NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 21 – 22

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[21➖22]_*

    
…………..Bayan Uncle yahaya yadawo daga salla suka zauna tattauna maganar Jiddah, bayani yay musu akan dukkan abinda ya faru, kafin ya
d’ora da batun malam Aliyu na bincike a gidan Alhaji Garba.
    Kowa ya jinjina maganar, domin wannan abune mai matuk’ar wahala agaresu, dama can babu wata alak’ar dangantaka a tsakaninsu, gakuma wannan batun na Jiddah daya gitta, Abba kam sunsan bama zai basu had’in kaiba, k’ilama idan sun masa bayani ya rusa komai, Hindu kam da ace abokiyar zamace ta kwarai dasai ta taimakesu tunda ita gidan zuwantane.
     Sunta tattauna mafita amma basu samuba, duk hanyar da suka k’ulla saisuga bazata 6illeba. Dole dai suka ajiye zancen akan sai sunyi tunani.
        Sund’an samu kowa yaci abinci, amma zukatansu dank’are da neman mafita suke.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

           Tunda suka idar da Sallar Magriba sai yayma malam sallama yanufi gida, dan yasan d’alibai nacan na jiransa, fatansa sallar isha’i ta riskesa acan.
      Kamar yanda yay fata kam saiya dace, duk da bawani nisabane tsakanin gidansa dana malam d’in, ya iske ana kiran sallar isha’i.
      Alwala ya sake ya shiga masallaci. Bayan an idar sukai zaman karatu. Bai samu shiga gidaba sai kusan goma saura.
        Cikin Sassanyar muryarsa yay sallama, Maimuna dake kwance cikin kujera tana kallon Sunna tv ta amsa tana tashi zaune, tsaf take cikin kwalliya tanata k’amshi, murmushi suka sakarma juna, yayinda Aliyu ya bud’e mata hannayensa alamar tazo.
       Ahankali tataso ta shige jikinsa tana fad’in “Nayi kewarka Annur”.
      “Nima haka habibati”. Malam Aliyu yafad’a a hankali cikin kunnenta.
    Fuskarta d’auke da murmushi har yanzu ta d’ago ta kallesa, goshinta ya sumbata da la66anta, kafin a hankali yace, “Mikika tanadarmin sarauniya?”.
     Cikin kashe ido da murya tace, “Komaima Na tanada maka harda abinda malam ya hana fad’a”.
      Dariya sukayi a tare, Aliyu yaja hannunta yana fad’in “Zomuje ki fad’amin, ai bazan fad’ama malam kin fad’aba”.
         “Yaya Ali kacika wayo wlhy”.
      “Aunty Maimoon kin cika wayo kema al”. ‘Aliyu  yay mahanar suna ida shigewa’.
                 Da taimakonta yay wanka sannan suka dawo falon, kullum dare fruits sune abincin Aliyu, gab da zai kwanta kuma yasha had’ad’d’en shayi irin Na larabawa Kofi d’aya, dan haka Maimunatu take k’ok’arin ganin tamusu nutsatstsan yanka.
        Sosai ya maida hankalinsa ga Tafseer d’in da akeyi a Sunnah tv Wanda ya tarar Maimuna na kallo, harta gama ajiye dukkan abinda zai buk’ata hankalinsa naga tv.
         “Yaya Aliyu”. ‘Maimuna tafad’a ashagwa6e’.
       Juyowa yay ya kalleta batare da ya amsaba, da ido ta nuna masa kayan gabansa. Ajiyar zuciya yad’an sauke kafin ya sauka k’asa saman kafet ya zauna, itama zama tayi, sunashan kayan marmarinsu suna kallon tafseer, lokaci-lokaci sukan jefi junansu da murmushi dakuma magana idan ta kama.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
   
            Jiddah bata farkaba sai kusan k’arfe goma, lokacin Mijin Aunty Nafisa yazo ya d’auketa, su Uncle yahaya ma suna shirin tafiya, amma farkawar tata saita dakatar dasu.
      Alhmdllh normal ta farka, dukda tanata ra6e-ra6e saboda ganin Uncle yahaya.
     Zarah ce data had’a Mata ruwan wanka ta taimaka Mata zuwa ban d’aki, bayan ta shiga ta dawo waje zaman jiranta, bata wani dad’eba ta fito ta d’aura alwala sannan ta koma d’aki, bata shafa maiba sai kayan da Walida ta ajiye mata ta canja tahau ramuwar sallolin da bata samu yiba.
         Su Uncle yahaya basubar gidanba saida sukaga taci abinci da fara amfani da wasu magungunan ta koma ta kwanta saboda jikinta duk babu k’wari.
     Sallama sukaima su Umma suka wuce gida.


★★★

      Washe gari normal Jiddah ta tashi, wandama bai saniba bazaice tashiga wani haliba jiya, koda Uncle yahaya yazo dubata d’aki ta shige ta 6uya, bai damuba shidai, dan yasan bawai yin kanta baneba. Sallama yay musu ya wuce kasuwa.
      Da d’an k’arfin gwiwa su Zarama sukai shirin makaranta suka tafi.
  
         Tundaga wannan lokaci abubuwa sukaima Jiddah sassauci, dukda har yanzu batasan namiji a kusa da ita, amma bata firgita ko fita hayyacinta danta samu kusanci dasu, magani kuma da ruwan addu’oi daya k’are ake aiko mata wani daga gidan malam, malam mustafa da kansa yazo yaymata maganar komawa makaranta saboda sunason sudai taje Saudia d’in, dan tunda sukaji batada aure sai suka ajiye batun waccen da suka za6a suka maida burunsu akan Jiddahn.
     Y’an ajinsu sunyi farin cikin dawowarta, musamman ma Madina. 
      Kuma himma sukai wajen Trining d’in Jiddah yanda zata kuma samun gogewar ilimi sosai dabin k’a’idojin gasar, kuma tana k’ok’arin maida hankalinta sosai, dukda duk lokacin da malami zai shigo musu karatu Jiddah batada sauran nutsuwa harya fice, amma haka take dakewa da yawan Addu’ar samun kwarin gwiwa harya fice.
     Duk dokokin da Aliyu yace ta kiyaye Alhmdllh tana iyakar k’ok’arinta, dama can ita bamai wasa da irin abubuwan nan baceba, zaman sihiri jikinta kawai k’addarace daga ubangji Mai jarabtar Bawa aduk sanda yaso, akuma lokacin fayaso.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

       Shirye-shiryen tafiya gasarsu ya kankama, dukda duk wannan hidimar da akeyi Abba bai saniba, rabonshi da zuwa gidan kusan watanni hud’u kenan, kuma yana zaune a garin babu inda yaje.
      Ganin yarage saura kwana biyu su Jiddah su tafi Uncle yahaya yaje har gida ya sameshi da maganar.
       A harabar gidan ya iske su kalifa na ball, kallo d’aya sukai masa suka d’auke Kansu tareda cigaba da kwallonsu.
     Murmushi Uncle yahaya yayi kawai shi yana k’arasawa garesu da fad’in “yarana kuna lafiya?”.
        Cike da rashin kulawa suka  amsa suna cigaba da harkar gabansu. “To ALLAH ya k’yauta” uncle yahaya yafad’a yana kamo hannun kalifa domin tambayarsa. Amma sai yaron yay azamar janye hannunsa yana wani 6ata fuska. Uncle yahaya baice komaiba sai tambayarsu Abba nanan da yay. Muneer kawai ya amsa da eh, amma Hassan da Hussain da kalifa tunima sun koma kan hayaniya akan cin Ball.
       Haka Uncle yahaya ya k’arasa ciki yana tausayin yayansa akan wad’annan yaran marasa tarbiyya, acikinma Hajia Hindu yatsine-yatsine taita masa, tana shirin cewa Abba baya gida saigashi ya fito saboda jin muryar d’an uwansa.
       Zama yay suka gaisa  Uncle Yahaya ya fad’a masa abinda ya kawoshi.
     Kallonsa Abba yay rai a 6ace, “Yahaya kace min dama wannan shine dalilin dayasa kuka kashe Mata aure?”.
         Uncle yahaya yay murmushin takaici yana gyara zamansa. “Yaya ba wannan maganar bace ta kawoni please, nidai yanzu amincewarka kawai da addu’arka muke buk’ata”.
        “Yo inda amincewarsa ake buk’ata Aida tini amfad’a masa basaida lokaci ya k’ureba”. ‘Hajia Hindu tai maganar tana gatsine-gatsine’.
     Murtike fuska Uncle yahaya yayi yana watsa mata wata muguwar harara, “Kinji na sakoki a cikin zancena Maman kalifa? To ki Kama kanki wannan ba huruminki baneba, kibari idan mungama Na wuce saikiyi keda shi”.
    Harara ta watsa masa tabar falon tana jan tsaki. Shima Uncle yahaya tsakin yayi ya mik’e.
     Abba yace, “Ni wlhy ina mamakin yanda kokad’an kaida Hindu bakwa zama inuwa d’aya, nasan dai yagana ce kawai ke rura wutar k’iyayya a tsakaninku kullum tamkar kuna ganin hanjin juna”.
       Baki Uncle yahaya ya ta6e kawai, “Yaya nawuce ni”.

         Uncle yahaya bai sakebi takan Abba ba tundaga ranar har yau dasu Jiddah ke shirin tafiya k’asa mai tsarki, jirginsu zai tashi k’arfe tara Na darene.

★★★*

       “ALLAH Yaya Jiddah harna Fara kewarki tunma da rana”.
       Harara Zarah ta zubama Walida Mai maganar, ta d’auki kwandon wanke-wanke data gama tana nufar kicin, “To Uwar iya, kema kad’ai kike kewarta kenan?”.
     Dariya Umma da Jiddah dake zaune kan tabarma sukayi, Jiddah ta janye albasar datake yanka wadda zasuci awara tana fad’in “Oni Hauwa, wlhy Zarah yanzu kinzama jarababbiya, wannan harar da kike Mata ai saikisa ta rud’e ta tsulma cikin rijiyar”.
     Daga kicin Zarah tace, “Yo Yaya Jiddah abunne da haushi, inama laifin tace munfara kewarki, amma saita wani ware kanta”.
     “Kishi kike da autata kenan Zarah?”. ‘Cewar Umma tana dariya’.
       “Umma barta ai Zan rama wlhy”.
      Zarah da Jiddah suka sanya dariya, yayinda Walida ta kwa6e fuska tana dangwarar da gugan hannunta tadawo kusada Umma ta zauna tana kumbura baki.
        Jawota Umma tayi jikinta itama tan danne dariyarta dak’yar saboda baki da Walida ta kumburo. “Kinga auta barsu kinji, saina rama miki nima bazan bar saita kwanaba”.
     “Yauwa Ummana shiyasa nake sonki”.
     Ha6a Jiddah ta rik’e tana fad’in “To a’a mu tsintomu akai madam, wato Ummanki ma ke kad’ai”. 
     Gwalo Walida tai musu, yayinda Zarah takai Mata dundu Umma ta tare. “ALLAH Zarah kika dokarmin yarinya saina rama mata”.
        Jiddah tace, “Umma harda fad’in ALLAH?”.
      “To tadaketa tagani”.
“Yaya Jiddah barsu, badai an waremu ba, yau kina tafiya gidan Uncle yahaya Zan koma nima”.
       “Haba dai y’ammatan Umma wasa muke muku”. ‘Umma da walida suka had’a baki wajen fad’a’.
     Dariya suka sanya suduka.

        Haka suka cigaba da hirarsu har bayan isha’i bayan sungama cin Awara, daga nan Jiddah tahau shiri dan Uncle yahaya yakura Umma yace ta shirya malam mustafa yace zaizo d’aukarsu.
      Karfe takwas da rabi kuwa sai gashi shida Uncle yahaya, alokacin kuma kuka yatashi a tsakanin su Jiddah, Umma ma dai tana dannewa ne kawai, suduka gidan sukai mata rakkiya har airport.
     Wannan dai shine Karon farko na zuwan Jiddah da ahalinta airport, dan haka sukaita zuba k’auyanci, Jiddah dai tanata kalle-kalle amma bata cewa komai sai dariya da take musu itada Uncle yahaya da malam mustafa.
          Saida kuma aka fara shelar matafiyan jirgin Saudia sannan jikinsu yay sanyi, su Zarah aka fara matse hawaye. Sunaji suna gani aka kira sunan Jiddah a bayan Na Uncle yahaya da malam mustafa. A d’arare ta shiga jirgin ga wani tsoro daketa kuma mamaye zuciyarta, Addu’a tafara karantowa a zuciyarta, indama ALLAH ya taimaketa kusada wata Mata malam mustafa ya nuna Mata ta zauna.
           Cikin k’ank’anin lokaci sabo ya shiga tsakanin Jiddah da Matar Mai yawan fara’a, da taimakonta Jiddah ta dake kewar y’an uwanta ta ragu Mata a zuciya.
           Ubangiji ya saukesu lafiya, inda Jirginsu ya sauka a Jidda, itadai Jiddah tanata tsarkake sunan ALLAH a zuciyarta, lallai duniya akwai abubuwan kallo, gaba d’aya saita koma cikakkiyar bak’auya zam, shi kansa Uncle yahaya sai tsarkake sunan ALLAH yakeyi, yau gashi sanadin d’iyar zumu yazo inda baiyi tunaniba (danshi baita6a zuwa makka ba) jiyay yana k’ara k’aunar Jiddah har k’asan ransa, wato zuminci babban abune da mutane ke wofantar dashi bisaga son zuciya, da mutane zasu nutsu su fahimci muhimman zuminci da sun rik’e, shidai babu abinda zai cema ALLAH sai godiya……………✍????






Kuyi maleji da wanga????????????‍♀

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button