NIDA AMARYATA 15-16

1⃣5⃣_1⃣6⃣
Asibiti suka kaita,inda Nan aka shiga bata taimakon gaggawa,duk Wanda yaga halin da Amina ke ciki Saiya tausaya mata.Haka ma Aunty Hama,domin duk ta canza kamanni,inda sosai rashin lafiyar yayar tata ke tabata,wadda take tamkar mahaifiya agareta.Kasancewar basu da kudi,yasa kawai
karamin treatment akawa Amina suka dawo gida.Inda kafin su taho likitan Saida ya Kara jaddada musu suyi kokari ayiwa Amina aiki.
Duk rayuwar tayiwa Aunty Hama kunci,Dan ita Nihila Bata ma San wata damuwa ba,amma takan tausayawa mahaifiyarta a duk lokacin data kalleta,Tasha cema Aunty Hama,”Wai Aunty meke damun mama ne?”
Takan ce mata”mama na fama da lalurar da bamuda kudin maganinta,sannan bamuda mataimaki sai Allah,muci gaba da Mata addu’a domin nasan har abada bazamu taba samun kudin da za’ai Mata aikin da akace ba”,takan karasa maganar tana kuka sosai,saita jawo Nihila ta rungumeta.Hakan kesa Nihila cewa,”ki daina Kuka Aunty! Idan nayi girma nayi kudi,zan biya ayiwa mama aiki,Zan sai Mana gida insai Mata mota”.ire-iren wadan Nan surutan Nihila keyi kusan kowanne lokaci.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya,Koda sun Samu Dan kudi,be wuce Wanda zasu ci abinci ba.Dan haka suka fawwalawa Allah dukkan lamuransu,suka zubawa sarautar Allah ido.
********
Kasancewar an Basu lokacin daya kamata su rinka kawota ana dubata,yasa yauma suka shirya Dan zuwa ganin likitan.Yau kam da Nihila Aunty ta shirya tafiya,domin ta Fara Jin tsoron barinta da takeyi a gidan ita kadai sai dai ta rufe ta waje duk da unguwar akwai security sosai Dan ta jama’a ce,amma yanzu zamanin ya canza,hakan yasa ta shirya ta itama,cikin Riga da wando ‘yan gwanjo,sai wani karamin hijab,Wanda duk da basuda hali,Aunty Hama Bata son kazanta,tana Kuma kokarin siyama Nihila sutura.
Kamar ko yaushe drop din adaidaita sahu suka dauka,wanda ya kaisu har asibitin.yau magunguna aka rubuta musu da wasu allurai masu tsada,Wanda dole sai anyi Mata su a yau din.Haka yasa Aunty Hama ta fito rike da hannun Nihila Dan suje pharmacy suji kudin maganin.Suna zuwa aka fada musu kudin,hankai Aunty Hama yayi mugun tashi,domin kuwa tasan basuda shi basuda ko kadarar da zasu sayar su Sami wannan kudin,hakan yasa ta kamo Hannun Nihila suka fito tana sharbar Hawaye,ganin tana kuka yasa itama Nihila tayata.
Ji sukayi ana musu sallama ta bayansu,da sauri suka juya ganin waye.Wani Alhaji ne,sanye cikin farin shadda babbar Riga Tasha aiki,rike yake da hannun wani yaro Wanda ahekarunsa zasu Kai goma da alama yaron ma baida lfy.amsa Masa Aunty Hama tayi yayin da take kokarin goge hawayen fuskarta.
Subahanallah! Ya furta,tare da fadin,”lafiya baiwar Allah Kuna tafe Kuna kuka?”
Cikin kukan tayi Masa bayanin abinda yasasu kuka,sosai ya tausaya musu,sannan yace,”assha! Ai rayuwa sai hakuri,kuyi hakuri kunji,dama rayuwar ta gaji haka.Dama tambayar ku zanyi” Nan ya shiga tambayar su inda yake son sani.Kwatance Tayi Masa,yayi Mata godiya,sannan yace ta tsaya ta jirashi anan yanzu zai dawo.
Haka ya tafi,ita Kuma ta tsaya tunanin ta tsaya ko ta tafi,ganin batada mafita yasa kawai ta zabi tsayawar.
Takai kusan awa daya a zaune,kafin ya dawo.Karbar takardar hannun nata yayi yace ta biyoshi.Sosai tayi makakin ganin ya siya musu allurar da magungunan,inda Dan tsabar farin ciki saita zube a gurin,tana Masa godiya tana kuka.sosai ya tausaya Mata Nan yake tambayar ta meye matsalar marar lafiyar,Nan take sanar mishi abinda ke faruwa.
Ya dau tsawon mintina Yana wani nazari kafin yace,”Allah yabata lfy,karamin katinsa ya Miko Mata tare da cewa wannan katina ne,in kina bukatar wani taimako kina iya kirana,sannan ya Miko Mata dubu biyar tare da Kara cewa,”sunana Alhaji kabeer! Ke fa?”
“NI sunana Hama!”
Kallonsa ya mayar ga kyakkyawar yarinyar dake gefenta,yace,” wannan “yarki ce?”
Da “Eh! Ta bashi amsa.
Girgiza Kai kawai yayi batare Daya Kara cewa komai ba domin yin wani nazari idonsa na kan Nihila,wadda duk take a takure, kasancewar kallon nasa.
Sallama yayi Mata sukaya juya ya tafi tana ta Kara mishi godiya.
Cikin azama da himma takaiwa doctor ledar maganin.nan aka shiga kokarin fara yi Mata.
*****
Shikuwa Alhaji Kabir,a mota kawai tunanin yadda zai taimaki wadannan bayin Allan yake,duk da baiga marar lafiyar ba Amma a labarin da Aunty Hama ta bashi ya fahimci tana cikin matsanancin hali.yawan kudin da ake bukata na aikin tabbas yasan baida shi Dan ko shi jarin shi bazai gaza hakan ba.gashi shi Kuma mutum ne me tausayi,sosai yake tunanin yadda zaiyi ya taimaka musu.
Maganarshi ce da Alhaji Sani ta fado mishi,inda yake cewa.”Kasan Allah Alhaji wannan karin kara’i zanyi,Dan gara in mori Abu biyu,yarinta ga Kuma haihuwa,Dan nagaji da auren guzumaye,gara in auri danya shatab,wadda Zan more girmana,tunda inada kudi,gara inyi abinda naga dama,Dan haka kawai in kasan wata me dama-dama ka samomin Dan kasan ni Banda time din dazan tsaya kula mace a waje,Dan haka nabaka wuka da nama”
Wannan maganar da sukayi ita ya dinga tunani,domin yasan Alhaji sani Koda yace ya taimaka musu yasan bazai taimaka ba,Dan shi mutum ne da Allah ya azurta da dukiya,Amma Sam baya taimako,daga cinya sai katara,sai Kuma auren jaraba.Da wannan tunanin ya karaso gida,inda yayi horn megadi ya bude masa ya shiga gidan zuciyarsa fall da tunanin yazaiyi ya bullowa wannan lamarin.
*_WANENE NE ALAHAJI SANI_*?
Shi Dan asalin garin jos ne,mahaifinsa Alhaji mansur tsohon Mai arziki ne,Wanda a lokacinsu Yana jerin lissafin wadanda za’a sayl sahun gaba na masu kudi.matansa biyu,Hajiya maryam,da Hajiya lubabatu,Hajiya maryam itace uwar gida Amma Bata taba haihuwa ba,Saida aka auro Hajiya lubabatu ta haifi yaronta namiji Wanda yaci suna Sani.daga kansa ba’a sake wata haihuwa ba a gidan,sosai yake samun soyayya ta ko wanne bangare,Dan hatta Hajiya Maryam da ba ita ta haifeshi ba yaga soyayya matuka.Sani na da shekara 12 a duniya mahaifinsa ya rasu,inda ya bar Masa tarin dukiya.
Sosai rayuwa taci gaba yayin da sani keyin karatu Kuma yana kasuwanci kasancewar yanzu ya mallaki hankalin kanshi.sam baya Nuna banbanci tsakanin iyayenshi Mata guda biyu,duk Yana Basu kulawa iyakar iyawarshi.sai dai fa Hali guda Daya dayake dashi Sam baya taimako,a cewarsa zakkar da yake fitarwa duk shekara ta isa komai,ana haka Hajiya Maryam ta rasu.bayan wani lokaci ya tattara mahaifiyar sa suka dawo kano da Zama,sosai yake neman kudi,domin duk onda yaga zai samu to fa zai nema,sosai suke rayuwa cikin Jin Dadi inda daga karshe dai yafara neman auren wata Hafsa kanwar abokinshi ce.ba’a wani dauki lokaci ba,akayi bikin domin duk suna son junansu, haihuwar farko Allah ya azurta shi da samun Diya mace,sai dai yayi farin ciki sosai inda yasa Mata suna maryam,ake kiranta Amira,cikin ikon Allah ana yaye Amira ta Kuma samun wani cikin inda ta haifo mishi wata macen aka Sanya Mata sunan mahaifiyar shi wato lubabatu inda suke kiranta da Ummi,ana tsaka da goyon ummi Kuma ta Kara samun wani cikin anan ne ya shiga addu’ar samun da namji domin Yana son yaga ya Tara zuriya sosai Dan dangin su basuda yawa.aikuwa saita Kara zabgo Masa ‘ya mace,duk cikin haihuwar baby Mai fama da rashin kulawa kamar wannan,domin duk Sam yaki ya Nuna farin cikinshi kiri kiri ya fito fili ya shaida Mata abinda ke ranshi.ta girgiza da Jin kalamanshi,Amma ba yadda zatayi,a cikin satin akayi suna yarinya taci suna Fatima.
Tun daga wannan lokacin haihuwa ta tsayawa Hafsa.da farko Bata wani damu ba ganin cewa shima mai gidan Bai Nuna damuwarsa ba,amma cikin lokaci kankani ya birkice Mata,akan tayi ciki ta haifo Masa d’a namiji ko Kuma ya Kara aure.Ba yadda ta iya,bisa dole ta dage kamar ita zata ba kanta cikin Amma Abu shuru.
Gadan gadan ya fada neman aure, lokacin Daya fada Mata ta girgiza Amma saita daure dayi fatan alkhairi,Hafsa nada kishi Amma tayi kokarin dannewa,Dan gudun jefa kanta a damuwa.
Bayan yayi auren ne Kuma ta dangana,suna zamansu lfy ba laifi,watan matar goma ta haihu,inda ta santalo Masa mace,babu ruwansa Dan Bai wani Nuna murna ba sosai,sai dai yayi kokarin yimata duk abinda yakamata,yarinyar bata wuce sati biyu ba Allah yakarbi rayuwar ta.duk sunji mutuwar ta taba iyayen.ba’a wani dauki lokaci ba ta Kuma samun wani cikin,Nan fa burinsa duk ya ta’allaka ga haihuwar d’a namiji.ana haka ko saigashi ta Kuma haihuwar ‘ya mace Nan fa kiri-kiri ya nuna abinsa karara, Wanda hakan yasa sukayi tashin hankali Wanda har yaja ya saketa.To fa daga nan ya bude kofar aure,Wanda hakan yasa munnira kanwar Hajiya Hafsa ta Fara zugata,Nan suka Fara shige-shigen malamai da bokaye,cikin ruwan sanyi suke korar duk matan da yayi ba tare da kowa ya ankara ba.
_wannan kenan_
washe gari tunda safe Alhaji kabeer yayiwa office din Alhaji sani tsinke, inda bayan sun gaisa Nan suka taba ‘yar rahar su ta abokai,Wanda Saida suka nutsa sannan Alhaji kabeer ke sanar Masa abinda yakawo shi,na cewar an Dace da ‘yar shilar da yake nema.
Dariya Alhaji sani yayi suka cafke hannu hannu.Inda nana yake shaidawa abokin nasa tafiya ta kamashi zuwa Cairo amma bazai Dade ba zai dawo,ayi komai da wuri Dan badan ma abin yazo a kurarren lokaci ba,da sai an daura ya tafi da amaryarsa..haka sukaita Hira har Alhaji kabeer yayi Masa sallama ya tafi,cike da tunanin Ina Kuma zai Nemo su Aunty Hama! Domin dai shi yabata compliment card dinshi,ita baima tambayi ko tana da wayar ba……
_gareku masu yadamin littafina,ki sani Koda kin siya a yanzu har yanzu Bai Zama mallakinki ba,domin Yana kasuwa ne,kisani ita Amana Daya ce,bazan taba ja Miki Allah ya Isa ba Akan abun duniya fararre kararre,Amma ki tuna duk kasuwanci kasuwanci sunansa,Kuma duk abinda akace na siyarwa ne! To fa Dan a siya aka kasa.Mu ba yara bane Bai kamata mu dinga abinda Bai Dace ba,na rokeki da girman Allah koma wacece kiyimin adalci Kuma ki tausayawa kanki,domin hakkin da kike rainawa Wallahi zai iya Miki dabaibayi da jagora zuwa wuta.Fatan zaku fahimceni._
*Kada kuga baku jini ba jiya Wallahi munada marasa lfy kunsan dai halin da ake ciki yanzu fatan zakumin uzuri*
*Alkalamin khady* ✍