basu da wata matsala yanzu sai na rarrabuwar kan Family.

***********

Tunda Mmn Maisa ta koma bata kuma Zuwa ba yanzu ana neman shekara guda kenan. Sai Maisa da Kabeer da Adda binta ne suka je mata.
Gaba d’aya garin ne ya fita kanta bata sha’awar ganinta a garin,duk da tana cike da Kewar yan uwanta.

Kamar yadda suka saba zuwa gidan Abba babba mostly weekends haka yau ma matar kawu da Farida suka je.

Hira suke amma hankalin Mamma yana kan Farida, har itama Farida ta fara tsarguwa da irin kallon da Mamma take mata.

Can dai Mamma ta shiga d’aki ta d’auko wayarta ta kira kawu.
Yana dagawa ko gaisuwarshi bata amsa ba tace “Khamis kar dai wani abin kunyan ka kuma yi mana. ”

“Kamar ya Adda A’i?”
Cikin b’acin rai tace “Ba ciki nake gani jikin Farida ba? ”

“wace Farida. ”
Ya fad’a da ka’rfi bakinshi na rawa.

“Farida nawa gareka khamis ? Farida nake nufi ‘yar cikin ka. ”

“Innaalillahi. ”
Yake ta nanatawa, jikinshi babu inda baya rawa.

“Ciki? A jikin Farida, yar karamar yarinyar da bata wuci 14 yrs ba?
Kuma ma wai shi Adda A’i take zargi. ”
Lallai yanzu ya tabbatar da tabon zina bata gogewa.

Allah ne ya Iso dashi gidan Abba babba lafiya sakamakon gudun da yayi ta shararawa a hanya.

Yana shiga ya fara Kiran Adda A’i.
Palourn Abba babba tace suje.
Ido jazur yake kallonta tana tabbatar mishi da lallai ita taga alamun ciki gun Farida.

Hindu ya kwala wa kira, tana isowa cikin hargowa yace “Wani d’an akuyan ne yama Farida ciki. ”

A gigice tace “Ciki? ”
Tana zaro ido kirjinta yana Lugude.

“Eh, ciki. ”
Ya fad’a yana muzurai.

Maida kallonta tayi kan Adda A’i kamar tana neman k’arin bayani.

“Ciki gareta Hindu, ke bakya gane mai ciki ne. ”

Dab’as, tayi zaman yan bori a tsakiyar falon, Kuka take tsakaninta da Allah, kukan bak’in ciki.
Cikin kukan take cewa “Kaga abinda ka jawo mana ko,Wnn jinjirar yarinya ace cikine da ita. ”

“Farida. ”
Ya kwala mata kira cikin b’acin rai, sai da taji cikinta ya d’uri ruwa, dama daga yadda taga Ya shigo a fusace da jin Kiran da yayiwa mamanta tasha jinin jikinta, jikinta ya bata akwai abinda ke faruwa.

Duk’awa tayi kusa da mahaifin nata, kan tayi magana ya d’auke ta da wata mahaukaciyar Mari.

“Wa ya miki ciki Fareeda, nace wani d’an akuyanne ya Miki ciki. ”

Hhhhh su kawu manya, ka manta ba d’an akuya bane d’an bunsuru ne.lol.
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

 

♣♣♣

In dedication to my swt sis.
*Halima Awwal.( Mmn Ayshat)*

Allah ya kara miki lafiya.

*23*.

Cikin gigita da zafin Mari ta fashe da kuka.
Ganin zata ba’ta masa lokaci yasa ya shakota, har idanunta suka fiffito.

“Nace wani tsinannen ne ya miki ciki, kashe ki xanyi Farida idan baki fad’amin ba. ”

Dakyar ta iya budan baki sbd shakar da tasha tace “Hamma Siraj ne .”

“Wani Hamma Siraj d’in. ”
Suka fad’a dukansu da ka’rfi.
Jiki a sanyaye kuma Babanta ya sake ta ta fad’i kasa tana rike da wuya tana tari.

Matsowa ya kuma yi kusa da ita, a sanyaye yace “Farida, wani Siraj kike nufi?”

“Hamma Siraj d’in Goggo Nenne. ”
Ta bashi amsa still tana rike da wuya..

Salati suka d’auka baki d’aya.
Basu matan ba shi kanshi wnn Suna da ta kira ya bashi mamaki.
Yaron da baya d’aga ido ya Kalli mutum.
Yaron da suke ganin ko yatsa aka saka mishi a baki bazai ciza ba.

Zama yayi ya dafe kanshi zuciyarshi na tafasa, shiru falon ya d’auka.
Can Mamma ta matso kusa da Farida ta dafa kanta.
“Farida ‘yata gaya min gaskiya, Siraj ne ya miki ciki ko kin fad’ane dan kinga baya magana. ”

Cikin Kuka tace “Wlh shine, ku tambayeshi, Wlh shine. ”

Shiru sukayi dukansu sun rasa ta ina zasu fara.
Tashi kawu yayi ya figeta ya fita da ita ko takalmi babu a kafarta.

Jefata yayi cikin matarsa kamar kayan wanki.
Snn ya shiga yaja.

Asibiti ya kaita ya roki a fitar da cikin, amma abin takaici aka bashi tabbacin cikin ya Kai wata shida, idan ance za’a fitar zata iya rasa rayuwarta.

Cikin bakin ciki suka dawo gidan Abba babba, zuciyarshi kamar zata yi gobara.

A inda suka barsu nan duka dawo suka samesu sai dai yanzu Abba babba ma yana falon.
Zama kawu yayi yana huci, ji yake kamar yaga Siraj a hanunshi, shi kanshi baisan irin hukuncin da zai mishi ba.

Shi kanshi Abba babba yaji mamakin cewar Sunan Siraj da ya ji an fad’a a matsayin wanda ya kamata wnn mummunar aiki, amma da ya tuna sharrin zuciya da na shaid’an sai yaga ba abin mamaki bane.

Goggo Nenne ya kira ya ce wata ta tambayi mijinta tazo gidanshi yanzu.

A kid’ime tazo gidan amma da taji musabbabin Kiran, sai ta fututtuke ta fara masifa, ita an ma d’anta sharri tasan bazai aikata.

Kiranshi Siraj d’in akayi, bai wani b’ata lokaci ba ya Iso gidan.
Ganinsu harda Farida cikin su yasa ya fahimci dalilinta Kiran.

Zama yayi ya Gaishesu duka kanshi a kasa, duk suka amsa banda Baban Farida.

Ko da aka tambayeshi baiji ko d’arr ya amsa shi ya mata.

Tsananin tsoro da mamaki suka bayyana a fiskokinsu, Shiko Siraj ko kallonsu baiyi ba bare yasan halin da fiskokinsu suke ciki.

Da aka tambayeshi dalilin cutar da kanwarshi, sai cewa yayi ya rama musu ne sharrin da Kawu ya ta musu akan Maisa duk ya jawo ana musu kallon yan iska.

Kure shi kawu yayi da ido, lallai mutum sai a barshi, bai tab’a Tsammanin yaron nan zai d’auki abinnan da zafi ba.
Dan ko lokacin da ya koresu daga gidanshi bai nuna b’acin rai a kan haka ba sai ma hakuri da ya bashi.
Ashe akwai abinda ya shirya.

Dukansu saida jikinsu yayi sanyi da amsar da ya bayar.

“Siraj, ba’a rama sharri da sharri, ba haka ya kamata kayi ba, yanzu ita yarinyar nan Meye laifinta, ai ba ita ta maka laifi ba, gashi yanzu sanadin fushi da d’aukan fansa ka lalata mata rayuwa, ka kuma b’ata mana sunan Zuri’a, shi kuma d’an da za’a Haifa ya rayu cikin bak’in ciki, shin idan ya girma ya tambayeku Kuce mishi me.
Bama Wannan ba, me zaku cewa mahaliccin ku?
Kai kana ganin Wannan hujja da ka bayar ya ishe ka hujjar kare kanka a gurin Allah ne? ”

Fad’a sosae Abba babba yayi tayi cikin damuwa da b’acin rai, kawu kam ba baki sai ido.

Shi kuwa Hamman namu ko d’agowa baiyi ba .

K’arshe dai Abba babba yace ma Goggo Nenne taje su shirya idan Farida ta haihu za’a d’aura musu aure da Siraj.

Daddagewa goggo Nenne tayi akan baza’a aurawa Siraj wacce baya so ba, ko da aka tambayi Siraj baiyi kasa a gwiwa ba yace baya sonta sbd da haka bazai aureta ba.

Sosae maganar ta shigi kawu, kallon yayarshi wacce suka fito ciki d’aya yakeyi, yau ita ke kyamar had’a jini da shi, lallai duniya abar tsoro ce, nadama ya dada shiganshi, ko me ya faru da ‘yarshi shi ya jawo mata.

Haka suna ji Suna gani Goggo Nenne taja d’anta suka fita.
Saida suka koma gida tasa shi gaba ta zage shi tass.

Washe gari Abba babba ya kira sauran yan uwansu Meeting nan suke jin abinda ya faru, duk da basu ji dad’in abinda ya faru ba amma Sun hakikance alhakin Rumaisa ke bibiyar Kawu.

Nan Abba babba ya kafa dokan kar d’an wani a cikin su ya kuma zuwa gidan wani da sunan zai Kwana biyu ko hutu kowa ya zauna gidan ubanshi. Ya k’ara da cewa, “Ke kuma Zaliha, naji har tura yarki kike gidan khamis dan ki huce mishi takaicin k’azafin da kuke ikrarin an mishi ko?
To kisani cewa duk abinda ya faru da ita ba ruwan kowa anan kada ki neme mu.
Dama yaya zumuncin nasu yanzu ya riga ya zama ana kallon juna ne kawai, kowa da abinda ke kasan ranshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button