ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Turo baki yayi irin na shagwab’abbun yarannan yace “Ni d’in kika San abinda take min, Wlh ko rabin son jikinta bani dashi. ”
“Na banu. ”
Maisa tace tana sunkuyar da kanta.
“Dan tayi son jiki ba laifi bane, kai kuma god’od’o dakai abu ba kyan gani Sam, kada ki yadda Maisa ke zaki wahala. ”
“Tare fa kika samemu Adda binta kuma haka zaki tafi ki bar mu, idan kika shiga tsakanin mu ma kunya zaki ji. ”
Kabeer ya fad’a yana dariya.
“Naji, yanzu da ka taso ni daga gida me kakeso na maka? ”
“Kitso fa zaki mana Addanmu, tun shekaran jiya wancan muka tsefe kuma mun gaji da ganinshi a tsefe.”
Tashi Rumaisa tayi ta nufi fridge dan samowa Adda binta abin jik’a mak’oshi.
“Kabeer Kaifa d’an rainin hankaline, da kullum ni nake zuwa na muku kitson?”
Langab’ar da Kai yayi snn yace “A’a mu muke zuwa yau dinma bamu son mu wahalar da baby ne yasa muka nemeki Addanmu. ”
Ladabin Kule kenan.
Gaisheta Maisa tayi bayan ta ajiye mata abinda ta kawo mata, ita kuma ta mata ya jiki.
Snn ta koma wani kujera daban ta zauna.
“Yauwa Adda binta kisa mana date muje shopping. ”
“Shopping na Meye kuma ni ‘ya su. ”
“Na kayan babies mana. ”
Ya fad’a yana kashe mata ido.
“Oh Allah, ni naga zarb’ab’i, har wani shopping na kayan babies daga yanzu Kabeer. ”
D’aure fiska yayi “Point of correction ,Baban Abdurrahman daga yau. Ko ya Maisa?”
Ya sako Maisa cikin zancen jin tayi shiru, ya sani Sarai Kunyar Adda binta takeji.
“Hmmm.” kawai tace tana d’an murmushi.
“To, ya Adda zamujenne? “ya sake tambayar Adda binta. ”
Rike baki tayi “Oh, ni binta, zamu je Kabeer shi kenan. ”
Hararan wasa ya mata, tayi saurin cewa “Sorry Baban Abdurrahman. ”
“In sha Allah. “Yace yana shafa fiskarshi yana kallon Rumaisa fiskarshi d’auke da murmushi…..
*Tammat bi hamdillah.*
Alhamdulillah, hamdan, katheeran, d’ayyiban, mubaarakan fiih.
Anan na kawo k’arshen littafi na *Zumuntar zamani.*
[ad_2]