NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 8

 *_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
  *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_



                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

________________________


_________________________


                 *_[8……]_*

    
…………..Zancen yarinyarnan data turoma malam Aliyu sak’o yata damunsa a rai da zuciya, dan haka ya buk’aci tabashi address Na inda suke.
     Batayi musuba ta turo masa suna cikin Kaduna ne.
    Washe Gari ya sanarma malam yanda sukayi. Kai tsaye malam yabashi Umarnin shiryawa suje shida Mahmud (kaninsa) da mustafa.
           A washe garin wannan ranar suka shirya domin cika umarnin malam.
      Bayan sun Isa kaduna masauki suka fara samu gidan babban malaminnan Sheirk Haruna bala, sanin zuwansu da yayi yaymusu tarba mai k’yau da mutuntawa, dan malam Abdul-ra’uff amininsane sosai. A ranar kam basu bar malam Aliyu ba, dukda gajiyar daya kwaso da daddare bayan isha’i saida ya gudanar musu da lecture Mai taken *_ILIMI DA RAYUWA ABOKAN TAFIYA_*.
     Washe Gari kusan misalin goma na safe ya nema yarinyar da sukazo dominta, dan yanaso a gobe su juyo Gidane.
         Da taimakonta suka iso gidan nasu, gidane babba badai can sosaiba, amma komai a tsare.
          Afrah yarinyar data turama malam sak’oce ta fito tarbarsu, k’yak’yk’yawace a fuska kam sosai, sannan akwai Fari amma irin na kanti, sanye take da hijjab iya gwiwa dan haka su malam basuda damar tantance shigarta, dukdama kallo d’aya sukai Mata kowa ya d’auke kansa, ita kanta cike take da kunyar ganinsu, dan haka kanta a k’asa tabasu umarnin shiga falon Abbansu da k’ofar take a harabar gidan.
     Bayan duk sun zauna ta fita, shidai malam Aliyu yana mamakin da tsarkake sunan ALLAH akan wannan hargitsatstsen al’amari.
           Kusan mintunanta goma da fita saigata tadawo itada wata dattijuwa d’auke da tirirrika, sudai su malam basuce komaiba, fita ta kumayi kafin mintuna kad’an ta sake dawowa ita kad’ai d’auke da wani tiren, bayan ta ajiye ta gaidasu.
      Duk amsawa sukayi.
Kanta a k’asa tace, “Malam kuyi hak’uri Dady bai dawo aiki baneba, amma yana hanya, dan yasan da zuwanku, dukda dai ban sanar masa ainahin abinda ya kawokuba”.
      “Masha ALLAH”. malam Mustafa ya fad’a.
    Malam Muhmud shima yace, “babu damuwa, ALLAH ya maidoshi lafiya”.
    Malam Aliyu dai baiyi maganaba, dan k’ok’arin amsa kiran da akai masa a waya yakeyi.
      Mik’ewa tayi tana rok’onsu dan ALLAH suci abincin.


     Zaman kusan mintuna talatin saiga Dadynsu Afrah ya shigo falon da sallama, da alama ma yadawo tuni, saida ya kimtsa ma sannan ya fito.
      Daka gansa kaga cikakken d’an boko kam, dan sanye yakema da wando tree quarter da T-shirt Mara nauyi, hannunsa rik’e da wayoyinsa, a hasashe zai iya kaiwa shekaru 60, Afrah Na matuk’ar Kama dashi, kawai dai shi bak’ine, itako tayi fari (amma na kanti???? ). Tarba ta mutunci yayma su malam Aliyu tankar ya sansu, dan sunkula mutumne Mai yawan fara’a. 
      Fuskarsa d’auke da murmushi yake fad’in “Lallai nazama Mai sa’a da farin ciki, yau sheirk Aliyu bin Andul-ra’uff maina ne da kansa a gidan, dukda bansan mike tafe dakuba ina muku lale marhabun, amma tabbas nayi mamaki sosai da wannan zunwan, tun jiya da Afrah ta sanarmin abin yak’i barin raina, harma Na tsareta da tambayar ina ta San babban mutum irinka? Dahar zaizo gidannan?”.
       Murmushi su Aliyu duk sukayi, kafin Aliyu yad’anyi gyaran murya, cikin sanyinsa da nutsuwa irinta masu ilimi yace, “Alhaji inafa manya, har gobe mu d’aliban ilimine, abinda ya kawomu kuwa gaskiya babban al’amarine Dani kaina yahana zuciyata da ayyukana sukuni, ina ganin har saina sauke kayan dake kainane Zan sami nutsuwa. Da farko dai tabbas nayi mamaki da kokwanto akan abindama ya kawonin, saboda ganin karanci da mutuncinka, saidai banida wani hurumi na k’in gaskatawar tunda nasamu zancen ne daga amintacciyarku”.
       Kai Dady ya jinjina, sannan ya gyara zama yana kuma damk’e kofin lemon hannunsa, “malam maganganunka sun sakani a duhu matuk’a, amma Zan kwantar da hankalina domin k’ara fahimtarsu daga gareka”.
         “Masha ALLAH, Alhamdllh Alhaji, mun gode da wannan karamci, da farkodai in babu damuwa ina son ganin dukkan iyalanka anan tare damu, wannan ne zai bamu damar fahimtar abinda ya taramun”. 
           “To shikenan babu damuwa, Nawwas ne dama kawai baya gida, amma nasan ya dawo insha ALLAH” duk kiran wayoyinsu yayi d’aya bayan d’aya, acikinsu Afrah ce kawai a tsorace, amma Nawwas da  Namrah duk basusan ma’anar kiranba.
        A yanda Nawwas da Namrah da mahaifiyarsu kawai suka shigo ya isa Fara gaskata zancen Afrah. Gaisuwa ma ta sifirin a kaima su malam????.
           Dan Hajia Mansura ma tana taunar cigam ta shigo, dukda dai cin masu aji ake masa bana karuwaiba, Afrah ce kawai a k’asa zaune, amma Nawwas da Namrah duk a kujera suka zauna kusama da juna, hannun Nawwas akan Na Namrah wadda ke sanye da wando da Riga masu bin jiki, sai siririn mayafi data yano, shima saida mamansu Tamata magana, kanta yaci uban kitson gashin doki, daka gantadai kaga wayayyun wannan zamanin. Shiko Nawwas wandone irin Na babansa iya gwiwa, sai singlet ruwan d’orawa, askin kansa abun takaici da kuka ga al’ummar musulmai, dan an saisaye gefe da gefe da k’eya,  anbar gashin iya tsakkiyar kai sannan akai masa k’itso kalba (Dada) daga kasan gashin bak’i, sama kuma k’arshen kitson Brown. 
       Duk a cikin mintuna kad’am su Malam Aliyu suka nazarcesu.
      Dady yace, “Malam ga iyalin mawa, d’ayane babu a ciki autansu, yana jami’ar legas yana karatu, kwannan ma yatafi, wannan itace matata mahaifiyar yarana, sai babban Nawwas mai shekaru 27 a duniya, yagama p.h.d d’insa, watansa shidda kenan, yanzu haka yana aikinsa. Sai Afrah, tagama degree d’inta itama kwannan, muna mata shirin zuwa masters, sai Namrah tana jami’a tanan jos L200 yanzu”.
         Masha ALLAH su malam Aliyu suka fad’a a tare, da d’orawa da addu’ar fatan alkairi.
             Daga Nana malam Aliyu ya d’ora da fad’in “Dalilin zuwanmu nan gidan shine yarinyarka Afrah”. Atare suka kalli Afrah da kanta ke a k’asa. Malam Aliyu yacigaba da fad’in “Wani sak’o daya kasa barin zuciyata ta turamin, harma naji nakasa hak’uri saina dangane da wannan family, Afrah indai ban shiga huruminki ba inason ki kuma maimaita abinda kika turamin domin Na tabbatar”.
     Hawayen dake d’iga a kumatunta ta share, kafin tace, “Dady da mah-mah Ku gafarceni, yau Zan bud’e sirrin daku baku saniba, saidai har a yanzu ina tambayar kaina Sakacinku ne kokuwa ak’idar boko ce? Da wautar barin tarbiyyar addinin islama?. Har yanzu zuciyata ta Gaza amsamin tambayar, amma ban saniba ko idan Na fad’a yanzu amsar zata fito”.
     Ba k’aramin fad’uwa gaban Nawwas yayiba, dukda baisan mi Afrah zata fad’aba yaji ya tsargu. Mik’ewa yay niyyar yi amma dad ya tsaidashi da Ido, dole ya koma ya zauna yana wani kumbura baki.
      Afrah takuma fashewa da kuka sannan tafara jawabi dalla-dalla kamar yanda taima malam Aliyu a sak’o, harma ta k’ara da abinda bata sanar masaba.
      Gaba d’aya falon jikin kowa ya mutu murus, Dady da mah-mah ma jikinsu rawa yakeyi, hakama Namrah datayi wani tsalle zuwa k’asa saboda tsorata, bata ta6a zaton wani mahaluki yasan suna tarayya da Nawwas ba, sannan bata ta6a zargin yanayin abinda yakeyi da ita da Afrah ba.
      Gani kawai sukayi Dady ya kifo k’asa, Mah-mah ma data mik’e domin zuwa garesa saita yanke jiki ta fad’i. Nawwas kam dukya rikice, yarasa ina zashi ya 6uya saboda kunya da tsantsar tashin hankali.
        A tsorace su malam Aliyu duk sukayo kan Dady, yayinda Afrah tayi kan mah-mah d’insu.

     *bayan awa biyu* su Dady suka dawo a hayyacinsu, saboda kiran likitansu da Namrah tayi, annan yake sanarda jininsu ne yahau sakamakon jin abinda ya tsoratasu.
     Bayan tafiyar doctor da nitsawar komai, malam Aliyu yafara magana a matuk’ar sanyaye da k’unar zuciya. Ya Fara dajan ayoyin alkur’ani da hadisai, sannan ya d’ora da nasiha Mai girgiza zuciya. 
        “Wlhy iyaye Ku farka????, karku d’auki wancan zancen matsayin labarin littafi kawai, wannan fitinace data shigo acikin wannan al’ummar, Uba kaga yana Neman y’ay’ansa, Uwa ta nemi d’anta ko abokin d’anta, ko abokin mijinta, ko makwafcinsu, Yaya da k’annensa suringa Neman junansu, Yaya da kanwa su ringa aikata mad’igo, ko Matar uba da y’ay’an miji????, aboki yaringa zina da d’iyar abokinsa, k’anin uwa ya ringa zina da Y’ar k’anwarsa ko yayarsa, k’anin Uba yana zina da y’ay’an d’an uwansa, shin dan ALLAH wad’anne irin al’umma muke son zamane? Anya kuwa muna tsoron mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi? Muna tuna duniya tak’aitaciyace? Innalillahi wa inna’ilairaji’un, wlhy kaiconmu da toshewar imani dana zuciya????, k’iri-k’iri munason barin dokokin addininmu muna aro Na yahudanci da tsantsar tsagwaron kafirci a matsayin wayewa, *MUTUM DA DUNIYAR, y’an uwana YA DACE MU GYARA KANMMU* dai tunkan lokaci ya k’ure mana,  wlhy tunkan muga kayinmu cikin WUTAR JAHANNAMA mu farka daga wannan barcin asarar, duk yanda muke kallon mutuwa a nesa damu saitazo garemu, domin a kullum k’ara kusantomu take a kowacce safiya, mimuka tanada mikuma zamu tarrar?”. 
     Malam ya k’are maganar hawaye Na cika idonsa, malam mustafa da malam Mahmud Kansu jikinsu Yakuma yin sanyi lis da maganar malam Aliyu.
             Kafin kacemi kuka ya 6alle a tsakanin wannan ahali, kowannensu yana kaico da koyi da al’adar yahudanci da barin tafarkin addininsu bisaga rud’in duniya da wayewa Mara amfanii a duniya da lahira. Duk Wanda ya kallesu saisun bashi matuk’ar tausayi. Har kusan magrib su malam Aliyu Na gidan, saida sukaga komai ya natsa sannan suka wuce, sukabar wannan ahali cikin tsantsar rud’ani da nadama.

         Gaba d’aya da zazza6i Malam Aliyu ya kwana a ranar, washe garima haka suka tafi kano baida lafiya, koda suka dawo har k’arin ruwa yasha, saboda azababben ciwon kai da damuwa sun kasa barin zuciyarsa, komai kallonsa yake tamkar ba gaske ba ma. Amma dole zuciyarsa ta tilasta masa gaskatawa tunda yaje yaga zahiri.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
              Sai da jarabawar su Jiddah takai kwanaki hud’u sannan sakamako ya fito. Cikin amincin Ubangiji Jiddah taci ita da Mariya Ibrahim wata y’ar ajin, sosai suka shiga farinciki da wannan nasara, nanfa y’an aji suka shiga tayasu, dukda zukatan wasu babu dad’i akan rashin nasarar.

       Da tsantsar farin ciki Jiddah ta iso gida, ta kanand’e Umma dake shanya kayan da take wanki.
         “An dace kenan?”.
Umma tafad’a tana dariya bayan ta juyo ta kalli Jiddah dake mak’ale da ita.
        “Alhmadllh Umman mu naci wlhy, kai ina cikin farin ciki”.
       “Alhmdllh Jiddon Uncle, ALLAH ya sanya albarka da nasara tagaba”.
       “Amin Ummana”.
  Su Zarah na shigowa gida Umma ta taresu da wannan farin ciki suma, tuni sun kaure da murna suna k’ara yima yayar tasu adduar nasara. Itama Aunty Nafisa suka takura saida Umma ta kurata ta gumtsa Mata. Sosai tayi farinciki itama. 


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


          Yau gaba d’aya Malam Aliyu a busy yake, saboda tafiyar da tazo masa babu shiri, dukda dama yasan da tafiyar, amma bai tsammaceta cikin wannan watanba.
        Muhimmancin abinda zashiyine ya sakashi shiryawa babu wata damuwa da zuwan tafiyar a yanayin rashin shiri. Ko d’alibansa bada kowa ya samu damar yin sallamaba, sai sak’on ban hak’uri daya barmusu, da d’ora malam Mustafa matsayin Wanda zai cigaba da yimusu karatu harya dawo tafiyarsa ta watanni uku zuwa hud’u insha ALLAH.
         Cikin gida ya Shiga yayma matan Malam sallama, y’an uwansa kuma dukya kirasu ta waya musamman Ruk’ayya da Siyama daya dad’e yana waya dasu domin yin sallama, yaso su had’u kafin ya wuce, amma ina lokaci yariga da ya k’ure sosai.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          “Haba hindu, fushinnan ya isa haka mana, tunda kika dawo kink’i saurarena, minene amfanin dawo da abinda akayi ya wuce, kuma nabaki hak’uri”. 
        Shiru tayi tamkar bata jisaba, tacigaba dacin abincinta, shiko ya k’ura Mata ido yana juya nasa cokalin akan filet.
              A haka su Hussain suka fito suka samesu, kowanne kujerar Dani d’in yaja ya zauna, ko sallama basuyima iyayen nasuba.
       Kalifa daya zauna kusada Abba ya kallesa yana fad’in “Abba wai sai yaushe zaka cikamin alk’awarina?, ALLAH wayarnan bana sonta, Su Faisal duk an canja musu ni bandani, harma kunyar zuwa school nake da wayata”.
      Murmushi Abba yayi ya shafa kan kalifa, “Haba babana ka kwantar min da hankalinka mana, aina fad’a maka Zan sake maka, yanzu wasu abubuwane suka d’an tushemin, amma kabani nanda k’arshen watannan insha ALLAH taka wayarma duksai tafi tasu, dan nayima Nabel magana ma ya za6o maka mai k’yau”.
    Washe hak’wara kalifa yayi yana rungume Abba da fad’in “Kana birgrni Abbana……”
       “Abbanmu dai”. Cewar Hassan cikin jin haushi.
    Kallonsa Hajia hindatu da Abba sukayi, yayinda kalifa ke antaya masa harara kafin yaja tsaki da fad’in “Jealousy”.
      Hassan ya ta6e baki shima yana hararar kalifan “Jealaus d’in Ubanmi za’a maka, gaskiya Abba muma ka siya mana phones, nidai nafasa sai munkai js3 d’inma, ai gashi Aisar nan suna dashi”.
         Hajia Hindu dake dariya tace, “Y’an biyun Abba da gaske dai kishin kukeyi da babban Yaya”.
        “ALLAH ya kiyaye wlhy Mom, kibarma hura masa wannan k’aton kan nasa”.
      “Kai dan Uwarka waye mai k’aton kan?”. Kalifa ya fad’a a fusace yana mik’ewa zai kaima Hussain dayay maganar duka. Amma sai Abba yay nasarar tarewa.
        “Haba yaran Abba minene abin fad’a anan, ya Isa haka to abar maganar, kowa za’a saya masa indai wayace. Kai Auta mikake buk’ata?”. ‘Abba ya k’are maganar da kallon Munner daketa kallonsu kawai’.
        “Abba ni sonake ka siyamin motar da muka gani ni da mom ranar, nace ta sayamin saitace kud’inta bazai kaiba”.
        Jinjina kai Abba yayi yana maida kallonsa ga Hajia Hindu. Da ido tai masa alamar anyi haka.
    Murmushi yayi, “To Auta mom zata rakani na saya maka insha ALLAH”.
    Sosai Munner yake murna shima.
       Haka dai suka cigaba dacin abincin kaya-kaya tamkar wasu kaji. Bayan sun gama kowa ya kama gabansa.
        Sayayyar da Abba yay alk’awarin yimasu Munner ce ta saka hajia Hindu sauka daga fishinta Na kwananda Abba yaje yayi a gidan Umma. Dan suna shiga d’aki ta rungumeshi.
    Sosai yaji dad’in, shiyyasa ya kudiri aniyar kokartawa ya siya musu duk abinda ya alk’awarta musu………………✍????

      (Humm????????‍♀????).







*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button