ZUMUNTAR ZAMANI Complete Hausa Novel

A zafafe yace “Wai yaya so kake ka nuna min ba ciki d’aya muka fito da mahaifiyar Maisa ba, kana nufin bani da cikakken iko akanta ne, ko a tunaninka ka fini jin zafin abinda akayi mata ne. ”
“Ko d’aya Khamis, idan ka manta in tuna maka ,nima ba ciki d’aya muka fito da mahaifiyarta ba.
Saboda haka ina magana ne a Matsayin d’an uwan mahaifiyarta wanda yasan zafin ta kuma babu bambanci tsakaninta yaranta da yaran da na Haifa, duk d’aya ne a guri na, so kasan abinda bakinka zai rika furtawa.”
Sosae sukayi ta sa in sa ,kowa ya kafe akan ra’ayinshi.
K’arshe dai yayannashi ya fita ya bar mishi gida dukansu ransu ba dad’i.
Washegari da sassafe sai ga Abba babba da sauran yan uwansu sunzo gidan kawu khamis.
Ganinsu ba k’aramin tayar mishi da hankali yayi ba.
Baban Kabeer yaso ayi komai cikin rufin asiri ba tare da kowa yaji ba, amma abin ya faskara, dole ya nemo sauran yan uwanshi, dan ya kudurta a ranshi dole Rumaisa tabar gidan kawun .
Sosae Maganar ta girgiza su,lokacin da ya gama yi musu bayani, snn ya d’ora da buk’atarshi naso a d’aga Rumaisa daga gidan da kuma dalilanshi.
Dukansu sun gamsu da dalilanshi, sun San mai afkuwa ta riga ta afku, amma dole su d’au mataki saboda gaba.
Sam kawu yaki amincewa, tun Suna magana kasa kasa har hayaniyarsu ta fara shiga kunnen matar kawu, da sauri ta kora yaran su tafi makaranta, snn tazo ta lab’e dan jin abinda yake faruwa.
Ta kuwa Jiyowa kanta abinda ya d’aga mata hankali, ga kawu ya dage baza’a d’aga Rumaisa daga gidanba.
Bata San lokacin da tayi Wuff ta shige falon kawu ba, sai jinta suka yi cikin masifa tana cewa, ” gwara ma ka barta ta tafi dan wallahi bazan zauna da karuwa a gidana ba.”
Tass kawu ya d’auke ta da Mari, cikin b’acin rai, jikinshi har rawa yakeyi .
“Ba Mari ba ko kasheni zakayi bazan zauna da itaba, idan kuwa Zata zauna saidai ni nabar maka gidan. ”
Ta fad’a cikin Kuka, kuma tana dafe da kuncinta da yasha Mari.
Yana huci yace “Uban wa ya hana ki tafiya, ga ki ga hanya, Alla raka taki gona,indan Rumaisa kike cewa baza ki zauna ba, Kiyi tafiyarki, Wannan matsalarkice. ”
Cikin b’acin rai da d’inbin mamaki, Abba babba yace “Hamisu kana da hankali kuwa, Akan Rumaisa zaka rabu da uwar ‘ya ‘yanka, to, ba damu za’a yi Wannan rashin hankalin ba, Rumaisa kuma dole tabar gidannan. ”
Da gudu ta fita daga d’akin taje ta kira mamanta a waya.
Gaba d’aya kawu ya fita hayyacinsa ya rasa wani mataki zai d’auka akan raba shi da Rumaisa da ake son yi.
Zama yayi dab’as a k’asa yace “Na yarda Zata bar gidan amma ku barni na maidata gurin mahaifiyarta da hanuna. ”
“Idan ka mayar da ita Kace mata me, fad’a mata zakayi dan baka da hankali, idan abun bai baka kunya ba mu abun kunya ne a wajen mu ace duk yawan mu mun gagara rike Rumaisa, mun kasa bata Tarbiya, saida ta lalace muka mayar da ita, babu inda zata Je, mu nan zamu riketa mu aurar da ita da yardar ubangiji kuma cikin rufin asiri.”
Suna cikin haka sai jin Maman matar kawu ta shigo tana bambami, ita dole a fitar da Rumaisa idan ba haka ba ta tafi da ‘yarta.
Fita suka yi zuwa inda take ta fad’a suka shiga bata hakuri, shi kuwa kawu zama yayi cikin falon ya dafe kanshi.
Baban Kabeer ne ya shiga d’akin Maisa dake kwance tana ta Kuka kamar ranta zai fita, duk abinda suke yi tana jiyosu.
Abubuwa uku ne suka had’e mata,.
Ga takaicin abinda ya faru da ita .
Ga fita harkarta da Kabeer yayi. Snn
Ga kuma rikicin da iyayen ta sukeyi, wanda tunda take bata tab’a gani ko jin labari ba kuma duk ta dalilinta ake yinshi……..
[8/12 15:07] +234 803 793 0727: *♣ZUMUNTAR ZAMANI♣*
*Fasaha Online Writers.*
F. O. W.
*Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
♣♣♣
*12*.
Da Sallama ya shigo d’akin, duk da ta gane mai sallamar hakan bai sa ta d’ago ba, sai wani sabon Kuka da ya kufce mata.
Duk da yaji zafin abinda ya faru amma Yana tausayawa Rumaisa dan cutuwa kam ta riga ta cutu, abin haushin shine rashin sanin wanda ya cutar da itan.
Zama yayi kusa da ita ya dafa kanta.
“Rumasa’u.”
Bai saurari amsar ta ba, itama kuma bata amsa ba amma ta sassauta kukan.
“Kukan ya isa haka, sai kijawa kanki wata cutar, yanzu ba lokacin Kuka bane, dan kin riga kin b’ata wayonki, kin lalata rayuwarki, Kin cuci kanki da yaran da zaki Haifa nan gaba dan Suma abinda kika aikata saiya shafesu, tunda koyaya sai an gaya musu abinda uwarsu ta aikata, kuma dole ya musu zafi, idan ba wani ikon Allah bama su tsane ki. ”
“Shawarar da Zan baki a yanzu itace ki dage da yawan istigfari, ki roki Allah gafara dan shi gafurur raheem ne.
Snn sharrud’an tuba sune, yin nadama akan abinda ka aikata, bayan haka ki k’udura a ranki baza ki kuma komawa zunubin da kikayi ba, kuma ki tsaya akan hakan har k’arshen rayuwar ki.
Wnn shine shawarar dazanbaki a matsayinki na ‘yata. ”
“Sai kuma abu na gaba yanzunnan ba sai anjima ba nakeso ki tashi ki tattara kayan ki Zan maida ki gidan Abba babba. ”
Ba musu ta tashi ta fara tattara kayanta, tana sauke ajiyar zuciya, tass ta kwashe duk wani abinda ya zama mallakinta, ta cika akwatunanta uku , da babbar jaka d’aya.
“Na gama kawu.”tace kanta a kasa, dan ita yanzu Kunyar had’a ido da kowa ma takeji.
Tayata yayi suka tattara kayan kaff, suka shigar cikin motar k’anin Su d’an autansu, daga nan ya umurceshi da ya kaita gidan Abba babba.
Saida suka ga fitanta hankalinsu ya kwanta suka daina tada jijiyoyin wuya, kafin mamanta ta tafi saida ta k’ara zugata akan kada ta sake a kuma dawo mata da Rumaisa gida.
Tunda kawu ya fahimci Maisa bata gidan ya tabbata Sun d’auketa, daganan ya tsiri fad’a akan banza da wofi, k’arshe ma Boys quarters ya koma a can yake Kwana.
*************
Tunda ta koma tabi ta takura kanta, ko yaushe tana kunshe cikin d’aki.
Sosae Mamma matar Abba babba take kokarin janta a jiki da kwantar mata da hankali.
Abu na farko da ta fara lura dashi game da Rumaisa shine, ko d’aurin zani bata iya ba.
Kullum cikin skirt, tops wando, three quarter, English gown, mostly kayanta English wears ne.
Idan ka ga atampa ,lace ko material, to d’inkin gown aka mata ko kuma riga da skirt.
Abu na biyu shine, babu abinda Rumaisa ta sani ta fannin girki, ko tafasa ruwa bata iya ba, ga d’an banzan ganda, bata son aiki sam.
Musamman Mamma ta aika aka saya mata atamfofi guda hud’u ta bada aka dinka wa Rumaisa.
Lokacin da aka nunawa Rumaisa kayan kamar ta fashe dan haushi, ji take kamar ta rusa ihu.
Gun koyon d’aurin zani, abin takaici abin dariya, idan ta d’aura ta fara tafiya saidai Aga ta wuntsila, sbd yadda zanin yake hard’e ta.
Saida aka dibi kwanaki masu yawa ta iya d’aura zani.
Maganar girki kuma saida da kyar ta yarda take shiga kitchen tare da masu aiki tana ganin yadda suke sarrafa kayan Abinci .
Shara, wanke wanke, wnn duk bata sansu ba, dan ko d’akinta tana da mai share mata shi a gidan kawu.
Hakan yasa Mamma ta hana kowa share mata d’akin da aka bata a gidan, gata kuma Sam bata son datti.
Tun tana Shara da mopping tana Kuka har tazo ta saba .
Wnn ba komai ya jawo mata shi ba sai rashin kula daga b’angaren mace wacce Zata zamo mazamin uwa,koda bata tare da Tata uwar, wacce Zata bata tarbiyyar da ya dace ace ta samu daga wajen Tata uwar, wacce Zata bata shawarwari game da abinda zai amfaneta a rayuwa.