HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Maisa. “Taji ya kira ta.
Wani abu taji yana mata yawo a jiki wanda ta kasa fassara menene shi, dan rabon da taji ya kira ta haka cikin nitsuwa har ta manta.

Tsinkayo shi tayi yana cewa “Ina fata baki manta alk’awarin da kika tab’a d’aukar min a hospital ba.
Dama na sanar dake akwai lokacin da zan bukaci ki Fad’e shi.”
Numfashi ya ja ya sauk’e, ya ci gaba da cewa “Lokacin yayi yanzu, so nake a yau ki fad’i maganar a gaban koma waye.”

“Zaki iya? ”
Taji ya jefo mata tambayar.

Wani irin juyawa taji cikin ta yayi, tuni taji hanjin cikinta suka Fara yamutsewa, hankalinta ya tashi.

No wonder, yake mata magana cikin taushin murya Ashe da manufa.

“Baza ki iya ba kenan?”
Taji yace.

“Oho, ruwanki da ki fad’a da karki fad’a duk uwar ubansu d’aya, kece cikin wahala, dan ni kome za’a min bazan sakeki ba, amma ki sani sai nayi trippling abinda nake miki.
Samun Kwanciyar hankalinki kawai kifito ki fad’a, idan kuma kink’i kece a wahale.”

Dadai sun Iso yasaki hanunta ya nemi wajen parking yayi, suka fito.

Kallonta ya kuma yi yace “kindai ji abinda nace miki. ”

Yayi gaba abinsa.
Itako gaba d’aya ta shiga rud’ani ta rasa inda zata Sa ranta taji dad’i, yanzu bata da wani burin da ya wuce taganta cikin toilet. ????????
Wuta sallau.

Koda suka shiga cikin gidan, cike yake da ‘yan uwa maza da mata, wani kululu taji cikinta ya sakeyi sbd da haka duk Sannu da zuwan da ake musu babu wanda ta Kula ,buta ta Zara tayi hanyar toilet. ……..

*Tuna baya.*

Familyn Alh.Abubakar manga,Wanda aka fi sani da Alh. Buba Manga Babban family ne wadda Allah ya azurtashi da yara da jikoki masu yawa.

Bak’i dogon bafulatani mai cikar haiba, mutumin kirki ya kuma San darajar d’an Adam, da kuma iya zama da mutane.
Sana’ar shi ya had’a da noma da kiwo dabbobi, most especially shanukai.

Matanshi hud’u ne, yaran da ya Haifa maza da mata a Sunkai ashirin da bakwai, acikinsu uku kawai suka rasu.

Ya tsaya tsayin daka wajen ganin ‘ya’yanshi sunyi karatu, both Arabic da boko.

K’aramin d’anshi yana da shekaru goma sha biyu Allah ya mishi rasuwa.

Wnn babban family Sun ga tashin hankali, dan sunyi babban rashi ,ba familynshi kawai bama harda mutane makwabta, ‘yan anguwarsu da sauran jamaar da suke huld’a tare. Rasuwan shi bai canza Komai ba na daga zaman lafiyar da akeyi a gidan sai ma k’ara had’a Kai da yaran sukayi ,suka rungume iyayensu mata ba bambanci .

Akwai had’in kai sosae cikin family dan Sam Alh. Manga bai yarda da raba kan yaranshi ba .
Yawancinsu sun taso da son harkar kasuwanci.
Sun taso da k’aunar juna, hakan yasa lokacin da suka girma suka Fara hayayyafa idan ba farin sani Kayi musu ba baka iya banbance Wannan d’an waye a cikinsu.

Yawancinsu kamannin Alh. Manga suka d’auka shi yasa suke kama sosae da juna kamannin kuma har yaransu da suka Haifa.

Kowani d’a a Familyn yana da ‘yancin ya zauna a duk gidan da ya ga daman zama.

Asalinsu yan Jalingo ne Taraba state.

Musamman ya sayi filaye a anguwanni mabambanta ya rabawa yaranshi, tun kafin ya rasu. yakan d’auki fili ya ba yara biyu wanda basu had’a uwa ba duk dan gudun kada zumuncin su ya lalace .

Cikin yaranshi mata akwai wad’anda suka yi aure cikin jalingon akwai kuma wad’anda suke wasu garuruwa.

Kamar mahaifiyar Rumaisa kenan wacce aure ya kaita Jigawa state.

A can ta haifi yaranta takwas wanda ya kasance Rumaisa ce ‘yarta ta biyar.

Tun tana ‘yar karamar ta ‘yar yayar mamanta wacce suke kira da Anty Hafsa, wacce ke aure a Abuja ta d’auketa riko.

Da fari Suna zaune lafiya zama mai dad’i, sai daga baya wata Kawar Aunty Hafsa ta fara bata shawarar ta mayar da ita gun uwarta ,idan ba haka ba Tana ji tana gani Zata rike ta ta girma mijinta zaice yana sonta.
Dan Rumaisa irin yarannan ne da tun suna kanana zaka gane zatayi cikar halitta.
ita kuma Aunty Hafsa ta nemi shawarar kawartata ne akan idan ta aiki Rumaisa gu mai nisa ko kuma ta ba ta aiki mai yawa mijinta yana mata fad’a akan hakan yana cewa tana bawa ‘yar mutane wahala, shine kuma ita Kawar Tata ta fara zugata.

Wasa wasa zuga ya shigi Aunty Hafsa, ta zo Jalingo da Rumaisa akan Zata maidata gun mahaifiyarta kafin ta koma Abuja.

Jin haka kuma kawun Rumaisa wanda take kira da kawu khamis ,kanin mamanta wanda suke had’a uba amma uwa daban daban yace ta bar mishi ita zai riketa dan shi bashi da ‘ya mace, yaranshi duk maza ne.

Mafari kenan zaman Rumaisa gidan Kawu khamis….

*Just d beginning.*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W..

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*8*.

Ba karamin shagwabata kawu Khamis yakeyi ba, duk wani abu da ya gani na yara mata yana saya mata, gatan da yake mata ko yaran da ya haifa ba ya musu.

Saida matar shi tayi da gaske ya barta take zuwa makarantar islamiyya da ta allo.
A cewarshi ana duka sosae.
Duk ranar data nuna bata son zuwa cewa yake a barta, sosae ya shagwabata.

Shi yake kaita makaranta ya d’auko ta sabanin yaranshi da driver yake kaisu.

Ko kad’an bayason b’acin ranta shi yasa yawanci tare da ita yake fita.

Maganar aiyukan gida kam babu su Dan ya kasa ya tsare. Shi yasa har ta girma ko tafasa ruwa bata iya ba.

Ta fannin sutura kuma saidai in ita tace bai mata ba.

Musamman yake kaita boutique nashi ta zab’i irin suturar da ta ke so.
Kayan kwalam kuma babu irin wanda bata sani ba.

Kowa gani yake dan bashi da ‘ya mace shi yasa yake mata gata haka, amma abin mamaki Koda Allah ya ba matarshi haihuwar ‘ya macen bata samu gatan da Rumaisa take samu ba.

Dalilin haka yasa matar shi ta fara jin haushin Rumaisa, amma fa saidai a zuciyarta bata isa ta nuna ba.

‘Yan uwanta Sun zugata ta d’au mataki amma abin ya gagara dan kawu khamis irin mutanen nan ne masu zafin tsiya, amma fa banda akan Rumaisa.

Idan Kaga yayi wa Rumaisa fad’a tofa ya ganta da wani namiji ne Koda kuwa a cikin family members ne.

Batayi nisa sosae ba a karatun arabiyya ya hanata zuwa wai ana dukanta, shi da kanshi ma zai koya mata karatun.

Bokon ma ba wani damunta yayi ba,
Mutum d’aya ne yake sata tayi karatun ko taki ko ta so shine *Kabeer*. Wanda kannenshi suke kira da *Bobbo*.

Kabeer shima d’an Kawunta ne wanda suke neighbors da gidan kawu khamis.

Shi ya d’auko zafin ran kawu khamis, yawanci kuma idan yazo daga makaranta a gidan kawu khamis yake sauk’a.

*Kabeer shine second born a gidan su, shi yake bin Adda Binta.
Tun tasowarsu da Adda binta haka suke kullum cikin fad’a, a cewarshi ta cika sa ido, ita kuma tace ya raina ta.

Sosae Kabeer ke matsa mata akan karatu, tun bata sa hankali har ta fara fahimta.

A maiduguri yayi karatunshi.
Duk lokacin da ya samu hutu ya dawo, to Rumaisa tasan dole ta nutsu tayi karatu.

Shi yake kiranta Baby Maisa, Saura ma suka bi bakinshi suke ce mata Maisa.

Har kawu ma Maisan Kawu yake ce mata.

Ganin irin shak’uwar data shiga tsakanin Kabeer da Rumaisa
Yasa kawu ya fara sa musu ido, har ya fara kiranshi yana nuna mishi baya so.

Maisa tana ss2 kawu ya mata registration ta rubuta SSCE.
Sai ya zamto babu abin da takeyi sai bacci da yawo.

Ko kula matar gidan batayi, tsakaninsu Gaisuwa ce sai d’an abinda baza’a rasa ba.

Lokacin da Kabeer ya kammala komai na karatunshi ya dawo gida, sai ya ci gaba da zama gidan kawu khamis.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button