HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Lafiya. ” yace a takaice.

Yaci gaba da cewa “Ba sai na tambayeki ya jiki ba nasan kin warke, so zaki fara normal duties d’inki kamar yadda kika saba, kar kiga jiya na saya miki abinci Kiyi tsammanin Yauma hakane, Sam bazan yi wahalan banza ba gwara ma ki tashi Kiyi abinda kika San ya dace dake. ”

Yana gama fad’ar haka ya fice daga d’akin.

Kuka ta fashe dashi tana fadin “Na shiga uku na, Bobbo yanaso yayi ajali na.”

Tunawa tayi da inta sake ya dawo ya sameta bata fara aiki ba wuya zatasha.
Hakanan yasa ta tashi ta shiga toilet ta wanke fiskarta snn ta fito ta fara aiyukan gida kamar yadda ta saba, share ko ina tayi ta yi mopping har da d’akinshi da nata, da wankin ????, snn ta koma kitchen nanma ta gyara ko ina kafin ta d’ora abinda zata karya dashi.

Duk Gajiyar da tayi gashi tana jin jikinta so weak, hakanan ta fita ta share compound na gidan.

Girkin ta k’arasa ta juye duka a food flask, ta nufi d’akin ta dashi dan tasan ko ta zuba mishi ba ci zaiyi ba.

Zata shiga d’akinta ta tsinkayo sallamar Adda binta, da sauri ta dawo da baya fiskarta d’auke da fara’a zuciyarta fal farin ciki, tana yi mata Sannu da zuwa.

A falon suka zauna bayan sun gaisa take tambayar ta Kabeer, tace ya fita.

“Ba dai abinba ya miki jiya ko?”

“Ba komai Adda. ”

“Kai ni jiya Kabeer ya ban mamaki, daga in tattara kaya sai kawai na juya naga dukanku biyu ba kwa nan. ”

Saida ta waiga ta Kalli k’ofa kamar mai tsoron kada wani ya jiyota, tace “Hmmm, nima Adda am farkawa kawai nayi na ganni a hanun mutum, ni na ma d’auka mafarki nakeyi. ”

Dariya Adda binta tayi snn tace “Amma Kabeer d’an duniya ne, sai da fa na kira Bbn kalipha yazo ya maida ni gida.
Barka dai da bai miki komai ba. ”

“Hmmm, “Tace snn ta k’ara da cewa “Adda binta ga abinci.

Zaro ido Adda binta tayi, “Ba dai Sai yanzu zakiyi breakfast ba, wai tsaya ma ke kika girka Abincin da kanki, ke da aka sallamo jiya daga asibitin. ”

“To ya xanyi Adda. ”

Gyad’a kai takeyi “Al’amarin Kabeer ya ta’azzara babu tausayi Sam, lallai dole a d’au mamaki, dole Manya Suji maganar nan, ke idan an tambayeki dalilin wnn abinda yake miki, cewa kike baki saniba ,shi kuma idan an tambayeshi, ya Raina wa mutane hankali, toh abun ya ishe ni haka, dole Manya susa baki idan abin ya gagara ku rabu kawai. ”

Har ta gama b’ab’atunta Rumaisa bata ce mata komai ba, cin abincinta take a tsanake.

Adda binta ce ta mata girkin rana tace ta kwanta ta huta.

Saida tayi wankanta da ruwa mai d’umi sosae snn ta kwanta tayi baccinta.

Haka rayuwa taci gaba kullum Rumaisa sai tayi dukkan Aiyukan gida, ga hantaranta da Kabeer yakeyi, kullum cikin gaya mata bakaken maganganu, bata da sukuni Sam a gidan, Gashi kuma sai ya fita ya barta ita d’aya a gidan . yanzu har ta saba, Kasancewar shi Doctor ba ko Yaushe yake Kwana a gidanba ,tun tana jin tsoro har ta saba da Kwana ita kad’ai a gida.

Kasancewar yau weekend babu inda yaje yana gida kamar yadda ya saba duk weekend sai dai in emergency ne ya taso mishi.

Wucewa tazoyi, ba tare da tasan ya fito palour ba, three quarter ne a jikinta fari da wata ‘Yar bingilar riga bak’a, tafiya takeyi cikin nitsuwa Zata shiga kitchen, saida ta isa tsakiyar falon ta ji yace “Ke. ”
Wani irin razana tayi har ta kusan sashi dariya .

Da hannu ya mata alamar ta zo gurinshi.

A tsorace tazo ta tsuguna daga gefe ta ce “Gani Bobbo. ”

“Matso yace mata. ”
Matsawa tayi kusa da shi a ranta addu’a take Allah ya kare ta daga sharrinshi.

Kamo rigar yayi ya ja, ya petta mata shi a jiki, yana bin duk ilahirin jikinta da Kallo.Kasancewar rigar rubber rubber ce, ta ko pettu pet, ta koma jikinta ta lafe.

A kasalance yace “Yaushe zaki fara jin magana ne Maisa?Bana hana ki saka wad’annan kaya a gidannan ba?”

Kallonshi tayi jin yadda yake maganar a sanyaye, suna had’a ido ya lumshe idanunshi, ba tare da ya bud’e su ba yace .
“Tashi ki bar nan. ”
Still a sanyaye yayi maganar.

Tashi tayi tana Hamdala a zuciyarta bai mata komai ba, Zata shiga d’aki taji yace.

“dawo kici gaba da aikinki. ”
“Ikon Allah.”
Tace a ranta.

Wucewa ta zo tayi ya bita da Kallo har ta shiga kitchen d’in snn ya sauk’e ajiye zuciya.

Har ta gama ayyukanta ta wuce ta koma d’akinta yana zaune a gun bai tashi .

Wayar shi ce tayi Kara , yana dubawa yaga Adda binta ce ke kiranshi.

“Kabeer yanzu abinnaka har yakai ga Bappa khamis, ma yasan abunda kake wa Rumaisa?
To ka shirya amsa tambayoyi dan yakai karar ka wajen Abba Babba, yanzu ya ce ince maka kazo kai da Maisa. Da alama zaman Maisa ya K’are a gidanka, ita ma kuma ta huta. ”

Baice komai ba ya kashe wayar yana maida numfashi.
A fili Yace “Bappa khamis ya Kai karata gun Abba Babba? Lallai ya kirawa kanshi ruwa. ”
Toh fa ????wai meke faruwane? …

Zakuga yau ina ta suburbud’o muku lbr ????????????
To fa na bankwana ne ,sai had’uwa ta gaba dan Zan shiga vibration cikin yan kwanaki nan, hidimomi nake dasu, in Allah yasa na gama da Raina da Lafiyata zaku jini.

*Allah ya sada mu da alkhairi. Luv u all. ????????????*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI ♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*Alhamdulillah !Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*

*Ma sha Allah.*
Allah ya bani lafiya,
Na gode da Addu’oinku gareni. Allah ya bar k’auna .

*7*.

Fitowarta kenan daga wanka, tana tsane gashin kanta da ta wanke da d’an karamin towel ta jishi yana kwala mata kira.
Amsa wa tayi tare da ajiye k’aramin towel d’in hanunta ta fito da sauri har towel d’in Jikinta yana faman fad’uwa rikewa tayi tana gyara zamanshi a jikinta har ta Iso ta durkusa.
“Gani Bobbo. ”

Tace, tana raba ido, gaba d’aya ta tsorata da Kiran da yake mata.

Kallonta yayi na d’an lokaci daga sama har k’asa, ya had’iyi busasshiyar yawu da ta kusa sashi ya k’ware , snn ya Kawar da kanshi wani gefen.

Kije ki shirya yanzunnan zamu je gidan Abba babba, Saura kuma Kiyi banzan dressing da kika saba. Kar kuma ki b’ata min lokaci.

Da sauri ta tashi tayi hanyar d’akinta nanma da Kallo ya bita yana tunani a ranshi anya ba da gangan Rumaisa take zuwa gunshi da irin wad’annan shiga ba.

Kawar da tunanin yayi ya gyara zama yana tunanin yadda za’a kaya a gidan Abba babba.

Har ta fito yana zaune a gurin, K’are mata kallo ya shigayi ,sanye take da riga da skirt na atamfa, Nouvo, kayan sun mata kyau sosae d’inkin ya zauna mata d’as sai Gyale kalar kayan da ta yafa da takalminta high hill Shima kalar gyalen.

Saida ta Iso ta ce “Bobbo na shirya. ”

Kamar wanda aka tasa a mafarki ya kalleta, sai kuma ya b’alla mata harara, “Wuce kije ki cire gyalennan wai ke bakya lullub’i mai mutunci ne? ”

Da sauri ta koma d’akinta, kallon kanta tayi a madubi, ta tab’e baki, Meye aibun Wannan gyalen, ita dai bata gani ba, after all mota ma zata shiga,
“Sa ido ne kawai irin nashi ”
Ta fad’a a hankali kamar mai rad’a.

A cikin manyan hijaban da ya sayo mata ta d’auko wanda ta ga ya dace da kayan jikinta ta saka ta fito.

Tafiya suke Irinna kurame ba mai yiwa wani magana a cikinsu, saidai ita takan saci kallonshi ganin yadda ya had’e rai kamar wadda aka Aikowa da sakon mutuwa.

Bata Zata ba taji ya kamo yatsunta yana murzasu a hankali.
Kallonshi tayi taga hankalinshi naga tukin da yakeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button