HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Sakeni Adda Binta. ”
Abinda yace kenan yana mata kallon banza.

Sakin baki tayi tana kallonshi, kamar kuma an mintsineta cikin azama ta damki kwalar rigar shi “Ashe baka mutunci Kabeer, ka kashe ‘yar mutane kuma ko damuwa bakayi ba. ”

“Sakar min riga. ” Ya kuma cewa a dake.

“Bazan sake ba Kabeer dakeni sai in tabbatar baka da mutunci.

D’aga hanunshi yayi kamar zai shak’eta sai kuma ya fasa ya sa hannunshi ya cire nata hanun daga rikon da taiwa wuyar rigarshi.

Cike da takaici ta koma gun Rumaisa da yashe har yanzu babu alamun numfashi tare da ita.

A guje ta fita daga gidan cikin tashin hankali taje ta taro mai adaidaita, har cikin gidan suka shigo.

Jin tsayuwan napep cikin gidan shi yasashi fitowa daga d’aki, yana shiga falo Suna shigowa tare da mai napep cikin falon.

Hannayen shi ya hard’e a jikinshi ya tsaya yana kallon abinda zasu yi.

“Gata nan. “Cewar Adda binta tana nuna Rumaisa tare da nufar wajenta.

Biyo bayanta mai Napep d’in yayi tana cewa “Taimaka min mu d’agata .”

Duk’awa yayi dan taimaka mata yaji wata gigitaciyar tsawar da ta razanashi “Zan Karya kazamin hanunka idan ka tab’amin mata .”

Ai da sauri mai napep yayi waje yaja napep d’inshi a 360.yana jinjina rashin imani Irinna Kabeer, wai kuma har matarshi yake cewa ko kunya babu.

Haushi, takaici, bakin ciki suka had’u suka cika zuciyar Adda Binta.
Ruwan sanyi ta d’ebo tazo ta yayyafa mata, sai da ta d’au lokaci tana shafa mata ruwan sanyin snn ta farfad’o.

Yana ganin ta farfad’o ya koma d’akinshi ya banko k’ofa zuciyarshi na tafasa.

“Adda binta ki raba ni da gidannan, Bobbo zai kasheni. “tace tana fashewa da kuka.

“Shhh , yi shiru abinki Rumaisa, yanzu kuwa zaki bar mishi gidan. D’an iskan yaro kawai. ”

Hijabinta taje ta d’auko mata, basu tsaya d’aukan wasu kaya ba taja hanunta suka fice daga gidan……….
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

*Fasaha Online Writers.*

*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*Dedicated to my besties.
*Maryam Mazad.*

$

*Lubabatu kyauta.*

*3*.

Jin shirun yayi yawa yasa shi fitowa palourn, duk a tunanin Suna cikin d’akine, yafi awa a zaune a falon da sunan Kallo yakeyi amma hankalinshi na gun d’akin.

A hankali ya je ya tsaya a jikin kofar bedroom d’in, ya jima yana tsaye, tsit yaji kamar ba mutane a gidan in ba T. V da yake karad’i ba babu alamun motsin wani a gidan.

D’aure fiska yayi ya tura k’ofa ya shiga d’akin cikin dakewa.
Ga mamakinshi babu kowa ciki sai wayarta dake kan gado kusa da pillow.

A sanyaye yasa hanu ya d’auka ya shiga bincike a wayar, Kwafa yayi ya cire sim card ya kakkarya, yana fadin “Sai Inga ta inda zaku rika communicating, ‘yan iska kawai. ”

Fita yayi da wayar snn ya fara duba ko ina a gidan ya kuma tabbatar bata nan.

Hannunshi na dama ya d’ora a lips d’inshi yana karkad’a Yatsunshi biyu, d’ayan hanun kuma ya rike kugunshi dashi. “Wato Adda binta tafiya tayi da yarinyar nan ko. ?Xanyi maganin ku dukanku.”
Ya fad’a yana ciza leb’enshi na kasa.

Cikin sauri ya shige d’akinshi ya d’auki car key ya fice daga gidan bayan ya kulle ko ina.

Kofar gidan Adda Binta yayi parking, ya fito fiskannan a murtuk’e da ka ganshi kasan no mutunci .

Sallamar ma saboda sanin muhimmancin ta yasa shi yinta .daga ciki aka amsa mishi sallamar, kafin ya shiga.

K’ananan yaran Adda binta ya samu a gidan, babbar cikinsu bata wuci 11 yrs ba.

Oyoyo Uncle Doctor, yaran suke cewa suka nufo shi da gudu, k’aramin ciknsu d’an 3yrs ya d’aga sama, yayi pecking fore head nashi, snn ya kamo hanun D’ayar mai 5yrs yana tambayarsu Ina Maminsu.

“Sun tafi asibiti “Yaran suka had’a baki wajen fad’a.

“Waye ba lafiya. “ya tambaya yana kallon babbar ciknsu.

“Pendo Maisa ce Mami takai asibiti .”

“Kuma tana ta Kuka. “cewar ‘yar 5yrs d’in.

Basarwa yayi kamar baijiba, ya ce, “wani asibiti sukaje?”

“Bata fad’a mana asibitinba tace mu zauna mu jirata Zata kai pendonmu asibiti .”

“Ina Umaimatu? ”

“Tare suka tafi asibitin ”

Sauk’e yaron yayi yace “Mu’allim, bari inje in dawo ko. ”

Kai yaron ya gyad’a mishi yana tsotsar babban yatsar shi.

Federal Medical Center ya fara zuwa, duk zagayenshi baiga alamunsu ba, ya koma specialist hospital nanma basa nan.
“Toh ina suke? ”
Ya tambayi kanshi bayan ya daidaita zaman shi cikin mota.

Wayar shi ya ciro yayi dialing no. Adda binta.
Da mamaki take kallon sunanshi da yake yawo kan screen d’in wayarta.
“Ko me d’an rainin hankalinnan zaice min yake kirana?”
Ta tambayi kanta.

Tab’e baki tayi ta d’aga wayar a zuciyarta tana cewa.
“bari dai inji kalar rashin Kunyar da zai min yanzu kuma.

“Meye kuma? ” tace mishi tana yatsina fiska kamar yana ganinta.

“Ina kuke? ” ya ce mata.

“Ban sani ba. ”

Sassauta murya yayi, “wani asibiti kuke Adda binta?”

“Bazan fad’a ba sai naji shak’a. ”

“Addana fad’a mukeyi ne? “ya fad’a yana dad’a sassauta murya.

“Ban sani ba ubana.”ta fad’a a kufule.
Murmushi yayi mai sauti snn yace “Ina ce dai ba barin garin kikayi ba, I must find u where ever you are. ”

Tsaki ta ja tace “Kanka ake ji. ”
Kit ta kashe wayar.

Bin wayar yayi da Kallo yana tunanin ta ina zai fara, Gate way, city clinic, Doctor Aisha, khairan ko kuma Umma.

K’arshe ya yanke shawarar fara zuwa Umma clinc.
Yana parking ya hango ‘yarta babba tana shiga cikin asibitin da flask a hanunta.

“Umaima. “Ya kwala mata kira bayan ya fito daga cikin mota .

Waige waige ta fara yi har ta hango shi, wajen shi ta kama zuwa Shima yana tahowa suka had’e a bakin gate na asibitin.

Gaisheshi tayi cikin girmamawa ya amsa tare da ce mata “Muje. ”
Tana gaba yana binta a baya har suka shiga d’akin da aka kwantar da Rumaisa.

Idonshi akanta har suka isa gurin da take kwance.
Idonta biyu amma jin Kamshin turarenshi ya sa zuciyarta tsinkewa a take kuma ta rufe idonta kamar mai bacci. Duk da bata da tabbacin ko shine hakan bai sa ta bud’e idonta ba, gudun kada ta ganewa kanta masifa duk da kuwa tana son bud’ewan.

Kallonta ya tsaya yi nad’an lokaci snn ya nemi guri ya zauna ya fiddo wayar shi ya fara dannawa.

Adda binta da ta shigo yanzu da Ledar magani a hanunta da bag na pure water, ta bishi da kallon mamaki, saida ta ajiye pure water n snn ta sake kallonshi, taga ko d’agowa baiyiba balle ma ya nuna yasan tana wajen.

Dogon tsaki ta ja amma gogan ko ya d’ago ya kalleta, tsakin ta kuma yi snn tace.

“Me ya kawoka nan Kabeer. ”
Ta fad’a tana harararshi kamar idanunta zasu fad’o k’asa………

*A dad’e anayi sai gaskiya, Allah ya bar minke sistona Haleema Auwal (Mmn Ayshat) . ????????????*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*4*.

Ci gaba yayi da danne dannenshi ko d’agowa baiyi ba.

“Kabeer tambayar ka nake me ya kawoka nan ” ta fad’a a fusace.

Sai a lokacin ya d’ago ya kalleta “Kin dawo ne? ”
Abunda yace mata kenan.

Shiru tayi kamar bata jishi ba.
Ganin a Kule take ya yi niyar kara Kular da ita “Ina kika je ne kika barta ita d’aya .”
Wayyo takaici kamar ya kashe Adda binta. Taso tayi shiru ta kyale shi sai kuma abun ya faskara, jin zuciyarta take kamar yana mata ciwo.
Harara ta zabga mishi tace “Inda ka Aikeni Marar mutunci. ”

Murmushinsa mai kyau yayi har fararen hakoranshi masu d’auke da wushirya suka bayyana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button