HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Murmushin mugunta yayi dan ya gama tsara abinda zaiyi yace “To yi sauri ki gama parking na kaiku kar ku b’ata min lokaci .”

Zuciya d’aya ta juya ta kama harhad’a kayansu.
sand’a yayi yaje a hankali ya d’aga Rumaisa dake sharar bacci hankali kwance.
A hankali yake tafiya har ya fita daga d’akin.

Cikin mafarki take ji an d’aga ta ,sai taji kamar zata fad’o.

A firgice ta farka, ganinta rike a hannunshi kamar wata jinjira yasa ta zaro ido, tana kallonshi.

Had’e rai yayi ya sauk’e ta tare da b’alla mata harara yace “Muje. ”

Gum tayi da bakinta ta bishi har suka isa wajen motarshi.

Shi ya bud’e mata motar ta shiga snn Shima ya shiga ya ta suka yi gaba.

***********

Adda binta na gama parking ta juyo tana kiran Rumaisa “Tashi mu tafi an sallamemu. ”
Wayar ta gani ba kowa a kan gadon.

“Maisa. “Ta kira da karfi har matar dake kusa da ita ta bud’e ido.

Da sauri tayi waje aiko taga Kabeer yaja mota a guje, bin gurin take da Kallo, kafin daga bisani ta maida kallonta sama,tana kallon yadda hadari ya d’auro.

Komawa tayi ciki kafin ta k’arasa har ruwan sama ya sauko.

Mijinta ta kira ya zo ya maida ita gida.

Rumaisa kam kirjinta sai dukan uku uku yakeyi, ta rasa ta cewa.

Ganin ya Iso kofar gidansu yasata fashewa da kuka .

Kallonta yayi da mamaki “Kukan me kikeyi? Idan baki rufemin bakinki sai kinyi mai dalili. ”

Mut tayi kamar Anyi ruwa an d’auke…….
[9/15, 3:06 PM] Maman Abdul&Nurain.: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

Wannan shafin musamman domin jin d’akinku ne.

*Halima Auwal.Mmn Aysha.*
*Aysha Ali Garkuwa.*
*Maryam A. I Gital.*
*Mira D’anfodio.*
*Xayynab*????????
*Ummin weedyan.*
*khairat Up*
*Teemerhlurv.*

Fasaha Online writers grp bna alfahari daku.
*5*.

Tana fita ya dad’a d’aure fiska ya cewa Rumaisa “Je Ki d’auki Abincin ki k’arasa .”

Babu yadda ta iya haka ta d’auka tana turawa dole kamar zata dawo da Abincin.

Tana cikin ci Adda binta ta dawo.
fiskar tausayi tayi tana kallon Adda binta.

Karb’a Adda binta ta sake yi tana cewa “Iskancin banza, a cikin mutum zaki sa Abincin ne. ”

“Amma dai Adda binta kinsan rashin cin abinci yana k’ara ciwo ko, kuma wa zai ta zama mata a asibitin .”

“Dama wa ya gayyato ka, Kiran ka akayi, ko ce maka nayi ka zo ka taya ni jinya. ”

“Wnn kuma hakkinta nake bata.”

“”Allah, Ashe ma kasan hakki?”
Ta fad’a tana kallonshi shek’ek’e. ”

Tashi yayi yazo ya rab’a ta gefenta ya wuce.

Ko kad’an basu yi tsammanin zai dawo ba, amma ga mamakinsu sai gashi ya dawo wajen K’arfe goma na dare.

Babu wanda ya kula shi cikinsu.
Tsabar rainin wayo irinnashi sai cewa yayi “Adda binta baki tafi ba dama, ina ta sauri nace ko an barta ita kad’ai. ”

Shiru tayi masa.
“Adda binta garin akwai hadari fa ya kamata ki koma gida hakanan. ”

Cikin takaici ta ce “Zo ka komar dani tunda kai ka kawo ni, bansan wani fitina ne ya dawo da kai ba, fitinannen yaro kawai. ”

Zaman shi yayi ba tare da ya tanka ta ba dama burinshi yasata maganane kuma tayi hankalinshi ya kwanta.

A takaice ranar tare da shi suka Kwana a asibitin duk zagin da Adda binta ke mishi yayi kamar baya jinta har ta gaji ta yi shiru.

Asubar fari ya fita daga asibitin ya tafi, basu sake ganinshi ba sai K’arfe sha d’aya na safe ya shigo sanye da lab coat a jikinshi ta dukkan alamu daga wajen aikinshi yake .

Saida ya fara shiga gurin Doctor think ya isa wajensu .
Bacci ya samu Rumaisa take yi, ita kuma Adda binta tana zaune da pocket sized Quran a hanunta tana karatantawa.

Gaisawa yayi da matar da ya gani kwance a gadon dake kusa da na Rumaisa ya mata ta jiki, ga dukkan alamu ba’a jima da kawo ta gurin ba.

Saida yaji takai aya snn ya gaisheta, harararshi tayi ta d’auke kai zata ci gaba da karatunta taji yace “Gaba dai babu kyau kinsani, nanma kuma Littafi mai tsarki kike karantawa. ”

Jikintane ya d’anyi sanyi amma sai ta basar tace “Ka kiyaye ni Kabeer, nifa ba abokiyar wasar ka bace ka sani. ”

Murmushi yayi mai sauti snn yace “Nama fiki sani, yanzu dai an sallameku Kiyi parking mu tafi. ”

“Ina zamu tafi? ”

Ta jefo mishi tambayar.

“Ina ya kamata mu je?”
Ya mayar mata.

“Gidan Abba Babba zaka kaimu dan can Rumaisa zata koma muga ta k’aryar rashin Kunya .”

Nuna ta yayi da yatsa yace “Kina nufin. ”

Sai kuma yayi shiru yana ciza lips d’inshi na k’asa. ”

With her full confidence tace” Eh, can Zata koma dan zamanta a gidanka kam ya K’are, idan baza ka kai mu ba kuma na kira Baban kalipha ya kaimu. ”

Murmushin mugunta yayi dan ya gama tsara abinda zaiyi yace “To yi sauri ki gama parking na kaiku kar ku b’ata min lokaci .”

Zuciya d’aya ta juya ta kama harhad’a kayansu.
sand’a yayi yaje a hankali ya d’aga Rumaisa dake sharar bacci hankali kwance.
A hankali yake tafiya har ya fita daga d’akin.

Cikin mafarki take ji an d’aga ta ,sai taji kamar zata fad’o.

A firgice ta farka, ganinta rike a hannunshi kamar wata jinjira yasa ta zaro ido, tana kallonshi.

Had’e rai yayi ya sauk’e ta tare da b’alla mata harara yace “Muje. ”

Gum tayi da bakinta ta bishi har suka isa wajen motarshi.

Shi ya bud’e mata motar ta shiga snn Shima ya shiga ya ta suka yi gaba.

***********

Adda binta na gama parking ta juyo tana kiran Rumaisa “Tashi mu tafi an sallamemu. ”
Wayar ta gani ba kowa a kan gadon.

“Maisa. “Ta kira da karfi har matar dake kusa da ita ta bud’e ido.

Da sauri tayi waje aiko taga Kabeer yaja mota a guje, bin gurin take da Kallo, kafin daga bisani ta maida kallonta sama,tana kallon yadda hadari ya d’auro.

Komawa tayi ciki kafin ta k’arasa har ruwan sama ya sauko.

Mijinta ta kira ya zo ya maida ita gida.

Rumaisa kam kirjinta sai dukan uku uku yakeyi, ta rasa ta cewa.

Ganin ya Iso kofar gidansu yasata fashewa da kuka .

Kallonta yayi da mamaki “Kukan me kikeyi? Idan baki rufemin bakinki sai kinyi mai dalili. ”

Mut tayi kamar Anyi ruwa an d’auke…….
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

*6*.

Tunda suka shiga ciki, take ta fatan ya fita itama ta samu ta fice daga gidan. D’akinta ta shige, bini bini ta lek’a ta ganshi yana zaune a falon.

Sanyi, da niimar ruwan sama da aka zabga yasa bacci mai nauyi da dad’i ya kwasheta ba tare da ta sani ba.

Kiran sallar azahar ne ya tashe ta daga bacci, toilet ta shiga ta d’auro Alwala.
Tana shimfid’a sallaya idonta ya sauka kan Leda kan dressing mirror d’inta, bud’ewa taje tayi taga take away da drinks. “First in history .”
Tace tana kad’a Kai.

Saida tayi sallah, snn ta d’auki Abincin taci ta rage Saura.
Mamakin baccin da tayi take tayi, ita da take fakonshi ya fita Itama ta fita, amma har yaje ya sayo abinci bata sani ba.

Lekawa ta kuma yi ta hango shi zaune da remote a hanunshi yana canza channel a T. V.

A hankali ta koma ta zauna tsakiyar d’akin ta buga tagumi. Can kamar an mintsineta ta tashi ta fara neman phone d’inta.

Har ta gaji da nema ta koma ta zauna tana tunanin inda ta jefar da wayar.

Har dare bata samu ta fita ba k’arshe dai hakura tayi tayi wanka ta kwanta tana tunanin makomar rayuwarta har bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari da sassafe bayan tayi sallah tana kwance kan sallaya, taji ya turo k’ofa ya shigo, da sauri ta tashi tana mutsike ido.
“Ina Kwana Bobbo. ”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button