NOVELSUncategorized

KWARATA 78

???? —— 76

         Ina ƙoƙarin ajiye wayata kiran Dikko ya shigo , fashe wa nayi da kuka naƙi ɗaukar wayar harya tsinke wani kiran ya sake shigowa ban ɗauka ba sai kuka nake mai tada hankali , wayata na yada na tashi da gudu nabi Inna ɗakin mijinta dawowar shi
kenan yana labarta mata yadda ɗaurin aure ya kasance , wai kuma ana gama la’asar za’a ɗauki amarya ! Ina zuwa na rungumeta tare da ƙara ɓarkewa da wani irin kuka mai kama zuciya , da tausayi ta ɗagoni daga jikinta itama hawayen ne kwance a idanuwanta amma bai zubo ba , da yanayin ko oho tace wai meye haka ? Bana san iskanci fa , shi kuma kukan na mene ne ?

      Inna na kirata tare da kallonta ina shashshekar kuka na kasa magana , murmushin ƙarfin hali Inna tayi ta jani muka fita ɗakin muka koma ɗakin ta , wata ƙawarta ce ta miƙomin wayata tace ana kiranki kuma har yanzu Dikko bai daina kirana ba , ina ansar wayar na kasheta gaba ɗaya………..!

Inna da ƙawayenta kuwa nasiha sukemin wallahi hankalina baya wurinsu kwata² banajin su kuma bana iya tuna abinda suka faɗamin har suka ƙari surutunsu suka gama a , a ciki bana iya tunawa , bayan an gama nasiha na tashi nayi sallah la’asar kuma har nayi sallah na gama hawaye ke ratata daga cikin kwarin idanuwana , ina gama sallah aka fara shiryani dan kaini ɗakin mijina.

     Babu wani daga ɓangaren ango daya zo bikon amarya , duk maganar Inna batayi tsegumi ba ita burinta kawai akaini ta huta dan a ganinta aurena shine natsuwa a gareta dan tasan idan ta tafi ta barni yawo zanci gaba dayi tunda Allah ya kawo mai kwasheni sauka lafiya….

      Babu abokin ango ko ɗaya duk motocin Dikko ne akayi amfani dasu wurin kai mutane gidan amarya , ni kuma a motar mijin Inna aka ɗaukeni dashi da ɗan uwan Inna sune suka kaini har gidan Dikko da kansu……

       Da farin ciki masoyana suka shiga gidan tare da dabar su Amisty domin sun riga amarya isowa sai aka shiga a tare kowa dai da abinda yake faɗa irin dai abun nan namu na mata yadda mukeyi idan ankai amarya kun dai gane irin abun ai , Jiddah kuwa ta murza wani irin ƙaton wanka na tashin hankali kamar zata tashi duniya dan haɗuwa kai Jiddah “yar gayun bala’e ce kanta yana hayaƙin rashin kunya , wata irin guɗa ta rangaɗa ayyuri yuriiii…….. Ƙawayenta suka ansa da barka da zuwa CACA ga caca ga tawagar karuwanta a baya fatan kunyo mana tsarabar kwalaben giya a cikin jikkunanku dan kunsan ba’a shiga kasuwa saida kuɗin siyayya amfani giya kenan sai ansha akejin muradin mace , giya mata caca sana’ar uban wata ƙawata ne , hehehe ram aka kashe kundai san iskancinmu na mata yadda yake…..

    Yayyen Dikko dai turawa ne sun huta tunda banajin abinda suke cewa kunsan ajiboters basu iya faɗa ba haka kuma basu iya hayani ba daga zaune dai suke ta watso nasu kalaman cikin harshen turanci , kuma su ƙawayen Inna babu wanda yayi musu magana , Mardiyya ce naji tana cewa gashi nan Aunty zai shigo , cikin yayun Dikko ne naji wata ta turance abinda yasa na fahimta naji Mardiyya tace Dikko ne , kila ta tambayi Mardiyya waye ne tace shine , kowa dake palon yayi tsitt , murmushi nayi a zuciyata tare da cewa sannu da zuwa jarumina , ban ganshi ba amma na hasko yadda zai fito daga mota ,

     Zaiyi parking cikin ɓacin rai , sai ya fito daga mota da yanayin shagwaɓa zai tunkaro palon cikin jarumta zaiyi mazurai da kyawawan idanuwanshi idan ya shigo , daddaɗar muryarsa zata bayyana yanzu , sallamarshi naji yayin da ake ƙoƙarin shiga dani hanyar da zata sadamu da inda aka bani mazauni da “yan uwanshi ya fara gaisawa sannan ya kira Jiddah suka wuce ciki.

     Ƙarshen ɗaki aka kaini wato bedroom saman tsadajjen gadona aka ajiyeni a gefen gado , nasiha dai aka ƙara yimin an nunamin matsayin haƙuri biyayyar aure kauda ido akan ƙaramin abu danne zuciya yayin fushi , ba abun duniya baya duk girmanshi tsabta naga yadda abiyar zamana takeyi inyi ƙoƙari in wuceta a gayu , babu wanda ya zauna saboda yanayin hararar da ƙawayen Jiddah ke watsoma “yan kawo amarya abinda yasa ma basuyi yunƙurin yin wani abu ba dan Dikko yana nan , shima Umar ne ya faɗa masa za’a tashi bama²n masifa a gidanshi shi yasa ya taho , duk wani abu da za’ayi a wurin walima idan Allah ya kaimu gobe Inna ta ƙanƙare da dangin miji , tayi gara na fita kunya kuma duk Dikko ne yayi dan ya siyamin mutunci a wurin ahalinshi….

        Amisty taso tayi magana dan na lura da bakinta amma ƙawayen Inna suka ce kowa yazo a tafi yanzu , amma tacemin akwai dawowa , inaji ina gani suka tafi suka barni , Oh saini ɗaya a ɗakina kamar mayya babu ƙawa ko ɗaya babu wasu “yan uwa da zasu kwana a gidana , jakata na jawo na fiddo wayata na kunna bayan ta gama kunnuwa na kira Inna , amma bata ɗauka ba , 

       “Yan palo kuwa kowa cikinsa ɗure da iskanci a ƙagare suke Dikko ya fita su caccakeni san ransu amma yaƙi fita har aka kira magrib , suna tunanin zai tafi masallaci a gida yayi sallah , isha’e ma haka , Yayyen shi ganin bashi da niyar fita sukayi mishi sallama suka wuce , godiya yayi musu tare da cewa ku huta gajiya , amma sun ɗauki gudirin zasu dawo idan Dikko baya nan , Sultana ta samu ɗagin ƙafa na yau basa so suyi rashin mutunci Dikko yana nan idan ya birkice musu gano dai²nshi sai Allah.

      Misalin 9pm ya kira Jiddah ɗakinshi ya faɗa mata cewa idan Allah ya kaimu gobe rai da lafiya duk wata ƙawarta data san tazo gidan nan to ta tattara ta kama gabanta har Mardiyya baisan ganin kowa idan kuwa ba haka ba za’a samu matsala , amma sai Jiddah tace ƙawaye na zasu tafi amma fa Mardiyya babu inda zataje wallahi tunda tuni Momy ta gama magana idan kuma dan kayi aure zaka tona min asiri saika haɗa hada ni ka koremu gaba ɗaya….

     Cikin ɓacin rai Dikko yace Mardiyya ta tafi daga gidana Jiddah , wallahi babu gidan ubanda zataje , Mardiyya ta barmin gidana gobe kafin raina ya ɓaci , wallahi ba zataje ko ina ba idan saboda kayi amarya ne sai haɗa hadani ka sakeni kuma kake maganar ta bar maka gida ai bani nace ta zauna ba Momy tace saboda haka ka bari sai ta dawo , tana faɗin haka tayi gaba abunta , shima tashi yayi ya nufi ɗakin amarya Sultana…

     Da ɓacin rai ya tunkari ɗakin Sultana yanajin tuƙuƙin maganar Jiddah da tace babu gidan ubanda Mardiyya zataje zaici uban yarinyar nan amma sai zuwa gaba dan yanzu duk idon jama’a akanshi yake yana iya mata wani abu ace daga yayi aure ya fara cusa mata damuwa , yana da cikin Jiddah duk ranar daya tashi haifeta zai wulaƙanta mata rayuwa yadda mai tunani baya zato, ina zaune a inda nayi sallah har yanzu ban tashi ba ina ta kiran wayar Inna ba’a ɗauka , babu ko sallama ya shigo ke An mata ni zakiƙi ɗaukar ma waya ne ? Dake kin ɗaukeni sakarai ma daga baya kika kashe wayar wai me kika maidani yana maganar yana shigowa cikin ɗakin , kai tsaye nace mahaukaci , kalmar hauka ya fita daga bakinki dan jiya ba yau bace doki , dokina ya ƙarasa maganar yana ɗaukata yaci gaba da cewa do ki , da iskanci yake faɗar do….. Sai yace ki , yana yin irin yadda akeyi idan an hau doki bari ki fara jin nauhi na sai ki fara kiyayata tun kafin mu fara wasan danbe ,

     Dikko bana so , a , a ya maƙale ƙafaɗar shi irin yadda ƙananan yara keyin ƙiwya yayi maganar a shagwaɓe yana yin wani ɗan kukan shagwaɓa mai sa mutum yaji yana lilo tsakanin sama da ƙasa , cikina naji yana halbawa jikina yanamin wani yami² a dai² lokacin daya saukeni saman gado yana min wani irin munafiki kallo mai nuni da zakici gidanku sannan ya sake cewa do ki yayi min kyakkyawan murmushin shi mai fiddo mishi da ai nahin kyawun shi ƙuramin ido yayi sannan yace ai dokina ne ke ko An matana ? Rufe idona nayi cikin jin kunya nayi murmushi kaɗan!

    Ina sanki , idona a rufe nace Dikko dan Allah kada kaimin komai , ke meye nace ? Cewa kayi kana so na , ke kuma meye kike faɗa ? Cewa fa nayi kawai ina sanki , to idan na faɗa nima bazakamin wani abu ba ? Naga alama dai idan banyi wani abu ba bazakiji daɗi ba dan na lura kina tsammani wani abu daga gareni , buɗe idona nayi tare da cewa , a , a , ido ɗaya ya kashe tare da ɗagamin gira yace sumbata ɗaya tak , ai nasan bazai tsaya a ɗayan bane , durƙusawa yayi a saman guyawunshi ya dafa hannuwanshi gefe da gefe ina tsakiya kallona yayi sannan yace kamar ya ? Cewa nayi nasan bazai tsaya a ɗayan bane ba , murmushi yayi tare da kwanciya saman jikina a gajiye buɗe bakinsa yayi kaɗan da ajiyar zuciya mara sauti sannan yace Oh to kenan kin yadda da sumbatar ashe ? To amma nasan bazaka tsaya a ɗayan ba , da hannunwanshi biyu ya riƙe kaina cikin kwantattar murya ya ɗora bakinsa a saman leɓuna na yace ɗaya tak ya faɗa da wata irin murya mai tayar da tsikar jiki , cikin mutuwar jiki nace amma dai karya wuce ɗaya , murmushi Dikko yayi tare dayin wata irin sukuwa a kaina cikin sigar mugunta kamar yadda yace sannan ya ɗagani yana cewa tausayinki nakeyi An mata nasan baki iya ɗaukar Dikko wahala zan baki “yar yarinya ta bara dai inzo muyi bacci kinji ko , yana faɗin haka ya fita da tafiyarshi ta sakakkin “ya “ya ,

     Ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe idanuwana ba haka naso wasan ya ƙare ba , me ma Dikko yake nufi yana nufin ido zai sakamin saboda nayi ƙarama kai kuji mugu fa , hmmm lallai Dikko ba baƙon mace bane ba , amma maƙetacin mace ne , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya kamar yana nan na rufe fuskata.

      Shiru² Dikko zai dawo babu shi ba labarinshi , tsoki nayi tare da gyara kwanciyata , tun ina tunanin Dikko zai dawo harna fitar da rai yana wurin Jiddah a can ya sauke damuwarshi yayi baccinshi ya manta dani , haka na haƙura nayi bacci da tunanin Dikko…

   Yauma nayi mafarki da mutumin nan kuma ya faɗamin ya ƙwaƙwale gobe saura ni tunda na shiga sahun ma’aurata , a firgice na farka tare da kwarara wani irin firgitaccen ihu wanda ya karaɗe kaf girman gidan gaba ɗaya duk mahaluƙin dake gidan babu wanda baiji ihuna ba , ina buɗe idona na nufo palo da gudu ban tsaya ko ina ba sai jikin firij na buɗe na ɗauka ruwa saboda wata irin ƙishirwa da nakeji kamar zan mutu , saida na shanye roba ɗaya ta ruwa , a wahalce na dawo da baya na zauna saman kujera ina goge zufa…

      Jiddah ce ta fito sanye cikin wasu irin kafirawan kayan bacci idonta da yanayin bacci tace uban waye nan yake mana kuka ? Kallo ɗaya nayi mata daga nesa na fahimci fitina ne ya fiddota kuma uwarta zanci yadda nake haƙe da ita saboda kirana da tayi da caca , ubanki ne yake kuka na bata ansa a dai² lokacin da Dikko ya dafa ƙarfen bene daga sama sboda mu dukanmu a yanzu muna ƙasa kowa ta sauko , ni abinda yasa na fito palon ƙasa nasan bazan samu ruwa a palo na ba shi yasa na gangaro na ƙasa nasan zan samu , ita kuma Jiddah masifa ya fito da ita ni kuma yau zan sauke mata duk wata tsutsar iskancin dake cizar mata kwalwa , An mata ya akayi ne ? Dikko ya tambaya , ruwa nasha na bashi ansa ba tare dana kalli inda yake ba , Jiddah kuma tace Caca ni kike zagi ? Sai in takaita miki rayuwa na illahta banza ba abinda za’ayi , Dikko ne yace kinsha ruwan ne ? Ey nasha , tashi kije ki kwanta tou , 

       Babu gardama na miƙe zan tafi Jiddah ta riƙoni ta baya ta fara zagina tana cewa ke “yar marasa tarbiya babana bazai zagu a bakinki ba danni Babana bai sakani a caca ba , shi Babana yasan darajar matansa yasan na “ya “yansa kaf zuri’armu bamu da “yan iska banza ahalin kwarata , Dikko ne yace An mata wuce kije ki kwanta kinji , tou na bashi ansa tare da ƙwacewa Jiddah ta sake riƙoni taci gaba da cewa…

     Kuma ni babu wanda ya siye gidan hayarmu ya mayar da gidan kiwon dawakai karuwar banza karuwar wofi , murmushin takaici Dikko yayi tare da cewa An mata taho , ƙyale Jiddah nayi na tafi ita kuma taci gaba da cewa ƙaryar banza ƙaryar wofi ba ance ke wata shegiya bace ba da kin tsaya dana ciccire miki gashin kai , Dikko yace gashin kanta kike baƙin ciki dashi ? Dan a lokacin Sultana ta shiga ɗaki bata san wainar da suke toyawa ba , yaci gaba da cewa mace kenan An mata ta burgeta ina ga maza kuma kenan ? Wannan shine zaɓi na farko dana fara cankowa a rayuwata ƙatuwar banza da ƙanƙanuwar yarinya ta fiki tunani , yana faɗin haka yabi bayan Sultana….

       Ai kaine ƙaton banza ko kunya bakaji kaje ka auro wannan “yar magen yarinyar idan ka isa kaje ka auromin min cikakkiyar mace wacce zata fito na fito itace kishiyata Dikko da zai shiga ɗakin Sultana yaba Jiddah ansa cewa wannan ma ta isheki yana faɗin haka ya shige , ita kuma taci gaba da cewa wannan yarinyar ni wallahi ba kishiyata bace ba “yar aiki ce ka kawomin kuma tayimin iskanci saina bata kashin bala’e , ƙawayenta suka fito suka jata suka koma ciki da ita suka ci gaba dayi mata huɗubar shaiɗan!

       An mata kukan me kike a tsakar daren nan ? Ba komai na faɗa cikin ɓacin rai , kusa dani ya zauna ya riƙoni na kwace kaina tare da matsawa daga kusa dashi dan haushin sa nakeji baizo ya kwana dani ba , kuma ko “yar kazar da ake bawa amare ni bai kawomin ba , ƙara matsowa Dikko yayi zai taɓani nace da Allah ka ƙyaleni , tou na ƙyaleki amma kiyi haƙuri dan ma an sakaki a caca to miye ? Shi a tunaninshi inayin fushi ne saboda maganganun Jiddah tou inajin ciwonsu amma nafi jin haushin shi a yanzu , 

        Gyara bakina nayi banyi magana ba , cire takalmin ƙafarshi yayi suba silifas ba kuma ba soso bane ba amma dai zubin slifas garesu , kwanciya yayi saman gadon yace tou taho ki faɗamin , yi nayi kamar banji ba , bai sake magana ba ya gyara kwanciyar shi yaci gaba da baccinshi hannunshi a saman cikinshi inajin har yanzu cikinsa bai daina ciwo ba , can nesa dashi na kwanta ina kallonshi ,

       Haba Jiddah ina wayewarki ? Ina barikinki ? Ina feƙewarki ? Maza fa idan sukayi sabon auren kansu rawa yakeyi ya kasa tsayawa wuri ɗaya ki fita sha’aninshi da matarshi ba jibi zai tafi ya barku ba ? Jiddah tace Eh to ki bari idan baya nan ki riƙa ci mata uwa la’ada waje idan gaban idonshi ne saiki riƙa tattalinta kina nuna mata soyayya ko ƙararki takai masa zaice bata san zaman lafiya , kibi sannu ki zuge mata rayuwar uwa kamar iccen zogala karki sake ki barta ta huta idan azaba tayi mata yawa ita da kanta zata gudu , salon mugunta sanka² suka koyawa Jiddah….

     Kiran sallah asuba ya tashi Dikko daga bacci ni har lokkacin banyi bacci ba saboda tsoro , da sauri na juya mishi baya na daina kallonshi , sauka yayi daga saman gadon ba tare da yayi magana ba ya fita daga ɗakin….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button