ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Ya mai jikin?” ya sake cewa yana kallonta.
Banza tayi mishi kamar bata jinshi, ta nemi guri ta zauna.
Cikin nitsuwa ya Mike ya Iso kusa da Rumaisa, sunkuyowa yayi dadai fiskarta har tana jin hucin numfashinsa.
Bugawar zuciyarta ne ya k’aru lokacin da ya Kai hanunshi kan wuyanta, da gan gan ya maida hanunshi dadai inda zuciyarta yake ya tab’a, shi kanshi saida yaji wani iri jin yadda hrt d’inta yake bugawa da sauri kuma d’a ka’rfi.
Kallon ta ya tsaya yi yana nazarinta, tabbas ya gane ba bacci take ba, likimo kawai tayi kuma ya sani dan shi tayi hakan.
Tausayin ta ya kama shi da ya tuna dukan da ya mata, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, yayi shiru , can kamar ya tuna wani abu, lokaci d’aya ya had’e fiska, tare da yin Kwafa ya koma wajen zaman shi ya ci gaba da pressing phone d’inshi.
Har akayi Kiran sallar maghrib, babu wanda ya sake magana a cikinsu .
Tashi yayi ya fita dan zuwa masallaci, yana fita Rumaisa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sai da Adda binta ta kalleta.
“Ya dai? ”
Adda binta ta tambaya.
“Ba komai.”
Tace tana mikewa a hankali.
Kwafa Adda binta tayi snn tace “Wannan fitinannen ya zo ya takura ki ko? Mtss, ni rasa gane abin da ya maida Kabeer haka Wlh, har tsoro ya fara bani, yaro kamar mai shaye shaye.”
“Hmmm. ” kawai Rumaisa ta iya cewa, dan gani take kamar idan ta tofa wani abu ma zai iya jiyota.
Sallar maghrib sukayi, Rumaisa tayi saurin komawa bakin gado ta zauna ko addu’ar kirki batayi ba.
Jin muryarshi tayi yana magana, da alamu waya yakeyi, da sauri ta koma ta kwanta ta lullub’e kanta.
Har ya shigo ya zauna bai gama wayar ba, ya dauki lokaci yana wayar kafin ya kashe ya maida dubanshi kan Adda binta dake zaune bisa sallaya Tana lazimi.
“”Ita Wannan bata sallah ne? ko dai arniya takeso ta koma ne? ”
Banza Adda binta tayi mishi, kallonta ya yi na d’an lokaci snn ya mayar da dubanshi kan Rumaisa.
“Ke, ” yace cikin kakkausar murya.
Jin tayi shiru yasa shi cewa.
“Idan kika bari na same ki a gun zaki gane kiranki, nasan ba bacci kike yi ba munafuka kawai. ”
Wuff ta tashi tana murza idanu “Nayi sallah fa Bobbo ”
Ta fad’a har muryarta na rawa dan tsoro.
“Yaushe kenan. ”
Yace tare da kafe ta da idanunshi masu razanata.
K’asa tayi da Kai “Kafin ka shigo nayi. ”
“Shine kuma har kika kwanta ko Addu’a baki yi ba tsabar lalaci, ba abinda kika iya sai Kwanciya. ”
Adda binta ce ta katse shi da cewa “wai Kabeer Lafiyarka kuwa, da, kullum sai ke yi mata sallar ko ko kabarinku d’aya ne, kai d’in me ya hana ka tsayawa Kayi addu’ar zaka wani ce batayi addu’a ba. ”
“Bafa dake nake ba Addana da matata nake magana. ”
Shiru tayi tana kallonshi a ranta take cewa “Anya ko Kabeer bai fara shaye shaye ba. ”
Katse mata tunaninta yayi da cewa “Ba zaku ci abinci bane? ”
“Cikinka ko namu? ”
Ta bashi amsa.
“Bafa ke bace damuwata, Maisa ce damuwata, ina ruwana da cikinki idan mijinki ya damu yazo ya tambayeki mana. ”
Bata San lokacin da “Ikon Allah “Ya sub’uce a bakinta ba.
Itako Rumaisa mamaki ne ya cikata har ta fara tunanin anya maganar Adda binta ba gaskiya bace. Ko dai da abinda ya shawo.
Satan kallonshi tayi taga ya maida hankalinshi ta wajen window ko me yake Kallo Oho .
Mijin Adda binta ne yayi Sallama ya shigo, Umaima ‘Yar ta na biye dashi a baya hanunta d’auke da basket na abinci.
Amsa sallamar suka yi dukansu snn Kabeer ya tashi cikin fara’a ya Mika mishi hanu suka yi musabaha. Tare da gaisawa cikin mutunta juna.
Gun Rumaisa ya juya cikin zolaya yace “yau matar Doctor a gadon asibiti. ”
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tana gaisheshi, ya jiki ya mata, snn ya juya ga matar shi yana mata ya mai jiki.
“Umaima sa mata abinci. ”
Yace yana kallon Umaimar.
Zuba mata Abincin tayi ta Mika mata, kamar zatayi Kuka take tura Abincin ganin yadda ya kafe ta da idanunshi, Sam batajin dad’in cin Abincin amma babu yadda ta iya tunda dodonta yana wajen.
Rabi taci ta mikawa Umaima Plate, “K’ara. ”
Taji yace, kamar zatayi Kuka ta Kalli Adda binta, da sauri Adda binta tazo ta karb’i plate d’in daga hanunta tana harararshi .
Kawar da kanshi yayi kamar baiga abunda tayi ba .
Maganar mijin Adda binta ne yasa shi Juyowa “Doctor ni Zan wuce, Allah ya Kara sauki.”
“Amin “yace tare da Mika mishi hanu.
“Mun gode sosae, Allah ya kaika gida lafiya.
Fita yayi Adda binta ta bishi a baya.
“Ke ,bi iyayenki.”
Yacewa Umaima.
Sumui ta fita daga d’akin…….
*Ina alfahari dake, Mira D’anfodio, Allah ya bar zumunci.Ana tare ????*
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: [9/8, 5:17 PM] Maman Abdul&Nurain.: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*5*.
Tana fita ya dad’a d’aure fiska ya cewa Rumaisa “Je Ki d’auki Abincin ki k’arasa .”
Babu yadda ta iya haka ta d’auka tana turawa dole kamar zata dawo da Abincin.
Tana cikin ci Adda binta ta dawo.
fiskar tausayi tayi tana kallon Adda binta.
Karb’a Adda binta ta sake zuwa tayi tana cewa “Iskancin banza, a cikin mutum zaki sa Abincin ne. ”
“Amma dai Adda binta kinsan rashin cin abinci yana k’ara ciwo ko, kuma wa zai ta zama mata a asibitin .”
“Dama wa ya gayyato ka, Kiran ka akayi, ko ce maka nayi ka zo ka taya ni jinya. ”
“Wnn kuma hakkinta nake bata.”
“”Allah, Ashe ma kasan hakki?”
Ta fad’a tana kallonshi shek’ek’e. ”
Tashi yayi yazo ya rab’a ta gefenta ya wuce.
Ko kad’an basu yi tsammanin zai dawo ba, amma ga mamakinsu sai gashi ya dawo wajen K’arfe goma na dare.
Babu wanda ya kula shi cikinsu.
Tsabar rainin wayo irinnashi sai cewa yayi “Adda binta baki tafi ba dama, ina ta sauri nace ko an barta ita kad’ai. ”
Shiru tayi masa.
“Adda binta garin akwai hadari fa ya kamata ki koma gida hakanan. ”
Cikin takaici ta ce “Zo ka komar dani tunda kai ka kawo ni, bansan wani fitina ne ya dawo da kai ba, fitinannen yaro kawai. ”
Zaman shi yayi ba tare da ya tanka ta ba dama burinshi yasata maganane kuma tayi hankalinshi ya kwanta.
A takaice ranar tare da shi suka Kwana a asibitin duk zagin da Adda binta ke mishi yayi kamar baya jinta har ta gaji ta yi shiru.
Asubar fari ya fita daga asibitin ya tafi, basu sake ganinshi ba sai K’arfe sha d’aya na safe ya shigo sanye da lab coat a jikinshi ta dukkan alamu daga wajen aikinshi yake .
Saida ya fara shiga gurin Doctor think ya isa wajensu .
Bacci ya samu Rumaisa take yi, ita kuma Adda binta tana zaune da pocket sized Quran a hanunta tana karatantawa.
Gaisawa yayi da mayar da ya gani kwance a gadon dake kusa da na Rumaisa ya mata ta jiki, ga dukkan alamu ba’a jima da kawo ta gurin ba.
Saida yaji takai aya snn ya gaisheta, harararshi tayi ta d’auke kai zata ci gaba da karatunta taji yace “Gaba dai babu kyau kinsani, nanma kuma Littafi mai tsarki kike karantawa. ”
Jikintane ya d’anyi sanyi amma sai ta basar tace “Ka kiyaye ni Kabeer, nifa ba abokiyar wasar ka bace ka sani. ”
Murmushi yayi mai sauti snn yace “Nama fiki sani, yanzu dai an sallameku Kiyi parking mu tafi. ”
“Ina zamu tafi? ”
Ta jefo mishi tambayar.
“Ina ya kamata mu je?”
Ya mayar mata.
“Gidan Abba Babba zaka kaimu dan can Rumaisa zata koma muga ta k’aryar rashin Kunya .”
Nuna ta yayi da yatsa yace “Kina nufin. ”
Sai kuma yayi shiru yana ciza lips d’inshi na k’asa. ”
With her full confidence tace” Eh, can Zata koma dan zamanta a gidanka kam ya K’are, idan baza ka kai mu ba kuma na kira Baban kalipha ya kaimu. ”