KWARATA 79

???? —— 77
Murmushi nayi tare da shiga toilet na ciko boket da ruwa nazo na sheƙawa Jiddah bala’e Caca ni kika jiƙa ta fara anbaliyar aman zagi na “yan tasha ban bi takanta ba na koma toilet na sake
cikowa nazo na zuba a gado sannan na mayar da bokitin na fito har yanzu bata daina zagi ba , bayan na fito na matsa gabanta nace sa idonki a nawa wace ce ke ? Waye Dikko ? Anshe goruba a hannun kuturu ba wuya yake ba , makaranta guda gareni da na tara taron mata nake basu ilimin zaman gidan aure nice malamar , ke har kin isa Dikko a nawa yake ? Bare kuma ke da baki da lissafi balbaɗaɗɗa mai tona asirin mijinta , ni bana kuri haka kuma bana cika baki a zahirance nake bayyanar da saƙona , maganar Dikko da ɗakinshi rashin cin kaza ko ya kwana a ɗakinki ba damuwa na ne ba , amma zan nuna miki yadda ɗakin miji ke zai gagareki shiga sakarar banza , kuma daga yau idan kika sake cemin Caca saina caccake miki idon uwa.
Wani irin duka takaimin a fuska a wahalance na riƙe hannunta tare da cewa bani zaki daka ba ki koma wurin wacce ta faɗa miki saiki faɗa mata abinda nace idan ta baki ansar magana na kya dawo , kokowa ta kamani dashi ga sulbin tiyels da aka jiƙa kuma ai Jiddah tafi ƙarfina tunda shekarunmu ba ɗaya ba , bamu wani daɗe muna cakusawa ba Dikko ya shigo cikin ɓacin rai gaba ɗayanmu saida ya zazzabga mana mari sannan yace meya haɗamu ?
Cikin fushi na juya mishi baya ina kuka ƙasa² , itama Jiddah kuka takeyi kunsan “yan gayu basa san wahala tasha mari ni kuma dama na saba , ni kuma yunwa ce ta saremin guyawuna da kuzarin jikina , cikin kuka take faɗawa Dikko abinda nayi mata da turanci , raina a ɓace nace idan ba munafurci ba a faɗa da yaran dana sani mana , Dikko yace ma Jiddah ta tafi , juyowa nayi tare da cewa ina zatace ? Ai babu inda zataje kayi gulma kace taje kuma ? Allah dai ya haɗani da munafikin miji.,
Nine munafiki An mata ? Eh idan ba munafurci ba kaje kacewa Jiddah ka ƙagara Mom inka ta dawo ta wulaƙantani baka so na ni jakace shi yasa baka siyomin kaza ba , ita kuma a daren farkon ta taci kaza tasha lemu ni ko ruwan faro baka bani ba , itace farar mace alkebbar amarya , bazanje ɗakinka na kwana ba shi yasa ta jiƙamin jikina da gadona wai a gidanmu ba’a hawan gado zan kwanta a ƙasa sanyi ya kamani ɗakin miji yafi ƙarfina bare na fara tunanin hawan saman gadonka , kuma jiya a ɗakinta ka kwana kana mata magiya , Dikko yace nine na kwana a ɗakinki ? Yayi maganar yana kallonta ? Yaci gaba da cewa nine nace miki ina jiran Momy ta dawo taci mutuncinta ? Ni nazo ɗakinki ???
Fuuu Jiddah ta fita daga ɗakin , kallona Dikko yayi sannan yace kebaki gane sharrin mata ? Na rantse da girma Allah bayan na fita daga ɗakin nan naje zanyi wanka in dawo kuma kema haka nace miki ina dawowa , toilet ina na samu Jiddah tanayin waya , nazo zan shiga toilet sai…. Tsoki Dikko yayi tare da cewa bama zan faɗa miki ba ni nasan abinda yasa ban dawo ba kiyi magani na , kawai kadaiji kunya an tirka ka.
Kuma ni bazanyi maganin ka ba saidai ayita ta ƙare kawai ka bani tikitin saki nayi gaba abuna , danni bana iya zaman takura haka kuma bazanyi haƙuri da wulaƙancin dangin miji ba , wai ke ni zaki maida ƙaramin yaro , ina faɗa kina faɗa ni zaki maida kamar mace kina sakani a shirmenku nine aka turke? Tou ki buɗe kunnen ki da kyau ki saurareni idan har nasan zan sakeki a rayuwata da bazan ɓatawa kaina lokaci na auroki ba , da bana sanki ko kuma nasan zan auroki dan naci zarafinki dana barki a tare dani kawai na zamar dake karuwata , idan zanyi kawai zanyi ne idan banayi banayi kamar iska haka nake yayin dana taho babu wanda ya isa ya tareni sai nakai , ni bana lallashi kuma ban iya ba saidai idan kinmin yarinta zan zaneki ba abinda ya dameni ki dawo da hankalinki jikinki kuma kisan inda yake miki ciwo ,
Bawai zan zauna nayi ta kare miki faɗa ba dan idan yau ina nan gobe bana nan , ki koyi haɗiye damuwa da ba abun duniya baya dan ba komai kake nema ka samu ba a rayuwa , kuma bawai kullum zakiji daɗi ba abinda kike so bashi zaki samu ba , domin rayuwa juyawa takeyi kuma tana tafe da darussa da dama wata rana uwa zaki zama dole sai kin zama jaruma a gidan aurenki domin ta haka kaɗai zaki fuskanci rayuwa , idonki zaki buɗe sosai ki gano abinda yake tafiya a gidan nan kiyi maganin damuwa tun kafin ta dameki kiyi ƙoƙarin gusar da abin harin rayuwarki tun kafin ya gama farautar abun harinsa ya fara farautar taki rayuwa , duk wanda kika gani a gidan mijinshi yana da tashi matsalar , wata uwar miji , wata dangin miji , wata abiyar zama wata mijin ne gaba ɗaya , keda kina nufin kinzo zaki kwanta idan abin ya dameki ki ɗaga waya ki kira Dikko ya tare miki faɗa ? Ki gyara tunanin dan wallahi ko a gabana Jiddah ta faɗar dake sannu bazance miki ba , bana san zama faɗa da zage² tayar da fitina yana lalata arziƙin namiji kiyi haƙuri duk abinda tayi miki wata rana zai zama labari , baki yunwa baki ƙishirwa ba rashin sutura ko damuwar wurin zama , idan zaki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya tou idan kuma kincemin yarinta ina da maganinki ,
Ita kuma Jiddah bata da lissafi tana tare da makashinta bata sani ba , nasan halinki sarai idan har na faɗa miki maganar nan kikayi gori wallahi idan naji saina zaneki da bulalar dukan doki , ni nace Mardiyya ta tafi Jiddah tace baza ta tafi ba , zagina fa tayi wai babu gidan ubanda zataje , tou idan baki sani ba Mardiyya ta turomin text , wai ga Aunty Jiddah can bata san zaman lafiya taje tana matsawa Aunty amarya , Aunty Jiddah bata san zaman lafiya ta cika tsatstsaga , amma zan faɗawa Jiddah dan tasan matsayin Mardiyya a wurinta dan ita tana ma Mardiyya kallon mai santa hmmm zata kaita ta barota domin duk ranar da haƙurina ya mutu zanyi ɓarna a gidan nan….
Ki fita harkar kowa kiyi rayuwarki tun kafin fushina ya shafeki , yanzu a ina zan kwana , cikin hayani yace ban sani ba , goge hawaye na nayi tare da matsawa can daga nesa shikenan kuma bazan ci kazar ba ? Fita yayi daga ɗakin bai sake magana ba , cire kayan jikina nayi na shiga wanka ina tunanin Mardiyya , tabbas a maganarta akwai lauje cikin naɗi , tana da wata manufa nata na daban , miye tsakaninta dani da har zata faɗawa Dikko ? Kuma har take goyon baya na ?
Ba kece damuwarta ba zuciyata ta bani amsa , yayin da maganganun Mardiyya suka fara dawomin a cikin kaina , Ni nan da kika ganni nafi haɗarin jirgin sama kyan gani , ni haɗarina girma ne dashi domin idan nabi ta rayuwar mutum na fita tou fa lallai ya gama rayuwa har abadan duniya , na shigo gidan nan da niyar tarwatsawa ai kin tuna labarin dana baki a mota ko ?
Lallai wani abu zai faru ko kuma yana faruwa , shi kuma Dikko yacemin idona zan buɗe sosai na gano abinda yake tafiya a gidan nan kiyi maganin damuwa tun kafin ta dameki kiyi ƙoƙarin gusar da abin harin rayuwarki tun kafin ya gama da abun harinsa ya fara farautar taki rayuwar , duk wanda kika gani a gidan mijinshi yana da tashi matsalar , ki gyara tunaninki dan wallahi ko a gabana Jiddah ta faɗar dake bazan miki sannu ba , wanka na naci gaba dayi ina tunanin duk amincin dake tsakanin Mardiyya da Jiddah shine take mata zagon ƙasa…….?
Jiddah ki farka idan bacci kikeyi Mardiyya bata sanki dan zata kaiki ta baroki , zata kaini ta baronin kai takai ta baro ne ? Tunda an ƙunsa ka a ɗaki an faɗa maka ƙarya da munafurci ai dole zakace bata so na , um umm ita ta faɗamin kuna faɗa da An mata wayarshi ya miƙa mata cewa duba ki gani , ansa tayi ta gani Dikko ganin ranta ya ɓaci yasa yace kindai gani ko ? Tou ki dakatar da ita domin da zaran na yanke hukunci tou fa ko kaina bana saurara……. Cikin ɓacin rai ta fita daga ɗaki ,
Daren jiya
An mata nasan baki iya ɗaukar Dikko wahala zan baki “yar yarinya ta bara dai inzo muyi bacci kinji ko ? Yana faɗin haka ya fita da tafiyarshi ta sakakkin ” ya “ya.
Wayoyinshi ya ɗauka daga palo ya shiga bedroom , a gefen gado ya ajiye ya tunkari ƙofar toilet kai tsaye , magana yaji ƙasa² a dai² lokacin daya dafa handle in da niyar murɗewa ya shiga muryar Jiddah yaji tana cewa Al ‘ Ameen Mardiyya tace kana kirana shiru , bayan wani lokaci tace taya zan fito bayan gidan yana cike da mutane idan an ganmu tare mutane zasu ɗauka wani abu a tsakaninmu tunda bakwa shiri yanzu , shiru , wane maganin ? Na zuba ai , ɗakinta , a , a idan ya gano da damuwa nan zai birkice kuma kaga damuwa za’a samu , ba komai mu haɗu ta ƙofar baya misalin 3:15 sai in baka , ba damuwa , idan kaje ka haɗani dashi zamuyi magana , yawwa sai anjima , fitowa tayi taga Dikko a tsaye a wayance yace ranki ya daɗe kema kinyi wankan ne ? A , a , ta bashi ansa , murmushi yayi tare da rumgumarta suka koma toilet in tare da tunanin me aka zuba a ina aka zuba ? Kardai itama An mata kamar na Sadiyya zai faru da ita ?, an zuba , kuma an kira ɗakin ta shine bai gane ba , bayan sun fito wanka ne ya kulle ƙofa yace ma Jiddah tare zasu kwana ,
A damuwance yaja ta zuwa saman gado bayan ya gama shirin kwanciya bacci , Sadiyya tazo mishi a zuciya ta tsaya mishi wayayya “yar gayu tanayin abu irin yanayin na An mata itama ma’aboci hawan jikinshi ce kafin suyi aure ,
A asibiti.
Ranta ne ke ta kai kawo tsakanin maƙoshi da zuciyarta , hawaye yana zuba daga idonta tace ka yafemin kuma karka riƙeni a zuciyarka ka manta da abinda nazo maka dashi a daren da yafi ko wane dare farin ciki , amma sai ya zamar maka dare mafi muni a wurinka , na kasa sarrafawa bana iya danne sha’awata ka yafemin don girman Allah ta haɗa hannayenta biyu ????????tana kallon Dikko ,
Riƙe hannayen nata yayi tare da cewa na yafe miki nifa dama ban wani riƙe ba na faɗa miki na yafe miki² na yafe miki Sadiyya ya ƙarasa maganar yana kwantar da kanshi a gefen allon kafaɗarta yana ci gaba da cewa wai miye matsalar kukan nan ne haba Sadiyyata ki daina saka damuwa a ranki har abadan duniya wallahi na manta da wannan damuwar a raina , kayi min alƙawari ko bayan bana nan bazaka faɗawa kowa ba , nayi alƙawari bare ma kina nan bazaki je ko ina ba muna tare insha Allah , faɗamin meye ne ? Ya ƙarasa maganar yana ɗagowa ya ƙureta da kallo.
Fashewa Sadiyya ta sakeyi da kuka Dikko ya riƙeta da riƙo mai nuni daya martabata yace bana san kuka fa nidai sauri ƙufula gareni faɗamin meye raina ya fara ɓaci zanyi fushi cikin mintuna biyu , cikin ɓacin rai yace me ne ? Murmushi Sadiyya tayi tare da cewa Allah zai baka lafiyar damuwarka idan na ganshi bana iya ganeshi amma idan naji muryarshi a yaranka zan gane maganar shi saboda bana ganinshi waya mukeyi yana bada saƙo ana kawomin kuma da sa hannunshi a lalurarka ya haɗa kai da matan Babanka an gurgunta maka rayuwa akan naira miliyan biyu , yayi amfani dakai ya kai min rayuwata ƙarshe bashi da imani duniyar kawai yake so shi akan kuɗin zai iya koma miye….
Waye ? Dikko ya tambayeta , sunan sa da sanin waye shi ban sani ba , ke me yayi miki ne ? Sama lumfashin Sadiyya ya ƙarayi cike da soyayya ta kalli Dikko sannan taci gaba da cewa.
Na taso cikin soyayya da kulawa ta iyaye , iyayena shahararrin “yan boko ne suna da cikar arziƙi yahudawa ne sosai wanda basu damu da rayuwar yaransu ba , gani na a sake yasa nakeyin rayuwar data tari gabana bawai rayuwar iskanci ba rashin ji lanƙwasa gandar aiki bana aikuwa idan na shige ɗaki sai zanje makaranta nake fitowa , ɗakina babu mai zuwamin daga ni sai rayuwata sai kuma wanda naba izinin shiga.
Rayuwata ta samu matsala ne a makarantar kwana { boarding }, bayan nayi jss3 a makarantar jeka ka dawo wato day aka kaini makarantar kwana , ni bana san boarding saboda wahalarta , amma fur Hajiya tace sai naje , na shiga damuwa Yayuna maza sukace dama da makarantar kwana na dace haka sukayi ta zugawa tun Dadynmu bashi da ra’ayin haka harya amince na tafi boarding.
Ina shan wahalar makaranta yadda ya kamata domin dai ina bacci kamar a gida ina fita sch amakare kulle sai prefect sun zaneni , ni ban saba da wahala ba , kullum haka ake cimin uwa amma kullum saina makara kuma basa gajiya sai sun zaneni.
Yauma gani durƙushe a gabansu S P inmu ce tace karku daketa ke zo nan , tashi nayi naje gabanta na durƙusa wasa tayi da bulala a jikina sannan tace me yasa bakyajin magana ke jakace kullum ayita dukanki bakyajin zafi ne ? Kiyi haƙuri bazan ƙara ba , kullum haka kike faɗa kin raina nasu ko ? A , a , hijabina ta cire ta zaneni saida ta tabbatar ta farfasamin jikina sannan ta wurgomin hijabin tace tashi kije.
Yinin ranar kuka na yini yi , tun daga wannan ranar ta sakamin ido ko hostel bata bari na zauna lafiya nine ibo mata ruwa wankinta tsefe mata kai gyaran ɗakinta komai dai nice nakeyi mata banda lokacin kaina sai nata , wahala yasa na rame nayi baƙiƙƙirin ,
Tsugunne nake a ƙofar ɗakinta ina jiran fitowarta daga kwanar wata ƙawarta da gudu ta safko daga saman gado tana dariya tace ke ɗaukomun ruwan wanka nan , ɗauka nayi nabi bayanta har toilet , ajiye ruwan nayi zan fita ta riƙoni tare da cewa kwancemin towel ina , cikin jin kunya nace yi haƙuri Aunty , bazanyi ba kunce shi kafin ince ke zakimin wanka nan cire kar na sake miki magana , kiyi haƙuri don Allah , idan kika sake bani haƙuri saina ja miki sharri na hanaki zaman lafiya a makarantar nan kuma zan sakawa rayuwarki ido kuma saina miki fyaɗe zan lalata ki ne ba abinda ya dameni , zaro idanuwa nayi nace fyaɗe kuma ? Dama mace tana ma mace fyaɗa ? Dan Allah kiyi haƙuri , idan kika bari na sake magana zanci ubanki , rufe idona nayi tare da kai hannuna saitin da nake tunanin tana nan ashe baya taja , buɗe idona nayi dan ganin ko banyi saiti ba , daga can ciki na ganta ta sake wuri tana cewa ke nake jira ,
Cikin toilet in na shiga dan daga waje nake , shigo ki rufe ƙofa , dan girman Allah kiyi haƙuri, bana san haƙurin nan daga bakinki kullemin ƙofa nace , shiga nayi tare da cewa ai zan kunce basai na rufe ba , murmushi tayi tare da matsowa ta rufe ƙofa ta cire towel in jikinta babu kunyar Allah bare ni , ciremin hijabina tayi ta ɗora a saman inda ta ajiye towel inta tace kina so in daina dukanki ? Shiru nayi idona a rufe , bakyaji ina magana buɗe idonki mu fahimci juna , ƙin buɗewa nayi kuma banyi magana ba ,
Dariya tayi tare da ƙoƙarin fara ciremin rigata , riƙe jikina nayi da karfi ta yadda bazata iya cirewa ba , murya a sanyaye tace Sadiyya buɗe idonki mana , ƙin buɗewa nayi danni gaba ɗaya kunya ya kamani wannan ƙatuwar zata cire kayanta jikinta a gabana , hannuna ta kamo ta ɗora a saman ƙirjinta kamar wacce aka watsa ma ruwan zafi na janye hannuna , cikin rarrashi tace buɗe idonki mana bazan sake dukanki daga yau ba , kuma nayi miki alƙawarin wahala ya ƙare zanyi ta baki kulawa har na bar makarantar nan , zaki dawo ɗakina da zama zakiyi bacci kuma nice zan riƙa miki wanki komai da kike min ni zan miki natsuwa kawai zaki bani yanzu zan nuna miki yadda zakiyimin saki jikinki zan cire miki rigarki ,
Feƙaƙƙiyar “yar maɗigo ce tasan hannunta a harkar lesbian , tunda ta sameni ta tattara sabgar ko wace mace ta zubar saini , ta dawo dani zama ɗakinta bana wahalar komai kullum ina kwance tana nunamin soyayya fiye da yadda miji yake kula da matarshi ta iya tattalin mace kuma tana da karuwanta a met insu amma tunda ta sameni kawai ta zama mijina na zama matarta ko wanka bata bari na nayi da kaina kafin wani lokaci nima na goge a harka dan Yusra mayya ce akan mace ,
Karuwanta ganin ta zubar dasu hankalinta yana kaina yasa suka taso ma rayuwata ido , dan ta ɓata da kowa saini , duk inda zataje dani take tafiya a hostel lokaci guda nima na faso na zama gogaggiyar “yar lesbian ta ƙarshe , Yusra kishi gareta na tashin hankali wannan dalilin yasa take yawo dani lokaci guda suna na ya fara zagawa a makaranta dan Yusra azzalimar shugaba ce , taga dama yarinyar tayi mata laifi kafin ta sanni tace ta sameta ɗakinta da daddare yarinyar ta biya mata buƙatar ta korata , tunda ta sameni sai Allah ya fitar mata da san ko wace irin mace a duniya saini.
Karuwanta kuwa neman sa’a na suke suci ubana , wasa² nima na fara halbawa neman mata , idan mace ta taho haka zan tsareta da ido ina kallon ƙirjinta ƙugunta yanayin zubinta da dirinta abun yana neman ya zamar min kamar wani bakin iyaye dan ko a sch na tuno da yadda muke rayuwa da Yusra idan ban ganta ta rumgemeni ta ɗan jagulani banajin daɗi , maganar karatu kuma na daina bana ganin kowa bana gane kowa sai Yusra , ko kora ta fita kafin ta dawo na fara kuka banda natsuwa sai tana nan , tun abun yana burgeta harna fara tada mata hankali domin yanzu na fita jaraba , wani lokaci sai munyi faɗa zan riƙeta a yunwance dana gaji nace mata nidai tunda kin gaji dani ki sakeni kawai zanje na sake wata tunda kin gaji dani , haƙuri ta bani wai ita bata gajiya dani kawai dai in fahimta bawai kullum akeyin abun ba sai an huta taya ƙarfinta bai gama dawowa ba zata iya bani wata natsuwar , ko abinci ne ka kwakwafe ma ɗaya saiya fitar maka a rai , haka nayi ta roƙon Yusra tou ta fitar min da lokaci na ni ɗaya idan ba haka ba gaskiya zan barta nayi gaba ,
Na rabu da Yusra ne a lokacin da asirinmu ya tonu , abokan harkarta suka sameni a ɗaki da safe ita kuma lokacin ta fita dan dubo yara dake shara , sukayi min duka har suka sumar dani , da Yusra ta dawo ta sameni hankalinta ya tashi bayan na dawo dani daga suma ta tambayeni abinda ya faru na faɗa mata , duk wanda ya dakeni saida Yusra ta buɗe masa kai da sukundireba , wannan ɗanyen aiki da tayi shine yaja mana zuwa wurin shugabar makaranta , anyi case mai girma domin kowa babanta attajiri ne kuma saida aka tattaro iyayenmu tonan asirin dai babu daɗi , haka aka zane Yusra bugun bala’e akayi mata bayan an ƙwace kallabinta aka koremu dukanmu daga makarantar ,
Nidai a gidanmu Yayuna maza sukamin bugun leƙa lahira ki dawo , bayan komai ya kwaranye e aka maidani makarantar jeka ka dawo , haka nayi ta farauto yara ina kawosu ɗakina in basu kuɗi , ganin ban fita harkar mata ba yasa aka cireni daga makaranta kwata² gashi bansan garin da Yusra take ba banda number wayarta na shiga tashin hankali harna rasa ina zan shiga , haka nan na haƙura na koma neman abokan Yayuna bana wani jin daɗinsu nidai Yusra ita kawai nake so ,
Ana cikin wannan badaƙalar ne Allah ya kawoka rayuwata , tunda na ganka natsuwa tazo min na fara mantawa da Yusra saboda tunanin ka nidai ban taɓa ganin namijin daya shigomin rayuwa ya tsareta ba kamar kai , ina sanka kuma naso na zama rayayya domin kai namijin duniya ne ina ma macen data samu gwarzon namiji kamar ka murna , duk kuwa wacce ta sameka a matsayin miji damuwa ya ƙare mata kuma ta zama abin a yaba mata ,
Bayan kazo gidanmu zuwan farko ka tafi aka fara kirana da wata number mai kiran nawa yana da wayau kuma bai shigo rayuwata ba saida ya gama bincike ni kaf , yasan matsalata neman mata da neman maza na , kiran farko yacemin shi wani almajiri ne dana bashi sadaka nace ni bana bada wata sadaka bana ma fita , sai yacemin ka bada ka tuna ai sai matsiyata ka bada ka manta wannan shine cikar arziƙi , ko kin tuna ko kin manta nidai zan taimakeki , a ina ka samu number na ne ? Musulmin aljani daga saudiyya ya turomin yace na taimaki Halimatus Sadiyya zaki tafi gidan miji bayan kin gama lalata mutuncinki a titi na baki taimako saboda halinki na ƙwarai , idan har kikayi aure namiji ya sameki ba a yadda yayi tunani ba da damuwa , zai wulaƙanta ki haka yay ta faɗomin rayuwata kamar yana karatun littafi , banyi tunanin haka zamuje ba , a dai² wannan lokacin ne Momyn Hafsa ta shigo.
Sadiyya taci gaba da cewa shine ya aikomin da wasu layu yace nayi ƙoƙarin sakasu a ƙasan katifa kafin ka kusanceni , idan ka kwanta dani kaji ni a yadda kaji inyi kuka ince ka rufamin asiri , hmmm ya cuceni ashe ba’ayin kuka wanda ya bashi tsibbun yace idan har nayi kuka tou zanyi ta kuka har ranar da za’ayi kukan rashi na , bayan ya tabbatar da hakan shine ya sake kirana ya faɗamin zan mutu kuma a ranar aka cire layina daga wayata kwata² bansan waye ya cire ba , saida ta goge hawaye tace kuma yace zan tafi tafiyar da babu dawowa duk macen da tayi yunƙurin shigar Dikko haka zaiyi ta aikasu ƙiyama babu sassauci , kuma shine yake da sa hannu a damuwarka da taimakon matar uba , shiru Sadiyya tayi daga nan maganar ta ya ƙare , jijjigata Dikko yayi amma shiru domin yana da tarin tambayoyi da zaiyi mata , wannan dalilin ne yasa Hafsa tace yayi kuka kamar rashin zai fita , a cikin ku waye ne …? Karku kashe An matana , tou ko kune take gani a bacci…… ?
Wannan dalili ya hana Dikko komawa ɗakin Sultana yaji an anbaci magani kuma ance ɗakinta tun a daren bai bacci ba har lokacin da Sultana tayi kuka a dai² lokacin da Jiddah ke dawowa daga wurin Al ‘ Ameen kuma ya fita ta kicin amma basuyi magana ba kuɗi kawai ta bashi ta dawo , shi yasa bai fito da sauri yaje wurin Sultana ba , ita tana hawowa ta ƙasa shi kuma daga sama yake saurarensu saitin ƙofar baya kamar yadda tace , haka yasa su biyun suka kasance a ƙasa shi a sama Jiddah da Sultana a ƙasa , kuma idonshi biyu Al ‘ Ameen ya kira wayarta kamar dai² lokacin da tace su haɗu , ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa yarana , to waye a cikin ku ? waye kai me kake so ne da rayuwata ?
Al ‘ Ameen ne gurfane a gaban bokanshi yace shi Jiddah ba damuwarshi bace ba yanzu Sultana itace matsalarshi boka yayi waje road da ita Mardiyya zataji da Jiddah.
Da kokowa Jiddah ta kama Mardiyya tana dan ubanki ni zaki ma munafurci yau sai kin bar gidan nan tunda ba gidan babanki bane ba , ni zaki kashewa aure Allah ya tona miki asiri kaza² , Mardiyya tace Aunty wai me akayi ne ? Kinje kin turawa Yaya text kince muna faɗa ke baƙar munafuka , cikin kwantar da murya Mardiyya tace Allah sarki Aunty ina tsaye ina tayaki kishi na ƙwaƙwafe a wurin ganin na ƙwatar miki “yan cinki amma bazaki gode ba , iyayena sai cewa suke na dawo gida amma ban tafi ba saboda ina so naga bayan Sultana daga gidan nan ta ƙarasa maganar tana fashewa da kukan makirci , tou a haka zakiyi ? Me yasa zaki tura text wa Yaya ?
Cike da ladabi tace Aunty dan ya yadda dani ya haɗani da kula da rayuwar Sultana ta haka zan shiga jikinta nasan sirrinta kafin ta ankara mai gamawa ta gama , amma kiyi haƙuri bansan abun zai miki babu daɗi ba , jakar bata gane komai ba sai tace tou kiyi haƙuri Mardiyya ai bansan haka kike nufi ba , wuri ta samu ta zauna Mardiyya taci gaba da kaita tana dawowa.
Lokacin dana fito wanka har an canja sabuwar katifa an goge ɗakin tas an sa masa turaren ƙamshi mai daɗi a gefe kuma wasu irin ƙatunan food flarks ne masu kyau a ajiye , wurin naje na buɗe dariya nayi tare da lashe bakina nace kajin ne ko me ne ne ? Koma dai miye zanci shagalina na gama na kwanta yarinya ta sake dawomin ɗakin ko tacemin caca saina kware mata fatar fuska.
Dikko kuwa daga wurin Jiddah wurin su Bello ya nufa , gaba ɗayansu sun zama abun tsoro sun saɓa kamannunsu abun dai sai Allah ya basu lafiya , Dady yaji uwar bari yasa an kawo kuɗi da takardun gonaye filaye da gidajen daya haɗa yayi handama da babakere , saida ya ƙara cin ubansu ya diddira musu yace ko a mafarki An mata ta sake ganin wani a cikinsu wallahi saiya takashi da mota yaja da’ira ya raba kowa da ita mai ƙararren kwana yazo , sunci uwasu har babansu sannan aka sakesu sai sun haɗu a wurin rabon gado , suka wuce shi kuma yayo gida.
Qerau cike take taf da mutane an zubar da gawar Nana a ƙofar gida ta zama abun kallo masu wayoyi sai ɗauka hoto sukeyi , abunda babu kyan gani mijinta kuwa mutuwarta ko jikinshi amma su Amisty sunji ta sosai , Hafsa kuma har yanzu bata dawo ba , yau zaman makoki da jimami a Qerau kuka da baƙin ciki yana wurin dangin gawa.
Saida naci na ƙoshi zuciyata ta fara tashi duk abinda naci dan na kwantar da tanzomar tashin zuciyar baya tsayawa kamar zanyi amai amma baya zuwa , toilet na shiga na wanke bakina na jawo amai amma yaƙi zuwa kam aiko sai kazo wallahi dan duk abinda naci ya tashi zuciyata fitarshi daga jikina shine natsuwa , saida na sheƙa amai hankalina ya kwanta , ina gamawa na gyara wurin na fita , hijabina na saka na fita dan samun abinda zanci dan gaskiya yunwa nakeji na tashin hankali.
Cikin yanayin gajiya na sauko na shigo palon da farin ciki , sai yanzu naji hayani , Aunty Suwaiba na gani zaune a saman keken guragunta a ɓangare ɗaya kuma ana riƙe Dikko yana saiya kasheta , yau kwata² baya riƙuwa duk wanda yaje kusa da Suwaiba dan ɗauketa sai Dikko yace kaima saina kashe ka , sai raba ido takeyi kamar karuwa ta tsare uztaz a ɗaki , ta sharara wani irin fitsari yafi liter goma ta ruwa , kallonta nayi sannan na kalli inda ake riƙe Dikko suna ta ƙoƙarin kaishi ƙasa amma yau sun kasa kwantar dashi , to me ya haɗa Dikko da Suwaiba kuma ? Kai………. duk saina kashe ku…… dukanku…… yayi wata irin girgirza tare da zazzage su Ashiru ya ɓarar dasu ƙasa , ya nufi wurin Suwaiba idan har yaje mata a yanayin nan zai maida ita kamar damejin milcose , Ashiru ne ya riƙe ƙafar shi daga kwance wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali yace kai zan kashe kaina………….. Zan mutu saina kashe kaina…………………
18/11/2019 ????????
*JAMILA MUSA…*