NIDA AMARYATA 13-14

1⃣3⃣-1⃣4⃣….
Malam yahya,haifeffen garin kano ne,Dan Asalin kauyen Garko,Yana da Mata guda Daya Amina wadda asalinta ‘yar garin adamawa ce,bafullatana kyakkyawar asali,suna da yara guda biyu Raliya sai Najwa,ita Raliya tayi Kama ne da mahaifinta yayin da Najwa take Kama da mahaifiyarta
sak,tun daga kansu Allah Bai Kara Basu haihuwa ba,malam yahya Yana sana’nar tireda ne,inda yake sayar da kayan shago dangin su sukari,maggi gishiri,batir,da dai sauran abubuwan da bazasu gaza daukar shagon ba.Ita Kuma Amina na sayar da kayan Miya busassu a gida,dasu suka Sami rufin asiri,Sam yaran nasu basuda zarafin sasu a makaranta.kasancewar basuda karfin yin hàkan,domin kuwa d’an abinda suke samu dashi suke rufawa kansu asiri,su biya haya sannan su samu abinda zasu ci,sai dai suna rayuwa ne Mai matukar burgewa domin suna kulawa da junansu matuka.
A yanzu Raliya nada shekara Sha hudu,yayin da Najwa keda shekara 11,suna tsaka da rayuwar su ta cikin gida,domin Babu Mai fita cikinsu saita Kama,suna tsaka da wannan rayuwar ne kwatsam wata Rana suna zaune wani yaro ya shigo cikin rudewa Babu ko sallama,yake shaida musu wani Mai mota ya Kade malam yahaya,Amma an nufi asibi dashi,duka ahlin wannan gidan sun shiga tashin hankali.haka suka nufi asibitin cikin kuka,Koda suka Isa sun tarar da tashin hankalin dayafi Wanda suke ciki,domin sun tarar da malam yahaya tuni ya cika,Dan ance tun a hanya ya mutu.fadar tashin hankalin da suka shiga ba’a cewa komai,daga Nan suka dauko gawar suka nufo gida da ita akayi Masa duk abinda yakamata aka kaishi makwancinshi na gaskiya,(Allah yasa mu cika da imani ameen).
Tunda malam yahaya ya mutu rayuwa ta canzawa gidan,domin kamar ya tafi da duk wani tallafin rayuwarsu,domin jarin kayan miyan ma yanzu Babu,ga ‘yan uwan malam yahaya duk ba masu karfi bane,gara ma ‘yan uwan baba Amina,amma Suma bamai taimakon ta,watan malam yahaya biyu da mutuwa baba Amina ta fahimci tanada ciki,domin yawan laulayin da taketa fama dashi,tayi kuka sosai Daya fahimci shigar cikin,domin yanzu Babu gatan Wanda zai rungume su.Bisa ga wannan dalili bisa dole su Najwa suka Fara sana’ar wake da shinkafa,tare suke fita su sayar Kuma cikin kamun Kai Dan ba ruwansu da kwaramniya irin ta yara masu tallah.da wannan suka samu asirin su ya rufu,sai dai fa abin tashin hankalin rashin lafiyar mahaifiyar su,domin tunda daga bayyanar cikin Nan kullum batada lfy,inda abun yayi tsanani sunyi yunkurin zuwa asibiti,saita ce a barshi,laulayi ne irin na ciki,tasan zata warke.Bisa dole suka hakura,Amma dai suna cikin damuwa.
Yau baba Amina ta tashi da nakuda,wadda kwana tayi tana yinta,ganin ta daure Amma Abu yaki,yasa tacewa yaran su tafi asibiti,bisa dole suka Nemo Mai adaidaita suka nemi taimakon makwabta,aka kamata duk suka dunguma zuwa asibitin.Nan ma Saida ta kuma kwana Bata haihu ba,gashi ta Fara fita a hayyacinta.hakan yasa hankalin yaran ya tashi dasu kansu likitocin,cikin wannan halin likitan yazo yasamesu yake shaida musu suje su Kira mahaifinsu ko wani wakilinsu Dan aiki za’ai Mata,bazata iya haihuwa da kanta ba,sosai suka shiga kuka suka tafi.bisa ga dole sukaje dakin mamansu suka binciko wata farar takarda Wanda aka rubuta nombobin waya da dama a jiki.wajen me cajin unguwarsu Raliya ta nufa Nan ta rokeshi Daya Kira Mata number guda Daya a ciki,Babu musu kuwa ya karba Dan yasan yaran nada kirki Kuma da gani suna cikin wani hali.cikin sa’a Yana Kira ya samu kuwa,Aunty Hama ce kanwar Amina,tana dagawa ya mikawa Raliya,cikin kuka ta shiga yima Aunty hama,abinda ke faruwa,iya rudewa ta rude,Dan Jin halin da ‘yar uwarta take ciki, kasancewar bisa ga dole ta shiga rarrashin su da kwantar musu da hankali, Nan take ce musu suyi hakuri suje subawa likitan number ta ya kirata zasuyi magana.Haka suka koma asibitin,da kyar likitan ya yadda ya Kira Aunty Hama,Nan tace ya taimaka yayi aikin zuwa yamma zata turo kudin,Saida ta rokeshi sosai sannan ya amince aka shiga da ita,anyi nasarar yi Mata aiki inda aka Ciro Mata diyarta mace kyakkyawar gaske,wadda ta Dame Amina a kyau ta shanye, sai dai fa Sam Amina batasan inda kanta yake ba.
Sunyi murna da ganin jinjirar Amma Jin halin da mahaifiyarsu ke ciki, yasa hankalinsu Kara tashi.
Da yamma saika Aunty Hama ta iso,Dan taje can gidan makwabta suka fada Mata asibitin da aka Kai ta.tana isa ta tarad da yaran cikin rashin kwanciyar hankali, direct office din likitan ta Isa,inda tana shiga likitan ya bukaci ta biya kudin aikin,bayan taje ta biya ta nemi Karin bayanin abinda ke faruwa da ‘yar uwarta,Nan yake shaida Mata cewar sakamakon labour din data Dade tanayi hàkan ya taba kwakwalwar ta,wadda dama tunda jimawa akwai wani ciwo Wanda yake a kwakwalwar ta Wanda ya kamata ace anyi aikin tun da wuri,amma yanzu ciwon yayi girman dayake bukatar aiki,ga Kuma wata lalurar ta shiga,Dan haka tana bukatar ai Mata aiki.
Cikin tashin hankali Aunty Hama tace,” to yanzu likita kamar nawa ake bukata wajen yin aikin?”
“Eh to gaskiya ana bukatar kudi masu yawa,Dan iya girman cutar iya adadin kudin,Wanda ni a iya sanina gaskiya Koda karama ce,Bata Dade da shiga ba akan kashe sama da miliyan goma,Dan Kinga ba’a Nan akeyin aikin ba,anayinsa ne kasan India ko Egypt,gaskiya ya zuwa yanzu ma bazan ce muku ga adadin kudin da za’a bukata ba,Dan lalurar tata babba ce”.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Aunty Hama ta furta,jiki ba kwari ta baro office din likitan,kuka takeyi sosai,yayin da Suma yaran ke nasu kukan,karbar yarinyar tayi inda ta zuba Mata ido,tabbas Allah yayi ikonsa a gurin,tasan sun hadu da kaddara da Kuma jarrabawar rayuwa,wadda Basu da mafita sai wadda Allah ya kawo musu,iya tashin hankalin da take ciki ma ya isheta,domin silar Kiran wayarta da likitan yayi yasa mijina sakinta,sakamakon mutum ne shi Mai bala’in zargi,tayi kokarin fahimtar dashi Amma yaki fahimta,yanzu haka ma kayan dakinta ta siyar sannan ta nufo kano.Ga Kuma abinda tazo ta tarar.Gaba Daya rungume yaran tayi suka dinga kuka.
Lokacin ko da sukaga halin da Amina take ciki sun tausaya mata,sun kuma yi kuka sosai.
Satin Amina biyu a asibiti dole suka dawo gida, sakamakon kudin dake hannun Aunty Hama ma duk sun Kare.
Sosai rayuwar su ta shiga kunci,sun nemi taimako har sun gaji,ba wani canji da aka samu.Duk Wanda yaga rayuwar da suke ciki sai ya tausaya musu,domin Aunty Hama ta dawo gidan da Zama Dan batada gurin zuwa dama su uku ne a dakinsu,daga babban yayansu sai Amina sai ita.Shima bamai Hali bane dum kanwar ja ce.
Jinjirar da aka Haifa sunan Amina suka Sa Mata,inda aka kiranta da suna Nihila.
Bisa ga dole sukaci gaba da sana’ar da sukeyi ada,ita ko Aunty Hama na gida tana kula da Amina da jaririyar.Haka suke rayuwa ba yabo ba fallasa.
****
Sosai yarinyar tayi wayau ga wani kyau na musamman da take dashi,Sam ba’a fita da ita,tunda su kansu basuda lokacin Zama da sun dawo daga tallah zasu Kama hidimar gidan da kiciniyar aikin gobe.
Haka Nihila ta tasa yayin da ciwon Amina na Nan yadda yake,Dan yanzu har miyau ke dalala a bakinta.
****
Rayuwa sannu sannu har Raliya ta Zama budurwa,inda ta Sami miji,cikin ikon Allah aka gagganda aka aurad da ita,Dan mijinta yace zaiyi Mata kayan daki Amma da kudin lefenta,hàkan yayi musu Dadi,inda bayan auren ba’ayi ko shekara ba gobara ta tashi a gidan da daddare,ga ciki Amma cikinsu ba Wanda ya fita.mutuwar Raliya ta girgiza mutan gidan,inda haka dole suka dangana,bayan wani.lokaci Kuma dole suka warware a lokacin Nihila na Kara girma sosai kyanta ke dada fitowa.
Najwa ce Alhakin tallar ya koma kanta, kasancewar ta kyakkyawa yasa tafi samun kasuwa fiye da da,sosai Najwa ke cinikin abinci,inda hakan yasa ta Dan Kara abubuwan da takeyi,sai dai duk abinta Bata harkar banza,ba Kuma ta bada fuska ga wadanda ke kawo Mata wannan shirmen.
Da haka itama tazo ta hadu da wani soja,ya yarda zai aureta,da farko taki,Saida Aunty Hama tayi da gaske sannan ta yadda, maiduguri aka kaita inda daga can aka tura mijin nata laberia,ya tafi da ita Amma Kuma want abin kaico,tun lokacin da suka bar kasar ba’a Kara Jin labarin ta ba,Wanda tun ana sa rai har an daina.
Haka rayuwa taci gaba da wanzuwa,inda bayan wani lokaci Nihila ta Kara girma,sai dai fa kawarta guda dayace ‘yar wata makociyar su,inda ita Bata fita,Dan Aunty Hama ta hanata,haka take rayuwa ba arabi ba boko,yayin da ita take sha’awar yin karatun,shiyasa in yaran unguwarsu sun dawo daga makaranta suyita shigowa,ita Kuma sai taita cewa su koya Mata turanci,to fa anan ne ta koyi turanci Dan amerika Dan ingila,sai dai Aunty Hama nada ilimin addini.ta dai daure ta koyar da Nihila Alhamdu.
Yanzu Aunty Hama keyin Abincin siyarwa,tasamu almajirai suke daukar Mata tallah,Bata barinsu su shigo gidan sai dai su tsaya iya zaure.
Yau suka tashi da jikin Amina ya rikice…..
*Kada ku Manta alkawari kayane,ban hanaku kuyi sharing ga duk Wanda kuke so ba,amma ku Kara hakuri har ya Zama mallakinku,Dan kamar ku ne ace kun kasa abu Dan mutane da yawa,sai mutum Daya yasiyi kaso Daya bisa dari,kawai sai ya hau rabawa mutanen da suke da burin siya ko wadanda ke jiran na bati,shi Wanda aka Bari da kaso casa’in da Tara to yazaiyi da sauran,hàkan ba kyau,idan na Gama baku ku bawa Wanda kuka ga dama hakkinku ne,fatan kun fahimce ni*
*Alkalamin khady* ✍