NOVELSUncategorized

NAJEEB 24

Ibtisam kam hakan da yayi mata sai bataji dad’i ba, Koba komai tunda ta gaidashi ya kamata ya amsa bawai ya shareta ba”haka ta nufi d’akinsu jiki a sanyaye domin babu dad’i ka gaida mutun kuma kasan yaji yayi banza dakai 


Koda ta isa d’akinsu babu wanda ya dawo, dan haka shiga tayi tasa wayar da kabir ya bata a caji tare da kwanciya, bata dad’e ba bacci yayi gaba da ita 

Zarah sai wajan 6 suka fito daka lecture Kai tsaye d’akinsu ta nufa taita nocking shuru saida ta dad’e “ibtisam dake bacci ta farka taji k’aran ana nocking sannan ta tashi ta nufi kofar tare da tambaya Waye? 

Zarah tace bud’e nice 

Bud’e kofar ibtisam tayi Zarah ta shigo tana fad’in haba ashe bacci kikeyi sai yasa naji shuru inata nocking 

Ibtisam tace Wlh bacci ya D’aukeni….

Katseta Zarah tayi tare da fad’in wannan wayar Waye a caji? 

Ibtisam tace nawa 

Zarah tace waya baki? 

ibtisam tace KABIR yaban shine ya kawo min wayar 

Zarah tace yazo ne KABIR din?

Ibtisam tace eh yazo bai dad’e da tafiya bama 

Nan Zarah ta d’auki wayar tana fad’in a’ah Amarya wajan barrister Kabir gaskiya yana ji dake fa Sosai, “irin wannan wayoyi har guda biyu manya ga iPhone ga Samsung 

Ibtisam dariya tayi tare da fad’in uhm bari kiga in fad’ama Ummi kar ta gani in shiga uku 

Zarah dariya tayi tare da fad’in Aikam, kin tuna abunda ya faru kenan? 

Ibtisam tace ai ban manta ba, saboda waya aka hanani zuwa skul gashi saboda Abun yasa zanyi aure ba tare dana kammala karatu ba, kaman yanda naso Nayi ba tun Farko…. D’aukar wayar da ummi tayi ne yasa ibtisam fad’in ummi Ina wuni? 

Ummi tace lafiya kalau ya karatu? 

Ibtisam tace lafiya kalau ummi.,”dama na kira in fad’a miki dazu KABIR yazo ya Kawo min wata waya, nace ya Bari tunda ga wanda yaban yace a’a wai yariga ya siya 

Ummi tace mutumin da yake hidiman aure shine yake wani K’ara siyan miki waya? Kai Allah ya kyauta, shikenan saiki ajiye d’aya kar ki ri’ke biyun a sace 

Ibtisam dariya tayi tare da fad’in haba Ummi sai kace autanki Ahamd 

Ummi tace au shikenan, “Ina Zarah 

Mi’ka ma Zarah wayar ibtisam tayi 

Gaida ummi Zarah tayi cikin girmamawa, Ummi tace ya karatun fatan dai komai lafiya? 

Zarah tace lafiya kalau ummi karatu Alhmdlh 

Ummi tace toh Masha Allah, sai a dage sannan a k’ara tsare mutunci banda kawayen banza 

Zarah tace insha Allah 

Sallama sukayi Bayan ummi ta kashe wayan Zarah ta kalli ibtisam tace Wai Mai kika dafa ne? 

Ibtisam tace Shinkafa da miya 

Nan Zarah ta tashi ta d’auko plate ta zuba abincin tare da d’auko Titus ta fasa ta zuba akan abincin ta Fara ci 

Ibtisam ita danna wayarta take abunda 

Zarah tace abincin yayi dad’i fah, gaskiya kin iya girki Sosai 

Ibtisam tace uhm Kedai kawai kice Kinji yunwa 

Washe gari ibtisam Nada lecture karfe 8 dai dai, dan haka da wuri ta shirya ita d’aya ta tafi domin har yanzu su Aisha basu dawo ba.

Ibtisam basu fito daka lecture ba sai karfe 10, “zama tayi akan wani dakali, dan tasan kota koma Zarah bata nan dan tace mata 10 suma suke da lecture 

Ibtisam na zaune tana danna wayarta gaba d’aya hankalinta nakan wayarta “sai jin muryan mutum tayi kaman daka sama ana fad’in madam danna waya 

Da sauri ta d’ago kanta taga salis ne.”murmushi ta saki tare da fad’in banga zuwanka bafa, kawai na daiji magananka daka sama 

Salis yace yaushe zaki ji, tunda kina Bussy wajan danna waya, kina chatting

Tace uhm wani chatting, game nakeyi a wayar 

Yace yau banga Aisha ta shigo lecture ba? 

Ibtisam tace eh bata nan 

Yace ok su Aisha manya indai mutum ya ganta a lecture Toh na Dr jibril ne, dan tasan baya wasa 

Ibtisam bata ce komai ba, tana dai sauraranshi 

Salis ya kira sunanta da fad’in ibtisam 

Tace na’am 

Yace ina son fad’a miki wata magana in babu damuwa 

Tace ka fad’a karka samu damuwa 

Yace OK… 

Lokaci d’aya ya fara magana kaman haka, ibtisam tun sanda na ganki na yaba da hankalinki da kuma nutsuwarki, “duk da d’akinku d’aya dasu Aisha amma sai naga ke dasu ba irin halinku d’aya bane, kuna da banbanci Sosai 

Ibtisam jinshi take 

Yace tun sanda na ganki naji Ina sonki, sai dai nasan bazan samu karbuwa ba, may be kice Nayi miki k’arami ko kice muna karatu tare, naso Nayi shuru na boye abunda ke raina sai naga is better in fad’a May be in dace 

Ibtisam tayi shuru Kafin tace”nagode da kauna, sai dai ina Mai baka hakuri akan biki na saura wata hudu da sati d’aya 

Salis yace kai aure? 

Ibtisam tace eh 

Salis yace wow na tayaki murna, gwara kiyi auren domin shine darajan mace,”amma fa wlh kin burgeni da zakiyi aure tun yanzu, ba irin matan da za suce sai sun gama karatu ba, daka karshe samun mijin ya musu wuya ba 

Ibtisam tace uhm ba tare da tace komai ba 

Salis yace ya kamata dai yanzu tunda zakiyi aure kina da miji sai mu zama friends amma wanda zai aureki yayi Sa’a, yamin shigan sauri 

Ibtisam dariya tayi domin maganan salis ta bata dariya yanda yace wanda zai aureta yayi mishi shigan sauri 

Suna nan zaune suna fira ita da salis harya tashi yace Bari yaje ya amso sa’ko 

Tace OK nima dai Bari inje in huta 

Duka suka jera tare shiya Mike ita tasha kwana domin zuwa hostel, “koda ta koma d’akin taga su Aisha da hauwa da kubra a d’akin suna ta raban kud’i 

Shigowan ibtisam yasa kubra fad’in matar Dr jibril 

Ibtisam tace wa? Rufamin asiri dan Allah “tare da kallon su Aisha tace Sannunku 

Aisha tace yauwa har an fito daka lecture din? 

Ibtisam tace eh tare da fad’in harya bamu text baki shigo ba 

Aisha tace bar shegen zanje in sameshi nasan Dan bai ganni bane ya bada text din, dan inje ya cini ne dan bura uba 

Hauwa tace Waye? 

Aisha tace Daniel mana 

Hauwa tace tir harda Arne yake cinki? Aiko anyi Asara 

Aisha tace Wlh banga Asara ba, wlh ki gwada bashi ya iya cin mace 

Hauwa tace Allah ya kiyaye ai duk iskanci na, Banyi da wanda ba musulmi ba wlh 

Kubra tace nima kaina ban hulda da Arne duk da ina yare, balle ku hausawa 

Aisha tace kwaji dashi 

ita kam ibtisam mamaki suke bata, yanda suke sakin zance anyhow babu boye boye ko tsoran Allah 

Suko kunyar junansu basayi, kai Allah ya kyauta yasa mu dace 

Nan suka zauna sunata fira

Kubra tace kun San Jamila fashion ta kusa da d’akin mu? 

Hauwa tace eh na santa naji ance wai ta shiga cult dagaske ne? 

Kubra tace gulman da zanyi muku kenan”ashe Kun sani? 

Aisha tace nidai ban sani ba, sai yanzu, “haba sai yasa take shiga cikin manya manyan motoci Ashe ta shiga cult? 

Aikam muna dan gaisawa zanyi taka tsan tsan da ita Wlh, kar taje ta bada jinina 
.dariya suka saki su duka 

Ibtisam kam Abun mamaki yake bata, dama an fad’a mata indai jami’a ne zata ga mutane iri iri, wasu y’an lesbians wasu bin maza, wasu y’an cult Ashe dagaske ne tunda gashi taji suna fad’i, “Aiko dole in dage da addu’a. 

Washe gari su ibtisam karfe 8 suke da lecture kaman jiya, yau dr jibril ne zai shigo musu 

Ibtisam da wuri ta isa tana shiga ita da Aisha shima ya shigo 

Bai wani bata lokaci ba Ya basu text, Bayan sun gama ya k’ara basu assignment tare da fad’in 5mrk ne assignment din, text shima 5 duka 10mrk 

Koda ya gama lecture fita yayi yabar ajin ba tare daya jira wani bayani daka bakin kowa ba 

Aisha kallon ibtisam tayi tare da fad’in naga sai kallonki yake tayi daka na d’aga ido sai inga yana satar kallonki 

Ibtisam tace Taya kika san ni yake kallo? Kenan Indai hakane Kema shi kike kallo 

Aisha ta kwashe da dariya tare da fad’in Toh fah, kodai kishi kikeyi ne? “kawai inna d’ago ne sai inga yana kallonki 

Ibtisam tace uhm Allah ya kyauta tare da tashi zata fita.”salis yace ina zaki yanzu wani kecturer zaizo 10 dai dai gwara ki zauna 

Zama tayi tare da fad’in au ai ban sani ba, nasha ko Mun gama babu Mai shigowa 

Salis yace Tab yau fah muna da lecture 4 ma Akwai lecturer din da zaizo mana 

Ibtisam tace Kai yau akwai zama.. 

Aisha tace ba kadan ba.. 

Suna nan zaune lecturer din ya shigo yayi musu lecture shima ya basu assignment ya fita

Ibtisam tashi tayi ta fita domin kabir ya kirata, tafiya take tana waya ita da Masoyin Nata cikin shauki da kaunar juna, “tun tube taci zata fad’i ji tayi an ri’keta Wanda idonta a lumshe yake gaba d’aya ta sadakar ta fad’i k’asa, “jin an ri’keta yasa ta bud’e ido a hankali ganin wanda ya ri’keta yasa ta tashi daka jikinshi da sauri 

Dr jibril yace ki dinga kallon gabanki 

A hankali cikin jin kunya tace ngd 

Jin maganan Kabir yana hello hello 

Yasa ta maida wayar kunnanta tare dayin gaba, Tana waya 

Shiko Dr jibril gaba yayi abunsa 




BAYAN 3MONTH

ibtisam da Zarah sun fuskanci abubuwa iri iri daka kawayen zamansu, inda suka dinga tura musu ra’ayi akan rayuwar banza, amma basu biye musu ba.

Shiko salis da ibtisam sunyi mugun sabo domin yana taimaka mata Sosai ta fannin karatu, “ganin haka ibtisam yasa ta sake dashi suke shiri Sosai dashi 

Sannan ta gefen Dr jibril yana bama ibtisam shawara Sosai, tare da fad’a mata ta kame kanta daka kawayen banza, sau da yawa inya ganta dasu Aisha saiya kirata akan ta rage hulda dasu, “duk da ta fad’a mishi dakinsu d’aya dasu 


Duk wanda ka gani a skul din zaka gansa yana karatu domin Sun kusa Fara exam, karatu suke Sosai Babu wasa. 

Zarah da ibtisam dasu salis suna zaune a wajan wani bishiya wayar Zarah tayi k’ara d’auka tayi taga Najeeb mamaki ya rufeta ganin number d’inshi na Nigeria, “tace yaushe yazo k’asar? 

D’auka tayi tare da fad’in bros yaushe kazo k’asar? 

Najeeb cikin hausarshi wacce ya dan Fara koya saboda granny yace kwana 3,”sai kuma ya sauya zuwa English yace come out Ina skul d’inku 

K’ara ta saki tare da fad’in kana ta wajan ina? 

Fad’a mata inda yake yayi, “tashi tayi ta Fara tafiya da sauri kai tsaye inda Najeeb ya fad’a mata ta nufa 

Hango wata mota tayi Prado tasan kuma ta gidansu ce, kai tsaye motar ta nufa tare da bud’e motar “k’ara ta saki ganin Mum da Najeeb

Tace mum dama har dake? 

Fitowa Mum tayi suka rungume juna ita da Zarah sannan suka koma cikin motar zarah tace driver yaja su k’ara gaba

Zarah gaida Najeeb tayi tare da fad’in bros Nayi missing din’ka. Ya America?

Najeeb fine kawai yace tare daci gaba da danna wayarshi 

Gab da inda su ibtisam suke zaune ita da salis suka faka motar, “Wanda dai dai lokacin Najeeb ya d’ago kansa Wanda idonshi ya sauka a kansu,”lokaci d’aya ya saki murmushi tare da fad’in wai ita ta shiga university har an fara wayewa tare da fira dako wani namiji 

Bud’e kofar motar din Mum tayi suka fita ita da Zarah. 

Ibtisam hango Mum yasa ta tashi tare da nufan Mum da sauri tayi hugging d’inta tana fad’in sannu da zuwa Mum 

Mum cikin dariya tace yauwa ibtisam, y’an jami’a. ” Ya karatun naku? 

Ibtisam tace lafiya kalau Mum Alhmdlh 

Muje ciki Mum 

Mum tace toh har sunyi gaba ibtisam tace ah Zarah kuje ina zuwa, wayoyina yana wajan salis bari in amso 

Zarah tace ok sukai gaba ita da Mum 

Kai tsaye ibtisam wajan salis ta nufa inda ta ganshi yana k’okarin tashi, “tace Ina zaka ga wayoyina a kusa dakai 

Kallon wayoyin yayi tare da fad’in kai Wlh ban Lura ba, kice dana tafi da wani ya samu

Dariya ta saki Tana fad’in dana shiga uku 

Salis shima dariya yayi tare da fad’in keda sai miki akeyi a free, ai baki da matsala 

Duk wannan abunda suke idon Najeeb na kansu, “tsaki ya danja ya tsana yaga mace tana sakewa dako wani namiji, “jiba yanda take mishi dariya kaman wani d’an uwanta

Ibtisam tace Bari inje sai munyi magana Ltr 

Yace OK tare dayin gaba 

K’aran da wayarta keyi ne yasa ta d’auka ganin Mum ce 

Bayan ta d’auka mum tace ibtisam kice Najeeb yazo mana yana Mota 

Ibtisam kallon motar tayi wanda ita bata san dashi aka zoba, “amsa mum tayi da Toh, jiyo muryan Zarah tayi tana fad’in Mum maza basa shiga hostel d’in mata muje dai waje wani restaurant 

Mum tace ok ibtisam barshi Bari mu fito ma 
.ibtisam dad’i taji, domin bata tunanin zata iya mishi magana, “ita Tama manta da wani Najeeb tunda hannunta ya warke, “amma jin an kira sunansu sai taji wani sabon tsanarshi cikin ranta, domin tunawa da abunda yayi mata

Cikin ranta tace mugu azzalumi sai Allah ya saka min.

Zama tayi a wajan tana jiran su Mum su k’araso 

Bayan su mum sun k’araso ibtisam ta tashi, Mum tace suje suci abinci 

Zarah tace suje wani restaurant a cikin skul din 

Zarah ta nufi mota tace Najeeb ya fito suje 

Kaman bazai fito ba, komai ya tuna kuma saiya fito 

Ibtisam ganin ya fito ta tamke fuska tare da kawar da kanta gefe 

Tafiya suka farayi kai tsaye har cikin restaurant din, matan dake wajan sai kallon Najeeb suke 

NAJEEB daya lura da hakan sai yaji abun ya bashi haushi, tare da fad’in matsalan matan Nigeria kenan, basu da aji 

Ibtisam tace ita bata cin komai, a koshe take.

Mum ta kalli Najeeb tace kaifa Mai zaka ci? 

Yace nothing 

Mum tace cikinku 

Mum fried rice tace a bata, Zarah kuma tuwo tace ita Tana so 

Mum tace a k’aro wani rice takeaway akai ma driver shima 

Ibtisam tace a kawo takai Mai Bayan an kawo abincin domin bata son zama inda Najeeb yake ko kad’an.

Amsan abincin tayi ta fita waje Kai tsaye driver taba abincin da ruwa, inda ya amsa yana mata godiya 

Aisha ce tazo inda ibtisam take tana fad’in ina kika samo wannan Mai k’aton motar haka? Ko Sanata kika samo? 

Ibtisam tace Rufamin asiri dan Allah 

Aisha tace toh na daiga kaman daka motar kika fito 

Ibtisam tace ba daga ita na fito ba sa’ko na bada 

Aisha ta kalli motar sabuwa fil tana she’ki tace ibtisam Waye mai motar plz? 

Dariya Aisha tana ibtisam domin yanda duk ta wani rud’e take tambaya Waye mai motar 

Aisha tace tsarki ya tabbata ga Allah kalla wani guy hadadd’e,  wannan daka ganinshi Balarabe ne 

Waigawa ibtisam tayi taga Najeeb ne wanda suka had’a ido, ta saki tsaki tare da Waigowa 

Ta gabansu yazo ya wuce “Aisha tace kai Kinji kamshi wayyo ya barmu da kamshin turare amma wannan guy din ya had’u….  Shuru tayi tare da sakan baki ganin Najeeb ya shiga motar da ibtisam tace ta bada sa’ko 

Aisha tace dama shine mai motar? 

Ibtisam tace yayan Zarah ne fah 

Aisha tace kina nufin Dan uwan Zarah ne?

Ibtisam tace eh 

Aisha tace kai Wlh sai naje na nemi number d’inshi Dan yayi min wlh 

Ibtisam tace gwara ki kama kanki wlh, domin gudun raini 

Aisha murmushi kawai tayi tare dayin gaba tana fad’in Indai dan uwan Zarah ne sai tasan yanda akayi ta had’asu 

Ibtisam wajan su Mum ta koma, bayan sun kammala cin abinci suka fito Kai tsaye wajan mota suka nufa inda Mum ta shiga tana fad’in zamu kama hanya 

Zarah tace Mum Abuja zaku tafi yanzu? 

Mum tace a’a kaduna zamu shiga gobe zamu koma yanzu yamma tayi ban son tafiyan dare 

Zarah tace Mum plz mu biku gobe sai mu dawo da kammu 

Mum tace OK Toh kuzo muje, “amma baku da lecture ?

Zarah tace nidai banda shi, ban dai sani ba ko ibtisam Nada shi 

Ibtisam tace banda lecture gobe sai 4

Mum tace toh kuzo muje

Zarah tace bari muje mu d’auko kaya, Jan hannun ibtisam tayi sukai ciki basu dad’e ba suka fito 

Najeeb ganin Sun shiga motar da yake shi yana gaba yasa shi fadin Mum Ina zasu kuma? 

Mum tace tare zamu gobe zasu dawo 

Tsaki yaja 

Driver dai tada motar yayi sukai gaba

Gudu driver din yake shararawa a titi, suna tafiya suna fira “Mum tace yanzu saura wata d’aya biki koh? 
.zarah tayi caraf tace eh mum, kuma za’ayi bikin muna hutu wlh ba k’aramin dad’i naji ba 

Mum tace Yadai kamata, naga ma ibtisam duk kin rame, ko karatu ne? 

Ibtisam murmushi kawai tayi 

Da yake da Hausa suke maganan najeeb na sauraransu sai dai wani ya gane wani kuma baya ganewa, Yadai San suna maganan ibtisam zatai aure, “cikin ranshi yace amma kam duk Wanda ya aureta zaiyi fama, yarinyar da kwata kwata nawa take? Shekararta nawa da za’ayi mata aure tun yanzu, “Wanda dai ya aureta zai auri rashin kunya sannan babu abunda zai samu dan banga alaman tana da abunda mata ke dasu ba 

Kai tsaye basu tsaya koh inaba sai hotel 17, inda suka Kama d’aki, guda hud’u, Mum ita d’aya Zarah da ibtisam d’aya sai NAJEEB d’aya driver d’aya.

Kowa shiga d’akinshi yayi danya huta.

NAJEEB Bayan ya shiga abinci yayi order yace a Kawo Mai, “domin yunwa yake ji, and bazai iya cin abincin dasu mum sukaci ba a skul din su Zarah

Washe gari k’arfe 10 duka suka gama shiri domin Kama hanya bayan sunyi breakfast a restaurant din hotel din “shi kam NAJEEB baici komai ba dan bai fito ba, koda ya fito yace kawai su kama hanya basai yaci abinci ba 

Zarah gaida Najeeb tayi ya amsa da fine kawai. ” ganin mum a wajan yasa ibtisam itama gaidashi Mai yakon ya amsa saiya saki tsaki tare dayin gaba “ibtisam  wani irin haushin kanta taji gashi Mum hankalinta baya wajansu dama ta sani bata ko kalleshi ba 


Mum tace ma driver ya kaisu garage susa su zarah a mota Kafin su tafi 

Haka koh akayi Kawo garage suka kaisu, inda akayi ciniki driver ya dawo ya fad’a ma Mum, ciro kud’i tayi taba masu Zarah sannan suka fita Bayan sunyi ma mum Allah kiyaye hanya.. 

Wani dan tasha ne ya shiga gaban ibtisam yana fad’in hjy Ina zaki, daka ta matsa saiya shiga gabanta “tace Malam ba tafiya bane 

Yace y’an mata kina dakyau fah ko zan samu number 

Tsaki taja tana k’okarin matsawa ya k’ara shiga gabanta 

Zarah tace Malam lafiya kuwa? 

Shima driver da yake gaba ya waigo yana kallonsu tare da dawowa 

Wanda a dai dai lokacin NAJEEB ya k’araso wajan wanda yana Mota yana kallon abunda ke faruwa bayan ya k’araso kallon mutumin yayi tare da tambaya lafiya kake shiga gabanta!? 

Mutumin da bajin turanci yake ba yayi gaba 

Najeeb kallon ibtisam yayi itama akaci Sa’a shi take kallo wani irin mugun kallo ya Mata tare da fad’in idiot, kallon Zarah yayi tare da fad’in kuzo muje mu saukeku sai mu wuce 

Zarah da ibtisam bayanshi suka bi 

Mum tace a’a ya kuka dawo? 

Najeeb yace Mum zamu mu saukesu 

Mum tace ai mun koma baya, sai kuma mun k’ara dawowa fah, suje su shiga mota kawai mana, muda ga hanyar mu nan 

Yace Mum plz, muje ban son long magana plz 

Mum shuru tayi ba tare da ta k’ara cewa komai ba 

Najeeb kallon driver yayi tare da fad’in what are you waiting for? 

Driver yace nothing, “tare da tada motar suka k’ara kama hanyar zaria 
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Cikin 45mnt suka k’arasa inda suka saukesu sannan suka Kama hanyar komawa kaduna dansu wuce Abuja 

Zarah ta kalli ibtisam tace Anya Najeeb baya sonki kuwa? 

Ibtisam tace kina da hankali kuwa zarah? 

Zarah tace da hankali na mana, kalla saboda ke fah yasa yace a Kawo Mu har skul, duk saboda abunda wannan mutumin yayi miki 

ibtisam yace badan ni yayi ba, karki k’ara fad’in haka, wlh a yanda dan uwanki ya tsaneni na tabbata ko fyad’e yaga wasu za suyi min bazai hanaba, kawai yayi hakan ne saboda ke 

Zarah tace ni kuma? Naga bani mutumin yayi ma Abu ba, ke akama Abu 

Ibtisam tace plz ya isa, ki daina min wannan maganan karki manta ni matar wani ce bikina saura wata d’aya so plz banso tare tajan tsaki tace ko maza sun k’are sai yayanki gwara in zauna banyi aure ba Tana fad’in haka tayi gaba cikin fushi……. 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button