NOVELSUncategorized

NIDA AMARYATA 19-20

1⃣9⃣_2⃣0⃣

      Shikam ya shiga uku,to Yanzu Ina yasan inda zai wani samo kuli-kuli,haka dai yaita rarrashinta,zuwa can yaga ta bingire alamun tayi bacci,Dan haka ya sauke ajiyar zuciya.Sosai ya shiga tunanin rayuwa,lallai akwai aiki a gabansa kenan.


*****
Yau kwance take kan kujera three seater ta mimmike kafafu tana chart, murmushi take ta saki, sakamakon hirar da sukeyi ita da Alhaji tana Mata dadi,.kamar kullum shigowa yayi tare da sallama a bakinsa,Karamar yarinyar su ta tashi da gudu ta nufi inda yake tana oyayoo Abba!batare da Nuna wata kulawa ba ya amsa da “yawwa ” Yana kokarin zareta daga jikinshi ya samu guri ya zauna,a baya idan ya dawo Sadiya na barin jiki take Masa sannu da zuwa,amma Yanzu Sam Bata wani Nuna damuwarta akan shi,shi Kuma marar tunanin ko’a jikinshi,burinshi Bai wuce ya cika cikinshi ba,Dan shi muddin bazata barshi da yunwa ba to ta Gama Masa komai.haka ta gabatar Masa da abinci,inda bayan ta zuba Masa ta hada masa komai,ta koma bakin aikinta wato dannar wayar,shima hakan ya fito da tashi wayar ya shiga dannawa yanacin abinci Yana charting,yayin da yarinyar su ke gefe guda abin tausayi har bacci ya kwasheta a kasan tiles din gurin,Amma babu Wanda yayi hankalin dauketa kowa hankali Naga waya.

Sannu- sannu alaka ta kullu Mai karfi tsakaninta da wannan Alhajin,duk da batajin soyayyar kowa a zuciyarta inba ta mijinta ba,Amma Kuma tafi Jin dadin hira da maxan social media fiye da muryar mijinta,Wanda in taga tasami lokacin sa to fa bukatar sa ce ta dawo dashi.

Yanzu Kam waya sosai takeyi da maza,sai dai duk da hakan Bata taba sha’awar haduwa da kowannen su ba,Kuma wani ikon Allah ba Wanda maganar banza ta shiga tsakaninsu,kowa batun aure yake Mata,gasu duk da alama masu kudi ne.Ko kadan Bata rasa katin kira,kusan kullum takan samu katin dubu biyar,Kuma abin takaicin tana samu zata Turawa mijin shima,Amma Bai taba tambayar ta Ina take samu ba,saima abin haushin wani lokacin ya kirata yace Kati yake so inda akwai.daga Kati Abu ya Fara girma,domin kuwa har kudi ake tura Mata a account dinta,duk da Bata roka,sai ya kasance wannan dabi’ar ita tasa take burge mazan duba da sukayi ‘yammatan Yanzu sun fiya roko da son abin duniya.

Sam basheer yazama sakaran namiji,fada hantara da kyara,uwa uba rashin Nuna kulawarsa akan ta ita da ‘yarta Koda basuda lfy,to fa Saiya ga sun jigata kafin yakaisu asibiti.Itako Sadiya Yanzu ganin tanada kudi yasa Sam ta fita shirginshi,ko nemanta yayi sai taga dama,Dan ji takeyi Yanzu ta Fara tsanarsa,shi kuwa Daya fita waje sai kule-kulen ‘yammata da karyar jaraba,Sam Bai maida hankali ga bukatar gidansa ba,ba bincike shidai yaci yasha,ko da Abincin Daya ci yasan yafi karfin kudin Daya bayar Amma Bai taba cewa Ina aka samu ba.

Itako Sadiya,tana can tana Kara baje kolinta,Dan kullum dada samun masoya take,duk da ba Wanda ta taba yadda suka hadu,Dan dama mafi akasarin su manyan mutane ne suna nesa da juna.

_wannan kenan_

****************

Rayuwar Gidan Alhaji sani a Yanzu kowa Bata zo Mai yadda yake so ba,shi dai amarcin dayayi niyyar ci ba samu ba,Dan inama yasamu damar yin hakan! Yarinyar da duk abinda yayi Mata saita fada,Wanda yayi fadan harya gaji,ya Kuma daka ta sanar da Aunty Hama tasashi biyan kudi.Dan haka ya hakura yake lallabawa.Itako Hajiya Maryam tana sane da duk abinda ke faruwa,sosai take yiwa Nihila wayo tana Jin meke wakana tsakaninta da Alhaji,Jin datakeyi ba wani abinda ke shiga tsakanin su yasa ta kwantar da hankalinta.yaran kuwa sai dai suyita janta tana musu shirme suna dariya,taita fada musu abinda Alhajin ke Mata su kuwa ko’a jikinsu har gara Amira in tana wajen Bata son Jin wannan shirmen.

Yau suna zaune a falo sukaji sallamar Ayuba,dukansu amsawa sukayi ya karaso falon tare da jaka katuwa Yana nishi.

Kallonsa Hajiya Hafsa tayi tare da fadin “wannan jakar fa daga Ina?” Cikin ladabi ya kalleta tare da dukar dakai yace,” Hajiya babba ce ta iso”(wato mahaifiyar Alhaji),dukansu kallon juna sukayi Dan sun San Hajiyar bala’i ta iso,kowa fara’ar fuskarta Saida ta dauke,Amma ya zasuyi,sun dai San tabbas kwanakin walwalarsa sun Sami tsaiko har zuwa lokacin da zata gaji ta bar musu gidan.

Cikin kankanin lokaci aka Gama shigo da kayanta tsaf akwati kusan hudu,Saida ta tabbatar an Gama shigar da kayan sannan ta shigo falon.

“Assalamualaikum fitinannun gidan,gani nazo d’an bakin ciki Saiya mutu,Dan wannan karon Zama daram dam gidan d’an albarka,duk bakin cikin mutum sai dai ya mutu,Dan Nan gani Nan Bari,na tabbatar Yanzu an auro gagara badau,wadda zata haifamin jika namiji Nima in gani inji Dadi ba gayyar Mata ba,wadanda wasu ma in ba’ai sa’ar aure ba daga shekara sai watanni za’a barsu su dinga fita,haka dai ta dinga maganganun ta,Wanda suke Kara bakanta ran Hajiya Hafsa,Amma take dannewa,Dan wani dalili nata na da ban.

Sosai suka shiga yimata sannu da zuwa amma ko kallon arziki Basu samu ba,bare ta amsa kawai Fadi takeyi,”Ina amarya ‘yar Albarka,irin haihuwar ‘ya’ya maza,fito maza in ganki ki ganni da alkhairi ta fada tana Mika wuya tare da neman gurin zama,tana ta surutan ta,yayin da su Amira suka mike suka shiga dakin da take sauka kusa da kafar benen,Dan su gyara Mata,duk da kusan kullum a share yake, inda suka dauki kayanta suka shiga dashi,yayin da ita Kuma taci gaba da zaginsu da Kuma Kiran amarya.

Nihila ce a daki,inda taketa wa Alhaji kuka Wai Saiya goyata,ya sauka kasa da ita,Wai bazata iya ba kafarta ciwo take.Wayo yake ta son yi Mata Dan yaji hayaniya a falon alamun yaran na nan,Dan haka yake son yaje ya koresu sannan yazo ya dauketa Amma Sam ta hanashi,ganin hakan yasa kawai yace ta tashi suje din.Cikin murna ta dane bayansa tana dariya,shima dariyar yakeyi tare da fadin wlh saita rama Masa Nan suka nufo kasan,Wanda maganar da Nihila ke Masa yasa Sam baiji maganar da Hajiya takeyi ba,har Saida ya iso falon sannan yaga Hajiyar,Nan ya shiga Nuna farin ciki da ganinta tare da kokarin sauke Nihila dake bayansa,wadda ita Kuma ta maqalqale shi tana fadin bazata sakko ba.

Hajiya kaka ce ta kalleta tare da fadin, “kin ci gidanku,’yar kaniyar uwa! So kikeyi ki Buda Masa kirji kome? Ina laifin ma ya goya yayar taki,Dan koba komai ita goyon soyayya ne bazaiji nauyi ba,amma ke gotai gotai dake kin wani d’are Masa baya,sai kace biri yasamu bishiya,sakko maza kan kisa ya Fara haki.

Nihila data zumburo Baki gaba tare da kallon Hajiya ta murguda Baki,sannan tace “to ai ‘yar goyo mukeyi ni dashi,yace Nima Zan rama Masa nace eh na yadda ko baba?” Ta karasa maganar tana leka fuskar Alhajin da zimmar tambaya,Wanda shi kunya duk ta dabaibayeshi so yakeyi ta sauka,Dan haka a takaice ya amsa Mata da “eh! Amma Yanzu sakko tukunna ki gaida Hajiyata .

Tana sakkowa Hajiya kaka ta shiga fadin,”ke ‘yar nan,da wa zakuyi ‘yar goyon? Kinga ni ban son shedanci,ku dama irin yaran Nan ‘yan boko,haka kuke,Wai mijin yayarki ya tabaki ya tabata,ku bakuda matsala,to Kuma gaku barakallah Allah yayi muku jiki kamar gwanda da tumatur,haka kawai garin tabe-taben Nan a tabo tsiya,to nidai bada ni ba,ban son wannan sakarcin,kiramin ita amaryar albarkar in fada mata,tayi hakuri ta hanaku wannan wasan Dan ko’a muslinci baida kyau ehe”.

Cikin Jin kunya,Alhajin ya tsugunna tare da Fara haisheta,Nan yake sanar da ita ai Nihila ce amaryar.

Shuru tayi????kamar me tunani,zuwa can Kuma ta juya ta kalli Nihila wadda take tsaye kyam bayan Alhaji,sannan tace cikin fara’a,” ah Dan Albarka kace wannan karon Kuma wannan muka samu,ah to kayi kyan Kai Kuma,Dan da alama duk Dan da za’a Haifa to na musamman ne,Dan kasan ance dama danyar mahaifa tafi daukar duk kwan da aka so dasawa,Dan haka nayi murna Allah yasanya alkhairi” ta karasa maganar tana kallon Nihila tare da sakar Mata murmushi.

Cikin Jin Dadi Alhajin ya dago Kai tare da kallon Nihila yace,”wannan itace Hajiyata zo ki gaisheta.


“Tabbb Inna gaisheta Allah yaimin Albarka,ba Yanzu ta Gama zaginmu ba,Kuma sai in gaisheta ai Wallahi sai dai ta bushe……????




*Sai kunyi hakuri da yanayin typing masoyana Ina alfahari daku*



*Alkalamin khady* ✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button