NOVELSUncategorized

NAJEEB 32

Ibtisam tashi tayi dakyar ta mi’ke tayi toilet domin ta wanke jikinta tsaki tayi mara sauti domin tunawa da tayi toh Ina zata samu pad, koda ta shiga toilet din abun mamaki ba jini ta gani ba, Ruwa ne fari Mai yauki yake zubar mata shine yake bi Mata k’afa, zama tayi akan toilet tana tunani toh mai yasa cikinta yake ciwo kuma ba period bane?? 


Tsaki taja tare da fad’in Aiko dan irin abunda wancan mugun yayi mata dole cikinta yayi ciwo 

Wani hawaye Mai zafi ne ya zubo mata a ido tunawa da tayi yanzu NAJEEB shine yayi dis virgin d’inta ba kabir ba, hawaye take Sosai tare da k’ara tsanar NAJEEB, lokaci d’aya ta tashi tayi wankan tsarki ta fito tasa kaya yanzu cikin Nata ya d’an lafa mata, dama ya murd’a ya lafa haka yakeyi 

Rigan daya cire mata shita maida tunda bacci zatayi, kallon gadon d’akin tayi wanda duk zanin gadon ya fita kaman sunyi dambe akai, tsaki taja ta Fara gyara gadon, ga yunwa Tana ji, gashi kuma tana son taji kamshin turarenshi tsaki tai taja tare da fad’in Wlh yunwa nake ji, ni ya kawo min tea insha 

Haka ibtisam taita zama tana tsaki, domin wani irin mugun yunwa takeji gashi ga kanta dake mata ciwo, wanda tasan tana cin abinci shikenan zai warke 

Tashi tayi ta nufi fridge d’auko 5alive tayi ta bud’e tare da kafa kanta Tana sha, tana cikin sha ta cire bakinta tare da nufa toilet ta Fara amai tana cikin amai din NAJEEB ya shigo d’akin 

Kai tsaye toilet din ya nufa tare da kamota yana buga mata baya, idonta duk ya firfito waje, alaman wahala 

Kuka ta sakar mishi tana fad’in dan Allah ka maidani skul, wlh banda lafiya kuma ni a nan bana samun abincin da nake so inci in koshi 

Najeeb kallon ta ya tsaya yayi tare da fad’in come out muje kisha tea din 

Ibtisam binshi tayi ta zauna akan gadon d’akin, tare da d’aura hannunta akan fuskanta tana nishi sama sama, idonshi na kanta gaba d’aya ya rasa wannan wani irin Abu ke damunta haka….  Nocking din da akayi yasa ya nufi kofa tare da anso heater da yasa a Kawo da kayan tea din 

Shida kanshi yasa ruwan zafi tare da fad’in tashi ki had’a…. 

Da sauri ta mi’ke kaman dama jira take, d’aukan cup din tayi ta zuba madara Sosai tare da Nescafe sannan tasa suger, ruwan Bayan ya tafasa ta had’a tea din ta farasha Tana kashe ido alaman tana jin dadinshi 

Najeeb dai wayarshi yake dannawa,lokaci d’aya ya tashi yahau kan gadon d’akin tare da kwanciya 

Kamshin turaren shi ya bugi Hancinta, ido ta lumshe tare da ajiye cup din tea din, Tana d’aga hanci dan taji kamshin dakyau 

Tana cikin haka NAJEEB ya waigo tayi sauri ta juya 

Baki ya tabe tare da fad’in off the lights 

Ibtisam kashe wutar tayi tare da kwanciya ta juya baya domin tasan dole a nan zata kwana, cikin ranta babu komai sai haushin NAJEEB tare da tsananshi domin ya bata mata rayuwa da kuma tsari gaba d’aya, Dan budurcin da take ta tattali takai gidan kabir gashi ya rushe mata shi, ido ta lumshe cikin jin zafin abunda yayi mata 

Bata dad’e ba bacci yayi gaba da ita 

Shi kam NAJEEB gaba d’aya ya kasa bacci ba komai yake tunani ba sai yanda zaiyi maganin matsalan ibtisam shidai yasan bawai Sonta yake ba, amma yana da kishi tunda an d’aura mai ita AI dole yayi hakuri, dan haka bazai iya barinta ta zauna a skull ba Tana hulda dako wani namiji, ganinta yayi sanda take zaune da Salees suna ta dariya dan tsaki yayi tare da fad’in Anya tana tuna tana da aure kuwa??? 

Hmmm dole inyi maganinta, only 1 tin zan mata wanda duniya zata San itafa matar aure ce, inma tana boyewa ne, abunda zan mata shine Ciki, I will make sure in Mata ciki kafin inbar k’asar nan, dole in k’ara kwanaki just to pregnant her, murmushin mugunta yayi duk da shima bawai yana bukatar haiyuwa bane amma Just kawai Dan yayi hurting ibtisam dole yaso haiyuwa yanzu 

And zai barta tayi karatu but Indai ta samu ciki aiya gama da ita, a cewar shi 

Wannan tunanin da yayi yasa yayi bacci cikin nishad’i 

Ibtisam kam ba ita ta farka ba,  sai wajan asuba kaman kullum tunda ta saba tashi, Kai tsaye tashi tayi ta shiga toilet tare dayin alwala har zata Fara sallah ta fasa tare da nufan NAJEEB ta Fara Tashin shi.

Najeeb dan bud’e ido yayi tare da fad’in what? 

Tace sallah 

Tsaki yayi tare da fad’in naji just leave me karki k’ara tashi na idan ina bacci 

Ibtisam cikin ranta tace Allah ya shirya, nidai na fita hakkinka

Sallah ta farayi Bayan ta idar ta tashi ta nufi fridge tare dashan ruwa sannan ta koma ta kwanta, tana kallon NAJEEB daya juya mata baya wani irin tsanarshi taji tana k’ara karuwa cikin ranta, tare da fad’in an kira sallah amma shi ko a jikinsa Hmmm Allah dai ya kyauta ya shirya shi, andai yi Asara Wlh shaidan ya gama dakai, nidai an cuceni da aka had’ani da wannan mashayin mara ibada, toh miye maraban Arne da musulmi??  A hankali ta furta sallah, kenan NAJEEB shiba musulmi bane tunda baya sallah, wayyo na shiga uku na lalace Wlh an batamin rayuwa nidai 

Wannan wace irin kazamar rayuwa yakeyi haka,? Babu sallah babu salati, sannan saiya kira kanshi musulmi??? 

Anya NAJEEB kodai yayi ridda NE? 

Domin dai musulmin kwarai bazai sha giya ba, musulmin kwarai bazaiji ana kiran sallah ba ya kasa tashi yayi ba, kenan baccin yafi mishi amsa kiran Allah? Innalillahi’wa inna ilaihirajiun..

Lokaci d’aya ta Fara bubbuga Shi tana fad’in ka tashi kayi sallah, ka tashi kayi sallah an kira sallah fah 

Najeeb tashi yayi tare da tureta yana fad’in I thought I warn you karki k’ara tashi na idan ina bacci?? 

Ibtisam tace ka fad’a amma idan akan sallah ne saina tasheka, NAJEEB sallah fah…

Yace enough ina ruwanki dani,?  Am warning you karki k’ara shiga rayuwata 

Ibtisam tace shikenan naji but set me free

Wani irin kallo ya watsa mata tare da tashi ya shiga toilet, yayi alwala ya fito yayi sallah 

Bayan ya idar ya tashi ya dawo yazo ya kwanta akan gadon ba tare daya kalleta ba 

Ibtisam tsaki taja Mai sauti saboda ba’kin ciki….. 

Najeeb lokaci d’aya ya janyota tare da matseta, duk yanda taso ta kwaci kanta ta kasa domin gaba d’aya bai mata ri’kon wasa ba.

Ibtisam tace ka sakeni, bana so.. 

Najeeb Banza da ita yayi ba tare da yayi magana ba 

Itama jin yayi Banza da ita tasan bazai saketa ba, dan haka tayi shuru tare da nutsuwa Tana sauraran kamshin turaren jikinsa 

Bata dad’e ba bacci ya d’auketa

Najeeb ganin tayi bacci yasa ya kura mata ido tare da kallon fuskanta, yakan rasa mai yasa Idan ya kura ma fuskanta ido sai yaji gaba d’aya jikinshi na mishi wani irin motsi, idonta dake rufe ya kura ma ido yana kallo,  lokaci d’aya idonshi ya sauka wajan bakinta murmushi ya saki wanda bai San yayi ba, domin ganin bakin Nata k’arami sai rashin kunya 

Gaba d’aya najeeb ya kasa bacci sai k’are ma jikinta kallo yake yana mamakin irin surar jikinta wanda bai taba expecting ba, danshi gaba d’aya ya raina ibtisam bai taba tunanin tana da nono da duwawu haka ba, danshi bai taba tunanin ko kirgan dangi ta Fara ba, koda yake ba kallonta nake ba lokaci d’aya NAJEEB ya kwantar da ita akan gadon tare da cireta daka jikinshi, tashi yayi yasa wasu kayan sannan ya fita 




KANO

Granny ce zaune tana fad’in ni yanzu wlh gaba d’aya hankali na ba’a kwance yake ba wlh 

Ummi tace Dame kuma mama? Ko bakya jin dad’i ne?? 

Granny tace inda bana jin dad’i Aida kin ganni a kwance ina lullube, amma kin ganni a zaune kina wani fad’in ko banda lafiya ne 

Ummi murmushi tayi domin Granny ita babu Mai iya mata sai jikokin ta 

Granny tace ni Wlh gaba d’aya tunanin ibtisam nake, Kun tashi kun turata makaranta irin haka Idan yarinya ta samu k’aruwa sai taje tasha wani magani bata san ciki gareta ba 

Ummi tace toh mama Ai bata da komai 

Granny tsuke baki tayi tare da fad’in tunda Kinje kin ganta ba? 

Ummi shuru tayi tana sauraran Granny, domin ta lura yau da fitina ta tashi, dan haka take wani zubin saita tashi taita fad’a akan an tura yarinya karatu kaza da kaza 

Granny ta Katse ummi da fad’in ni yaushe zasu dawo gida nema?? 

Ummi tace sun Kusa Fara jarabawa ai, suna gamawa sai hutu 

Granny shuru tayi lokaci d’aya kuma tace kiramun ibtisam din 

Ummi kiran ibtisam tai tayi bata d’aga ba, dan haka tace hala tana aji ko tana bacci 

Gefen kabir tunda ya daina d’aukan wayar ibtisam, kullum yana cikin damuwa, ganin garin Kano ya mishi zafi yasa ya tattara shida hafsat suka koma Abuja da zama kawai 

Gidan daya gina a Kano yace bazai saka hafsat a ciki ba, domin bada sunanta yayi ginin ba, ran iyayenshi ya baci akan yana hauka ne da zaice haka? Shidai KABIR ya kafe harda wannan dalilin yasa ya d’auketa suka koma Abuja 

Abban ibtisam ya kira kabir akan yana son magana dashi, kabir yaje ya amsa kiran Abba inda Abba ya bu’kaci ya fad’i abunda ya kashe a akwatin daya had’ama ibtisam domin a bashi kud’in 

Kabir yace yabar mata akwatin halak malak, sannan ya k’ara duk da ban auri ibtisam ba, ni nasan haka Allah ya nufa, komai na bata ya zama Nata, ibtisam tafi karfin wannan akwatin a wajena 

Abba ganin haka yasa yace a’a bari toh a bashi kayan, dama akwai wanda tayi amfani dasu sai yasa muka yanke duka mu biya 

Kabir yace Abba Idan aka bani wannan kayan an nuna min ni bare ne bad’an gida ba, wlh Abba in inada abunda yafi wannan zanba MA ibtisam domin tafi karfinshi 

Abba yayi mishi godiya tare dasa mishi albarka 

Bayan KABIR ya fita gaba d’aya Abba tausayin yaron ne ya kamashi ganin yanda ya rame Sosai, kaman bashi ba, Allah sarki rayuwa kenan, kana naka Allah na nashi, duk Wanda ya maka wannan Sharrin da makircin Allah zai saka maka ko Waye, insha Allah 

Kabir gaba d’aya ya kasa amsar hafsat a matsayin mata, domin shi gaba d’aya baya son koda jin magananta, danshi so d’aya yaba ma ibtisam, domin indai ibtisam na Raye baya tunanin zaiso wata mace bayanta, Kai koma Bayan ranta wanda baya fatan ta rigashi barin duniyar yafi son shiya rigata barin duniyar 

Kabir gaba d’aya ya canza Abu kad’an fad’a, sannan bai cika son magana ba yanzu, shida kanshi yakan ji tausayin hafsat domin tana mishi duk wani abu daya dace mace tama miji, sai dai shi gaba d’aya ya kasa biya Mata hakkinta dake kanshi, Wanda shida kanshi yasan yana cutarta toh amma ya zaiyi?  Gaba d’aya zuciyarshi da idonshi bata kaunar kallon wata mace Inba ibtisam ba, lallai so mugun ciwo ne lallai so masiba ne, bai taba tunani a rayuwa zai shiga irin wannan matsanancin halin ba akan so, ibtisam Tana da waje Mai girma cikin zuciyarshi da rayuwarshi, amma yaya iya dole ya amshi kaddara data fad’a mishi…. 

Yana zaune shi d’aya Bayan ya dawo daka office, direct d’akinshi ya shiga ya zauna 

Hafsat ce ta shigo cikin d’akin ta sameshi idon shi, na kallon k’asa 

Kiran sunanshi tayi da my barrister 

D’agowa yayi tare da kallonta, lokaci d’aya kuma ya kuma yin k’asa da kanshi. 

Dan murmushi tayi tare da fad’in kazo kaci abinci, naga tun d’azu baka fito ba 

Kabir yace no am OK bana jin yunwa 

Hafsat shuru tayi tana kallonshi Kafin ta kuma cewa, dan Allah ina son ka cire komai ka manta da komai duk da nasan is not easy but Ina son ka sani am your wife, inada hakki a kanka, koda bakai min komai ba ina bukatar fira dakai, ina bukatar dariyanka Ina bukatar yin abubuwa dakai alot, you are my husband plz kabir ka tausaya min kaji tausayi na, Nasan baka sona amma ina son ka amsheni a matsayin kaddara, bazance dole saika soni ba, but plz ka dinga nuna min caring plz am begging you…..  Sai kuma tasa kuka mai ban tausayi 

Kabir shuru yayi amma jikinshi yayi sanyi which yasan abunda hafsat ta fad’a gaskiya ne, tabbas Tana da hakki a kansa, in ba haka ba, yasan Allah bazai barshi ba, Allah zai kamashi, domin ya tauye mata hakki 

Kabir d’ago dakai yayi tare da fad’in hafsat kibar wannan kukan, insha Allah daka yau I will change 

Kamota yayi tare da d’agota tsaye yace let go and eat 

Hafsat ba k’aramin dad’i taji ba, Sosai,  tun daka wannan ranan KABIR ya canza ya fara sakar ma hafsat, yana biya mata duk wata bukata, kuma yaji dad’in daya sameta a budurwa domin saida jini ya fito ranan daya sadu da ita, duk da bako wace mace ce ke jini ba.

Kabir ya sakar ma hafsat Sosai yana bata kulawa, sai dai fah ya kasa sata cikin zuciyarshi domin ibtisam ce kad’ai a cikinta

Itama da kanta hafsat din tasan haka, and tana matukar kishin ibtisam Sosai, domin tace saboda ita ne yasa mijinta har yanzu baya nuna mata tsan tsar so, sai dai yayi mata fake love

Hafsat tana kishin ibtisam Sosai har take mata fatan dama tabar duniyar kowa ya huta, a cewarta inta bar duniya ai dole ya cireta cikin ranshi 





ZARIA

ibtisam bacci take Sosai sai wajan 10 ta farka tare dayin mi’ka, ta bud’e idonta, lokaci d’aya kuma ta tashi da sauri tare da kallon d’akin taga najeeb baya nan, a hankali ta furta where is he?? 

Tashi tayi ta sauka akan gadon d’akin tare da nufa kofa ta jita a rufe, tsaki taja tare da kallon kofar toilet tace ko yana ciki ne?? 

Komawa tayi ta zauna, jin kanta na Mata ciwo yasa ta tashi danta had’a tea, tasha 

Tana cikin zuba madara aka bud’e kofar, da sauri ta kalli kofar taga najeeb ne ya shigo cikin d’akin, cikin ranta tace A Shema baya nan, ajiye spoon din tayi ta nufi toilet da sauri ido ya bita dashi 

Koda ta shiga toilet brush tayi tare da wanke fuskanta sannan ta fito ta ganshi yana tube kayan jikinsa, kallo d’aya tayi mai ta kauda ido, gaba d’aya tunda ya shigo kamshin turarenshi ya gauraye d’akin, ta rasa ina yake boye turaran, dan tsaki tayi mara sauti, tare da had’a tea d’inta zama tayi akan kujeran d’akin ta Fara sha Tana kashe ido alaman tana jin dad’in tea din

Kallonta najeeb yayi tare da tabe baki yace mai zaki ci?? 

Kaman jira take yayi mata magana tace waina da miya Asa Man shanu a ciki 

Najeeb kallonta yayi lokaci d’aya kuma yaja tsaki tare da fad’in a Ina za’a samo miki? Kin San a hotel basa yin waina, so just change it 

Ibtisam tace ana sai dawa a wani waje, idan aka duba za’a samu 

Najeeb yace I said no, baza kici ba, just tell me mai zaki ci??.. 

Ibtisam tayi rau rau da ido tare da fad’in na koshi bana cin komai 

Najeeb kafad’a ya d’aga alaman I don’t carry, cikin kine ba nawa ba 

Ibtisam ji tayi kaman ta buga mishi cup din dake hannunta tayi saboda takaici da haushi 

Bayan ta gama shan tea din ta tashi ta shiga toilet ta dauraye cup din tare da fitowa ta ajiye, sannan ta koma tayi wanka 

Koda ta fito da kayan jikinta ta fito domin ta manta bata d’auki Wanda zata canza ba 

Najeeb ganin ta fito yasan wanda tayi domin yanda jikinta ya ji’ke da kayan da tasa, ganin ta dauki ledan kayan yasa yayi tsaki tare da fad’in idiot 

Toilet ta koma tana duba wacce zata saka mai dan dama dama, gaba d’aya kayan sai a hankali, tsaki tai taja a toilet din tana fad’in nifa Wlh na gaji, miye na kawo ni nan ya ajiye ni ba tare da son raina ba, gashi inada lecture yau, tsaki ta kuma ja yanzu kowa yake son ya saka wannan kayan ya fita ohon mishi 

Wata riga tasa wanda ta Kalli kanta a madubi, gaba d’aya rigan ana ganin komai nata, da sauri ta cire tare da fad’in Allah ya kyauta insa wannan in fita dashi 

Wata ta d’auka itama dai duk sam makai,amma ita wannan Tana da Dan kauri sai dai samanta wajan nonon da tasa ana ganin tsakiyar nononta domin rigan akwai tsaga a wajan sai kuma ya kamata daka wajan cikinta zuwa duwawunta, rigan ta tsaya Mata dai dai giwa 

Ta dad’e a toilet din kafun ta fito daka ciki Tana tafiya a hankali 

Shikam NAJEEB kallo d’aya yayi mata ya kauda kai, domin baya son ya dinga bada kanshi ta raina shi, danshi bazai d’auki rainin taba 

Ibtisam ganin baya kallonta yasa ta saki tare dajin dad’in hakan 

Kiran waya yayi tare da fad’in shigo da kayan da muka siyo, yana fad’in haka ya kashe wayar, idonshi yakai kan ibtisam dake zaune ta juya mishi baya, gaba d’aya shape din duwawunta ya bayyana cikin rigan, wani irin miyau ya hadiye lokaci d’aya kuma yaji yana bukatar ya taba 

Nocking akayi wanda yasa ibtisam ta waigo ta kalleshi, ido suka had’a Wanda ita yake kallo dama, da sauri ta tashi ta waigo domin taga mai yake kallo irin haka.. 

Wai gawan da tayi yasa nononta dake bud’e suka sauka akan idonshi, da yake dan duniya ne saiya basar tare da fad’in mai zaki ci? 

Ibtisam tace na koshi nace 

Yace OK tare da tashi danya bud’e kofar yana fad’in karki cemin kina jin yunwa anjima 

Ibtisam Hararanshi tayi ta baya, cikin ranta tace kaji dashi nidai kawai Malam ka Mai dani skul 

Najeeb bud’e kofar yayi ya amshi ledoji yazo ya ajiye sannan ya rufe kofar 

Kallon ibtisam yayi tare da fad’in ga kaya nan, wanda zaki iya fita dasu 

Ibtisam kallon ledan daya nuna mata tayi tare da tashi ta nufi ledan ta bud’e 

Jallabiya ne guda biyar different colour and design gaba d’aya size d’inta ne, domin tana saka size 60 tayi mamaki daya kawo mata dai dai size d’inta 

Kallonshi tayi wanda taga wayarshi yake dannawa, tace inada lecture 4 I have to go now 

Najeeb kallonta yayi tare da k’ura mata ido, lokaci d’aya yace bazaki ba, skul din na hanaki zuwa daka yau 

Ibtisam tace akan wani dalili? Nika bud’emin kofa in tafi 

Najeeb yace saboda am your husband 

Ibtisam tace husband indeed, sai Kuma ta saki dariya tare da fad’in am not your wife an d’aura maka ni by mistake, so just divorce me p…. 

Ganin ya taso yasa tayi shuru domin tsoran Karya taba ta, matsowa yayi gab da ita tare da janyota ya rukota da hannunshi huda d’aya, “matseta yayi yana fad’in repeat what you are saying right now 

Ibtisam ganin idonshi na kanta yasa tayi saurin rufe ido.. 

Najeeb fuskanta ya kura ma ido wanda yake jin wani iri a jikinsa, ya rasa mai yasa in yana kallon fuskanta yake shiga cikin wani yanayi, lokaci d’aya ya fara K’asa da kanshi tare da k’ara d’agota yasa bakinshi cikin Nata ya fara kissing d’inta 

Ibtisam kokarin tureshi take amma ta kasa Saida yayi kissing d’inta wajan 3mnt kafin ya saketa tare da d’agota ya k’ara matseta a jikinsa yana fad’in, ki daina bata ma kanki lokaci, me and you will live together forever, babu saki, daraja d’aya kika ci niba namiji bane Mai son tara mata da yawa da saina k’ara aure but may be nan gaba in naga wacce nake so in k’ara aure….. 

Ibtisam tureshi tayi amma ko gezau baiyi ba.

Yace kina bama kanki wahala 

Ibtisam hawaye ke zuba a idonta tace NAJEEB bazan taba zama dakai ba har abada, domin bana Sonka ban….. 

Sakinta yayi tare da sha’ko mata wuya yace same with me, keda kanki kin San bana sonki, nafi karfinki har abada, niba type d’inki bane but what should I do? An cuceni an bani ke, tunda na yarda zanyi hakuri dake kema you must dole ki zauna dani 

Ibtisam da NAJEEB ya shaketa hawaye ke zuban Mata shar shar tace Najeeb zaka iya Yimin Komai Amma Ina son ka sani, bana bukatar zama dakai, ka tausaya min ka sakeni Dan Allah ni nasan bama son juna ku…..  Sakinta yayi tare da marinta k’asa ta fad’i tana kuka 

Shiko najeeb gaba d’aya idonshi ne ya kad’a yayi ja alamun ranshi a bace yake 

Yace I don’t care Either you love me or not, is none of my business infact to hell with your love, the only tin I want you to knw is dat dole ki zauna dani, either you like it or not……  Dan shuru yayi kafin yaci gaba da fad’in and this should be the last and first time in your life da zaki k’ara confronting d’ina kice bakya sona, if that tin happen again….. Shuru yayi tare da lumshe ido, lokaci d’aya kuma ya bud’e yace only God knows what Will happen 

ita dai ibtisam bata komai sai kuka, lokaci d’aya ya daka mata tsawa tare da fad’in keep quiet, nonsense 

Batai shuru ba taci gaba da kukan 

Lokaci d’aya yaji zuciyarshi na karaya domin kwata kwata ji yayi baya son jin kukanta, gashi taki yin shuru dan haka fita yayi daka d’akin 

Ibtisam ganin ya fita yasa ta k’ara fashewa da wani sabon kukan ga kanta na Mata ciwo, wanda tasan yunwa ne, ga cikinta dake son ya fara Mata ciwo 

Tashi tayi dakyar taje ta had’a tea, sha ta farayi da gudu ta tashi tayi toilet ta Fara kwarara amai kaman hanjin cikinta zai fita, zama tayi a akan bath Tana sauke ajiyan zuciya ga idonta daya firfito saboda wahala 

Gaba d’aya bakinta taji yana mata d’aci, abinci taji Tana son ci, kuma dambu taji Tana kwadayi da zobo 

Lokaci d’aya tasa kuka, tunawa da tayi NAJEEB ya fita gashi ya kulleta, kuka take Sosai ganin kanta yana k’ara Mata ciwo yasa ta tashi ta dauraye fuskanta tare da fitowa ta kwanta akan gadon d’akin, lokaci d’aya zazzabi ya rufeta Tana ta rawan sanyi, duk da ta lulluba da blanket 

Shikam Najeen koda ya fita, zama yayi a reception tare da d’aura hannunsa akansa gaba d’aya ya rasa maike damunshi, tunda ibtisam ta shigo rayuwarshi Tana k’okarin ta canza mishi lissafi da tunani.. 

Gaba d’aya tasa yana abunda bayayi, Tana k’okarin kawo mishi damuwa cikin rayuwarshi, shi bai San miye tunani ba ko damuwa amma gashi yanzu ibtisam tasa ya fara wanda kwata kwata bayayi, kanshi yaji yana mishi ciwo, ciwon kai din Sosai dole tashi yayi ya koma ciki domin ya bukatar ya kwanta harya kusa zuwa kofar d’akin ya tuna da ya barta tana kuka sanda zai fita, tsaki yayi ya juya tare da kiran driver akan yazo su fita Dan baya son jin kukan nata ko kad’an 

Ibtisam kam, bacci ta samu ya d’auketa 

Najeeb bai dawo ba sai wajan 3 shima tunawa da yayi ya rufeta yasa ya dawo cikin sauri Bayan yayi mata siyayan abunda zata iya ci 

Koda ya dawo ya ganta a kwance alaman tana bacci, sai yaji ta bashi tausayi a karo na farko, tare da fad’in yasan baccin wahala ne 

Nufan gadon yayi Bayan ya ajiye Mata ledojin, zama yayi a kusa da ita tare da kallon fuskanta ya kura mata ido sai yaga kaman tana kyarma.. 

Taba jikinta yayi da sauri yaji zafi Sosai, yace fever, a hankali ya kira sunanta da ibtisam 

Tace uhm, sai a sannan ya gane ba bacci take ba, 

Yace baki da lafiya ne?? 

Bata bashi amsa ba 

Ganin haka yasa ya d’agota tare da kamota yana son sauketa akan gadon, yace muje hspt a dubaki 

Ibtisam tace plz ka barni  I need only paracetamol, and food 

Jin haka sai yaji ya k’ara jin tausayinta Sosai, ya tabbata tana jin yunwa Sosai 

Yace OK ga waina nan na samo miki, zauna kici Bari inje in d’auko miki paracetamol a cikin mota 

Zaunar da ita yayi tare da kawo mata ledar da aka saka take away, din waina din a ciki ya bud’e mata ledan kamshin wainar da taji yasa ta k’osa ta faraci ga kuma kamshin turaren najeeb din wanda take mutuwar so 

ibtisam tun kafun yace taci ta faraci kaman mayya ci take Sosai, 

Najeeb daya k’ura mata ido sai yaji ta bashi tausayi Sosai, lokaci d’aya ya nufi fridge ya d’auko mata Ruwa tare da fita danya d’auko mata paracetamol din tasha 

Koda ya dawo gani yayi harta cinye kuma wainar Nada yawa, Abun mamaki ya bashi, nufanta yayi tare da bud’e mata maganin gudu biyu ya bata tasha, zata kwanta ya hanata tare da fad’in no tsaya kiyi kaman 10mnt saiki kwanta ba’a shan magani a kwanta 

Ibtisam zama tayi lokaci d’aya kuma ta tashi, da ido ya bita ganin ta shiga toilet yasa ya kauda idonshi daka kanta, kwashe kayan da taci abinci tayi tare da sakawa a wata Leda ya fitar dashi waje 

Koda NAJEEB ya dawo d’akin yaga Tana sallah, da alama sallah azahar take, tana cikin yi aka kira la’asar shima ji yayi yana son yaje masallaci yayi sallah a jam’i

Toilet din ya fad’a yayi alwala tare da fita Bayan ya rufe kofar 

Ibtisam Bayan ta idar kwanciya tayi a wajan, yanzu taji dan dama dama zazzabin Ya fara sauka, ba k’aramin dad’i taji ba da taci wainar daya kawo mata ba, taji dad’in wainar Sosai.

Najeeb ne ya shigo d’akin, ganinta a k’asa yasa shi fad’in lafiya? 

D’ago dakai tayi ta kalleshi Wanda suka had’a ido su duka, itace ta Fara kawar da idonta gefe tare da sauke wani irin ajiyan zuciya 

Najeeb ido ya lumshe tare da fad’in ya zaki kwanta a k’asa? Keda kanki kike janyo ma kanki ciwo, kina fever and you sleep on d floor 

Ibtisam bata kulashi ba sannan bata tashi ba 

Ganin haka yasa ya dauketa cak yayi gado da ita

Shima kwanciya yayi a bayanta, tare da janyota ya rungumota da hannunshi 

Ido ya lumshe yana wani irin sauke ajiyan zuciya, gaba d’aya ya rasa maike damunshi….

Ita kam ibtisam batai kokarin matsawa ba, domin tana shakar kamshin turarenshi Wanda take cewa ya boye ne, tunda duk ta fesa turaren nashi amma bata ji kamshin ba, sai dai a jikinsa take ji, kuma daka ya shigo d’akin take ji ko inya matso kusa da ita 

Gashi wani abun takaicin duk yanda taso ta mishi Abu, saita kasa indai taji kamshin turaren nashi ita da kanta tana mamakin irin sauyin ta, amma tabi bama kanta macijin ciki ke damunta shine yake sata take irin wannan mugun cin, wanda ya wuce misali 

Lokaci d’aya ta kira sunan Najeeb 

Yace plz allow me to slp 

Tace magana zanyi and you must listen to me 

Najeeb tashi yayi ya zauna tare da fad’in mai yasa bazaki banni in huta ba, and kinsha magani Kema plz slp Quickly and allow me to slp too 

ibtisam tace uhm nifa inada lecture 4 gashi time harya wuce 

Najeeb yace tunda Kema kin San time ya wuce so just keep quiet 

Ibtisam tace toh yanzu mai kake nufi dani? Ko a nan zanyi ta zama?.. 

Najeeb murmushi yayi tare da fad’in exactly that is what am thinking 

Ibtisam tace Hmmm, nidai Dan Allah ka barni in tafi 

Najeeb yace ashe kin iya ro’kan mutum 

Ibtisam tace uhm I can apologize Indai zaka barni, inma kana son I should go on my kneel and apologize I can do it, indai zaka barni in tafi I will do what ever you ask 

Kallonta yayi tare da fad’in saboda kije ki dinga hulda da maza right???? 

Da sauri ta kalleshi tare da nanata Kalman hulda da maza as how?? 

Najeeb tashi yayi tare da fad’in I tell you I will never allow you to go to that skul har sai naga kinyi ciki….. 

Ido ta zaro waje tare da fad’in ciki? Gabanta taji ya fad’i gaba d’aya hankalinta ya tashi ita sai yanzu tama tuna da sex din da yayi da ita zata iya samun ciki….  Innalillahi’wa inna ilaihirajiun kodai cikin ma gareni??  Ina yawan Kwadayi tare da cin abinci anyhow gashi 2month kenan banga period d’ina ba….. 

Dira tayi akan gadon tare da fad’in dan Allah NAJEEB Ina son inje hospital ayi min test 

Kallonta yake cikin mamaki, lokaci d’aya yace test??? Wani irin test?? 

Tace plz najeeb bani da lokacin bayani I need to see a doctor plz najeeb Ina son ganin dr dan Allah sai kuma tasa mishi kuka tare da nufanshi ta ri’ke mishi hannu Tana fad’in NAJEEB ka taimaka ka kaini hospital na shiga uku, Allah ba Ameen ba, wayyo Allah na.. 

Najeeb yace ibtisam maike damunki? Cikin damuwa yake mata maganan 

Tace najeeb ina cikin wani hali bazan iyayi maka bayani ba, idan abunda yake tunani ya tabbata Wlh bazan yarda domin kabir….. 

Wani irin tureta yayi daka jikinta tare da sha’ko mata wuya yace how dare you….. 

Shuru yayi na wani lokaci kafin yace how many times did I warn you not to call his name in front of me???. Tell me how many times did I warn you…..  Lokaci d’aya kuma yayi shuru tare da fad’in wait you say you want to go and see doctor for a test and kince bazaki yarda ba Indai abunda kike tunani ya faru what did you mean? And you are calling dat stupid guy name 

Ibtisam shuru tayi tana kuka 

Najeeb jijjigata yayi tare da fad’in mai kika aikata keda shi????? 

Jin tayi shuru yasa ya sakar mata wani Mari cikin tsana tare da fad’in tell me……  Shuru yayi lokaci d’aya yana kallonta hannunshi yasa a kai tare da fad’in no wander but koma miye we should go and see doctor right now for a test…….  Janyota yayi yana k’okarin bud’e kofa ya tsaya lokaci d’aya ya waigo ya kalleta, ganin kayan jikinta yasa ya sakar mata hannu tare da komawa ciki ya d’auko mata d’aya daka cikin jallabiyoyinta ya jefa mata a fuska alaman tasa 

Ibtisam jiki a sanyaye ta d’auki jallabiyan taja shiga toilet tasa tare da wanke fuskanta wanda ya kumbura musamman ta wajan daya mareta 

Koda ta fito ganinshi tayi yana kaiwa da komowa a d’akin, ganin ta fito yasa yaja hannunta sukai waje 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button