HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

Lura yayi da bata damu da shiga dangi ba, ya fara sata ziyara Koda bata so haka yake tasata a gaba su ziyarci ‘yan uwa.

Yawanci gidan Adda binta yake kaita tayi kitso, yana zaune tana mata kitso, suyi ta fad’an nasu na fama ,Itako Rumaisa Dariya abunnasu yake bata.

Koda kawu ya fahimci yawan fitarsu da kabeer, sosae ya nuna mata b’acin ranshi.

Duk yadda taso kin fita da Kabeer bata iyawa dan Shima bata so ta b’ata mishi rai.

Fahimtar hakan yasa kawu ya tsiri fita da ita duk kuwa da yanzu ta girma ba kamar da ba.

Kabeer baiso haka ba amma babu yadda ya iya, matarshi ma ta yi iya kokarinta har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.

Basa samun isasshen lokaci amma hakan baya hana Kabeer squeezing ya samu su d’an samu zama.

Kullum cikin yawon Sayan kwalam da makulashe suke, sune, Senate plaza, Ni’ima cool, Ostrich bakery da dai sauransu.

Yayyunshi ne suka ga abun yayi yawa suka kira shi suka mishi magana, snn aka samu ya rage yawan fita da ita.

A hankali soyayya mai ka’rfi ya shiga tsakanin Kabeer da Rumaisa, sosae suka shak’u, tsabtataccen soyayya suke gwada wa juna.

Tun kawu bai fahimta ba har ya gane, ba karamin tashin hankali ya shiga ba da ya fahimci soyayyarsu tayi nisa.

Duk yadda yaso ya rabasu abu ya gagara, sbd haka sai ya fara kuntatawa Rumaisa, kullum cikin zaginta yakeyi, wani lokacin har da duka yake hada’wa .

Koda aka tambayeshi abinda ya shiga tsakaninsu da ‘yar lelenshi, cewa yayi tana yawan kula ‘yan iskan samari,kuma idan ya kyale lalatata zasuyi.

ita ma matarshi da yaranshi mamaki abin ya shiga basu, amma matar fa taji dad’in yadda al’amarin ya Juyawa Rumaisa, dan gani take ta takurawa rayuwarta data ‘ya’yanta.

Hanata fita ko ina yayi, snn idan ya fita Shima baya wani jimawa yake Dawowa gida, duk ya hana kanshi sukuni.

K’arshe ganin raba Rumaisa da Kabeer ya gagara sai yaje gurin mahaifin Kabeer yace mishi, yazo sanar da shine,
Muddin aka ga Rumaisa ta lalace ,to Kabeer ne ya lalatata, shi kam yayi iya kokarinshi abu ya gagareshi, dan haka BABAN Kabeer d’in ma ya jawa Kabeer kunne akan Rumaisa dan shi Sam bai yarda da tsakaninsu ba………
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W..

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*Wannan shafin nakine Habiba Muh’d Abdullah.*
Ke mai k’aunatace na sani, Allah ya bar mu tare.

*9*.

Tashin hankali sosae BABAN Kabeer d’in ya shiga, kiranshi yayi ya nuna mishi b’acin ranshi a kan tarayyarsu da Rumaisa, har yana ce mishi wai shi da ya kamata ya kula da ita ya hana ta Kula samari,amma shike kokarin lalata mata rayuwa, to duk abinda ya b’ullo yayi Kuka da kanshi.

B’acin ran da Kabeer ya shiga baya misaltuwa dan tabbas yasan aikin kawune, wanda su kuma suke kira da Bappa.

Daga nan suka shiga ‘yar tsama da Bappan nashi, k’arshe dai da yaga zaman gidan ba mai yiyuwa bane a gareshi ya tattara ya koma gidansu.

Hakan kuwa yayiwa Kawu dad’i dan a cewarshi ya huta da ganin abin takaici.

Rumaisa ko bata ji dad’in hakan ba amma babu yadda ta iya, ta kuma tambayeshi dalilin barin gidan yace mata, haka kawai.

Yanzu ita ke yawan shiga gidansu Kabeer, duk yadda Baban Kabeer yasa hankali a kansu dan fahimtar irin alakar dake tsakaninsu, bai ga wani aibu a ciki ba, k’arshe dai ya bisu da Addu’a, Allah ya kare mishi su dukansu.

Da kawu ya gane yawan shiga gidan su Kabeer da ta keyi nanma Ya sa mata kahon zuqa.
Basu samu sukuni ba saida Kabeer ya samu aiki a specialist hospital, a Matsayin gyenea Doctor.
Zuwa aikin da yake yi ne ya sa ba ko Yaushe suke samun had’uwa ba.

Wani abin mamaki shine, yanzu duk gatan da kawu keyi wa Rumaisa, bai hanata Yunkurin guduwa ba, sau biyu yana kamata tana shirin guduwa, hankalinshi yayi bala’in tashi.
K’arshe ya kira meeting ya sanar da ‘yan uwanshi halin da ake ciki, har ce musu yayi shi yana tunanin wani ne yake Hure mata kunne, ko kuma yawon banza take so ta tafi.

Da aka tambayeta cewa tayi ita gidan take so ta bari.ta gaji da gidan.

Cikin tashin hankali ya fara kumfar baki yana cewa, dan taga yana takurata yana hanata tsayuwa da samari shi yasa take so ta bar gidanshi.

Da kyar aka lallab’ata ta zauna bayan dogon nasihar da ta sha a gun Iyayennata.

Daga nan wata sabuwar kulawa take samu daga wajen Kawu,kullum cikin rarrashinta yake, komai nata daban ne a gidan, ya zamanto ko abincin da za’a dafa sai wanda ta zab’a.

Sosae hankalin matar kawu ya tashi taje ta fad’a wa iyayenta.
Kiranshi sukayi suka mishi magana akan hakan.

Da ya dawo gida kuwa saida ta gwammaci da bata kai kararshi ba dan sosae ya ci mata mutunci har Kaurace mata yayi na sati biyu.

Gaba d’aya gidan ya zama ba dad’i, yaran gidan yanzu Suma mugun jin haushin Rumaisa sukeyi dan a cewarsu ita take haddasa duk wata fitina dake Tasowa a gidan. Tun da yanzu kawu ko da yaran da ya Haifa yaga Rumaisa sai yayi ta zaginsu.

Ranar da Kabeer bazai tab’a mantawa ba a rayuwarshi, Ranar da ya sa mata suna da bak’ar rana, wata ranar talata, tunda Kabeer ya tashi yakejin jikinshi ba dad’i, sakamakon mafarki da yayi da daddare wanda ya gagara gane kanshi.
Sai kuma fad’uwar gaba da ya sashi a gaba.

Da kyar ya shirya ya tafi wajen aiki, ko da ya je ma ya kasa sukuni, aikin ma gaba d’aya ya gagareshi, jin jikinshi yake a mace.

Fitowa yayi daga asibitin ya dawo gida, gidan kawu ya fara shiga ya tambayi labarin Maisa, akace mishi yanzu suka fita da kawu khamis.

Gidansu ya shiga nan kuma Maman shi ta ce mishi d’azu Rumaisa ta shigo bata sameshi ba.

D’akinshi ya shiga ,ya zauna, ya rasa gane abinda yake damunshi.

Alwala yaje ya d’auro yayi nafila, tare da addu’a, kafin ya fita ya kama hanyar komawa asibiti, yana maimaita Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji uun, sbd fad’uwar gaba da ta dameshi.

Yana parking ya fito ya nufi hanyar office d’inshi.
Hankalinshi ne ya gagara Kwanciya ganin yadda mutane suka taru a emergency unit, ga dukkan alamu accident victims aka kawo.

Har yayi kamar zai wuce sbd in wnn ne Sun saba gani, amma abin mamaki sai wucewar ta gagareshi.

Gurin mutanen ya kutsa sai gani yayi ana daga wata da alama suma tayi ga jini kuma yana bin jikinta.

Dubawannan da zaiyi sai ganin Rumaisa ce a sume.

“Subhanallah. “yace da ka’rfi cikin azama kuma yasa hanu ya karb’eta bai damu da sauran da ake kokarin d’auka a gun ba.

Hankali tashe ya shiga da ita aka fara bata taimakon gaggawa, ba wani ciwo sosae taji ba, goshinta ne ya fashe, sai hannayenta da suka kwarzane.

Amma abinda ya basu mamaki shine bleeding d’in da takeyi ba kakkautawa.

Kabeer ne ya shiga dubata da kanshi, dan tun d’azu tsaye yake yana kallonsu ba tare da ya sa musu hanu ba.

K’arshe dai ya yanke shawarar ya mata scanning dan gano abinda ya sa ta bleeding.

Abinda ya gani ne ya yi bala’in tayar mishi da hankali, har tuñaninshi ya shud’e na wucin gadi……….

..Toh fans Me Bobbo Kabeer ya gani ne?
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

 

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W..

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*

♣♣♣

*10*.

 

Unbelievable, office d’inne ya shiga juya mishi, take yaji duhu na mamaye idanunshi.
Hanunshi duka biyu ya dafe kanshi dasu tare da rintse idonshi tamau.

Tuni ya fara jin kanshi kamar zai tsage, ya rabu gida biyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button