NOVELSUncategorized

KWARATA 77

???? —— 75
        *_Ga saƙon godiya Ummiee Zaria Jikar Lerawa Sultana tace a gaishe ki tana miki fatan alkairi…_*
       Nifa bazanje ba kaje kawai zan jiraka a mota , da Allah wuce mu tafi banasan yawan magana ji nake kamar zan faɗi , nidai kaje abinka dan Allah , zaki
wuce muje ko saina baki kunya , ai kaima zakaji kunyar , ni banajin komai idan ban ɗaukeki ba kice ba Dikko nake ba kuma idan na ɗaukeki saina fita ƙofar gida a tsakiyar mutane zan ajiyeki in dawo ,
  Kaɗan ne daga cikin aikinshi dan haka nace muje badan halinka ba , naji muje dan naki halinki kuma da bakije ba yau da kinga yadda ake saɓanin igiyar ruwa , tafiya nayi na barshi a baya biyo bayana yayi yana cewa “yar raini magana fa nake kuma nasan kinaji na…

     Kai aini yanzu na girma banda lokacin yarinta , dariya yayi yace ai nine zan baki girman kinga kina ƙasana har yau har gobe kullum ma kina ƙasa ina samanki yarinya kin gane abinda nake nufi yayi maganar tare da wucewa yayi gaba da ɗan gudu nima da sauri nabishi ina ƙarema gidan kallo gaskiya wannan gida ya haɗu masu kuɗi basu da aike sai bautawa ƙasar da bata da tabbas duk wannan ginin a kwana a tashi sai an tafi an barshi kuma ƙasar ce zata hiɗiye bata gajiya…

     Wata “yar munafikar ƙara yayi “yar ƙarama yace wayyo cikina kuma bai daina tafiya ba nima ban daina binshi ba , gangarewa yayi ƙasa da gudu nima da gudun na bishi muka sauka muna sauka naga mun fito waje irin na farkon gidan amma ba inda Ashiru yayi parking ba , tsayawa nayi ina kallon wurin da mamaki jin ban biyoshi ba yasa ya dawo da sauri kamar za’a kamashi ya jani ta baya ina kallon wurin shi kuma yana jana da sauri , jinjina kaina nayi tare da cewa “yan gayu , ai kune gayun An mata mu “ya “yanku ne…….

    Taho jirana akeyi , juyawa nayi na kalli gabana nace ina zamuje ? Can zamuje ai , ni gaskiya bazan je ba , ke da Allah wuce muje yanzun nan kika gama cemin kin girma ashe har yanzu An matance , nidai gaskiya bazanje ba , mi yasa ne ? Nifa tsoro nakeji , tsoron mi ? Da Allah wuce muje ke komai sai kinyi yarinta , ƙwacewa nayi nayo hanyar da muka fito da gudu , shima da gudu ya biyoni harna fara hawa matakal ya riƙoni yace wai me yasa kikemin haka ne ? Cikin kuka nace nidai bazanje ba , jawoni yayi kusa dashi yace tou in rungumeki sai muje ? Nidai bana so , yace um ummm Dikko ne fa ya faɗa tare dayimin kallon ƙauna , zo jikina kiji natsuwa An matana , a gajiye na sauka jikinshi cikin mutuwar jiki , yace tou ya kikaji akwai daɗi ko ? Eyy tou sauka muje babu wani abu da zai faru wallahi…. Ka tabbata na tabbata miki ya ƙarasa maganar yana duƙuwo dai² bakina na sumbaci gefen fuskarshi yace yawwa jarumata muje….

      Yanzu bai riƙeni ba mukaci gaba da tafiya ta wata ƙofar gidan da ba’a rusa ba amma an fasa ƙofa ya shigo cikin gidan muka shiga shine a gaba ina baya kamar yadda yace nazo jikinshi zanji natsuwa na samu natsuwar banajin tsoro cikin dakewa nake binshi har muka shiga ciki…

       Wani irin yagegen palo ne kuma an ƙawatashi da wasu irin mahaukatan kujeru masu kyau palon yana da girma maisa kaji juwa ta kamaka anyi masa ado dai² da zamani , mutane ne cike a wurin maza da mata “yan gayu ibar farko sai ƙamshin gayu ke tashi , muna shiga Dikko yace tou ga An mata nan ku gaisa ina zuwa yana faɗin haka ya wuce , binshi nayi da ido harya shige ciki ,

      Dawo da hankalina nayi wurin “yan cikin palo nace sannunku , yawwa ki zauna mana , a , a zan wuce ne kawai ina faɗin haka nabi Dikko inda naga ya shiga , suka ce kizo ki jirashi ya fito , ko saurarensu banyi ba na wuce ciki , a gefen gado na sameshi durƙushe rabin jikinshi a saman gado idonshi a rufe hawaye na zubowa daga cikin idonshi , da sauri na isa wurinshi nayi yadda naga yayi sannan nace masa Dikko wai miye ? Ba tare daya buɗe idonshi ba yace An mata cikina kamar zan mutu haka nakeji , kace kanajin yunwa kaci abinci to , bana iya cin abinci a yadda nakeji na , to kasha magani mana , zan sha jeki palo ki jirani kinji ko ? Cikin kuka na matsa kusa dashi nace nidai zan zauna nan , a , a karki zauna kinji jeki ina zuwa yanzu , nidai , cikin hayani yace da Allah malama fita ki bani wuri nace kije ki jirani ki tashi kusa dani bana san numfashinki yana sauka a jikina , matsawa nayi na zauna gefen gadon nace tou zan jiraka anan ,

      Wani irin kallo yayi min tare dayin dariya , murmushi nayi nima nace meya baka dariya ne ? Ɗaure fuska yayi sannan yace ba dariya bace fusata ce , da gudu na tashi nabar ɗakin , tsoki Dikko yayi yace kin rufawa kanki asiri dana yi miki maganin kafiya , cire kayanshi yayi ya shiga wanka a daddafe….

    A palo kuma sai caccakar abinci sukeyi yayin da wasu kuma ke tacin ɗamara cikin shiga irin ta mahaya doki sai naɗa rawani sukeyi , wuri na samu na zauna bana kallon kowa zuciyata ce ƙawar firana tana haskomin Dikko da ɗabi’unshi , murmushi nayi ƙasa² nayi magana nace mutumine kenan….

       A hankali mutane suka fara ragewa dan har yanzu Dikko bai fito ba abinda dai na fuskanta ko wane yana tare da budurwarshi ne ko matarshi ne nidai shine ban gane ba dan banga sunyi kama da masu zaman “yan ci ba , ina wannan tunanin ne Ashiru ya shigo hannunshi riƙe da kofi inda nake zaune yazo ya bani da girmamawa yace wai mai gida yace in baki ki kai mishi , kai tsaye nace bazanje ba , murmushi Ashiru yayi tare da cewa yi haƙuri kije ki daina haka babu kyau kinfa san halinshi sarai haba ranki ya daɗe ki riƙa mishi uzuri , ni bazanyi uzirin ba a cikin ni dashi waye ya kamata yayi uziri wa wani ? Kiyi haƙuri duk wanda yayi haƙuri bai iske ba kaɗan yayi ki ƙara haƙuri wata rana zai zama tarihi , wane tarihi kullum abu ɗaya ni na gaji wallahi , yi haƙuri ki ansa kinga gashi yana kira , ƙin ansa nayi na gyara zamana , ɗaukar wayar yayi yace E mai gida , tou gashi nan zata kawo maka ya tsinke wayarshi , yace dan Allah ansa ki kai mishi , ansar kofin nayi na tafi ɗakin kai tsaye !

     Bayan ƙofa ya laɓe ina shiga ya kulle ƙofar da makulli , a ɗan razane nace masa gashi cikin girmamawa , kalli can ya nuna min gado , kallo nayi sannan na kalli Dikko da yanayin tuhuma , yace haka kika ganshi ɗazu ? Girgiza kaina nayi alamar a , a yace ai kin rainani ko ? Tou yau so nake mu fidda raini dani dake , da sauri na kalli kofin na sake kallon gadon ya gyareshe tas , meye a kofin ne ? Ya tambayeni bansan ko miye ba , tou shanyeshi sai in buɗe miki ƙofa ki tafi idan ba haka ba kuma in ɗoraki saman gado kema in miki yadda kika ganshi , nidai ka ansa tafiya zanyi gida , ai ba wani gidan da zaki yau yayi maganar tare da matsawa jikin madubi yana kallon kanshi saida ya shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan ya fara cewa one , bayan wani lokaci yace tow , three , four , five , da sauri nace me zanyi ? A harzuƙe ya kalleni yace shanyewa zakiyi sai kizo ki dafa ƙafata kice kin gode , idan kuma kika bari na irga goma saidai kiji Dikko a saman ruwan cikinki….

    Six yaci gaba seven , eight , nine ….. Da sauri na ɗaga kofin na shanye na riƙe moƙoshi na tare dayin wata irin ƙara sannan na fashe da kuka na jefar da kofin kamar nasha guba har a zuciyata kamar an kwaremin ita ƙirjina zafi maƙoshina kamar an tsatstsargar minshi , dariya Dikko yayi yace services gobe ma ki sakemin kafiya zo ki gode , da sauri na isa gabanshi kaina yana juyawa na dafa ƙafarshi ina kyarma nace na gode , to jeki Ashiru ya maida ke gida sai mun haɗu a ɗakina gobe idan Allah ya kaimu , da sauri na miƙe yace kimin addu’ar saukowa doki lafiya , har yanzu wuyana kamar zai fita nace Allah ya tsare yasa ka sauko lafiya , daure fuskarshi yayi yace yawwa kije ngode , yayi maganar yana tillomin makullin ƙofar , da sauri na ɗauka na buɗe na fita ina kuka….

        A inda nabar Ashiru a wurin na sameshi nayi gaba cikin ɓacin rai yace ta nan zamu bi , banza nayi dashi na wuce , maganar Dikko naji da tunda na fito ya biyo bayana naji yana cewa ina zakije nan bakiji ana miki magana bane zo nan , ba tare da nayi magana ba na dawo da hannu ya nunamin yace wuce ta nan kuje kuma karki daina kukan zanzo da daddare ,

    Kallonshi nayi , cikin tsawa yace ki daina kallona ki wuce marece yanayi sai ina miki magana kita kikkifa ido kina kallona , bayan Ashiru nabi har yanzu ban daina kuka ba , komawa Dikko yayi yaci gaba da shirinshi wai zasu hau taka ango duk wani abokinshi na nesa dana kusa idan dai yana da rai da lafiya yazo , yasa an ɗauko An mata da ya ɗorata doki amma ta ɓata mishi , kayan daya ajiye mata ta saka ma badasu zaiyi tunda batajin magana…

        Abokanshi sunso ayi shagali amma Dikko yace a , a , sun tambayeshi dalili yace shi yasan dalili kawai bazaiyi ba , shine suka tsiro hawan doki dan tayashi murna kuma shima zai hau dan yana bawa hawan doki mutunci na musamman ,

     Tunda muka taho kuka nake ina jinjina irin cuta da zalinci na Dikko , har yanzu wuyana bai daina maƙaƙi ba zafi yake daga ƙirjina har abinda ya sauko zuwa ramin zuciyata , goge hawayen da suka sake taruwa a idona nayi sannan na fara tunanin ya akayi Dikko ya kasu gida biyu ? To waye ya kwanta yace in matsa gefe ? Da nayi kuka kuma ya akayi naga banga na kwance ba naga Dikko ya ɗago ? Mafarki ne zuciyata ta tabbatar min da haka dan haka na manta da wani da na gani yana kwanciya a mota….

     A ƙofar gida Ashiru ya saukeni ya wuce da gudu ni kuma na shiga cikin gida , duk sallamar da nakeyi babu wanda ya jini bare nasa ran za’a ansamin Inna da matan Baba ƙarami suke ta faɗa wai ni na koyawa Safiyya iskanci kuma naje na anshi gadon su Babana na lashe duk wannan bai isheni ba saida nasa Dikko ya ɗaure mijinsu sunga yadda za’ayi a ɗauramin aure , Inna tace aure anyi an gama ba fashi ko ƙarami ya ɗaura aure ko karya ɗaura sai an ɗaura auren Sultana idan Allah ya kaimu lafiya gobe kuma ko ni sai in fita in ɗaura mata aure tunda ba shegiya bace ba , shaggu ma an ɗaura aurensu bare Sultana , dama waye yake nemar a fasa aure ai jiki magayi dan hausawa kuwa cewa sukayi ko wattuna bara baiji daɗin bana ba , ai hangen duniya ne yasa kike harin bashi ɗiya ke haɗamammiya , Inna tace haɗama sai wanda ya isa yakeyi wani yayi yaga idan zai samu cusa kai babu ƙwarjini , matan Baba ƙarami sukace murnar mutuwa dai murnar banza yadda yayi ma mijinsu itama zai mata haka nan , banji abinda Inna tace ba na shiga ciki raina ɓace na fara kiran wayar Dikko….

     Takalmi zanoty ne a ƙafarshi wando kamun ƙafa jawha milihi “yar gabas , babbar riga girken nufe yasha rawani mai bakin fara sai wuƙar hawan doki dake rataye jikinshi a jirge yadda dai masu hawan doki keyi , yasha kyau harya gode ma Allah sai hotuna ake ɗaukarsu a ɗan yamutse yake dan bayajin daɗi sosai komai cikin ƙarfin hali yakeyi…

     Bayan sun gama ɗaukar hotunan suka ɗunguma suka nufi inda aka ajiye dawakan duk wanda zai hau doki sunsha ado sosai , gaban dokinshi ya tsaya da yasha ado da sirdi tunbas ajikin sirdin anyi masa kwalliya da bishiri guda huɗu , kayan azurfa gaban fuskar doki ɗan wuya ɗan gaba , ƙasan sirdi aka sa labbati mai kyau ɗan gabas da sha hirji… Yana ƙoƙarin hawa tsadajjen dokin kiran Sultana ya shigo….

      Ɗauka yayi ya kara a kunnenshi tare da cewa inajinki , wai kai da Allah Dikko mi yasa bakayin abu da lissafi ? Tafiya ya farayi dan komawa ciki saboda wurin yayi taron mutane da yawa Sultana kuma taci gaba da cewa in banda hauka ƙanin babana zakasa a ɗaure ? Ai kinsan ni mahaukacin ne kika faɗamin damuwarki me yasa ke mai hankali bakiyi maganin matsalarki ba sai kin sako mahaukaci a ciki to ? Dana faɗa maka cewa nayi kasa a kulleshi ? Wanda zai ɗauramin auren Dikko ? Tou ai sai a fito dashi ya ɗaura auren idan ya gama saiya koma , cikin hayani nace kai mahaukaci….. Kafin in faɗi maganar da zan faɗa yace ai kinsan inda kika barni kizo ki sameni in nuna miki girman haukata shi baya san ke ɗiyar ɗan uwanshi ce ba yayi ƙararki duk sansanci da aka kasayi a gida to inda ya kaiki a can zasu sasanta nine nakeyin shari’ar ne ? Ko nine nake ƙararshi ? Yarinya dake kuma kece mahaukaciya ni ina da hankalina dokin Dikko kawai dake in hau kuma inyi sukuwa……… Yana faɗin haka ya kashe wayarshi !

      Cikin ɓacin rai ya fita ji yakeyi baima ɓatama An mata rai ba dama yace saiya zaneta iyakar raini duk girman duniyar nan baiga wanda ya rainashi ba kamar yadda An mata ta rainashi ba , ta kalli tsabar idonshi ta kirashi mahaukaci ta faffaɗa mishi duk maganar daya zo bakinta baida wata ƙima a idonta amma zataci ƙaniyarta , da ɓacin ran An mata ya hau saman doki ya zakuɗa yadda sukeyi idan zasu gyara , bayan ya gyara yayi ma dokin diddige kowa yahau nashi suka wuce cikin tsari da gogewa irin tasu ta mahaya doki ango a gaba abokanshi a baya suna taka ma ango wannan shine ake kira taka ango zasu ɗan zagane inda sukaga ya kamata abunsu dai na manya…..

        Dikko yana kashe wayarshi Inna tana shigowa , wuri ta samu ta zauna take tambayata abinda ya haɗani da Ba ƙarami , duk abinda ya faru dani bayan bata nan saida na zayyane matashi kaf amma ban faɗa mata zance Dikko yamin fyaɗe ba amma duk abinda nayi bayan na Dikko ban ɓoyewa Inna komai ba , bayan na gama tace yanzu inashi Baban Hafsa ? Bansan inda yake ba , shifa Bello ? Shima bansan yana ina ba , Hmmm Inna tayi cikin takaici sannan tace to dan uban ƙarami ya manta ni kenan ? Amma ina cikin gidan nan har aka kawo miki sammaci saboda Dikko ya fini mutunci kika saƙe a jikinki har kikaje kika kai mishi ina nan kwance Sultana ? Inna ranar baki lafiya bana so na tayar miki hankali , jinjina kai Inna tayi sannan tace naso ace ahalin babanki suka ɗaura miki aure amma nasan haka baza ta samu ba dan bana tunanin ƙarami zai iya ɗaura auren ki saidai “yan uwana su ɗaura miki aure………..!

   Ba tare dana kalli Inna ba nace ba naki ahalin ba na Babana , Baba ƙarami ne zai ɗaura aurena da kanshi gobe idan Allah ya kaimu a ƙofar marusa ƙofar gidan su Babana haka na faɗa ma Dikko kuma haka yasa aka rubuta a jikin i v kuma a gidan za’a ɗauki amarya Inna dangi uwa sunyi kuma suna nuna soyayya mai girma da fifiko wa nasu akan ahalin uba kowa dai da nashi wurin , amma su ahalin uba garkuwar rayuwa ne gaba ɗaya daga zaran baka dasu tou fa ka koma liƙe² , Inna tace a jikin i v masallacin G R A za’a ɗaura aure haka aka rubuta ana gama sallar juma’a , kuma ko ƙarami ya ɗaura ko bazai ɗaura ba mijina zai ɗaura aurenki idan mai kowa mai komai ya bamu aron rayuwa da lafiya anan gidan za’a ɗauki amarya duk wanda bazai zo ba yasha zamanshi a gida…. Tana kaiwa nan tace in fito za’amin ƙunshi mai ƙunshi tun ɗazu take jiranki , wai duk girman kwana takwas sai yau za’ayi ƙunshin biki idan Allah ya kaimu gobe naje saloon sai kace auren wasan yara danni ina kallon abun kamar a mafarki ne….

      Daren yau duk inda ka shiga a gari maganar su Dikko akeyi labari ya barbazu duk inda ba’a tunani ya dangane , sunyi hawa mai kyau da burgewa abokanshi sunyi mishi kara sosai wasu ma basu taɓa zuwa katsina ba sai dalilin wannan aure , dan duk auren da yayi duka biyun ba’a a katsina akayi ba , sai yau mutane suka tabbatar suka kuma yadda da wannan aure , hotuna sai yawo suke a social media , duk abin nan sai yau Momy ta samu damar buɗe wayarta , shi kuma Dady ya kira Dikko yace ya rufe kaf wayoyinshi karya tsaya duk inda wani zai ganshi tunda yace shi damuwarshi a ɗaura auren idan an ɗaura zaiji da sauran matsalolin , Dikko yace E fatan alkairi Dady yayi masa sukayi sallama ,

     Dikko yaso yaje wurin An mata bayan sun sauko daga hawa amma baya iya zuwa ga gajiyan doki ga kuma ciwon ciki dake neman hanashi ya miƙe tsaye koda suka dawo a daddafe yayi sallar magrib yayi isha’e sannan suka shiga gida a saman kafet ya kwanta a wahalce ya kifa fuskarshi saman pilow shi kaɗai yasan azabar da yakeji , abokanshi kuma sun daɗe suna fira bayan sunci abincin dare ne suka fara tafiya wasu zasu koma gidanjensu anan cikin gari , baƙi kuma suna tafiya masauki ,

   Bayan kowa ya gama tafiya ne aka rage Dikko dashi dasu Ashiru , wayar wani ya ansa a yaranshi ya kira An mata amma duk kiran da yayi ba’a ɗauka ba saboda tabar wayar a ɗaki tana waje ana mata lalle , gajiya yayi da kira ba’a ɗauka ba ya mayar mishi da wayarshi , yace ma Ashiru ya samo mishi fura yaji ko zata shiga , fura dai itace ya samu yasha abinci dai ya gagareshi yau , abincin saidai aka fitar dashi dan ya lalace….

    Bayan ta saka layinta Jiddah ta fara kira ko “ya “yanta bata nema ba sai Jiddah ta fara taɓowa ɗiyar zumuncin Allah Jiddah da ƙawayenta suna zaune a palon Sultana dan neman magana saboda bayan an gama jere an rufe da makulli amma sai ta kira aka ɓalle mata ƙofar wai wannan kujerun sunfi ƙarfin siyen ahalin caca mijinta ne ya siya dan haka babu wanda zai mata iyaka da dukiyar mijinta , komai na ɗakin amfani sukeyi dashi kuma cikin ƙeta da mugunta shi Dikko baisan abinda Jiddah take ciki ba dan ko ranar da Inna tace saidai ya rabawa Sultana gida bata faɗa masa cewa Jiddah tayi iskanci ba tace masa dai kawai ya rabawa Sultana gida da matarshi dan ta fahimci kawai da damuwa , shine Dikkon yace gidanshi bai gagareshi ba kuma shi babu macen data fi ƙarfinshi….

     Jiddah tana ganin number waje ta san Momy ce dan haka tana ɗauka ta ɓarke da wani irin kuka mai tada hankali , na shiga3 na lalace ƙaryata ta ƙare kece garkuwata da bakya nan na zama abin tausayi duka na safe daban na rana daban har tsakar dare bai barni na huta ba saboda kawai zaiyi aure , wane irin aure kuma ? Momy wai baki sani ba ? Aure zaiyi har anyi jere yau duk inda kika shiga a garin katsina maganar hawan taka angonsu akeyi yace yayi hawan barin tarihi a katsina tunda ya auro muradinshi ni matar sadaka ce shi yasa baiyi ba a aurena dashi , Momy tace wai waye zaiyi auren ne ?

      Saida ta sake ɓarkewa da kuka cikin makirci irin ancucetan nan tace Yaya zaiyi aure har anyi jere gobe ɗaurin aure haka akazo jere jiya bakiji yadda sukemin habaici ba suna zazzagina nayi haƙuri na ƙyalesu Momy ina cikin matsala , wai wane Yayan zaiyi aure ? Inji Momy , Jiddah tace Ya DK , Momy tace wai Dikko nawa ? Ko wane Dikkon ? Jiddah tace shi , Dady dake zaune saman abin sallah yana lazimi ƙaddarawa yayi ma bata wurin , Momy tace wace ce zai aura ? Caca zai aura , Momy tace wace ce Caca ? Wannan karuwar , wata irin zufa ta ketowa Momy cikin tashin hankali tace Dikkon wai ? Jiddah tace Eh , kashe waya Momy tayi ta fara kiran wayar Dikko amma a kashe yake , Ashiru ta kira bayan ya ɗauka tace ya bata Dikko yasan da kwanan zance dan hakanyace mai gida yaje kaduna wurin wasan polo , haka Dikko yace duk wanda Momy ta kira a cikinsu baya nan yana kaduna tunda dama zaije polo saukar da akeyi ma Sultana shine ya hanashi zuwa , Momy tace shi da waye ya tafi kadunar ? Ashiru yace shida wani abokinshi , turomin number abokin nashi , har zata kashe waya taji bata iyawa tace ubanshi ne yahau doki yau zakacemin yaje kaduna ?

Ashiru yace nidai ban sani ba hajiya nasan dai mai gida baya nan bara na turo miki number abokin nashi , ina jiranka ta tsinke wayarta , gyara kwanciya Dikko yayi bayan Ashiru ya gama waya da Momy dakel ya fara karanta tsohon layin Sultana dake hannunshi , bayan ya gama faɗa Ashiru ya tura mata ,

      Tana gama waya da Ashiru ta kalli Dady tace kaji wai Dikko zaiyi aure , Allah yasa alkairi , Dady ya faɗa , Momy tace wai har Dikko nawa yake zaiyi mata biyu ? Dady yace yo shi ɗin na wasa ne ? Karuwa fa ? Karuwar aini daya faɗamin zaiyi auren nan da banyi tafiyar nan ba , kunga tun nan Dady ya zame kanshi , Momy tace kaima bai faɗa maka ba ? Dady yace um umm , haka Momy tayi ta gwada number da aka turo mata amma batayi , cikin daren ta kira “ya “yanta mata tace idan Allah ya kaimu gobe lafiya suje gidan Dikko daga amarya har danginta suyi musu terere …….!

    Hmmm tou waye ma zaije ya tashi rashin kunya har gidan Dikko duk girman mutum Dikko ya sauke mishi rashin mutunci , baka zo gidanshi ba kayi masa yaje ya isko ka har mazaunin ka ya gwagwaɗa maka rashin mutunci ina kuma ga ka hawo layinshi a cikin gidanshi……………. ?

      Ranar ɗaurin aure !

Tunda safe Inna da kanta ta ɗaukeni a mota ta kaini gidan Kaka hmmm wai ni za’ama nasihar zaman aure , murmushi saida ta ƙari karatunta Inna ta ansa itama tayi har miyan bakinta ya kusa ƙarewa sannan tayi shiru kuma duk maganarta akan Dikko ne , daga gidan Kaka ta ajiyeni wurin wankin kai tace zataje ta dawo ,

      Har aka gama abinda za’amin Inna bata dawo ba , ina nan zaune ina zaman jiranta kiran Yazeed ya shigo wayata , ɗauka nayi bayan mun gaisa yacemin An mata kanki ɗaya ? Nace meya faru ne ? Ki rasa wanda zaki aura sai DK haba An mata me zakiyi da DK ? Wallahi ba baki nayi miki ba ko kinje sai kin dawo kinsan iskancin DK kuwa ? Kuma wallahi ba sanki yakeyi ba yaudara ce kawai bakiga auren naku duk a munafurce akeyinshi ba ? Duk auren da yayi babu wanda baiyi hidima da shagali na tashin hankali ba , duk matan daya aura wallahi lefe akwatina 200 yayi kinga banbanci biyu ya fito ko ? Ji naki babu wani shagali tun nan kisan baya maraba da auren saboda baya sabgar mata yake so ya moreki ya koraki bayan ya gama hora miki zuciyarki da soyayyarshi , banbanci na gaba lefe akwati 24 yayi miki , kuma zai haɗaki gida ɗaya da matarshi cewa yayi wai bazai iya ajiyeki goruba ba gidan yafi ƙarfinki kinji yadda yake aibata ki ? Hmmm uwa uba kuma ga duka kwata² baisan darajarki ba mahaifiyarshi bata sanki ga masifar DK gana matarshi “yan uwanshi da mahaifiyarshi ina zaki saka kanki ? Ya ganki “yar yarinya shi yasa ya liƙe miki yayi ta cin zalinki Dikko mugune na bugawa a jarida kiyi karatun ta natsu kuma ki cire number na a wayarki nasan zai sake miki sabon layi ne ki kirani da sabon layin zan baki shawara , jiki a sanyaye nace tou ,

     Ina kashe wayata Dikko ya riƙa zuwamin a zuciyata , kyawun fuskarshi maganarshi da yakeyi cikin sanyi sai kuma tsadajjen murmushin shi mai ɗaukar hankali kallonshi mai tayar da tsikar jiki rigimarshi idan ya kafe yana faɗa dani da gaskiyarshi jina yake kamar wata sa’arshi , murmushi nayi a zuciyata nace mutumi na Allah ya baka lafiya , amma fa maganar gaskiya Dikko yana da cuta a rayuwarshi , horn in Inna ya dawo dani daga tunanin dana lula , jakata na ɗauka nayi musu sallama na wuce….

     Lokacin da muka dawo gida gidan ya fara ɗaukar taron jama’a ƙawayen Inna wankakkin matan da suka san abinda sukeyi , kuma matan Baba ƙarami sunzo dan rashin kunya da “yan uwan Inna , ɗakin mijinta ta wuce dan itama gobe zasu bar nigeria , ko walima bata tsayawa ayi da ita shi yasa bata da wani ishashshen lokaci kula da mutane tana ta shirinta ,

      Ɗakin Inna na shiga ƙawayenta suka sa ni nayi wanka ina fitowa suka rubdigarmin suna min shiri na musamman nidai sai yanzu jikina ya fara sanyi da lamarin Dikko tsoranshi naji ya kamani da maganar da yayi min jiya a goruba wai muje saman gado mu fidda raini , sai wayar da mukayi dashi wai nice dokinshi zaiyi sukawa akaina , sai maganar Yazeed da yace Dikko ya ganni “yar yarinya shi yasa ya liƙemin zaiyi ta cuta na ne , fashewa nayi da wani irin kuka mai tada hankali nace nidai wallahi bana sansa ,

    Inna data shigo yanzu cikin shiga ta wayayyin mata tace wane ne bakya so ? Dikko , dariya ƙawayenta sukayi gaba ɗayansu cikin shaƙiyanci suka kalleni cikin yanayin wayyo muna tausaya miki , Inna tace kin manta daren ɗaurin aurenki da Sultan abinda kikace akan Dikko ? Aimu saidai muce Allah ya baku zaman lafiya… 

Ƙara sheƙewa sukayi da dariya , kamar wata taɓaɓɓa haka nabisu da kallo ɗaya bayan ɗaya Inna tace ke da Allah ki rufe mana baki ko ki fita ki bamu wuri , wata ce tace a , a karta fita tazo nan ta zauna , saman gado na koma bayansu na zauna sukaci gaba da firarsu na tafiyar Inna…… !

      Bayan sallah juma’a dubun mutane suka sheda ɗaurin auren *DIKKO U DK* da amaryarshi *MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA…* akan sadaki naira dubu ɗari ɗaya lakadan ba ajalan ba , ɗaurin aure yayi albarka wanda manyan mutane da dama suka samu damar halakta daga jahohi da dama , Baba Ƙarami yaje amma yaƙi yadda ya ɗaura aure mijin Inna ya zama waliyin Sultana , ana gama ɗaurin aure Dikko ya buɗe wayoyinshi , yana buɗewa saƙon Momy ya shigo !

    _Idan ka kuskura ka ɗauko “yar duniya ka watsa kanka ka watsa gidanka , kuma tunda bansan yarinyar nan ko ka aureta saika saketa…..!_

      Murmushi Dikko yayi tare daci gaba da duba saƙonni , hada Yayarshi itama ta zazzageshi tass murmushi ya sakeyi sannan yace aike a cikin kayan miya ko matsayin ruwa baki kai ba sharar bakin kwata dake , na ɗayar Yayarshi ya duba itama dai abun babu kyan gani da daɗin ji , kanku akeji , saƙon Dady ya gani shi kaɗai ke masa fatan alkairi , bayan ya gama dubawa Ashiru yaba wayoyin yana gaisawa da mutane.

       Wallahi Uncle na zuba , Mardiyya ce tsaye a gaban Al ‘ Ameen yace haba Doughter da kin zuba maganin nan idan an ɗaura auren nan niba ɗan Babana bane , tayi masa rantsuwa cewa ta zuba saidai idan bashi ne yaci abincin ba ko kuma baici ba , dan abincin sa daban aka zuba mishi , jinjina kai Al ‘ Ameen yayi tare da cewa aiki ya kwana uban gayya ya mutu , muna fama da Jiddah Sultana ta shigo , dolensu kowa zata kama gabanta amma Jiddah ce farko sai Sultana tabi bayanta , Mardiyya tace Uncle tare zasu tafi gaskiya , Al ‘ Ameen yace tabbas ki faɗawa waccan jakar boka yace azo a anshi saƙo gobe , Mardiyya tace to ta wuce ciki , tana wucewa Al ‘ Ameen yace zaki bani motarki da manki da kuɗinki inje in biyawa kaina buƙata…….

     A wahalce Dady ya kalli Bello saida yayi nishin wahala sannan yace ɗan iskan yaron nan ma inajin ma ya mata damu ! Bello yace kaidai mu fita lafiya , Dady yace nidai jibi idan Allah ya kaimu za’a kawomin kuɗin nan na bashi na huta da wahala Dikko ɗan iskan yaro ne , dariya Bello yayi ta taɓaɓɓi yace mai naɗawa manya kashi….

     Umar dai baya gajiya da gulma da kanshi yaje har gidan Amisty ya faɗa musu mai gida ya auri Sultana , Hafsa ita bata nan tana abuja wurin wata shaƙaƙƙiyar mata ta hawan kwakwa mai ranar bacci , Amisty tanajin labarin auren Sultana ta haɗa dabar karuwanta hada su wane yaro tace kowa ya shirya su tara gidan amarya amma kar a faɗawa Hafsa dan gudowa zatayi ta dawo kuma tayi zubin kuɗinta dan bata ɗaukar asara ,

     Momy kuwa tana daga can ta tattara kan yaranta ta turasu gidan Dikko tace idan suka ragawa Sultana da duk masu rakota sai taci ubansu , dan haka suma suka taho ko wace kanta ɗure da iskanci suka iso gidan ,

      Mardiyya kuma ta ɗora Jiddah saida ta tabbatar tafi jirgin sama tashi hankalinta ya kwanta , kuma faɗa mata Uncle zaije zaria boka yayi kira , Jiddah tace zasu haɗu da daddare.

     Yazeed kuwa sai ƙara kirana yake yana jaddadamin na cire numbershi karna manta ya sanni da mantuwa , raina ya ɓaci dan haka kallo biyu nayi ma numbobin suka zauna akaina gaba ɗayansu…..

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button