HAUSA NOVELZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

“Wai Rumaisa da ciki?”

Abinda ya ke maimaitawa a ranshi kenan.

Toh ta ina ta same shi?

Duk Wannan tsaro da Bappan yake mata amfanin me yayi?

Wani shegen ne ya mata ciki?

Wad’annan tambayoyi su yayi ta jerawa kanshi, duk da bashi da amsar ko d’aya daga cikin su.

Ya jima yana zaune a gurin, kafin daga bisani ya yanke shawarar yayi flushing na cikin kawai tun da ya fahimci kamar lalacewa yake sanyi.

Hakan kuwa akayi harda wanki ciki ya mata.

Ward aka kaita, aka d’aura mata drip.
Sai sharar baccinta take, alluran bacci na ta aiki a jikinta.

Office d’inshi ya kulle, yadawo kan kujeran ya zaune tare da d’ora kanshi kan table.
Wasu hawaye masu d’umi da rad’ad’i suka Fara zubo mishi.

Kuka ya yi sosae, kafin yad’an ji sauk’in abunda ya tokare mishi kahon zuciya.

“Why, Baby Maisa, why? Me yasa zaki min haka?
Laifin me nayi da na cancanci Wannan sakamako mai muni?
Me ya kaiki zubar da mutunci da darajar ki ta ‘Ya mace a titi.?
Menene amfanin tsaron da Baffa yayi ta miki?
Me zaki cewa Allah ranar gobe k’iyama.? ”
Surutai yayi ta yi cikin kukan bakin ciki.

Ranar yayi kukan da bai tab’a yin irinshi ba.
Dakyar ya samu yayi controlling na kanshi ya goge fiskar shi, snn ya bud’e drawer ya d’au bak’in eye glasses d’inshi ya toshe idanunshi da shi.

Inda aka kwantar da ita ya je ya tsaya yana K’are mata Kallo.
Ya jima yana zaune yana kallonta yana rasa gane wace irin Tunani zaiyi akan ala’marinta.

Yarinyar da ya zab’a ta zamo uwar ‘ya’yansa.

Yarinyar da tun tana k’arama yake mata matsanancin so.

Yarinyar da ya rayu da k’aunarta.yau itace d’auke da cikin wani kuma ba ta hanyar aure ba.
Hawayen da suka sake zubo mishi ya sa hand kerchief ya goge.

Sai daga baya ya yi tunanin ya kira gida ya sanar da su.

Anan suke fad’a mishi Suna hanya, yanzu aka fad’a musu Maisa da Kawu khamis sunyi accident.

Sai a lokacin yasan tare da kawu abin ya faru dan shi baima Kalli sauran victims d’in ba ,hankalinshi na ga Rumaisa.

Dakyar ya ja kafafunshi ya fita don uwa duba Baffanshi.

Acan suka had’u da iyayenshi suka shiga tare dan dubashi.

Daga bisani suka koma wajen Rumaisa.

Bai sanar da kowa ba saida ta warke bayan an sallameta, ya samu mahaifinshi ya sanar da shi abinda ya faru.

Iya kad’uwa da tashin hankali Babansu Kabeer ya shiga.
Kallon Kabeer yake kamar wadda yaga bakuwar fiska hardai Kabeer ya tsargu da kallon da Babbannashi yake mishi, ya fara tunanin ko dai bai yarda da zancen shi bane.

Numfasawa, Babanshi yayi kafin ya fara jera kalmar Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji uun.
Har sau uku.
Kafin ya bi da.

Allahumma ajirnii fii musiibaty wa’akhlifnii khairan minhu.

Sai da ya kuma d’aukan lokaci kafin yaji mugun bugun da zuciyarshi keyi ya sassauta.

“Muhammad Kabeer. ”
Yaji babanshi ya kirashi da dakusasshiyar murya.

Tsinkewar zuciyace ta ziyarce shi da yaji yadda babanshi ya kirashi.

“Na’am Baba.”yace tare da d’agowa yana kallon Babbanashi.

“Ka tabbata abinda ka fad’i gaskiya ce ”

“Wlh iyakar gaskiyata kenan, abinda na gani na fad’a maka, ni na mata scanning da hanuna. ”

Kura mishi ido baban ya kuma “Kabeer, Kaji tsoron Allah ka fad’a min gaskiya, kana da wata masaniya akan cikin nan ko babu. ”

A gigice ya d’ago ya kalleshi, “Masaniya kamar ya Baba?”

“Ina nufin, ko kanada alaqa da samun cikin Rumasa’u, dan ku ‘ya’yan yanzu an haife ku ne ba’a haifi halinku ba, sbd haka babu yadda za’ayi a shaide ku, more especially idan akayi la’akari da yawan kawo karar ka da Baffanka yakeyi game da tsakaninka da Rumasa’u…….

 

*Wnn shine ana wata ga wata, Bobbo Kabee yashiga tsaka mai wuya.*
[8/12 15:07] ‪+234 803 793 0727‬: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*

*Fasaha Online Writers.*

F. O. W.

*Anty Rukie (Mmn Abduljalal )*

♣♣♣

*11*.

A take wani irin b’acin rai, bak’in ciki, da kuma tsantsar kiyayyar da tsanar kawu da Rumaisa suka ziyarce shi, more especially, Baffa khamis, ji yake kamar ya shakeshi sai yaji Kamshin lahira tukun ya sake shi.

Jajayen idanunshi da suka rine dan bakin ciki ya d’ago ya saukesu kan babanshi.
Still kallonshi yakeyi ba kakkautawa dan amsar Kabeer kawai yake jira a halin yanzu.

“Baba idan na rantse zaka yarda da ni? ”

“Wallahil azeem bani da masaniya akan cikinnan, idan ba Ranar da tayi accident ba, babu wata alaqa makamancin haka data tab’a shiga tsakaninmu. ”

Ya k’arashe maganar yanaji kamar ya rushe da Kuka.

Ko ba komai Baba ya d’an samu relief, tunda yaji Kabeer ya rantse, amma abin tambayar anan.
Wa ya aikata Wannan aika aikar?

Numfasawa Baba yayi “Naji abinda Kace Kabiru, na kuma yarda, sai dai abinda ya kulle min Kai wa ya lalatawa Rumasa’u rayuwa? ”

Cikin takaici Kabeer yace, “Abinda ban sani ba kenan Baba saidai ko tambayarta za’a yi aji daga bakinta. ”

“Hakanma yayi, tashi Jeka, Allah ya maka albarka, zamu san abin yi.

Musamman Baba ya shiga gidan kanin nashi kawu khamis, cikin lumana ya fahimtar dashi abinda ke faruwa snn ya bukaci a kira mishi Rumaisa.

Cikin tsananin tashin hankali, kawu ya shiga har d’akin Rumaisa ya kirawota.
Tambayar duniyar nan Baba ya mata, amma taki magana sai kuka takeyi, Kuka mai ban tausayi. Har ya gaji ya ce ta tashi ta tafi.

Maida hankalinshi yayi kan d’an uwanshi dake zaune kamar mutum mutumi, da ka ganshi kasan baya cikin hayyacinshi ya shiga Tunani mai zurfi.

Dafa shi Baba yayi.
“Khamis, ina so ka kwantar da hankalinka akan wnn abu da ya faru, kada ka sashi a rai ya jawo maka wata cutar, ka d’auka wnn abu kaddarace babu wanda ya fi karfinta, sai dai muce ,Allah ya kiyaye gaba, amma ni a Tunani na mai zai hana a d’aga Rumasa’u daga wnn gida, ta koma gidana ko gidan yaya saboda wasu dalilai da Basai na tsaya zayyanasu ba yanzu, ko ya ka gani. ”

Hankali a tashe Kawu ya kalleshi.
“Kana nufin wai Maisa ta bar gidannan? ”

Gyad’a mishi kai yai tare da cewa “Eh, haka nake nufi. ”

Girgiza kai ya shiga yi “Bazai yiyu ba Yaya, Maisa baza ta bar gidannan ba, yadda na raineta tun tana yarinya haka zata ci gaba da zama har ranar da Allah zai rabamu, wato idan tayi aure ko dayanmu ya mutu. ”

Wani Kallo Baba ya mishi “Wannan magana kakeyi Hamisu, dole Rumaisa tabar gidannan ko don ta samu kula da tarbiyar da ya dace ace ta samu daga wajen uwa wadda babu shi a gidanka, muna da masaniyar tsakanin mai d’akinka da Rumasa’u babu wata shiri, Wannan Kuma ba laifin kowa bane sai naka, sbd haka dole mu sama mata wnn kulawar kafin komai ya gama kwab’e mana. ”

“Yaya Kai ka bani Maisa ne? ”

Ya fad’a cikin b’acin rai.

“Ko ba Nina baka ita ba, dole insa hankali akan tarbiyarta, dan nima ‘ya tace, ka tuna wani hali mahaifiyarta Zata shiga idan taji abunda ya faru da ‘yarta?
Me kake tsammani Zata tuna? Barin Maisa gidannan dole ne ko don ta samu kulawar da ta dace. ”

“Dan Allah yaya ka barni naji da abinda ke damuna, Zan gyara komai da kaina. ”

“Khamis nifa mamaki ma kake bani, duk kulawa da takurawar da Kayi wa yarinyar nan, ya akayi haka ya faru da ita, me zaka iya gyarawa wadda bakayi shi tun da.
Wai ina zafin naka yake?
Ya akayi wani ya lalata mata rayuwa ba tare da ka sani ba?
Waye kuma ya aikata hakan?”

Katse shi yayi da cewa “Nima abunda nakeso na gano kenan, dole na tsaurara bincike dan gano wanda ya aikata Wannan aiki. ”

“Good, amma kafinnan tau Rumasa’u Zata bar gidannan na gaya maka. ”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button