NOVELSUncategorized

KWARATA 83

                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
                         &
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 81
     Me ya sameki ne ? Ya sake tambaya a karo na biyu , nayi ɓari ne , kallon ɗakin yayi sannan ya dawo da kallonshi wurina yace wane ɓari ? Yayi tambayar a cikin rashin fahimta , ina da ciki ne shine ya lalace , ɓacin rai kwance a idonshi ya gyara zaman hular saman kanshi ya duƙo inda nake kwance sai yanzu ya lura da jinin dake kwance a wurin , shi bai gani ba amma Nabeela tun shigowarta ta fahimta , cikin tsananin ɓacin rai yace ban gane ba fa….
    Ban sake magana ba daga haka dan maganar ta isheni kuma a wahalce nakeyinta , Nabeela……….. Ya ƙwala mata kira da sanyayayyar muryarshi , da gudu ta shigo jikinta yana kyarma ta tsaya daga can gefe cewa Yaya gani , bai kalleta ba yace me ya faru ? Cikin rawar murya tace Yaya wallahi , tare ta yayi da cewa karki cemin wallahi² me ya sameta ?
     Yaya ina makaranta , karki faɗamin kina makaranta me ya faru………….. ? Idan na sake magana zan kashe ki…… , cikin kuka tace matar Yaya ki faɗa masa abinda ya faru bayan bana nan , ke karki ɗaukeni sakarai ai na ganta na kiraki , nunawa yayi da hannunshi ya fara one , two , three , four cikin rawar murya tace Jiddah……..
     Ba damuwa na Jiddah ba abinda ya sami An mata nake tambayarki , ƙara fashewa tayi da kuka ta sake kallona tana cewa matar Yaya kiyi magana , tashi yayi yaje gabanta ya yanka mata wani irin mari harsai da ta duƙe yace idan kika sake mata magana saina karya miki maƙoshi me ya faru……..?
     Yaya wallahi bana nan naje makaranta yanzu na dawo lokacin da zan tafi na barta tana bacci , a ina take baccin ne ? Saman gado , ya akayi ta sauko ƙasa to ? Kila ta tashi ne ta faɗi , jeki palo ki jirani zan fito idan kuma kika kuskura kika bar gidan nan na rantse da Allah saina baki wahala , cikin kuka tace tou sannan ta fita.
      Dawowa yayi kusa dani , ya kalleni yanayin shi ya nuna yana nazari ne , bayan wani lokaci yace tashi , a tsorace na fara ƙoƙarin miƙewa amma na kasa , da Allah tashi bana san iskanci , tou na faɗa tare da tashi durƙushe dakel , tsugunawa yayi gabana yace ya akayi ciki ya lalace ? Yayi tambayar da harshe mai tada hankali , fashewa nayi da kuka nace Dikko , An mata ya akayi ciki ya lalace ya tsareni da idanuwanshi masu tada hankali idan yana fushi , kayi haƙuri na faɗa cikin rawar murya , bansan shi ba yaci gaba da cewa wato banda iskancin hotunan da kikayi har ma kike tunanin zan barki ciki ya zube ? Ba zubewar ciki ba yau ko naƙuda kikeyi saina zaneki , tashi kije ki gyara jikinki yana faɗin haka ya fita daga ɗakin.
       Gaba ɗaya ji nayi kamar an tsintsinkemin lakar jikina , idan kuma Dikko yasan naje wurin Yazeed wace matsalar zan fuskanta ? Ya zanyi ? Ni ba lalacewar cikin ne damuwana ba rayuwar da zan fuskanta idan ya gano cewa na fita naje wurin Yazeed , dakel na shiga toilet dan wanka ,
     Cikin tsananin ɓacin rai yaje ɗakinshi , gefen gado ya zauna ya dafe kanshi , zuciyarshi tana mishi babu daɗi miƙewa yayi ya matsa jikin window ya zuge labile yana kallon yadda rayuwar gidanshi ke tafiya , kowa sabgar gabanshi yakeyi ɗora fuskar shi yayi jikin window ya dafa hannunshi a sama yana kallon waje , a zuciyarshi yake zance cewa An mata baki da lissafi ko kaɗan na rayuwa , ina baki dama ta rayuwa amma baki gane abinda nake nufi dake sai idan bana nan duniyar zaki san ni ɗin na gina miki rayuwa , baki da Baba mahaifiyarki ba take , take ba tana can ta kama sabgar gabanta tana gina sabuwar rayuwarta , baku da ahali mai kyau kwata² , Jiddah ce ta shigo ɗakin da sallama.
     Ansawa yayi tare da juyowa ya kalleta so ɗaya ya koma yadda yake yaci gaba da zance zuci “yar rashin kunya da kinsan ina tausayinki iskancin da zaki zazzaga a gidan nan ba ɗan ƙarami bane ba mu zuba dani dake duk wanda ya fasa yaji kunya , tashi yayi a wurin ya nufi hanyar toilet yaga Jiddah zaune a gefen gado , ya akayi ne ? Ya tambayeta cikin kwarkwasa tace ba komai ta ƙarasa maganar tana kakkaɓa ido dan ibar mishi hankali , tou yayi jeki zanyi wanka , tashi tayi tana mummurza tafiya da salo mai ɗaukar hankali ta nufi wurinshi.
     Murmushi yayi ya bita da kallo harta iso wurinshi ta shige jikinshi , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙeta sosai yana kallon fuskarta da tasha ado da kwalliya , ɗan shanye idon dama tayi tare da cewa nayi ne ? Sassauta ganinshi yayi tare da ɗauke idonshi baiyi magana ba , gyara tsayuwarta tayi ta fara rattafa bayani kamar yadda Mardiyya ta turota cewa.
        Bayan Jiddah da Yayar Dikko sun gama dukan Sultana Jiddah ta kwakwkwaɗa mata bokitin ƙarfe a ciki suka danneta suka ɗura mata allura , suna gamawa suka fita a ɗakin , bata samu Mardiyya a ɗakinta ba data koma tana wurin Al ‘ Ameen , dan itama Mardiyyar tana gama ɗaukar video ganin zasu fito yasa ta fice da sauri ta ɓoye ƙasan bene , suna wucewa tayi wurin uncle.
     Uncle gabana faɗuwa yakeyi fa , da Allah can matsoraciyar banza badai kinyi video ba ? Eh kwantar da hankali yau duk bala’e ni na faɗa miki gaba ɗaya gidan nan zai watse , tabbas idan mai gida yaji labarin ɓarewar ciki ranshi zai ɓaci , da zaran yayi fushi baya iya saita kanshi dan haka zai fara duka babu ji babu gani kuma bazai saurari kowa ba , abinda za’ayi yanzu ki faɗawa Jiddah idan mai gida ya dawo taje ta faɗa masa , murmushi yayi tare daci gaba da cewa zai sakesu gaba ɗaya , ita Sultana zai saketa saboda hoton nan , ita kuma Jiddah zai saketa ne idan ya daketa zatace bana auren duka sai ka sakeni dama mun rufeta da wannan asirin duk wanda yazo zatace bazata zauna ba sai an saketa tabbas saiya saketa , Yayarshi kuma bayanin hukuncinta yana wurin Jiddah dama itace ƙatuwar munafukar kinga sun rabu kawai sai kuyi aurenku ya faɗa yana murmushi , kina shiga sai ki haihu idan namiji ne sai mu kashe shi mu cinye dukiyarshi , idan mace ce sai a bari sai an ƙara , dariya sukayi tare da tafawa….
    Bara inyi wanka in fito Dikko ya faɗa tare da fitar da Jiddah daga jikinshi , gefen gado ta koma ta zauna tana jiran fitowarshi shi kuma ya shiga toilet….
     Lokacin dana fito daga wanka Nabeela ta gyara wurin dana ɓata tass kuma har yanzu bata daina kuka ba , ina fitowa toilet ta shiga da kanta ta wanke kayan dana cire ta wanke toilet in , bayan ta fito tace matar Yaya tsakaninki da Allah ni ina nan wani abu ya faru dake ? Ko inda take ban kalla ba na fara saka kayana.
    Har Dikko ya fito daga wanka Jiddah tana nan , saida ya gama shiryawa yana saka kaya tace Yaya gaskiya abinda Aunty Rabiya takeyi bata kyautawa , Yayarshi kenan , ba tare daya kalleta ba yace me tayi miki ne ? A dai² lokacin da yake ɗaura belt a ƙugunshi , kaga dai ko ni kishirya Caca bana iya yimata irin abinda ita Aunty tayi , a dai² lokacin da yake saka riga , yace kiyi maganarki kai tsaye mana yana kallon kanshi a madubi tare da gyara zaman rigarshi , Caca ce take da ciki shine tace sai ta zubar dashi dan ita ƙawayenta sunce babu aihuwa a tsarin rayuwarsu , tsayawa cak Dikko yayi tare da daina ɓalle botiran rigarshi ya kalli Jiddah ta cikin madubi , data faɗamin zata zubar da cikinta dan ita zatayi gaba , shine na bata haƙuri tace bata yadda sai ta fitar ita ba zata zauna wani rainon ciki da “ya “ya ba taje ta tsufe ta lalata ƙuruciyarta , ni kuma sai nayi ma Aunty Rabiya waya a matsayinta na babba tazo tayi ma Caca magana dan karta zubar da cikin , shine tace ita ai bata so ka haihu dama shine fa tazo tayi mata allurar zubar da ciki….
      Shiru Dikko yayi yana addu’a a zuciyarshi dan ya saita kanshi amma ya kasa sarrafawa , yayi ya riƙe yaƙi riƙuwa , a zuciye ya fita daga ɗakin zuciyarshi tana tafarfasa da wurin Momy zaije amma yana kawowa ƙofar ɗakin Sultana yaji baya iya wucewa , shiga yayi Nabeela tana ganinshi ta durƙushe irin gani na miƙo kaina , bai kalleta ba ya kalleni yace nidai ko An mata…… ? Dikko dai ko ? Ya tsareni da ido , kayi haƙuri , kamar jira yake inyi magana yace ke…………. Saina kashe ki ya fara wani irin gurnani mai tada hankali , da gudu Nabeela ta fita tana neman ɗauki dan ita a tunaninta itace Dikko ya faɗa zai kashe , cikin sanyi nace ba komai kashe ni na faɗa hawaye na gangarowa daga cikin idona , dan bana iya tashi , nunani yayi cewa rufe min bakin munafuka jaka dake da bakisan inda duniya ta nufa ba na tsaneki……. Bana sanki haka kuma bana san ganin ki ya faɗa tare da kaimin wani irin halbi yana ci gaba da cewa ai baki burgeni ba da baki haɗa hada kanki kika mutu ba , bani kika cuta ba rayuwarki ce , zanje in dawo yau mai kwatarki a wurina sai Allah banza ƙazama…..
     Fuuuu ya fita daga ɗakin , a palon ƙasa ya haɗu dasu Ashiru ko inda suke bai kalla ba ya wuce ya fita da sauri ji yayi G H tayi masa nisa wani irin ihu ya kurmama mai tsananin tada hankali ya durƙushe a wurin wai……. Wai , wai Allahna , wayyo , kai………saina kashe kaina ya riƙe wuyanshi da ƙarfin bala’e , duk yadda akayi a ɓanɓare hannun Dikko daga wuyanshi yaƙi fita , kuma daga durƙushen an kasa kwantar dashi tashin hankalin ya girmi tunanin duk mai tunani , a ruɗe Nabeela ta fara kiran wayar Momy amma bata ɗauka ba , Yayarsu ta kira ta faɗa mata sannan ta turawa Dady text kuma har yanzu Dikko bai kwanta ba kuma bai cire hannunshi daga wuyashi ba har yaji ma kanshi ciwo jini yana fita daga wuyanshi.
       A wannan halin Dady ya samu Dikko idan hankalinshi yayi dubu ya tashi , itama Yayarshi haka tazo ta sameshi duk wani mai san rayuwar Dikko haka suka zo suka sameshi har Momy kuma zuwa wannan lokacin ya daina lumfashi gaba ɗayanshi ya ɗauke , Ashiru Dady ya kalla yace me yayi zafi haka ? Cike da damuwa Ashiru yace muna Abuja yacemin yaji gabanshi yana faɗuwa tabbas wani abu ya faru da Hajiya amarya shine yace in kirata dama sun kwana biyu basa waya ni bansan abinda ya haɗasu ba , Momy tace shegiya ɗiyar matsiyata idan wani abu ya samu ɗana itama sai an ratayeta.
    Hannu Dady ya ɗaga mata ya dakatar da ita sannan yace ma Ashiru ina jin ka , sai na kirata bata ɗauka ba , yace na kira Nabeela itama bata ɗauka ba itama Hajiya Jiddah shine yace na kira Mardiyya bayan na kirata na tambayeta tana gida tace min Ey nace me ya faru a gidan ne ? Shine tacemin ita dai taji ana cewa an zubar da cikin Aunty amarya ne , bayan na gama wayar nace masa Mardiyya bata gida gudun karya shiga damuwa shine ya matsa muka taho katsina , ni daga haka bansan komai ba.
      Dady yasa aka kira Mardiyya bayan tazo ya tambayeta abinda ya faru , tace Aunty Rabiya ce tazo tayi ma Aunty Amarya allurar zubar da ciki , Rabiya zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , shiru tayi tana kallon Jiddah , Dady yasa aka ɗauki Dikko gaba ɗaya kowa da kowa aka nufi ɗakinshi dashi , a ƙasa Dady yasa aka kwantar dashi sannan ya umarci kowa ya fita har Momy , fita sukayi gaba ɗayansu , magani ya fiddo a cikin wata kwalba ya zuba mishi a kunne dan tun lokacin daya bi Dady ranar da gaya hotunan Sultana zata sha giya idan baku manta ba ai a ranar ya fara faɗa zai kashe kanshi , daga nan Dady yace zasuje saudiyya sai aje da Dikko wurin magani , salati yayi tare da buɗe idonshi , Dady yace Babana ka rufa man asiri ka barni na zauna lafiya…..
         Kai……… Saina kashe Rabiya….. Riƙeshi Dady yayi idonshi ɗauke da hawaye yace yi haƙuri Babana , a , a , saina kasheta……… Kuma saina ɗaure mijinta daya barta take fita har tanayin iskanci a gidana birkicewa yayi daga hannun Dady yayo waje da gudu , Rabiya na ganinshi ta sauka ƙasa da sauri amma kafin ta ida gangarawa ya rigata sauka saboda shi ta sama ya sauko , yana ƙoƙarin riƙeta tace Jiddah ce…… Jiddah tana gani kowa yana rugawa amma sai ta tsaya , sokewa yayi saman guyawunshi zuwa ɗaya yayi mata ta faɗi ƙasa somammiya miƙewa yayi da gudu yabi Rabiya Dady yace ku riƙeshi mana , kai……… Karku taɓani idan kuka taɓani saina kashe kaina , daf da zata fita daga cikin palon yayi mata wani irin halbi ta fice somammiya , itama An mata saina kashe ta……….. Dady yace wai bazaku kwantar dashi ba , wata irin zabura Dikko yayi bana kwanciya ya nufi hanyar ɗakin Sultana , da gudu su Ashiru suka bishi , kai…… Karku taɓani , wai har so nawa zan faɗa bana so ana riƙeni ne…………. ? Ya juya tare da sauke ma Ashiru hannu a ciki ya koma baya ya faɗi ƙasa yana ihu , wurina ya nufo yana zabura cewa saina kashe ki……… Da sauri na jawo lokar bedsite na ɗauko abuna yana matsowa na feshe mishi fuska ya faɗo saman gado ruf da ciki saida ya kalleni sannan ya rufe idonshi a hankali ya tafi hutun taƙin lokaci , haka kawai zan zauna ne aljanu su lahanani ? Sun tsaya bayan fage suna ta iskanci an kasa maganinsu tou ni nice maganin su Allah dai ya bani lafiya.
      Dady bai shigo ɗakina ba Momy ce ta shigo saida ta zageni tas tace kuma Dikkon zai dawo daga duniyar suma zata faɗa masa nice na zubar da cikin zaici ubana kuma zai sakeni , a raina nace wane dare ne jemage bai gani ba ? Aini halin Dikko da duk haukarshi saidai in ba wani labari dan nayi imani nice mutum na farko dana fara ganowa shi mahaukaci ne ,
    Dani da Rabiya da Jiddah aka tattara aka nufi asibiti damu umarnin Dady bayan an tafi dasu Sultana Dady yasa aka fiddo Dikko daga ɗakin Sultana aka maidashi ɗakinshi ,
    Washe gari , duk wani taimako daya kamata anyi mana dukanmu nidai saida akayi min wankin ciki domin likita ya tabbatar da cikin ya lalace saboda allurar ta daɗe a jikina babu wani abu da zasu iyayi , Rabiya kuwa tunda ta dawo batayi ma kowa magana ba , Jiddah kuwa kuka take bata zama da Dikko saiya saketa tana ta ɓaɓɓarka zagi ita ba jaka bace ko a gidansu ba’a taɓa dukanta ba sai wani can ƙaton banza , gaba ɗayanmu dai sallamarmu akayi dukanmu kwananmu ɗaya a asibiti , Yayar Dikko mijinta ya ɗauketa Jiddah Al ‘ Ameen ni kuma Ashiru muka nufi gida , Jiddah kuma wurin Momy ta tafi sai an saketa…..
      A ƙofar shiga ciki naci karo dashi , shi zai fita ni zan shiga ran nan nashi a haɗe yana waya ko inda nake bai kalla ba , gaishe shi nayi ƙaddarawa yayi baiji ba ya wuce , jiki a sanyaye na shiga ciki , Nabeela ta gyara ɗakin ta gogeshi ta sakar mishi ƙamshi mai daɗin shaƙa , sannu da jiki tayimin , kaɗan na ansa na wuce bedroom na kwanta.
      Yana shiga mota kiran Yazeed ya shigo a wayarshi , kallo ɗaya yayi ma wayar ya ajiyeta a gefe yana ƙoƙarin tashin motar wani kiran ya sake shigowa , bai ɗauka ba ya fita daga gidan da tuƙin rashin sanin darajar rayuwarshi , ya kusa isa inda zaije text ya shigo , ɗauka yayi ya duba Yazeed ne mai turo saƙon , hannunshi ɗaya riƙe da sitiyari ɗayan riƙe da waya , dubawa yayi , 
_DK An mata ta fita hanyata , kaga dai har yanzu bata daina bibiyata ba sai bina takeyi ka duba a whatsapp na ajiye maka saƙo danni gaskiya bana san mayata…._
     Da hannu ɗayan daya riƙe wayar ya tura masa…..
_Wace ce An mata kuma…..?_
    _Matar ka…..!_
_Wace…..?_
_Sultana ɗiyar ɗan caca_
_Oh wai An matana……?_
    _Eh_
_Me tayi maka ne ?_
_Tana biyoni duk inda naje…_
     _Tou yi haƙuri ina driving , amma kana ina yanzu sai inzo in sameka muyi magana….._
     Yazeed bai sake turo saƙo ba , ajiye wayar Dikko yayi yana cewa zakaci ubanka idan na riƙe ka , mtsww ko saƙon meye ya ajiye Koma dai miye saina gama zan duba , itama An mata saina sa ta rana kanta tunda bata da wayau bazan sake mata murmushi ba sai tayi nadamar sani na , banda Dady ya bashi haƙuri yace mishi babu mai laifin sai Rabiya tunda taje tayi abinda batayi shawara ba , dan yadda Mardiyya ta faɗa masa ya yadda da hakan shi yasa ya faɗawa Dikko aka ɗorawa Rabiya laifi gaba ɗaga banda haka da saiya tada Sultana aiki yadda ko bata tare dashi ta zama condem bata sake amfanin komai sakara ƙarar yarinya da ita…..
    Bayan ya isa inda zaije yayi parking , bai fita a mota ba tunanin jiya ya farayi , duk abinda yayi ya dawo mishi a kanshi , Allah ka yayemin wahala , lallai An mata ni zata ma haka ko ? Wato ni zata feshe ma fuska ? Lallai yarinyar nan duk yadda akayi har yanzu tana da wani kuɗiri akaina , wata zuciyar tace ba haka bane ba , wani sashe na zuciyar shi yace kaima kawai ka yada ƙwallon mangwaro ka huta da ƙuda , murmushi yayi a bayyane yace An mata bata yaduwa kuma ita ba ƙwallon mangwaro bane ba idan na yadar da ita ina zataje ? Wane hali zata shiga ? Idan har na rabata dani banyi mata adalci ba gaskiya zama da ita dole saidai zan bata wahala a daren yau saina zane mata jikinta tasss , zan zauna lafiya na kwana biyu idan kuma zafin ya huce zan ƙara mata tunda ita ta zama doki sai an daketa zata tafi , bayan kwana biyu kuma zamu haɗu a saman bargo Allah ya baki lafiya jarumata…..
   Fita yayi daga motar ya wuce ranshi a ɗan sauƙaƙen damuwa , kafin ya isa inda ya dosa su Ashiru har sun bayyana a wurin , a hankali mutane suka fara kawo hankalinsu wurin saboda zuwan su Ashiru , DK ya faɗa tare da riƙo hannun Dikko suka taɓa murmushi Dikko yayi kaɗan , abokin nashi ya cire hannunshi tare da nunawa da hannunshi ranka shi daɗe ya kake ya kyau ya zati ya ƙwarjini ya iko ? Murmushi Dikko ya sakeyi yace hali dai na nan Saminu me kazo yi nan ne…..? Ya tambaye shi yana wucewa abunshi ,
      Bin bayan Dikko yayi yana cewa Allah ya kawoni kai ka fito ta can ni kuma na hudo ta nan kaga yauni lafiya lau kenan gani ga mai girma DK , Dikko bai sake magana ba ya wuce ciki saida ya gama dube²nshi yace da yaranshi dake binshi ku shiga ku dubomin shi , sun duba sosai basu ga Al ‘ Ameen ba , jinjina kanshi yayi yace ku wuce muje , yayi gaba suka rufa mishi baya , abokin nashi ne yace DK sallamarni mana nima in sheda , Dikko yace ni kuɗina basu zuwa wasan danbe , dan girman Allah ni yaushe rabona da danbe ai na bar ma su Yazeed , Dikko yace tunda aka fashe idon ka zakace ya faɗa yana dariya , nidai dan girman Allah DK bani , kai ba abinda zan baka , har wurin mota yabi Dikko yana haɗashi da Allah , Dikko kuwa mamakin yadda Saminu ya lalata ma kanshi rayuwa harya dawo ya fara maula abun bai mishi daɗi ba kuma baiso mishi haka ba , saida sukaje mota ya bashi kuɗin da babbban dumtsiya , cah…. Mutane suka rufo wurin suna maula.
      Nidai Momy saiya sakeni , Momy tace ke sakarar banza karki kuskura Dikko ya sakeki ba dan ni na haifeshi ba Dikko miji ne ki riƙeshi wannan lalurar nashi zai zamar mishi tarihi Jiddah ki kwantar da hankalinki ki maido natsuwarki a jikin ki karki kuskura ki bari ya rubuta ko ya furta kalmar saki Dikko da kike ganinshi baida mutunci , haka kuma baida haƙuri kamar amai amma ida kikayi haƙuri komai zai zama dai² amma maganar saki ya fita harshenki ,
Nidai gaskiya bana sansa , cikin rarrashi Momy tace keda ɗan uwanki idan baki so sa dan komai ba kiso sa dan zumunci mana haba Jiddah ina wayanki ina lissafinki ina tunaninki ? Karki ma kuskura kiyi wannan rashin wayan a gaban Dikko dan nayi imani da Allah ko da wasa kikayi masa maganar saki saiya sakeki duk kuwa yadda yake sanki ko zai mutu saiya rabu dake ,
    Nifa gaskiya na gaji ko za’ayi tashin hankalin da ba’a ƙara maimaita kamarshi saiya sakeni , Momy tace ji Jiddah karki yi abinda zai baki damuwa daga baya fa , idan ya sakeni duk ranar dana zo nace kisa ya maidani ki tunomin wannan ranar , Momy tace ai bana fata ma yanzu tashi kije kiyi wanka kici abinci ki huta zuciyarki tayi sanyi , ni babu ranar da zuciyata zata huta sai ya sakeni , Momy tace yi haƙuri Jiddah idan kina gidan Dikko waye ya isa ya shiga ya katantane ? Bare idan “yan uwanshi sunje a watsar dasu a palo , idan kina gidan dake da duk wani ɗan dana haifa da “yan uwana gidan bazaku zama a raɓe ba , kuma idan ma dan wannan karuwar sakinta zaiyi kinga daga ke baza sake aure ba , nidai ko ya saketa bana zama , Jiddah kalmar saki ya fita daga bakinki bakisan hakin Dikko ba , tashi kije kiyi wanka kiyi bacci , tashi tayi tana ko za’ayi tashin hankali sai Dikko ya saketa.
    Al ‘ Ameen dake rakuɓe yace Hajiya ki bari yayi mata ɗaya kila ta huce , Momy tace da Allah rufemin baki ɗan iska fita ka bani wuri , Allah ya taimakeki ya faɗa tare da fita , cikin farin ciki yace a gaban mai gida zata faɗa na gama da wannan wasan sauran Sultana….. Lokacin mu ya kusa farawa !
       Suwaiba kalleni , Dikko ne zaune saman kujera ya kashe zamanshi da ƙafa ɗaya saman ɗaya , duƙar da kanta ƙasa tayi tana kuka , tunda nake faɗin kisa ban taɓa kashe wa ba amma zanyi rantsuwa kuma kinsan halina na faɗa ma na cika bare kuma na rantse idan har kika kuskura nayi rantsuwa zan kashe ki saina kashe ki , in kashe ki kuma na kashe banza dake da ɓeran gidana babu banbanci yadda zan kashe shi ba’a tuhumata abinda yasa na kashe shi haka zan ɓatar dake cikin mintuna biyar zan shafe labarinki a garin katsina ,
Waye……. ? Na rantse girman Allah ga sunanshi a zuciyata amma bana iya faɗa , Dikko yace duk halakacin da nayi miki dake za’a haɗa hannu na zama lusarin namiji ? Me nayi miki haka don Allah….. ? Ki faɗamin shi kawai sai insa a maida ke gidanki cikin mutunci da mutuntawa , wallahi ranka ya daɗe ga sunan shi a zuciyata amma bana iya faɗa , cikin ɓacin rai Dikko yace ku fiddomin zuciyar ta , ta ni idan na duba zan gane ko waye……
25/11/2019 ????????
*JAMILA MUSA….* ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button