KWARATA 82

???? —— 80
Wata irin shewa sukeyi tasu ta matan tasha , gaba ɗaya sun haukata gidan da hayani suna ta nuna yadda sukayi maraicin junansu , bayan sun gama murnar haɗuwarsu kuma suka runguɗa sukayo kicin ɗina cike da
gadara da nuna isa kamar irin gidan baban nan nasu.
Ina tsaye ina ɓare magi suka shigo dan na daina cin abincin gidan kwata² saboda duk idan na ci sai naji tashin zuciya sai nayi amai hankalina yake natsuwa shi yasa na zage nake girkawa da taimakon Nabeela.
Ko inda suke ban kallah ba naci gaba da abinda ya shafeni tunda nasan iskanci ne ya kawo su dan bama kicin ɗaya da Jiddah kowa da nashi , Nabeela tana zaune gefe saman kujera tana waya da ƙawarta suka faɗo tare da fara buɗe² , ke Mardiyya ƙara ruwa ki ƙara yawan magi ki zuba shinkafa bama cin kuskus naci uwar kuskus naci uwar mai dafa kuskus ɗin yarinya tayi magana in shaƙe mata wuyan uwa , duk inji Jiddah fa,
Hahaha suka gaggaɓe da dariya gaba ɗayansu tare da kashewa aka rangaɗa guda cikin iskanci , wacce tayi hoto dani tace yarinya kuma tace uhum taga yadda zamu naɗa mata shegen duka a gidan nan idan kin isa ki kalleni koda motsin kirki kiga yadda zamu ci uwar ɗiyar ɗan wasan caca , suka sake sheƙewa da dariya a dai² lokacin da Mardiyya zata zuba ruwa a tukunya ,
Jiddah kuma ta kwashe magin gabana tana cewa babu fa a gidan ubanta amma dan wani kilbibi hada wani zuba magi sai kace an saba ci a gida , wacce tayi hoto dani tace tsoho harya karci ƙasa baya gane testing in magi baya gane gishiri , Mardiyya tace taya kuwa zai gane bayan baki ya mutu da giya anzo nan za’a nuna mana ƙaryar rashin kunya dama ɗan talaka bai iya samun wuri ba , kashe waya Nabeela tayi tace ke ya zaki ƙara mana ruwa bayan kinga muna sauri shi yasa muke dafa abu mai sauƙi , kallona tayi sannan taci gaba da cewa matar Yaya ya kina kallonsu bazakiyi wani abu ba ? Kinfa san inajin yunwa a gabanki zaki bari a dawo mana aiki baya…..
Ke karki zuba ruwan nan , Jiddah tace zuba , Nabeela tace idan ko kika zuba su za’a samu matsala , ansar ruwan Jiddah tayi tare da zubawa tace ni na zuba “yar gadon rashin kunya marasa ragowa , ni bana neman suna haka kuma bana neman gindin zama tare da Dikko bare a kaɗamin ganye , masu so asan dasu kuma suke so su zauna su haƙuri ya duba dan gudun kar a korasu a koma cin ƙanzo da garin kwali danni a gidan Babana ban rasa komai ba , hehehehe bafa garin kwali ba garin kwaki , Oh ????????♀kinsan abinda baka sani ba danni bansan da labarin gari ba saida na haɗu da Caca
Yarinya tayi iskanci ta koma gidansu aje can aci gaba da cin abinda aka fi wayau dashi , Mardiyya tace sai Aliyu ya sake sakata a caca , Jiddah tace ni kuma zan siye gidan in ajiye karnuka tunda shi dawakai ya ajiye , cikin ɓacin rai Nabeela ta taso daga inda take itama dai “yar babbar bala’e ce ni kuma fita nayi daga cikin kicin ɗin cikin ɓacin rai , wani irin mari Nabeela ta zabga ma Jiddah tare da ɓaro ruwan daga saman gas cikin masifa tace shin ba nace karki zuba mana ba ? To zan sake zuba wasu idan akwai wata “yar ƙaramar mara kunya ta sake taɓawa taga idan ban ƙona mata fuska ba banzaye ƙazaman banza duk kun cika mana wuri da tsamin dauɗa.
Jiddah tace ni kika mara ? Nabeela tace an mareki dan ita Nabeela ba Sultana ta shigar ma faɗa ba cikinta take ma yaƙi sake ɗora tukunyar tayi saman gas ta zuba wasu ruwan , itama Jiddah ta sake ebowa ta ƙara zubawa akan wanda Nabeela ta ɗora sannan ta yanka mata mari wai ta rama marinta , sake ɓare ruwan Nabeela tayi suka sake tashar magana zuwa harshen turanci kowa yana faɗawa ɗan uwanshi kalamai masu zafi daga baya kuma suka fara bige².
Kokowa ta rikice tsakanin Jiddah da Nabeela tun a kicin har suka fito waje , Jiddah na cewa ke har kin isa kice muna tsamin dauɗa , Nabeela tace nafa sanki tun baki san abinda kike ba duk ƙaryar shafa turaren da saka suturar waye ya koya miki in ba ni ba ? Wato yanzu kin waye iskancin ki zai sauka a kaina ko ? Mutuncin da duk wani feleƙe ma nice na siya miki rigar mutunci a gidan auren idan na zare hannuna daga kanki kashin ki ya bushe dusar gero dake…
Mardiyya kuwa komawa tayi daga gefe taci gaba da video , duk yadda akayi a raba faɗan ƙin rabuwa sukayi domin Nabeela tsatstsaga gareta itama kafiya kamar na Dikko kuma ƙarfi gareta dan duk ƙawayen Jiddah shigar mata sukayi , faɗa yayi nisa kuma Nabeela taƙi ta haƙura gashi sunyi mata taron dangi dole saida aka kira Babbar ɗakinsu Dikko wacce ke zaulayarshi tana cewa saida tayi aure aka haifeshi , itace tazo kuma ko ita Jiddah bata ragamawa ba saida ta zagate tasss ta uwa ta uba.
Da mamaki ta kalli Jiddah tace ni kike zagi ? Na zageki dangi masifa ahalin rashin mutunci , bana tsoron uban kowa a cikinku duk wacce tayimin sai inci uwarta , haƙuri taba Jiddah tare da cewa ita Nabeela tazo su tafi , Nabeela tace bazata ko ina ba tunda bata jin tsoron kowa kuma idan ta sake ganin yarinya a kicin ɗin sai ta kunna mata wuta , tayi tsoki ta nufi kicin tana gunguni ,
Ina kwance ɗaki ta shigo taita zagina wai nice munafuka nazo da asiri dan na firgita Jiddah na hanata zaman lafiya da mijinta , saida ta zageni tas itama tayimin mari da ƙwanya ta tsitstsinen min albarka tayimin gori sannan ta tafi.
Daga gidan Dikko G H ta wuce taje ta faɗawa Momy sai an miƙe tsaye da addu’a akan Jiddah yau taga aikin asiri dan tunda take da Jiddah tun kafin asan zata auri Dikko tana ganin mutuncinta kuma tana darata ta amma yau saboda aikin asiri ita Jiddah ta zaga wai mune dangi masifa ahalin rashin mutunci bata tsoron uban kowa a cikinmu duk wacce tayi mata sai taci uwar yarinya , Momy ki duba lamarin nan fa duk da dai niɗin ina da zaulaya ina shiga sabgar yara amma ko Dikko da nake masa hawan ƙawara ina masa abinda bayajin daɗi duk rashin mutunci sa yana ɗagamin ƙafa ni Jiddah ta zaga ?
Gaskiya Momy kija linzamin abun tun wuri idan har kika bari Dikko yasan halin da ake ciki zaije yayi abinda bai kamata ba idan ya dakar musu “ya ko ya saketa zuminchie zai lalace , ya saki wannan karuwar tun abun nan ana iya dakatar dashi kafin yakai fagen da bakya iya tsawatawa , Momy tace taje zatayi magana da Dikko kuma zatayi magana da Jiddah.
Mardiyya ta turama Dikko video n faɗa ya gani amma baiyi magana ba kuma bai kira Nabeela ba nima daya kirani ban ɗauka ba , ya kira har ya gaji ya daina kira dan kanshi.
Mardiyya ita ta dafa abinci wa su Jiddah kuma haka ta barbaɗe shi tas da asiri takai ma kidahumar ta lashe , ni kam kafin Nabeela ta gama ta dawo har nayi bacci tsabar ɓacin rai……
Haka dai nake dogara rayuwar gidan Dikko babu daɗi tsakanina da “yan uwanshi sai kyara sai hantara ga gori basa so na ko kaɗan , Momy kuwa sai bawa Jiddah shawara takeyi tana ɗorata a hanya yadda zata zauna lafiya amma tana nan shawarar ke amfani da zaran ta tafi Mardiyya zata warwareta kaf !
Ƙawayenta ma haka suke wulaƙanta ni san ransu yanzu kwata² ma na daina fita ko palo kullum ina ɗaki sai sun gama iskancinsu sun tashi nake fita da sauri naje nayi abinda zanyi na dawo ɗaki bawai dan ina tsoronsu ba saidai dan gudun rayuwar da zanyi dan a halin yanzu idan nabar gidan Dikko bansan ina zanje ba , gidan Kaka yafi ƙarfina saboda gidan ɗan uwan Inna ne kuma ban auri ɗansa Sultan ba an buɗa , gidan Baba ƙarami bazaije gareni ba Dikko yasa an ɗaureshi saboda ni , Inna bata nan kuma har yanzu ban samu wayarta ba kuma babu wanda yace min yana waya da ita , idan na tashi hankali nayi faɗa da Jidda tabbas Momy zata iya korata idan an koreni nikam ina zanje ? Dan haka zaman gidan Dikko shine mafita zanyi haƙuri idan ma na tayar da hankalina Dikko ya sakeni bansan ina zan nufa da rayuwata ba ,
Ga Bello ga Dady suma duk ni suke jira , shin rayuwar bariki zanje inyi ? Shin zan dawwa a harkar bariki kenan ? Haƙuri shine maslaha kuma na haƙura , ina tare da damuwa sosai na rasa wa zan faɗawa inji sanyi dan haka kawai zan faɗawa Yazeed , dan yace mu haɗu a washe garin waccan ranar banje ba amma ina jira idan ya sake kirana zan fita idan har ya yadda zai bani mafita kuma zai zamar min garkuwa kawai zan fita daga gidan Dikko inje in auri dai² ni sai in zauna lafiya….
Kwance nake a gado ina nazari yadda rayuwata zata kasance idan na fita daga wurin Dikko , tsikar jikina ta tashi a dai² lokacin dana tuno ranar da zai tafi , yadda lokacin ya kasance yazo a zuciyata ya tsayamin kukan da yakeyi nakeji a raina sautin kukanshi cikin shagwaɓa Dikko baijin magana dana tuna sai inji hankalina ya tashi tsigar jikina duk ta mimmiƙe bana tunanin komai sai san kasancewa dashi , Dikko jarumin namiji ne a fagen daga ya iya jan linzamin mace a filin wasan danbe cikakken namiji ne mai zanawa mace natsuwa mara gogewa a rayuwa taya zan iya rabuwa dakai ne…………………?
Muna waya da Yazeed kuma har yanzu nace masa zamu haɗu amma banje ba banma fita ba gaba ɗaya , har Dikko yayi wata 3 da sati3 da tafiya kuma har yanzu ƙawayen Jiddah suna nan kuma suna hantara sbd sun nemeni da les naƙi , sun nunamin duk wani karuwanci naƙi yadda , da sukaji haushi sai suke tira Jiddah ta riƙa jamin sharri a wurin Momy , haka zata turo “yan uwan Dikko su wulaƙantani wani lokaci su mammareni , kawayen Jiddah kuma sunyi alƙawarin zasu jamin sharri wanda bana iya fitar dakaina a wurin Dikko wai ya sakeni in koma inda nafi wayau lokacin nice zan nemesu idan na nemi na abinci da wurin zama na rasa , gashi banda lafiya ni bansan abinda yake damuna ba sam bana san hayani kuma bana san yawan magana , Mardiyya kuwa tuni ta cire hoton da ƙawayen Jiddah suka ɗaukeni a wayarsu wanda suka ɗaukeni washe garin da aka kawoni ta turama Dikko bansan iyakar sharrin data faɗa ba ko na kirashi waya baya ɗauka rabon da nayi waya dashi tun ranar data tura mishi hoton ya turamin kuma ya kirani yace shi bazai sakeni ba duk abinda naji ina iyawa inje inyi kaina nayi ma, ba bugu ba zagi amma idan na kasheshi na huta , gashi shi baya tsayawa ya fahimceke idan dai ya sauke nashi shikenan ,
Na rasa wanda zanyi shawara dashi , da na fara tunanin su Amisty sai zuciyata ta gargaɗeni da na fita hanyarsu gara dai na faɗawa Yazeed tunda tun farko shine ya faɗamin cewa idan ina da damuwa na faɗa masa zai bani shawara , wayata na ɗauka na kirashi bayan mun gaisa nace yau zan fito ina zan sameka ne ? Wai yana jibiya , zanzo jibiyar wurin ina kake ne ? Ba’a kai jibiya ba kinsan me mujiya ? Ina ne haka ? Hirji matattara tantirai , yaushe zaka dawo ne ? Sai DK ya dawo , yaushe zai dawo ne ? Gobe idan Allah ya kaimu , zanzo hirjin , sai kinzo yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
Dakel nayi wanka na shirya cikin riga da siket na material cikin kayan da Yazeed ya kawomin wanda wurin kai ɗinkinsu ne Bello ya sossoka min wuƙa , kwalli kaɗai na shafa sai viseline dana shafama bakina kaɗa bayan na shafa mai da powder a fuskata , Nabeela tace nayi kyau kuma saida tayimin hoto , komawa nayi gefen gado na zauna bayan ta gama ɗaukana hoton ina neman sa’ar fita , wato inaji Dikko bai faɗa zai dawo ba kawai zaiyi mamaye ne dan da Jiddah tasan zai dawo ƙawayenta zasu bar gidan kuma dole zatayi gyara na musamman dan taci burin dawowarshi duk kuwa data kira aurenta dashi na ƙaddara ne.
Nabeela tana shiga toilet wanka na ɗauki jakata gyale na da makullin goruba na fice abuna , a bakin get na samu Umar muka gaisa yace Hajiya ina zakije ne ? Goruba na faɗa kai tsaye , yo ke baki san mai gida ya dawo ba ? Yana ina ne ? Yana abuja ai shi yasa ƙawayen hajiya zasu tafi nine na samo musu mota tasha baki ga har an fara fitowa da kayansu ba , waye ya faɗa musu ya dawo ne ? Ni na faɗa musu nima abinda yasa na sani Ashiru yacemin na gyara masa ɗakinshi kila shigowar dare zasuyi gobe idan Allah ya kaimu , daga cewa kayi shara sai kazo kayi ta surutu kai bakinka me yasa baya shiru ?
Dariya yayi tare da cewa tubani neke ranki ya daɗe , murmushi nayi cewa tou bani aron motarka na dawo , bani yayi na wuce na shiga naja nabar gidan cike da damuwa , naso ace Dikko ya samu ƙawayen Jiddah yaci ubansu , amma nasan ba saboda su yayi shiru da dawowarshi ba nasan dan Al ‘ Ameen ne , saida na fara zuwa goruba na gyara ɗakin na kama hanyar jibiya.
Wata irin zuba Al ‘ Ameen ya goge da boka ya kirashi a waya ya sanar dashi cewa Sultana tana da ciki , tashin hankali gashi Dikko zai dawo gobe kuma yanzu Zaria bata zuwa gareshi kuma boka ya tabbatar ma Al ‘ Ameen ita kanta Sultana bata san tana da cikin ba , idan kuma har Dikko ya dawo cikin bazai zubdu ba duk irin baƙin asiri da za’ayi shawara ɗaya yasan yadda za’ayi a zubar da cikin dan wallahi ɗa namiji ne zata aifa ,
Cike da tashin hankali Al ‘ Ameen ya kashe wayar ya kira Jiddah ya faɗa mata cewa idan har ta kuskura aka haifi cikin nan wallahi ƙaryarta ta ƙare duk yadda za’ayi a zuba mata abinda zata ci cikin ya zube , cikin rashin fahimta Jiddah tace wake da ciki ne ? Al’ Ameen yace Sultana mana Jiddah tace yaushe ta samu cikin kuma waye yayi mata cikin ? Al ‘ Ameen yace mai aurenta mana , Jiddah tace ƙarya ne ai Yaya bai kwana da ita ba , Al ‘ Ameen yace tou tana dai da ciki kuma ɗa namiji zata haifa idan ko ta haifi ɗan nan na rantse da girman Allah ƙaryarki ta ƙare kisan yadda zakiyi da cikin nan ko maganin zubar da ciki ne ki bata a abinci ko abun shanta , saida Jiddah ta sunsunkuya zagi ta luƙaƙashi sannan tace ta daina cin duk abinci da ba itace ta dafa ba a gidan nan dan uban uwarta , shawara dai Al ‘ Ameen ya bata akan ta kira Yayyen mai gida ta sanar dasu ya faɗa mata abinda zata faɗa musu , godiya Jiddah tayi tare sa kashe wayarta tana neman mafita , kam ya zata yadda ita bata aihu ba sai wata data zo ɗazu da safen nan………? Bazai yuwu ba koda duka sai sun fitar da cikin nan.
Da tambaya har na isa inda Yazeed yake tunda ni bansan wuri ba mutane ne sukayi ta ɗorani a hanya har naje , bayan na isa na sanar da Yazeed nazo na faɗa masa inda nake yace yana zuwa , an daɗe sosai sannan yazo ta wata munafukar santa ya fito da mota , gaba yayi nabi bayanshi munyi tafiya mai nisan gaske wanda har na fara tunanin na kawo kaina , wato abun ba’a cikin inda za’a gansu sukeyi ba sunyi nisa da mutane , daga inda yace na sameshi zuwa inda ake wasan tafiya ce mai nisan gaske inajin su kaɗai ne suka san wurin.
Muna isa na samu wuri nayi parking dandazon mata ne kamar ƙasa karuwai da suka ansa sunansu , murzajjin “yan iska da suka sha iskanci har sukayi gyatsa saboda lalacewa , wai ana gabatar da shirin wasan danbe babu jimawa , dan haka maganata Yazeed ya hana na faɗa wai in jira inga yadda ake wasan danbe sai muyi magana daga baya , haka mukayi ta ratsa mutane muna wucewa da yawa a wurin na sansu , Safiyya ɗiyar Baba ƙarami tana gani na ta taho da gudu tana zage² wai nice nasa aka kulle babansu , Yazeed ya dakatar da ita wai ta kiyayi kanta idan ba haka ba zai goge sunanta dama Kaka ta matsa masa yaa saka sunanta , laƙwas ta koma bata sake magana ba , gabana sai faɗuwa yakeyi nake bin bayan Yazeed , wato abinda na lura karuwan kila akwai manya akwai ƙanana domin an kasasu wuri daban² haka muka wuce har muka isa wani ƙaton wuri , tsakar fili ne na gida amma an zagaye wani wuri daban an ɗaga wurin da ciko yayi sama yadda duk inda kake zaka iya hange kamar dai yadda akeyin na restyling daga saman wurin kuma an ƙawatashi da wasu irin manyan katifai da pilaluwa an shinfiɗe da zanin gado ,
Wurin wasu lafiyayin maza ya kaini duk gajeren wando ne a jikinsu wai in gaisa dasu sune mazan da zasuyi wasa , murmushi nayi kaɗan na anshi karka rasa fuskata ɗauke da damuwa , bayan mun gaisa yace musu matar DK ce , DK ???? suka zazzaro ido da mamaki sannan suka bini da kallo har naji babu daɗi , bayan sun gama kalleni tsaf sukace tou su babu ruwansu suka ci gaba da lissafin kuɗinsu , Yazeed yace taho nan ki kyalesu matsoratan banza ,
A , a , ni tafiya zanyi kawai mayi waya ai bansan haka wurin yake ba , Yazeed yace da Allah ki jira kiga danben dana baki labari kwanaki baki sani ba , a , a basai na kalla ba , wayarshi ya ciro a aljihu yana cewa tsaya ki gani mana kafin na ankara ya ɗaga wayarshi ya kwaso mu hoto solfie , zan masa magana akan me yasa ya ɗaukeni hoto Amisty ta shigo da gudu ta rungumeni cikin farin ciki da sauri na juya amma Yazeed ya ɓacemin , wata irin zuba ta ketomin yayin da zuciyata tace bakiyi zufa ba tukun ƙaryarki ta ƙare……
Amisty tace ai ana cemin kinzo kinji daɗin da naji , cikin tashin hankali na saki Amisty nabi hanyar da zan nemo Yazeed iya dubawa ta ban ganshi ba , tou me yake nufi ko ya ɗauka ne dan ya riƙa hansar kuɗaɗe a wurina kamar yadda na riƙayi a baya ? Kwawalwata tace ya ɗaukeni dan ya turawa Dikko idan ya gani zai sakeki shi kuma saiya ɗaukeki ya sakaki a danbe yana kasuwanci dake dan dama haka ya faɗa a baya…….
Dariya Yazeed yayi a dai² wannan lokacin cewa alhamdulillah nasara tazo haba ina zan bar DK da wannan babbar ƙaddarar ? Yarinya kyakkyawa mai kyan diri da siga mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayen namiji , kai ko mara lafiyar ya ganta dan ubanshi saita burgeshi munafiki ya samu “yar yarinya yana hutawa abunshi ai ba taka bace ba wannan nagartacciyar surar , tunda dai ban aura ba gara kowa ya rasa , ka tsere ma kaf abokanmu a naira riga mota matar ma sai kafi kowa ? Idan mun yadda kenan kai mana wayau , yadda nake ƙarƙashin ka gara na samu ko da macen na tsira , kai sarkin dabara kawai kaje ka ɗauko ɗanyen jini dan ka bamu wahala haka zamuje muna ganinta hankalinmu yana tashi to ni burina kawai ka saketa hankalina ya kwanta dan nan gaba yarinyar nan ta goge bata riƙuwa ga kuɗi ga hutu ga gayu dan yadda DK yake ɗan gaye dole komai nasa ya zama ɗan gayu , gara ni in kwasheta idan kuma bata aureni ba sai kawai in barta a wasan danbe nasan duk lokacin dana buƙace ta zan ɗan rage zafi uwa uba kuma zan linka arziƙi dan duk katsina banga irin mazan da zanba ita ba.
Na nemi Yazeed har na gaji ban ganshi ba , kuma na kirashi bai ɗauki waya ba , dan haka na haƙura na fito daga inda nake dubashi na sake dawowa wurin da ake taron danben a lokacin wurin ya cika taf tsit kake ji babu wata hayani ana kiran sunaye….
Hamida Aliyu Muhammed Binna , shine sunan da naji an kira tsagal² ta tashi ta shiga saman filin aka ɗauki ihu da tafi yayin da wasu ke busa usir , idan mutun ya shiga filin saiya tsaya ya kalli mutane sannan ya tuɓe kayanshi ya tafi da kwarkwasa ya hau saman katifa , sai a sake kiran wata itama haka zatayi duk sai an gama kiran sunayen matan sun hau katifa sai a kira mazajen da zasuyi wasan su jera layi sai aci gaba dakai naushi.
Banda lokacinsu domin ina tare da tashin hankalin daya fi wanda naga Hamida a ciki tunda ita tayi kuma kowa yasan tayi fita nayi daga wurin ina kuka , nifa ? Ina hotona zaije ? Kai nidai jakace…….
Aunty kusan abinyi fa dan Caca ciki gareta kuma wallahi ko ranar da aka kawota Yaya dani ya kwana a ɗakinshi kuma washe gari ya tafi amma tana da ciki , idan har ya dawo ya samu cikin nan zai yadda yace nasa ne saboda ta gama dashi za’a ɓata muku ahali shege ya fito a cikinku , idan kuma aka saketa ta fita da cikin nan shima idan ta haife cikin shima shine zaice nasa ne , gobe zai dawo meye mafita ? Zan shigo idan Allah ya kaimu suka ajiye waya , bata faɗawa Momy ba kawai ta yanke hukunci a kanta….
Sai bayan isha’e na dawo gida a gajiye a waje na bada makullin motar Umar a ajiye mishi idan ya dawo , Nabeela tana gani na tace ke kinji kunya kika shigo da cikin shege a gidan aurenki , kin ɗirka dabkekiyar asara ai Yayan zai dawo zaki faɗa masa a gidan uban waye kikayi ciki…
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji na wuce ciki ban nuna damuwa ba , ikon Allah ashe ciki gareni ? Allahu akbar sai yanzu ma na tuna da yaushe rabon da inyi jinin al’ada , daɗi naji sosai a zuciyata addu’ata ta farko Allah yasa in haifi mai kama da Dikko komai da komai , tunani na biyu ya akayi suka san ina da ciki bayan ni ban gane ba ? Can su suka sani dai , kuma Dikko zaizo ya faɗa musu shine yayi cikin ba cikin shege bane ba , da farin ciki nayi bacci tare da tunanin Dikko.
Da asuba bayan nayi sallah bacci na koma , ban daɗe da kwanciya ba na tafi bacci yauma ya bayyana a mafarki na , kinga inda ya ajiye ne ko kuwa ? Ya tambaye ni , ban gani ba kuma na tambayeshi yace baya san surutu , tou albishiri na kwakwale amma yau ba’a mutu ba kina da ciki kuma zasu zubar da ciki kiyi ƙoƙari ki samoshi idan ba haka ba haɗuwa ta gaba tafiya ce babu fashi , waye zai zubar dashi , ta inda mutumin nan ya fito a ranar da nayi mafarki a goruba yauma ta wurin ya fito ya kamashi da kokowa , yana cewa waye yace ka faɗa ne ? Kokowa sukeyi sosai har mai cewa ya kwakwale ido ya samu damar cire abunda mutumin ya rufe fuskarshi , Al ‘ Ameen na faɗa lokacin da aka cire abun daya rufe fuskarshi a dai² wannan lokaci naji saukar bulali a jikina……
A firgice na farka daga bacci Jiddah da Yayar Dikko suke ta dukana babu ji babu gani , da sauri na sauko daga saman gado ina cewa me nayi muku ne ? Jiddah tace dole ki tambaya abinda kikayi tunda kinje kin samu an ɗuro miki ciki ke zakici dukiya tou Allah ya warware miki asiri tun ba’ayi nisa ba , riƙeni Yayarshi tayi Jiddah tayi ta kaimin duka a ciki da bokitin ƙarfe wani irin ihu nayi nunfashina ya tafi sama na kasa kwacewa , saida ta gaji sannan suka danneni ƙasa Yayar Dikko tayi min allura suka fita daga ɗakin bansan inda kaina yake ba.
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un Dikko ya faɗa tare da cewa Ashiru An mata wani abu ya sameta , Ashiru yace me kuwa zai sameta mai gida , Dikko yace tabbas wani abu ya faru wallahi dan naji a jikina wanda rabon da inji haka har na mata kiramin ita , duk kiran da akayi ma Sultana bata ɗauka ba , cikin tashin hankali yace kiramin Nabeela itama bata ɗauka ba , Jiddah yace a kira , itama bata ɗauka ba dan tabar wayarta a ɗaki tana ɗakin Dikko ita Mardiyya wai suna gyarawa , Mardiyya yasa aka kira tana ganin wayar Dikko ta fita daga wurin Jiddah sannan ta ɗauka , bayan ta gaishe da Ashiru yace mai gida yace kina gida ne ? Eh , tou meya faru a gidan ? Saida tayi dube² tace nidai naji ana cewa an zubar da cikin Aunty Amarya….
Kallon Dikko Ashiru yayi tare da cewa mai gida wai bata gida bayan ya kashe wayar , tsoki Dikko yayi cewa tafiya katsina ya kamani yanzu , Ashiru yace ka bari sai anjimar mana , umm umm muje yanzu , kallon agogo yayi yace la’asar tayimin a katsina.
Mardiyya kuma komawa tayi suka ci gaba da aikinsu , Nabeela kuwa bata nan bata san abinda akeyi ba dan tana makarata , su kuma hidimarsu sukaci gaba dayi mai kwalliya ta musamman Jiddah ta gayyato danni taci gayu yadda zata yaƙi zuciyar Dikko , Mardiyya ta tsareta da kallo mai tattare da maganganu.
Sai bayan la’asar Nabeela ta dawo har yanzu ina kwance a wurin da akamin allura na suma har na dawo da kaina na kasa ko motsin kirki wani irin ciwo cikina kammar raina zai fita , cike da fargaba Nabeela ta durƙusa gabana tace waye yace miki ana zubar da cikin shege a gida ? Daga na faɗa miki sai ki kashe kanki tou ni tafiya zanyi wallahi bakija min sharri , tana faɗin haka ta miƙe ta fara tattara kayanta , bata gama haɗawa ba Dikko ya bayyana a ɗakina misalin ƙarfe 4:29pm.
A tsorace Nabeela ta gaishe shi ta fita daga bedroom in , bai ansa gaisuwar ba ya nufo inda nake , hararata yayi cewa wani kuma sabon rashin mutunci ne kwanciya a ƙasa ? Yayi maganar yana ɗan tauna cingom bakinshi a rufe , kifa kaina nayi ƙasa dakel nace banda lafiya , me ya sameki ya tambaya cikin sigar lallashi….
Shiru nayi , da damuwa fa , banda lafiya ga naje wurin Yazeed kuma ban san laifin da nayi ma Dikko ya daina ɗaukar wayata ba , idan kuwa ya gano ni yau idan ya fara dukana waye zai ƙwaceni gashi ban iya tashi………?
24/11/2019 ????????
*JAMILA MUSA…..* ????????