HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Allah ya kare mu da sharrin ZUMUNTAR ZAMANI.
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

 

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

 

♣♣♣

*Dedicated to all fasaha novel group members at large, luv u all.????*

*24*.

Haka taro ya watse ba dad’in rai.
Kulawa sosae Hindu take bawa yarta don tausayi take bata,banda Mmn Hindu babu wanda ya san da maganar cikin, cikin dangin Hindu.

Shi kuwa Siraj daga baya sai yaji ya fara tausayawa Farida, Ammafa baya ganin zai iya auranta dan shi yana da wacce yakeso.

A Kwana a tashi ba wuya har cikin Farida yakai haihuwa.
Wata ranar alhamis ta tashi da nakuda mai zafi bada jimawa ba jini ya b’alle mata.
Cikin tashin hankali suka kaita asibiti, sai bayan sun isa asibitin ne kawu ya sanar da Abba babba.

Suna gama waya Abba babba ya kira Goggo Nenne yace ta sanar da d’anta Farida tana nakuda yazo maza ya karb’i d’anshi idan ta haihu.

Haka kawai taji zuciyarta ya tsinke, da sauri ta kwala wa Siraj dake hanyar fita kira.
Yana zuwa ta fad’a mishi abinda Abba babba yace.

Cikin sauri ya fita daga gidan tana kiranshi ko waiwayo wa baiyi ba.

“Kana nufin baza ka je ba kenan. ”
Ta d’aga murya ta fad’a.

Ina yayi gaba ko waiwaye babu.

Abba babba ya kira yaji asibitin da suke.
“Medical Center .”
Ya ce mishi.

Yana isa yaga nurse ta fito da gudu ta nufo su Mamma da Hindu.
“Ina mijinta?”
Nurse d’in take tambaya.

“Gani. ”
Shine amsar da suka ji a bayansu .
Da sauri duka suka waiwaya dan ganin waye.
Siraj suka gani ya kure nurse da ido k’arin bayani yake jira.

“Doctor yana son ganinka. ”
Tace tare da Juyawa da sauri.
Bin bayanta yayi shima da saurin kamar zai tashi sama.

Takarda Doctor ya bashi yayi signing dan bazata iya haihuwa da kanta ba.

Ba gardama yayi signing snn ya nemi izinin ganinta.
Dakyar suka yarda dan cewa suka yanzu zasu yi aikin, sun bashi minti biyar su gana ya fito.

Nurse ce a gaba yana binta a baya har suka shiga d’akin da take.

A sanyaye ya k’arasa bakin gadon yana kallon yadda ta galabaita duk ta fita kamanninta.
Gani yayi ma kamar an canza ta.

Fita nurse d’in tayi taja musu k’ofa.
Hanunta ya riko yana kiran sunanta, duk jikinshi ya gama sanyi.
Nadamar abinda ya aikata ne ya shige shi ga tausayinta da yasa idanunshi suka cika taff da k’walla.

“Fareeda. ”
Ya sake kiranta muryarshi na rawa.

A hankali take bud’e idonta da ta Rintse har ta gama ware su kan fiskarshi.

“Fareeda, ki yafemin, ki gafarceni, na tuba.”

Matse hanunshi dake cikin hanunta tayi ta kuma Rintse idanunta tana cewa “La Haula wala quwwata Illa billah. ”
Tayata yayi suka k’arasa tare.

Saida abin ya Lafa mata snn ta sake bud’e idonta ta kalleshi.

“Ina mummy na? ”
Tace mishi a hankali.
“Tana waje. ”
Ya bata amsa.

“Daddy na fa?”
“Yana waje Shima. ”
Yace mata.

“Hamma Kace su yafemin, mutuwa zanyi.”

A gigice yace “Baza ki mutu ba Fareeda, zaki haihu lafiya, ki daure dan Allah. ”

Girgiza kanta takeyi a hankali “Ni dai nasan mutuwa zanyi.”

“Baza ki mutu ba nace Fareeda, Kiyi hakuri ki tashi Wlh Zan aureki. ”

Murmushi ta d’an yi kad’an snn tace “Na yafe maka Hamma, Kace kowa ya yafe min. ”

Kuka yanzu kam yakeyi sosae maganar ma ta gagareshi.

“Inna lillahi wa innaa ilaihirraji uun. ”
Ta fad’a da dan ka’rfi snn ta koma yi a hankali, tun yana jinta har ya koma bakinta ne kawai yake motsi.

Hanunta dake cikin nashi yaji yana sakewa da sauri ya rike hanun yana cewa “Kar ki min haka Fareeda, Wlh zan aureki. ”

Turo k’ofa akayi bai ma d’ago ba surutan shi yaci gaba da yi har likitocin suka karaso.

Kallo d’aya suka ma Fareeda suka gane rai yayi halinsa.

Dafashi babban Doctor yayi cikin karaya yake cewa “Kad’an bamu waje zamu dubata. ”

Fiskokinsu kawai ya kalla ya girgiza kai ya kama hanya fita.
Yana Kai bakin k’ofa ya juyo, sai gani yayi ana rufe ta har fiska.

Fad’uwar shi suka jiyo suka dawo kanshi.

Kawu yana jin Tilon yarshi mace ta rasu Shima ya fadi, take a gurin stroke ya bugeshi.

Har aka kaita makwancinta Siraj bai dawo hayyacinshiba.

Saida ya Kwana ya wuni snn aka sallameshi, tunda ya koma gida ya shige d’akinshi babu abinda yake fito da shi sai sallah, sosae mutuwar ta shigeshi.

Hindu kam abunne ya had’e mata, ga rashin yarta mace tilo ga kuma ciwon mijinta ,gaba d’aya ta rame ta zabge ta zama abar tausayi..
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie. (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*Dedicated to my lovely son *Abdurrahman Bashir Bello.*
Allah ya rayamin ku tafarkin addinin musulunci.

*25*.

Rasuwar Fareeda ne yasa Maisa zuwa gidan kawu, sosae itama rasuwar ya shigeta tayi Kuka har ta gode Allah.

Kawu kam ya zama ba baki ba k’afa,
Sai ido kawai.

Mmn Rumaisa ma tazo, tana ganin halin da kawu yake ciki ta fashe da kuka, Kuka tayi tayi na tausayin d’an uwanta, ya zamo kamar ba shine lafiyayye kakkarfannan ba.
Rayuwa kenan.

A cikin zuciyarta take cewa ta yafe mishi abinda ya mata.

Wata guda tayi kafin ta koma, lokacin kawu ya d’an fara magana amma idan yanayi zakaji kamar fizgar maganar yake da ka’rfi.

A hakan ya Nemi yafiyarta ta yafe mishi .
Ya kuma roketa ta ta roka mishi gafarar Maisa, dan tunda ya kwanta ciwo sau d’aya tazo dubashi lokacin kuma bai fara magana ba.

Kabeer yana zuwa dubashi amma ba sosae ba.

Har gida Mmn Maisa ta samesu ta roka wa kawu gafara, suka yafe mishi.

***************
Hirar su suke cikin shauqi da ishqi, kwanciyar hankali da nishad’i, da ka gansu Kaga masoya masu matukar k’aunar junansu, masoyan da suka yi bala’in dacewa da juna.
Jinsu suke tamkar su kad’ai ne masoyan da suka rage a fad’in duniya.

Sallamar Adda binta ce ta katse musu hirar duk suka yi tsit kamar masu so su tabbatar da sallamar.

“Bobbo kamar Adda Binta ce take Sallama. ”

“To ki amsa mana Maisa. ”

“D’agani in tashi kafin ta shigo. ”

Idonshi a lumshe, ya dad’a narkewa kan cinyarta yana kwance kamar wani k’aramin yaro,yace
“Sai an tashi ake amsa sallama ne, amsa Kice ta shigo. ”

Sallama Adda binta ta sake kwadawa a karo na biyu .
Ware murya Kabeer yayi ya amsa sallamar tare da cewa ta shigo.

Tura kanshi ta farayi “dan Allah Bobbo ka tashi kafin ta shigo. ”

Gyara kwanciyarshi yayi tare da saka hannayenshi k’ark’ashin cinyoyinta ya Matse saida ta d’an yi k’ara .

“Me nake ganin nan god’od’o dakai ka wani kwanta mata kan cinya, karyata zakayi?”

Adda binta da ta shigo yanzu, take fad’a bayan ta Waro idanu kamar wacce taga abin mamaki.

“Nifa takurace bana so, ya daga zuwanki gidan mutane zaki fara damunsu da surutu idan kinsan sa ido ne ya kawo ki ki koma. ”
Kabeer ya fad’a yana kallon Adda binta.

Maisa duk kunya ta gama isarta.

“Dama ka kirani nazo ka min wulakancine, ina ce min Kayi Maisa ba lafiya ka d’agamin hankali Ase karya kake. ”

“Ah, Haba dai Adda binta da girma na Kice ina k’arya, ki tambayeta kiji da gaske bata da lafiya. ”

“Me ke damunki Maisa. ”
K’asa tayi da Kai takiyin magana.

“Tunda taki fad’a ni barin in fad’a miki, baby na ke damunta, Wlh Kwana biyunnan duk amai takeyi. ”

Ya fad’a yana mik’ewa zaune.

“Inna lillahi. “Maisa tace.

“Ma sha Allah, Allah ya inganta. “Adda binta ta fad’a fiskarta d’auke da fara’a.

“Amma shine kuma ka kanainayeta kamar kaine Marar lafiyan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button