MUTUM DA DUNIYARSA 41 – 42

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[41➖42]_*
…………..Aliyu bai samu shigowa gidaba sai wajen sha biyu, gidan yayi tsit
bakajin komai sai k’arar Gen… Da aka kunna, sashen Maimunatu ya nufa, nanma dai tsit yake, komai kuma a kashe, bedroom d’inta ya wuce.
Tana kwance tayi luf tamkar mai barci, amma idanunta biyu tana kuka Mara sauti, jin an bud’e kofar yasata saurin share hawayenta cikin dabara kafin ya kunna wutar d’akin.
Cikin sanyinsa yake takowa gaban gadon yana fad’in “Habibty kalb badai barciba?”.
Maimuna najinsa amma tayi shiru, ya zauna a bakin gadon yana lek’a fuskarta, kasa daurewa tayi tasaki murmushi saboda hannunsa daya tura a rigarta. Hannunsa ta janye tana tashi zaune cikin kumbura fuskar shagwa6a. “Haba dai Yaya barcifa nake amma ka tadani”.
“O ALLAH yaushe wannan malamar tafara koyan k’arya?”. ‘yak’are maganar dajan hancinta’.
Dariya tayi, tace, “Ya gajiyar taro?”.
“Uhm wannan Ku za’a tambaya ai Habibty, yanzu dai ya za’ayi dani?”.
Idanunta tad’an waro waje, “Yaya a wajenmi?”.
“Komaima madam”.
“To yanzu dai tashi kaje kayi wanka ka baza turare kaje wajen k’anwata tana jiranka, nikam sai jango wlhy barci sosai nakeji ga gajiya”.
Matsawa yay jikinta yana murmushi, “Haba hajiyata kod’an wankanma baza’a tausaya amunba yau?”.
Maimuna ta marairaice fuska tana fad’in “ALLAH yaya bakaji jikinaba, ko ina ciwo yakeyi, danma nasamu zazza6in ya saukane fa”.
Cikin tausayawa yakuma rungume ta yana k’ara jinjina mata da k’aunarta mai girma dake kuma k’arfi a ransa, tunda yashigo ya fahimci kuka take, amma kasancewar Matar kwarai saita had’iye ta taresa da farin ciki, shikam yama za’ayi ya wulak’anta wannan baiwar? Ai ta wuce hakan a garesa.
Yanda ya matseta sosai yasata sakin k’aramar k’ara, da sauri ya sassauta Mata rik’on tareda kallon fuskarta, yanda ta tura bakin gaba yabashi damar d’ora nasa akai. Tunma tana zame-zamen bataso harta nutsu tabashi had’inkai.????
Bai bartaba saida ya tabbatar jikinta yay sanyi da zuciyarta sannan ya kwantar da ita yana shafa matashin cikinta daya fara d’agowa.
Addu’ar barci yafara karanto Mata, itadai tanata kallonshi da k’arajin k’aunarsa musamman da kishinsa, tanaji tana gani yau zasu raba shinfid’a, tunda tazo gidan hakan bai ta6a faruwaba sai dai idan tafiya yayi, amma yazatayi? Idan har takasance mai tsannatawa saidai ta saka kanta a musabar damuwa da rashin kwanciyar hankali, dan bata isa yin jayayya da hukuncin ubangiji ba.
Bayan ya shafa Mata addu’ar ya kwanto jikinta, zatayi magana ya d’ora hannunsa saman bakinta alamar tayi shiru. Shirun kuwa tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Iska yafara hura Mata a kunne, ahankali tafara lumshe idanunta, saida yaga barci yafara cin galaba akanta kafin Yakoma Mata tausa, dand’in hakan yasaka nannauyan barci kwasheta, dama gashi gajiya tamata ligif. Saida ya tabbatar barcinta yayi nauyi sannan ya kuma tofeta da addu’oi ya gyara Mata kwanciya ya kashe fitilar ya fice yana murmushin dashi kad’ai yasan ma’anar kayansa.
Nasa sashen yanufa, Wanda ya kasance a tsakkiyar nasu Jiddah, amma shifa falone kawai da bedroom, shima kuma yaune zai Fara amfani dashi, danda a d’ayan bedroom d’in sashen Maimunatu yake, bayan d’aura aurensa da Jiddah kuma ya gyara nasa, dukda bai ta6a kwanaba saikuma yau.
Komai an saka, bakajin komai sai k’amshin sabon kaya Dana turaren da Maimuna ta saka. Baiwani 6ata lokaciba yashiga wanka ya fito, jallabiya Fara k’al mai gajeren hannu ya saka, yad’an saka turare ya fito, Gen… Yaje ya kashe, saima yaga an maido wuta wadda yake k’yautata zaton yanzu suka kawota, canjawa yay sanan ya doshi sashen jiddah.
Garin yakumayin tsitt dan d’aya takusa, sosai ya yaba da k’ok’arin iyayenta, sai fad’ar “Masha ALLAH yakeyi, komai yagama dacewa da sashen.
Saida ya lek’a bedroom d’in farko yaga babu kowa, sai dai nanma komai tsaf yake, ga k’amshi mai dad’i yana tashi. ‘Dayan ya nufa, inda ya hango Jiddah kwance a kan gadon, tawani takure waje d’aya.
Bata dad’e dayin barci ba, dan fuskartama jik’e take da d’anyun hawaye daya kuma tabbatar masa hakan, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana zama kusa da ita, yakai hannu ya d’auke gyalen dayad’an rufe mata fuska kad’an, babu wata kwalliya mai yawa a fuskarta, saima ruwan hawaye dake jik’e da fuskar, murmushi yayi aransa yana jinjina k’aunarta da kuka, akance yacika saurin kuka, amma yalura jiddah senior d’insace.
Yanda jijiyoyin kanta suka tashi saiya fahimci batada isashshiyar lafiya, yakai hannunsa saman goshinta, hakanne yasaka Jiddah farkawa ta bud’e Idonta, da sauri ta tashi zaune jikinta yana 6arin tsorata. Saurin rik’o hannunta yayi dan ya lura tsorata tayi.
“Relax Hajiyar tsoro”.
Dukda ta fahimci shine hakan baisakata nutsuwaba, dan bata Saba kusanci da wani namiji irin hakaba, balle ace sukad’aine a waje. Muryarta Na rawa amalar tahowar kuka tace, ”Inayini?”.
Murmushi yayi yana sakar Mata hannu, sai dai a k’asan ransa yana mamakinta, yanda take masa bai Kama da wadda tata6a aureba, a 6angaren ciwonta kuma Alhmdllh sun sami mafita ai, duk da bazasuce tadawo normal ba lokaci d’aya, ciwo shike shigar Bawa a lokaci d’aya, sauk’i kam sai a hankali.
Kallonsa Yakuma maidawa kanta, tana sanyane cikin lifaya orange da d’igo-d’igon blue, ga ainahin kitson bare-bari akanta, saita koma masa kanuri sosai, ”Kibar kukannan haka dan ALLAH, kingama kanki ciwo yakeyi harma da zazza6i, tashi ki canja kayanki nakawo miki magani kisha”.
Baijira amsartaba yatashi yafita, kukanta tacigaba da rairawa itako, babu abinda kecin zuciyarta sai kewar y’an uwanta da Ummanta, jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta koma garesu. Harya dawo bata motsaba balle ta canja kayan. Baice Mata komaiba ya ajiye kofin hannunsa daketa turiri da magani.
Akwatin da aka kawota dashi ya bud’e, kayantane na sakawa sai kayan barci kala uku a sama, ta farko dai tacika k’ank’anta, sai d’aya kuma wando da rigane, amma sunda kauri, suya fido ya maida akwatin ya rufe yadawo bakin gadon ya zauna kusa da ita sosai.
Jitai kawai ya d’agota ya sakata a jikinsa, duksai takuma daburcewa, baice da ita komaiba yafara warware lafayan jikinta, blue d’in rigar ciki mai dogon hannu databi jikinta ta bayya, saurin kare k’irjinta tayi, dan rigar sosai ta fidda surarta, Sheikh Aliy yay murmushi mai sauti dayin magana cikin rad’a, “Ah Qurratul ain bar wahalar 6oyewa, narigada nagani”.
Ba k’aramin kunya tajiba, dan haka tayi sarin k’udundune jikinta tana gyara lifayar.
“Yi hak’uri wasa nake banga komaiba, tashi ki canja kayan kisha magani ki kwanta ki huta, kinga har d’aya tayi, nanda minti uku kuma zan dawo nacanja miki da kaina idan bakiyiba”. ‘yana gama fad’a yatashi ya fita’.
Dak’yar ta iya sakkowa a gadon, tabud’e akwatin ta d’auki hijjab sannan ta d’au kayan barcin daya d’akko tashiga bayi.
Kusan mintuna goma ta fito hannunta rik’e da kayan data ciren, Aliyu dake zaune ya d’ago ido yana kallonta. Tsaye tayi akusan tsakkiyar d’akin takasa k’arasowa, taa duk’ar dakanta dan sai yanzu ta ganshi.
“Na tasone?”. ‘yafad’a yana k’ok’arin mik’ewa’.
Da sauri ta k’araso har tana had’awa da sassarfa, shi abunma dariya yabashi, amma saiya danne yay guntun murmushi kawai.
Kayan ta d’aura saman akwati kafin tazo ta zauna a k’asa saman kafet d’in dake jikin gadon.
Shima sakkowa yay ya zauna kusa da ita tareda bata tea d’in, kanta dake duk’e ta girgiza masa alamar ta k’oshi.
Hannu yasaka ya d’ago ha6arta, ta lumshe idanunta dan batason su had’a idanu, saukar la66ansa kawai taji a bakinta, dan haka tai masifar rikicewa, jikinta yahau rawa tana yunk’urin zamewa amma babu dama.
Cikin sauke numfashi ya janye bakinsa yana fad’in “To Yaya zakisha yanzu kokuwa nakuma wani abun…….”
Da sauri tace, “Zansha d’in”.
Dariya taso kufce masa yanada yaga tayi da fuska, ga hawaye Na tsiyaya kamar anbud’e fanfo, jikinta kuwa banda tsumar tsoro babu abinda yakeyi. Kofin yakuma d’akkowa yabata, babu musu ta amsa tafara sha, dayake babu zafi sosai dandanan tasha da yawa sannan ta ajiye, bai takura mataba yabata maganin da saida akasha fama sannan Tasha, dan Jiddah batason magani sai dai dole, daka bata magani gara kaimata allura a wuce wajen kawai.
“Tashi ki kwanta to”.
Batayi musuba ta mik’e tahau gadon ta kwanta a mauk’ar takure, addu’a yay Mata ya tofa a hannunta ta shafa, shima ya tofa mata yana fad’in “ALLAH ya tashemu lafiya Amarsu”.
Itadai Jiddah kanta kad’ai ta iya d’aga masa ta lumshe idanu, shikuma yamik’e ya fita harda kashe Mata wuta tamkar gaske. Ganin haka yasata sauke nannauyar ajiyar zuciya da fad’in ”Alhamddllh” a fili..
Aliyu dake tsaye bai fitaba yana jinta saiya Saki murmushi. Baiyi motsiba yanda zata jisa, soyake saitayi barci. Cikin sa’a kuwa yaji numfashinta yafara sauka a hankali alamar tayi barci, dan tattare take da gajiya, ga rashin samun barcin da tai Na kwanakin bikinnan da damuwar mahaifinsu.
Wayarsa ya Ciro a aljihu ya danna, da hasken screen d’in yay amfani yataka zuwa gaban gadon a hankali.
Yaja kusan mintuna uku yana k’are Mata kallo dukda acikin hijjab take, kafin ya sauke numfashi tareda zare Mata hijjabin cikin dabara shima ya zagaya d’ayan gefen ya kwanta yanda bazataji motsinsaba balle ta farka..
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Hajiya deluwa Na hakimce a falo taringajin shigowar motoci ana rabga bud’a, mamakine ya kamata, tamik’e cikeda masifar mak’wafta sun takura musu, harda cewa “koma Ubanwaye ya haihu suka takurama kunnuwanmu?”. Jin hayaniyar tamkar a cikin gidantane yasata lek’awa Mamaki ya kamata matuk’a ganin a harabar gidansunefa, jikinta har 6ari yake ta fito, Cikin daka tsawa tafara tambayar y’an kawo amarya, “Kai lafiya kuka cikamin gida da ihu? Kodai 6atan Kai kukayine?”.
Wata hamshak’iya a cikinsu ta daddage ta callara gud’a kafin ta kalli Hajia deluwa shek’ek’e, “Madam Mijin naki bai sanar dake tauraruwarsa zata shigo baneba?”.
Kan hajiya deluwa saiya k’ara d’aurewa, yayinda can k’asan ranta kewani irin lugud’en tsoro, jikinta sai tsuma yakeyi.
Y’an kawo amarya kam basu kumabi takantaba suka nufi sashen Jiddah na da akabar Deluwa nan tsaye.
Jin tana Neman fad’uwa yasata saurin barin harabar gidan takoma sashenta, waya ta d’auka takira Alhaji garba, harta tsinke bai d’agaba, bata hak’uraba ta sake Kira. Yana d’agawa babuko sallama tahau masa tambayoyi. Tsaki yaja kafin yace, “inma kin kwantar da hankalinki ai gidan zan dawo Na kwana, dan babu angon dazai guji k’amshin a maryarsa a daren farko”.
Baijira cewartaba ya yanke wayar.
Cikin matuk’ar gigita hajia deluwa tayi wurgi da wayarta saman tayis tana huci tamkar wata bajima, wata ashar ta lailayo ta dire da cire d’an kwalinta ta d’aure k’ugu alamar yau akwai bala’i kenan.
⛹♀⛹♀saimun dawo jin yanda za’a k’are????????.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kiran sallar farko Na asubahi malam ya farka.
Hakama Jiddah motsinsane ya farkar da ita, ahankali take karanto addu’ar tashi barci, Sam tama manta a inda take, jinta a kamar ajikin mutum yasata bud’e ido sosai, gabantane ya fad’i jinta d’are-d’are a jikin Sheikh Aliy, tayi k’ok’arin jan jikinta amma saiya kuma rik’eta sosai, wayarsa yajawo a k’asan filo ya danna screen d’in ya kawo haske, ganin hakan yasa Jiddah cusa kanta a k’irjinsa saboda wata masifar kunya data baibayeta.
Idanunsa ya lumshe yana murmushi, baice komaiba ya kunna fitilar wayar sosai dan da’alama an d’auke wuta. Tashi yay zaune, Jiddah ma tasamu tamik’e tareda sauka ta d’ayan 6angaren tai saurin cacumo hijjabinta ta saka tana mamakin yama akai ta cire? Yaushe kuma ya sheikh ya dawo d’akin?…..
Motsin shigarsa bayi yasata waigawa ta kalli wajen, ganin harya shige saita koma ta kwanta tana shak’ar k’amshin turarensa daya barmata.
A haka yafito ya sameta, fuskarsa jik’e da ruwa alamar yayi alwala ya tako side d’in da take, “Kuluwa sarkin kuka a tashi ayi haramar alwala ko”.
Daga kwancen ta d’aga masa kanta, ganin bazata tashiba saboda yana d’akin saiya kamo hannunta ya sumbata sannan ya fice da cemata saiya dawo. Sosai Jiddah taji sumbar har a yatsun k’afarta, ta k’ank’ame jikinta tana matseshi waje d’aya, ga zuciyarta tana wani irin Kai kawo kamar zata fito, (duk abinda baka sababa arayuwa yanada wahalar d’auka) gaba d’aya Jiddah jitake al’amuran malam sunmata girma, tanada ilimi sanin zaman takewar aure, amma ko kad’an ba haka take tunaninsa ba.
Da k’yar ta iya tashi jin ya fice, itama alwalar tayo tazo ta canja kayan jikinta zuwa doguwar Riga.
Aliyu na fita sashen Maimuna ya nufa, zaune ya isketa a bakin gado ta tashi, shigowarsace ta sakata waigowa tana kallonsa, da sauri ta kauda kanta, dan wani Abu taji ya tokare mak’oshinta, atake tafara karanto sunayen ALLAH domin samun nutsuwa, kai kishi yanada zafi, amma tana rok’on Ubangiji yabata jarumtar koyi da matayen Manzon ALLAH wajenyin mai tsafta…….
Hannunta da ya sumbatane ya maidota hayyacinta, ta Saki murmushin k’arfin hali batareda ta kallesaba.
“Gimbiya gajiyarce har yanzun?”.
Kanta ta d’aga masa batareda ta kalleshi d’inba, kamata yay ya mik’ar tsaye.
A hankali tace, “Nagode yaya” ta ra6a ta gefensa tawuce bayi.
Binta yayi da kallo harta shige, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi da girgiza kansa kafin yajuya ya fita.
★★★★★
Aliyu bai dawo gidanba sai da gari yay haske sosai, lokacin har Jiddah ta kammala azkar d’inta ta gyara d’akin tsaf tasaka turare, a 6angaren iya gyara da girki batada Matsala, dan mahaifiyarsu tsaye take a kansu tun suna k’ananunsu, zuwa makaranta da suke bai hanata tsayawa wajen koya musu dukkan abinda zai amfanesuba idan sunbar gabanta, gakuma lecture ta musamman da Yaruwaiya taringama Jiddah gabannin aurenta.
Gawayin nan Na kunnawa ta kunna ta saka turare sannan tafito falo, Masha ALLAH tafad’a kwalla Na cika Idonta dajin k’arin k’aunar Uncle Yahya, basuda abinda zasu biya bawannan dashi saidai addu’a, da kowanne dangi zasu zama irin Uncle yahya da zuminci bai lalaceba a wannan zamanin. Saida ta zagaya har kicin da d’ayan d’akin kafin ta dawo tafara d’an kakka6e kurar daba’a rasaba, dan babu wani datti kam. Tana gamawa takoma d’akin da suka kwana tashiga wanka, alokacinne Sheikh ya dawo, jin motsinta a bayi yasashi komawa nasa sashen.
Maimuna ma dai haka ta dage tahau gyaran sashenta tana hawaye, harga ALLAH taji tananin kishin mijinta a yau fiye da ko yaushe, shikenan yazama nasu su biyu, a fili tace, “ALLAH ka bamu zaman lafiya, kasakamin danganar hak’uri nida y’ar uwata, ka kad’e dukkan wata fitina dazata saka mu fitini adalin mijinmu” da wannan tad’anji sanyi a ranta, tacigaba da gyaranta tana Kama dukkan addu’ar datazo bakinta. Tsaf ta kimtsa ko ina, ta shiga kicin tana tunanin miya kamata tayi musu Na Karin kumallo?.
Tsaf Jiddah ta shirya cikin atanfa ruwan hanta da zanen ganye manya ruwan toka, sai bak’i kad’an daya ratsa, kayan sunmata k’yau, dan d’inkin ya zauna d’as a jikinta, aunty Nafisa ce takaima telanta yayma Jiddah d’inkuna na garari, dan basujira lefeba suka had’a y’an kud’ad’ensu sukai Mata kusan kala ashirin danta samu Na kwalliyar amarci, tunda babu Wanda yasaka ran lefen, saikuma gashi an Kai ana gobe zata tare. Su hajiya Jiddah ba’a iya d’aurin y’an gayuba????????. Zama tayi tanata juya d’an kwalin a hannu, “ALLAH Sarki Zarah, kullum saikin rok’eni na zauna ta koyamin amma nak’i, yau ga ranar hakan a gareni”.
Aliyu dake tsaye a bakin k’ofa yana saurarenta ya murmusa, kafin ya ida takowa ciki bakinsa d’auke da sallama.
Saurin Jan hijjab tayi zata saka amma sai yay azamar rik’e hannunta tareda rankwafowa ta bayanta suka kalli juna ta madubin. K’asa tayi da idonta kunya Na cinta tamkar zata nutse. Hijab d’in ya zare daga hannunta ya maida ya ajiye inda ta d’auka. “Daga yau inhar ba salla ba ko bak’i ko fita na haramta saka hijjab a gidannan madam”.
Kamar ta fasa ihu taji, dan wannan dokar tasa tamata tsauri da yawa, ta ina zata iya zama a gabansa ahaka? Ai da kunya……
Tunaninta ya katse saboda jin hannunsa saman kanta yana shafa kitsonta dayay masifar tafiya dashi, musamman ma Wanda ya zubo gaban goshinta da aka tufk’e ya kwanta luf a fuskarta, bakinsa yakai ya sumbaci kan yana fad’in “سُبْحَانَ اللهِ!
Subhanal-lah!. (Tsarki ya tabbata ga ALLAH.) Juddatulkhair gaskiya kitsonan ya kitsu, اللهُ أَكْبرُ!
ALLAHU akbar (ALLAH ne mafi girma)”.
Murmushi kawai tayi, aranta tana fad’in irin wannan santi haka? Kujimin mutum.
Shidai sai kuma shafa kitson yakeyi da mamakin yandama ta iya zama aka yisa k’ananu haka.
Ganin santin nashi yagaza k’arewa ta zamo ta durk’usa k’asa tana gaisheshi.
“Lafiya lau Amaryar Aliy, barkanki da shigowa gidan Aliyu. Jiya bansamu danar miki maraba ba saboda kina a yanayin da bai kamata a takurakiba”.
Murmushi tad’anyi kanta a k’asa tana kallon k’afarsa zuwa k’afar wandonsa na milk d’in shadda da bata sauka k’asaba sosai.
Kafad’unta ya kamo ya tadata tsaye, “Zauna ni Na d’aura miki d’an kwalin tunda kin kasa ke”..
Jiddah tarufe fuskarta da hannayenta tana fad’in “Na iyafa”.
“To zauna ki d’aura Na gani”.
“To saika fita”.
Y’ar dariya yayi yana zame hannunta data rufe fuskar, yace, “Na takura miki ko?”.
Kasa magana tayi, sai kanta data girgiza alamar a’a, shima bai samu bata amsaba ya zaunar da ita a stool d’in madubin yana k’ok’arin Ciro wayarsa a aljihu da ake Kira………..✍????
_A daina gulmar ya sheikh y’an Groups d’in mutum da duniyarsa????, gashinan baiyi komaiba dai????, duk kunbi kun saka masa ido, shiyyasa yayi kawaici????????⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀_
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????