NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 20

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_

                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[20]_*


    
…………..Tunda suka tafi Uncle yahya keta tofama Jiddah addu’a saboda fisge-fisgen da takeyi da wata Y’ar siririyar k’ara maikama da muryarta ta dishe. a cikin wannan halin malam Alfah ya faka motarsa k’ofar wata cibiyar magungunan musulunci. Shikad’ai ya fita yana fad’ama Uncle yahya yana zuwa.
    Kai kawai Uncle yahya ya iya d’aga masa, idonsa yay jajir yana rik’e da Jiddah daketa fiffisgewa har yanzun.
        Bud’e motar da a kai ya saka Uncle yahya d’ago kansa ya kalli malam Alfah dake k’ok’arin zama a mazauninsa.
      “Baba Malam miya faru?”.
     “An samu matsalane yahaya, malam tajudden baya nan, amma anmana kwatancen wani wajen a Gadon k’aya, dukda shi bawai yana bada magunguna bane, yana taimakawa dai idan yaga abun ya tsananta ne, sai dai na rok’i alfarmar d’aya daga cikin almajiran malam tajudden wani ya rakamu, ga shinan zuwa”.
     “To baba malam muje cand’in, ALLAH ya saka da alkairi”.
     Gosulon da suka fuskanta a hanya yahanasu damar isowa da wuri, Ana sallar la’asar suka iso dai-dai masallacin bisa jagorancin kwatancen Zubairu Almajirin malam tajudden.
      Malam Alfan ne kawai da zubairu suka fito, massalacine babba dake jingine da wani babban gida shima, anguwar tayi tsitt sai sautin karatun salla dake tashi cikin wata sassanyar murya. Alwala su malam Alfah sukayi suma suka shiga sallar, amma Uncle yahaya yana wajen Jiddah dan ba’a barta ita kaid’aiba..
     Bayan an idar mutane suka fara fitowa d’ai-d’ai, sai da kowa ya fito, aka bar malam kawai da wasu tsirarun mutane a masallacin, su malam alfah suka k’arasa ga malam dake shirin fita shima.
        Cikin mutunta juna malam da malam alfah suka gaisa, sosai malam zai iya girmar malam alfah a shekaru, shima zubairu ya gaisheshi kafin ya masa bayanin abinda ya kawosu.
    Cikin jinjina kai malan ya amsa sannan suka fito.
        Ana k’ok’arin fiddo Jiddah amota za’a shiga da ita ciki malam mustafa ya iso wajen, da mamaki yake kallon Uncle yahaya dake share zufa daya had’a saboda rik’e Jiddah.
      “Uh uhm malam yahaya kaine yau a anguwarmu? Injidai lafiya?”.
      Juyowa Uncle yahaya yayi damson ganin Mai maganar, shima cikin mamaki yace, “A malam Mustafa dama nan anguwar kake? Amma Alhamdllh nayi farin cikin ganinka, wlhy Jiddah ce babu lafiya muka kawota”.
         “ALLAH Sarki, jiddah dai dana sani? Wadda akai biki watannin baya?”.
       “Wlhy kuwa malam Mustafa itace”.
     “Subahanallahi, ina mijin nata? mike faruwa haka?”.
     Murmushin takaici Uncle yahaya yayi, yana gyara tsaiwarsa, “Malam Mustafa labarin maid’an tsawone, amma bara mushiga da ita dan malam Na jiranmu”.
       “To ba laifi, amma inaga ad’an matsar da motar gaba saboda idanun jama’a”.
    Shawarar malam mustafa sukabi, aka matsar da motar kusada k’ofa sosai ta yanda ko an fito da Jiddah babu mai ganinta.

              Tunda Aka shigo da Jiddah cikin falon malam Abdul-ra’uff maina take wata k’ara da jijjiga da fisge-fisgen guduwa.
        Tausayin Jiddah da tunanin yaushe tagamu da wannan lalurar ya ishi malam mustafa. Sai dai bashida zarafin neman k’arin bayani a halin da ake yanzu…… 
     Maganar Malam Abdul-ra’uff ta katse masa tunani ya maida hankalinsa gareshi.
       Kallon Uncle yahaya dake rik’e da Jiddah malam Abdul-ra’uff yayi yana fad’in “kaga inkaso sakarta kawai”.
        “Malam da an saketa guduwa zatayi”. ‘Uncle yahaya yafad’a tamkar zai saka ihu’.
     Murmushi malam Abdul’ra’uff yayi yana gyara zamansa, “Karka damu sakarta, babu inda zataje insha ALLAH”,
     Sakinta Uncle yahaya yayi ya matsa gefe, yayinda Jiddah keta bige-bige tana wani irin gunji, ga uwar zufa da takeyi tamkar fanka bata aiki a falon. 
         “mustafa jonamin abin turarennan na gefenka”.
      “To Malam”. Malam mustafa ya amsa cike da girmamawa..
      Tunda Malam Abdul-ra’uff yafara zuba garin magani Na turare hayak’i ya fara tashi sai bige-bigen Jiddah ya k’aru, hakama gunjin da takeyi, sai dai kuma tak’i magana, kamar yanda malam yake buk’ata. Kusan mintuna goma sha biyar ana Abu d’aya lamari Na Neman cin tura, gadai alamun shaid’anin dake tare da ita yana jigatuwa, amma taurinkai ya hana yayi magana.
      Malam ya tsaya daga tofama Jiddah Addu’a mik’ewa yay ya fito yana fad’in su Uncle yahaya su biyosa.
        A zaurensa bisa rukunin kujerun ya zauna yana kallon su Uncle yahaya cikin yarce gumi.
         “Wato maganar gaskiya yarinyarnan akwai sihiri mai k’arfi a jikinta, bisa alamu kuma anyi ne cikeda makirci mai wahalar fassara, dan shaid’anin dake jikinta ma kunga yak’i nuna kansa, alhalin kuma alamu sun nuna yana jigata da addu’oin dake ratsashi, shin kozaku bani wani haske akan al’amarin?”.
      Kafin Uncle yahaya yay magana malam mustafa ya sanarma malama wacece Jiddah. Sosai malam Abdul-ra’uff yay mamaki, danshi ko kad’an bai ganetaba, dandanan hankalinsa Yakuma tashi, ya shiga tambayar Uncle yahaya Yaya akai haka? Miya faru da Jiddah bayan gaba d’aya dayin aurenta bata wuce watanni biyarba.
        Kan Uncle yahaya a duk’e yana tsiyayar da hawaye yayma su Malam bayani dalla-dalla akan auren Jiddah da sanadinsa harma k’arewarsa sanadin matsalar da ayanzu Jiddah ke ciki.
       Ran Malam Abdul-ra’uff ya6aci sosai, ga tsananin tausayin Jiddah da k’aunarta ke k’ara ratsashi, nawa yarinyar take da mahaifinta zai za6i sakata a gararin rayuwa irin wannan saboda cikar burinsa? Lallai alokacin dayasan irin auren da za’ama Jiddah kenan koda nuna k’arfine dasai ya aurama Aliyu ita. Amma babu komai, ya d’auki hakan a matsarin *RUBUTACCIYAR K’ADDARA* a gareta, babu wani mahaluki daya isa gogeta kuma………..
             Malam nacikin tattaunawa da zuciyarsa sukaji sassanyar Muryar Sheikh Aliyu cikin sallama. Gaba d’ayansu amsa masa sukayi suna d’agowa da kallonsa. Sanye yake cikin shadda boyal ruwan k’asa mai haske, sai hularsa itama ruwan k’asa amma tad’anyi duhu kad’an, hanunsa rik’e da waya da key d’in mota daya saya tun bayan aurensa da Maimunatu. Kallo d’aya zakai masa ka fahimci hankalinsa a kwance yake, yad’anyi k’iba kuma yay fayau dashi alamun akwai kwanciyar hankali da nutsuwa a duniyarsa.
    ‘Daya bayan d’aya ya basu hannu suka gaisa bayan ya gaida malam dake kallonsa tamkar zaiga maganin warakar Jiddah a jikinsa.
    Kallon malam Mustafa yay yana fad’in “Ashe kana nan?”.
       “Eh wlhy, tun bayan sallar la’asar nazo dama Na sanarma malam yarinyar da muka za6a”.
       “Masha ALLAH, to bara na shiga cikin gida Na gaidasu, idan kun gama Na dawo”.
     Harya mik’e malam ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa.
      “Aliyu!”.
“Na’am baba” ya amsa yana maida kallonsa garesa.
      “Ku shiga kaida mustafa Falona akwai yarinya Mai lalura ka dubamin ita”.
      A sanyaye yace, “To Baba”.
         Malam Mustafa na gaba shi yana baya suka shiga, Jiddah Na kwance tayi ligif kamar matacciya, dan tunda su malam suka fita saita bar abinda takeyi ta nutsu, dama matsalarta maza ne kuma sun fita, amma su Malam Mustafa na shiga tahau fisge-fisge da kwalla k’arar datafi wadda takeyi a d’azun.
     Hannu Aliyu yasa ya toshe kunnensa yana lumshe idanu danjin k’arar har cikin kwanyar kansa. 
      Ganin zata fice malam Mustafa yay saurin zungurinsa, idanunsa ya bud’e yana janye hannunsa daga kunnen, taku d’aya ya fisgo hijjabinta ya maidota baya ta fad’in yaraf tana wata irin jijjiga.
     Tuni idonsa yayi jajur da 6acin rai (karku manta tunkan Aliyu yaje saudia yanada wajen saida magungunan musulinci dama), kallon Jiddah daketa faman takurewa a jikin bango tana k’yarma yayi, sai duk’unk’une fuskarta take a cikin hijjab. Yaja kujera ta roba dake gefe ya zauna d’an nesa da ita. Nuni yayma malam mustafa dake tsaye yana kallonsu da yabashi ruwa.
        Malam mustafa ya mik’a masa ruwan daya d’ebo a Kofi, kar6a yay yafara tofa addu’a a ciki yana kallon Jiddah dahar yanzu take mutsu-mutsu, sai dai takasa yin k’arar sosai, dan ta k’udundune kanta a hijjab.
      Ruwan Addu’ar daya watsa mata a jikine ya sakata zabura tana fasa wani kuka, bai sauraretaba ya cigaba, sai kuma mamuk’e bango take tamkar xata koma cikinsa.
     Ransa a 6ace, amma hakan bai hana muryarsa fita da sanyiba yace, “Kai wane irin shaid’anine Mai taurin kai? Kana azabtuwa amma bazaka nunaba?”.
     Shiru Jiddah ko nace aljani bai maganaba, k’yalesa Aliyu yayi, ya d’auki Qur’an malam Mustafa ma haka suka Fara karatu cikin suratul bak’ara.
    Karkarwa jikin jiddah ya cigaba dayi tana wata irin zufa maiban mamaki. “Babu inda zanje, bazan fitaba, nace bazan fitaba, ni kubar k’onani bazan fitaba…….” wad’annan sune kalamun dake fitowa a bakin Jiddah tana kuka. Hakan kuma baisa su Aliyu dakatawaba, kusan mintuna talatin suna janyo ayoyin Ubangiji cikin surori daban-daban, sosai Jiddah ta jigata matuk’a, muryartama ko fita batayi, daga k’arshe kuma tama kwanta k’asa tamkar wata matacciya, cigaba da karatu su Aliyu sukayi, sai bayan kamar mintuna goma suka dakata saboda jin numfashin Jiddah ya daidaita.
       Sassanyar ajiyar zuciya Sheikh Aly ya sauke yana rufe Qur’anin, ya kalli malam mustafa shima dake rufe nasa, “Mustafa wacece wannan d’in wai? Minene kuma matsalarta?”.
      Nisawa malam mustafa yayi fuskarsa da tsantsar damuwa yake fad’ama Aliyu komai game da Jiddah, harma yunk’urin had’ashi aure da malam yay da ita tun farko, amma suka iske mahaifinta yamata miji”.
       Shiru kawai Aliyu yayi yana kallon wani waje daban, shi mutumne mai tsananin tausayi da shiga damuwa akan damuwar wani, tuni hawaye harsun cika masa idanu, ya zari handkerchief daga aljihunsa yay saurin tsanesu. Batare daya yima malam mustafa maganaba yatashi ya fice.
       Inda su malam suke zaune yad’an kalla kafin ya kauda idonsa gefe dan kar malam ya fahimci yayi kuka, “Baba ina zuwa su jirani”.
       “To saika dawo Ali” ‘malam yafad’a cikin murmushi’.
    Yana fita malam Mustafa ya fito, kallonsa malam yay “Mustafa miya farune?”.
       “Malam tasamu barcine, inaga zai had’o magungunane”.
     “To Alhamdllh, ALLAH kai mana maganin abinda yafi k’arfinmu, harma wanda muke gani munfi karfinsa”.
     Amin malam, suka fad’a gaba d’aya falon harsu Uncle.
     cikin zolaya malam yakuma kallon mustafa yana cewa, “Halan abokinka yauma halin ya ta6a?”.
     Malam mustafa yay murmushi yana bama malam amsa, “Malam ai wannan wajib ne ga Aliyu, sai dai in Abu bai raunana zuciyarsa baneba”.
      “To ALLAH ya kiyaye, Yaro ya maida kansa kamar wani mace, Abu kad’an yafara zubda hawaye”.
    Duk murmusawa sukayi har su Uncle yahaya dake zaune suna saurarensu. Sosai Uncle yahaya yakumajin k’aunar Aliyu da samun nutsuwa akan maganar da suka gama da malam yanzu.

*********

  Kusan mintuna talatin da fitar Sheikh Ali saigashi ya dawo d’auke da farar Leda madaidaiciya, zama yay yana bud’e ledar, dalla-dalla yayma Uncle yahaya bayanin yanda Jiddah zatayi amfani da magungunan, kafin ya d’ora da fad’in, “Ko kunada damar tura wani can gidan data baro yad’an mana wani bincike? Dan ina zargin kamar akwai abinda aka ajiye ko aka binne dake saka aljanin koda yatafi yake dawowa jikinta, abinda na lura dashi kuma kamar shine ke tsoratata inhar tasamu kusanci da namiji, alamun shine tushen sihirin jikinta, sai kuma mun samu rusa wancan kullin nasu da izinin ALLAH koda komai zai dai-daita, sadai insha ALLAH indai tacigaba da amfani da wad’annan magungunan sannan ta tsare yin azkar da salla akan lokaci, ta kiyaye yawo babu d’ankwali da yawo babu takalmi a tsakar gida, ta kiyaye sauraren wak’a ko shiga bayi batareda tayi addu’a ba, da yawaita kusanta kanta da Qur’ani, to muna fatan dacewa wajen samun sauk’i insha ALLAH”.
       Alhmdllh kowa ya shiga maimaitawa da fatan dacewa. Uncle yahaya ya d’ora da fad’in ”Zamuga yanda za’ayi a bincika d’in insha ALLAH, mungode sosai ALLAH yak’ara girma da hak’urin taimakon bayin ALLAH”..  
      Amin duk suka amsa dashi, Aliyu daya amsa a la66ansa ya mik’e yana fad’in “Zaku iya tafiya da ita”.
      Sun amsa da to, shikuma yay yunk’urin shigewa cikin gida.
       Da sauri Uncle yahaya yace, “Malam bakai maganar kud’i ba ai”.
      Murmushi Aliyu yayi, batare daya juyoba yace, “ALLAH yabata lafiya” kawai ya ida shigewa.
     Uncle yahaya ya maido kallonsa ga Malam zaiyi magana. Murmushi malam yayi shima, “Malam yahaya wane maganar kud’i kuma? Tunda kaji yace haka bazai amsaba, kuma ai yima kainema, ALLAH yabata lafiya dai mu shine fatanmu”.
      “Amin malam, ALLAH ya saka da alkairi, ya albarkaci zuri’a, ALLAH ya k’ara girma”.
      Kowa ya amsa da amin.

     Uncle yahaya yakai Jiddah dabatasan mi akeba mota, har k’ofar gidan malam da Malam Mustafa suka rakosu, suna niyyar tafiya Aliyu ya fito, hannu kawai ya d’aga musu ya wuce domin haramar d’aura alwalar magriba dake gabatowa.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


        Su Umma na zaune zugum-zugum itadasu walida da Maman Sadiq da Aunty Nafisa wadda tazo sake duba jikin Jiddah ta iske kuma basanan saita tsaya.
     Alkubus d’inma da Jiddah ke k’ok’arin d’aurawa sai Aunty Nafisar ce ta k’arasa, dan Umma ma takasa ta6uka komai tunda aka fita da Jiddah.
      Su Zarah kam tunda suka dawo makaranta sukaji halinda Y’ar uwarsu ke ciki sai suka hau kuka, alkubus d’inma tunda aka gamashi babu Wanda yako kallesa.
    Jin tsayuwar mota ya sakasu mik’ewa a tare suka lek’a. 
     Sune suka shigo da jiddah wadda take barci har yanzu. Uncle yahaya ya biyo bayansu da ledar maganin bayan yayima malam alfah godiya sosai.
     Shima yana ajiye ledar fita yay massalaci, dan ankira sallar magriba.
     Jiddah kam d’akin Umma aka kaita aka kwantar da ita, suma suka fito dan suyi haramar sallar magriba, koba komai hankalinsu yad’an kwanta…………..✍????



*_????jiya kwace kodai Abba zakarine ya biya bashin da ake binsa dani????????, wani uzirine ya tasomin batareda Na shirya masaba????, messages d’in PC ma sai yanzu zanje Na amsa mukusu tun kusan Na kwana uku⛹‍♀, wad’anda suka turo kumin afuwa yanzu Zan amsa insha ALLAH.????_*

Ina fata duk kuna lafiya?.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button