NOVELSUncategorized

KWARATA 59

???? —— 59
       Uhum wai ashe duk abin nan inna tana cikin garin katsina ita da iyayenta “yan gayu dasu sun wani shige cikin ƙaton gidansu sunayin farin ciki basu da wata damuwa abun su a cikin ɓarkeken gidansu dake cikin anguwar layout , yanzu Inna suna da wannan gidan wace ƙaddara taja mata auren Babana taja mukaje mukayi ta rayuwar cin ƙanzo
da garin kwaki , wannan irin ƙaton gida an ƙawatashi da ciyayi ga ma’aikata an baza ta ko ina , amma dan mugunta suka bar Inna tayi rayuwa a gidan haya ina ma amfanin arziƙin da baka samma wanin ka…..

     Ashiru da kanshi ya shigar min da kayana har cikin ƙaton palon gidan da aka ƙayatashi da wasu irin azababbin kujeru masu kyau da tsada tayils in palon yasha guga duk dare ne sai ɗaukar ido yakeyi tvn bango da sifiku umm amma yanayin palon ya nuna tsohuwa ce ke rayuwa a gidan , wuri Ashiru ya samu ya ajiyemin jakata ya zauna gefen jakar…!

      Nima rakuɓewa nayi ina tunanin Dikko Allah yasa karya tafi yabar katsina tsakanin layout da goruba road ai ba wani tashin hankali bane kawai sai in riƙa zuwa ina yini wurinshi in dawo nan in kwana ! Murmushi nayi cikin yanayin jin kunya na rufe idanuwana tare da kwantar da kaina gefe ina tunanin yadda na kasance a jikin Dikko ,

     Hannunshi mai laushi baya da wata wahala a cikinshi kamar ba’a amfani dashi , ƙara sinsina jikina nayi turaren Dikko a jikina kamar nice na shafashi , murmushi na sakeyi ina ƙara tunano yadda ya kamani dakel a jikinshi ya rungumeni , ajiyar zuciyarshi dana tuno itace tasa naji tsikar jikina ta mimmiƙe gaskiya Dikko yayi ya gama haɗuwa tako ina , ga aji ga natsuwa ga kyau ga wayewa ga gayu sai maganarshi mai sa mutum cikin halin tunani babu dare ba rana…

     Maganar Ashiru ta dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , buɗe idona nayi naga wata dattijuwa mai cikar kyawu da asali kame a saman kujera tasha lulluɓi da gyale mai kyau kanta babu kallabi ta ɗora gyalen a saman kanta ta fiddo kunnuwata waje kodan ta nunawa mutane tasa “yan kunne zinari oho , kila kuma nata ra’ayin ne haka…

     Gaisheta nayi yayin da nakeji dama ahalin Babana ne dan duk cikar arziƙi ko asali na uwa tou wallahi na uba ne a sama dan uba dashi ake tunƙaho shine ado ga kowa ɗa , duk cikar arziƙi irin na mutum da duk wani mulki ko sarauta da yake taƙama dashi da bazar uba yake taƙama , da zaran ka rasa ahalin Baba na gari tou ka zama sai a hankali , cikin sakin fuska ta ansa gaisuwa daga nan na kama bakina nayi shiru sukaci gaba da fira da Ashiru , a cikin firarsu ne naji tana cewa wai inna ta tana Dubai kunji fa…..

    Sun daɗe suna fira da Ashiru kuma har sukayi suka gama ban saka musu baki ba , da Ashiru ya tashi tafiya saida na rakashi har mota ina cewa ya gaishemin da Dikko sosai kuma yace masa idan na kirashi waya ya ɗauka zanyi magana dashi yace insha Allah , saida ya tafi sannan na dawo ciki ,

    Lokacin dana dawo har an shigar da kayana ciki , tsohuwar da nake tunanin itace kakata tayi min jagora zuwa ɗakin da zan zauna tana ta jana da fira cikin soyayya amma ni wallahi banajin maganar kowa saita Dikko domin duk ilahirin hankalina da tunani na yana wurin tunanin shi , abinda yafi tsayamin a rai kawai rungumar da yayi min da kuma fitar sautin ajiyar zuciyarshi…

    Gajiya tayi da surutu ta fita dan dai Sultana bata ita take ba , tana fita na shiga toilet nayi alwallah nazo nayi sallah bayan na gama kawomin abinci akayi naci ina gama cin abinci na soke saman gado na fara kiran wayar mai gida Dikko……!

      Na kirashi bansan so adadi ba amma bai ɗauka ba , tun inayi daga kwance har na tashi zaune haka kira zai shiga yaje ya dawo Dikko baya ɗauka , faɗuwa gabana yayi shikenan ƙarshe kawai zai kashe wayarshi ne daga nan sai ya manta dani , bansan yadda akayi ba kawai naji hawaye na gangaromin daga cikin idanuwana saida nasha kuka har na gode Allah bansan sadda bacci ya ɗaukeni ba na kwanta da tunanin Dikko a zuciyata ,

Yauma horon safe akayi ma Bello yaci ubanshi cikin farashi mai tsada , yayi kuka harya gode Allah , bayan an mishi kashedi akan karya kuskura ya bari auren Sultana ya mutu saida suka haɗa mishi jini da majina sannan suka sallameshi , yana fitowa ya faɗi a wurin da taimakon wasu tsirarun mutane suka ɗauki banza suka wuce dashi asibiti suna zuwa gado aka bashi dan lalubo mishi sauran rayuwa.

      Dikko kuwa sai asuba ya farko kuma da ihun saiya kashe Al ‘ Ameen ya dawo , dakel Momy ta rarrashi Dikko akan ya fita hanyar Al ‘ Ameen cikin gamsuwa yace mata ya barshi bazai mishi komai ba , Momy ta ƙara da cewa dan Allah uban masu gida kar na sake jin wani maganar kisa ya fita daga bakinka kar kuma ka sake ka dakeshi , jinjina kanshi yayi alamar bazaiyi ba ya ƙare ajiye kan da murmushi ,

Momy da kanta ta rakashi ɗakinshi , acan yayi wanka ya canja kaya ya fita masallaci , daga masallaci gidanshi ya wuce ko Jiddah bata san ya shigo ba kai tsaye ɗakinshi ya wuce dan har yanzu gajiya ke murzar mishi jiki .

     Tunda nayi sallah asuba naci gaba da kiran wayar Dikko amma sam bai ɗauka ba , ganin baya ɗauka na haƙura na kwanta bacci tunda na kwanta kamar jaka ko motsowa banyi ba sai bayan azahar , dan nima ina tattare da nau’en gajiya , akwai gajiyan gudu da jifar dasu Al ‘ Ameen suka min , dukan da Dikko yayi min sai gajiyan hawa doki…

      Ina tashi da wayata na fara na duba ko Dikko ya kira babu miss call inshi , saida na sake kiranshi bai ɗauka ba ni kuma nayi alƙawari daga nan har a busa ƙaho idan ba shine ya kira ba bazan sake kiranshi ba.

      Yinin ranar yau dai har dare Dikko bai kirani ba kuma nima na basar da lamarinshi , da daddare kuma kaka ta haɗani da gyatima mukayi waya wai nace Inna ni zata dake ma kashedi kar na sake ce mata Inna , nace gwaggo zance miki ko me ? Dariya tayi tare da canja maganar da wata fira ta daban , mun daɗe sosai muna waya da ita cikin farin ciki daga baya mukayi sallama na maida ma kaka wayarta danni dama ban wani san wannan kakar ba gaskiya sai a hoto nake ganinta dan Babana baya bari ina zuwa ko ina kuma duk inda zanje tare muke tafiya dan abinda na fahimta a can baya akwai “yar tsama data faru tsakanin Inna da iyayenta da kuma Babana ɗan uwan Inna ɗaya kawai na sani shima saboda yana mana hidima ne lokacin muna tare da Inna a gidan Baba !

Bayan nayi sallah isha’e ina shirin kwanciya mai aikin Kaka ta shigo wai nayi baƙo a waje , cikin farin ciki na tashi na ƙara gyarawa na fesa turare gyale na ɗauka da sauri na fita ,

     Ina fitowa motar Yazeed na gani parke a wurin da aka tanada dan ajiye motoci , cikin farin ciki na isa wurin dan a tunani na shida Dikko ne kuma jiya da zan taho Yazeed yace min zaizo jibi , kenan sai gobe ne ranar da zaizo , cike da farin ciki na isa jikin motar ina zuwa Yazeed ya buɗe motar ya fiddo ƙafarshi ɗaya waje yana kallona cikin yanayin farin ciki , 

    Gaishe shi nayi ina leƙa cikin motar ko zanga Dikko , murmushi yayi irin na wayayyin maza yace An mata ni bada DK nazo , me yasa baku zo tare ba ne ? Nima bansan zanzo ba kawai hanya ya kawoni nace bara in biyo miki da mamaki kafin zanzo gobe , a yatsine nace kazo yau gobe ka dawo ? Yace Eyy mana jibi ma zanzo kullum zanyi ta zuwa har sai bana nan ne kaɗai bazan zo ba…..!

    Kallon rainin hankali nayi mishi nace to meye nasabar hakan ? Kula mana , meye halaƙar ka ta san kula dani ? Neman kusanci ! Ta wane dalili kusanci zai ƙullu tsakanin namiji da mace ? Abokanta ka , ai babu abota tsakanin mace da namiji , murmushi yayi tare kauda maganar ta hanyar cewa tou ya kike ya gajiyar kuka da hawan doki ? Ya ƙarasa maganar yanamin kallon ƙarƙashin ido….

    Lafiya qalau na faɗa a ƙagare , fitowa yayi daga cikin motar ya jera dani , ja baya nayi sannan na juya mishi baya , murmushi yayi tare da cewa haba An mata miye kikeyi haka ? Babu kyau kinsan yana daga cikin ɗabi’u masu kyau martaba baƙo irin wannan tarbar zakimin haba An mata yadda ya ƙarasa faɗar An matar sai naji kamar maganar Dikko , ba tare dana juyo ba nace yi haƙuri bacci nakeji ne ,

     Iyya yi haƙuri na tuna kinayin bacci da wuri to zan tafi zanzo goben fa , Allah ya kaimu ina faɗin haka nayi gaba abuna , da gudu na isa ɗakina cikin ɓacin rai ina shiga wayata na duba dan ganin ko Dikko ya kirani , ya kuwa kira amma miss call ɗaya ne , shine duk kiran da nayi masa bai ɗauka ba ni zaima wannan miss call ɗin ɗaya dan ya maidani bansan abinda nakeyi ba ? Tsoki nayi tare da kiran wayarshi dan da bai kirani ba nayi alƙawari bazan sake nemanshi har abadan abada.

      Saida kiran ya kusa ƙarewa ya ɗauka , cikin disashshiyar murya kamar wanda mura ya kama yace An matana ya kike ? Ban ansa ba nace me ya sameka muryarka wata iri , gyaran murya yayi irin dandai maganar ta tafi dai² yace babu daɗi ko ? Murmushi nayi tare da kwanciya saman gado nace da daɗi mana , yace wallahi muryar shaƙewa tayi bansan abinda yasa ba kinga kuma ni bana huɗɗa da abu mai sanyi da sai ince mura ya kamani , sannu nace masa yace yawwa yaci gaba da cewa wallahi wayar a mota na barshi sai yanzu dana fita naga tulin miss calls kuma ke na fara kira An mata… Yayi maganar a sakace,

Murmushi nayi cikin yanayin jin daɗin yadda yayi maganar nace tou amma yanzu ka fasa tafiya ko ? Yace zanyi tafi amma sai wani satin banajin daɗi ne duk jikina ciwo yakemin , ni kuma nace ciwon tunani nakeyi , murmushi Dikko yayi tare da cewa Allah ya baki lafiya saida safe… Yana faɗin haka ya tsinke kiran,

     Cikin jin haushi na sake kiranshi amma yaƙi ɗauka , ni bansan abinda yasa yakemin irin wannan abun ba , ko wurina yazo baya so ya daɗe , idan inayin waya dashi a ƙagare yake ya barni anya Dikko zai soni kamar yadda nake sansa ……?

      Murmushi yayi bayan ya tsinke kiran yace An mata kenan itafa nan a wayan ta so take ta ganni amma bazata iya faɗa inzo ba sai ta fake wai tana ciwon tunani tou ai sai kisha magani ko kin samu sauƙi…..

      Daga G R A kai tsaye tsohuwar anguwar su Sultana ya taho inda gidan da yake kiwon dawakai yake , tunda ya shigo anguwar ya ganta cike da taron jama’a maza da mata kuma duk wadda ka gani kasan cikakken ɗan iska ne maza “yan daudu mata karuwai duk wacce ta ansa sunanta tanaji ita wata shegiya ce a cikin iskanci ta hallara a wurin gaba ɗaya anguwar ta karaɗe da kiɗa ko wane ɗan iska da iyayenshi suka ce jeka ka gani su Amisty sun hallarar dashi a wurin , 

       Da gudun bala’e ya shiga cikin santar saboda tsabar gudu motarshi har wani tsalle takeyi , kamar fari haka mutane suka riƙa tashi da gudu dan keɓe rayuwarsu daga faɗawa mummunar rayuwa , a ƙofar gida yayi parking ya fita ya shiga ciki rai a haɗe , shigarshi hayani ta fara tashi kowa dai da abinda yake faɗa akanshi ,

      Bayan ya gama abinda yakeyi zai fito Umar ya biyo bayanshi yake cewa mai gida yau kaga anguwar namu cike ? Banza Dikko yayi dashi bai bashi ansa ba shi kuma yaci gaba da cewa wata karuwa ce take ajo na cika shekaru biyu da fara barikinta sai kuma shagalin samun “yan cin kai na zaman kanta watanni bakwai , Dikko dai baiyi magana ba yana fitowa ya shiga motarshi ya fice da ribos har ƙarshen santar yana kaiwa titi ya juya sitiyarin motar shi ya wuce inda suke majalisarsu , Hafsa kuma tabi bayanshi ,

     Umar kuma mamaki yakeyi ko akwai abinda yake damun Dikko duk dai haka yake amma kamar wani abu ya taɓashi , ko wani abu ya ɓata mishi rai idan an gaishe shi zaice yawwa , ko lfy ko da kyau ko yayi amma yau duk wanda ya gaishe a gidan nan bai ansa gaisuwar kowa ba kuma baiyi magana da kowa ba har ya shigo ya fita…

       Har yanzu ban daina kiran wayar Dikko ba , duk kiran daya shigo wayarshi na Sultana yana kallo saida yazo goruba gidanshi sannan ya ɗauki wayar cikin tsananin ɓacin rai da hayani yace wai me ye ne…………? Ni bana san maita sai kirana kikeyi kin dameni bansan masifa da kwakwa da Allah mayya kawai , cikin tashin hankali na tashi zaune tare da sake kallon lambar wani abu naji yazo ya tokare min a zuciya nace Dikko nice mayya….? Eyyy kece nace mayya ko ba mayyar bace , nima kamar an sakani cikin ɓacin rai nace kaine maye marar tunani wanda baka san ina duniya ya nufa ba , kamar ƙaramin yaro haka Dikko ya biyemin mukai ta zage² duk abinda yace min saina rama ,

Daga ƙarshe ya zageni tass da turanci , cikin kuka nace Dikko An mata ce fa , tsoki yayi ya kashe wayarshi , wayyo Allahna meke faruwa haka ? Yanzu na gama waya da Dikko lafiya qalau sai kuma in sake kiranshi ya zageni me yayi zafi haka don Allah ? Wayyo Allahna , da sauri na kalli agogo 9:24pm zuciyata kamar zata tsage saboda tashin hankali idona kuwa banda aman hawaye babu abinda yakeyi , da gudu na fito har bakin get , wanda nake tunanin shine driver naje gabanshi a rikice na fara magana cikin rawar baki nace da Allah ka kaini goruba road taimakeni don girman Allah na ƙarasa maganar ina jan hannunshi….

Lafiya ya tambaye ni ? Babu lafiya muje don Allah zan baka kuɗi idan muka dawo yanzu zamu je mu dawo yi sauri don Allah na ƙarasa maganar ina goge hawaye idona , muje ya faɗa yayi gaba nabi bayanshi ,

      Ko a mota a gaba na kasance ina ce masa yayi sauri , sauri ׳ malam driver , gudu yakeyi sosai amma kayi sauri kawai nake cewa har muka isa goruba road , a harabar gidan na haɗu da Hafsa Dikko ya bata kashin bala’e ana ta riƙonshi ya haukace gaba ɗaya , cikin tausawa na kalli “yar uwata dake duƙe tana kuka Dikko sai ruwan rashin mutunci yakeyi ana bashi haƙuri kamar ana ƙara tunzurashi yana sai ya tattaka ta ,

Wurin Hafsa naje na kamata na miƙar da ita ina bata haƙuri tare da tambayarta meya faru ? Kallona tayi amma bata ce wani abu ba sai kuka takeyi , sakinta nayi zanyi wurin Dikko aka tareni cike da iskanci yake cewa kizo ku barta tazo yayi maganar yana kirawoni da kanshi , turesu nayi na tunkari Dikko kai tsaye ina isa ya yankamin wani irin mari saida na wurwura kamar ranfa na dawo gaban Hafsa ko gabana bana gani sai duhu , kafin in dawo hayyacina na sake komawa inda nakejin sautin muryar Dikko dan kawai ji nake gara in mutu da masifar da zan fuskanta a gaba dan rabuwa ta da Dikko a halin yanzu na dangana abun kawai da mutuwa ta ,

      Riƙeni akayi cikin ihu nace ku sakeni saiya kasheni , ka kasheni Dikko kasheni bana so ka barni da raina gani na matsa gabanshi ina kuka , da ƙafarshi yayi min wani irin halbi saida aka ɗagani sama sannan na faɗo ƙasa ruf da ciki  ,  da sauri na sake tashi cikin kuka na sake tafiya wurin Dikko wani irin tsalle yayi ya ɗaga hannunshi sama rigarshi ta ɗage har kana gani cibiyarshi yace idan taurin kaine ɗabi’arki nine kangara zai kaimin duka saman kai Yazeed ya riƙeshi birkicewa Dikko yayi yana saina kasheta , andaiyi tashin hankali sosai munyi zage² da Dikko abun dai babu daɗi dakel Yazeed ya sani mota muka dawo gida can na baro Hafsa kuma bansan abinda ya haɗata da Dikko ba kuma babu wanda yasan abinda ya jawoma Dikko wannan haukar ba,

      Sultana tana tafiya Dikko yace zancen banza zance wofi yau duk wani mai tsohon laifi a wurina an famomin ciwon dana daɗe ina raino a cikin zuciyata saura waccan ɗayan ɗan iska yau duk wanda ya hawoni saina lalata mishi rayuwa , yana faɗin haka ya shiga mota ya nufi gidansu ,

      Yau duk wanda yaga Dikko lafewa yakeyi saboda tsoro , wurin mahaifiyar shi ya fara shiga itama da yanayin tsorata ta kalli Dikko tace kai lafiya kuma ? Banda lafiya kuma yau duk wanda yayi gigin shigomin rayuwa ko waye saina mishi babu daɗi ba ruwanki yau saina kashe Al ‘ Ameen a gidan nan kar wani yayi gigin taɓani ko zuwa kusa dani idan ba haka ba yau zan tara majiyyata da yawa a gidan nan , Dikko badai zaka barni na zauna lafiya ba ko ? Cikin hayani yace da ko wane daƙiƙi na rayuwata shi nake jira yau bana iya bacci saina kasheshi yana faɗin haka yayi waje…..

       A tsorace Momy tabi bayan Dikko amma lokacin data fito ko sahun ƙafarshi babu tuni ya ɓace , tsayuwa tayi tana tunanin mafita taji gaba ɗaya gidan ya gauraye da hayani da sauri ta nufi inda take jiyo hananiyar tana zuwa Dikko ta gani shaƙe da wuyan Al ‘ Ameen ya riƙeshi duk wanda ya matso wurinshi halbi ɗaya yake mishi sai mutum yayi sama ya dawo ƙasa somamme…

       Ƙatti majiya ƙarfi sunfi nawa amma sun zagaye Dikko an kasa samun wani da zai sake matsawa kusa dashi , cikin ɓacin rai Dikko yace har so nawa zan faɗa bana san wani ya sake zuwa kusa dani idan akwai mai sha’awar jinya ko mutuwa yazo….. Ya faɗi maganar a dai² lokacin daya ɗaga Al ‘ Ameen sama ya dakashi da ƙasa , Momy tace ku riƙe minshi mana , wani yabi ta bayanshi dan ya kamashi amma yana isa Dikko ya halbeshi ta baya shima saida yayi sama ya dawo some , cikin ɓacin rai yace har sau nawa zan faɗa bana so azo kusa dani kuci gaba da shigowa duk saina ƙarar daku a dai² lokacin da yayi wani irin tsalle ya dira akan ruwan cikin Al ‘ Ameen dako motsi bayayi yace zaka fita harkata ne ko zakaci gaba da shiga ? Kun hanani na zauna lafiya yayi maganar yana ɗaukar Al ‘ Ameen kamar ya ɗauki kaza yayi jifa dashi jikin wani ƙarfen fitila , yanayin jifa dashi gaba ɗaya suka rufa kanshi dan su riƙe shi , wani irin ihu yayi kai…… Wayyo wai…… Yaci gaba da dukansu babu ji babu gani duk wanda ya hawo saida Dikko ya kwantar dashi yau kam saida ya tsamama ma duk wanda ya hawo layin shi jiki ya kama gabanshi…..

     Goruba road ya koma a daren yana neman wayarshi , kowa ce masa yake baya kyautawa abinda yake yi , baima kowa magana ba yace ina wayarshi , cikin girmamawa Ashiru yace gata mai gida , cikin ɓacin rai yace kiramin An mata , kallonshi Yazeed yayi yace “Yar matan daka wulaƙanta kake tunanin zaka kirata ta ɗauka , ai saboda wannan lalurar yasa na sakata a tarko , Yazeed yace dan kayi ta zalincin ta kana ɗaukar alhakinta ka ɓata rai kayi ta rashin mutunci warware hannun rigarshi yakeyi yana cewa dole sai tasan fushina kuma ta riƙa kiyayeshi na faɗa mata idan nayi fushi bani ne ba , ɓatamin rai tayi data kama hanya ta taho kuma nace bana so tana yawo ita sarkin soyayya dan nace mata mayya taji haushi tayimin zagin rashin mutinci.

      Wani ne yace to kai me yasa kace mata mayyar ne ? Raina ne ya ɓaci a dai² lokacin da fushi ya hau kaina ita kuma taita kirana dana ɗauka na sauke fushin a kanta , tunda har zan zama mijinta dole ta koyi ansar laifin da ba nata ba , domin da zaran nayi fushi tofa ko kaina bana saurara…..

    Tambayar shi suka sakeyi meya ɓata mishi rai haka da yawa har ya daki Sultana da yake iƙirarin ko wani ya taɓata saiya rama mata , cike da damuwa Dikko yace karuwai ne na gani ƙanan yara wanda shekarunsu bai dace da karuwanci ba “yan kuci²n yara wai su nan har sun giga sun tafasa har sun ƙone sun bushe fitilar idonsu wai sunsan daɗin maza , sun gagari iyayensu abin ne ya tadamin hankali , bansan masifar dake damun mutanen wannan zamani ba , wallahi wata “yar ƙaramar yarinya na gani sai kuma yayi shiru hawaye ya cika mishi ido a dai² lokancin da Ashiru ya miƙo mishi waya Sultana ta ɗauka , An mata miye kike kuka kina tunanin zan iya fushi dake ? Cikin kuka nace shine ka zageni kace min mayya kuma ka dakeni  , haba An mata ki riƙa min uzuri don Allah ai kinsa bada gangan na faɗa ba fushi ne , tou nidai kazo in ganka , kallon agogo yayi yace dare yayi ki bari da safe zanzo , nidai kazo yanzu , cikin sansanyar muryarshi yace gani nan zuwa….

      Gaba ɗaya kowa yace sai yaje yaga yadda za’a ƙare , yayin da wani yake cewa Allah yasa itama tasa ayi maka shegen duka , murmushi Dikko yayi a dai² lokacin da suka fito daga palon yace An mata bata iya fushi dani har abadan duniya domin wannan lalurar ne yasa na sanya mata maitata a zuciyarta , babban muradin ta a yanzu na aureta kaga idan na aureta ta zama tawa , idan har na auri An mata ba maganar yaji dan babu inda zata iya tafiya tabar Dikko muyi faɗa mu shirya danma tana da ƙananan shekaru har yanzu ta kasa kullema 20 , motoci suka shiga suka nufi gidansu Sultana…

      11:52pm a gidan Kaka tayi ma su Dikko kuma duka ciki suka shigo da motocinsu , ba waya yayimin yazo ba kukan motarshi kawai naji nayo waje , saida na gaishe da duk abokanshi na shiga mota yana baya zaune ina shiga Ashiru ya fita , fashewa nayi da kuka na rungume Dikko cikin kuka nace shine kacemin mayya ? Yace ai mayyar ce ko ke ba mayyar Dikko bace ba , nima ai mayenki ne kuma ba kin rama ba , to ai har zagina kayi da turanci , murmushi Dikko yayi da gefen bakinshi yace ni wallahi ba zaginki nayi ba , iyakar mayya dana ce ban wani ɓoye da wani harshe na aibataki ba , gaki kin fara zama jajirtacciya soyayyata ta hana ki gano matsalata , haka zakiyi ta haƙuri dani An mata har Allah ya bani lafiya kinji , ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi. Nace to me kacemin da turanci ? Saida yayi dariya yace cewa nayi “yar ƙaramar yarinya kin hanani zaman lafiya , duk wannan doguwar maganar a “yar wannan kalmar ya tsaya ? Ajiyar zuciya ya sauke baiyi magana ba ,

    Shashshekar kuka nayi tare da cewa tou me nayi maka haka da ciwo don Allah , riƙeni yayi da hannunshi na haggu har yanzu ina kwance a jikinshi shi kuma ya kwantar da fuskarshi a saman kaina ya fara magana cikin sanyinshi , yace An mata taron karuwai na gani abun ya gigitani wata “yar ƙaramar yarinya ba zata wuce shekarunki ba kinsan abinda na gani anayi da ita , shiru nayi ba tare dana bashi amsa ba , cikin kuka Dikko yace to maza ke layi akan yarinyar yadda kika san ana ɗaukar mutum a abun hawa a anshi kuɗi haka maza ke hawan yarinyar suna sauka suna bata kuɗi , ɗimuwar rayuwa ta sameni duk taron mutanen da aka tara An mata batajin kunya wai ta keɓe gefe ɗaya tayi ma maza masauki a jikinta , mata basu san illar namiji ba duk mayatar mace da masifar maitar namiji bata iya kashe namiji 2 a bariki , namiji kuwa sai ya kashe mace sama da goma yana nan zamzam , rayuwar mace taƙaitacciya ce amma rashin tunani ya hana su gane haka tunda na shiga anguwar da wanda ke gefe na da wanda ke gabana da duk wanda yake bayana zan iya baki labari , kallo ɗaya zanma abu na gama dashi yanayin mutum na kalla zan iya faɗa miki komai akanshi,

      Ni mamaki ma nayi duk wa’an nan “yan iska ina ita wacce ta tarasu ta samo su ? Wai ke kinga taron ? Ya ubangiji ka tsare mana imaninmu ka shirya bayinka daga faɗawa tarkon zina , ina cikin jimami ke kuma kin dameni da kira a lokaci ni kuma ina so na samu natsuwa na kiraki ke kuma kin gagara daina kirana ne ina cikin tashi hankali bana so ban ɗauka kiranki ba kuma kiji babu daɗi ina magana dake raina ya ɓaci nayi ta faɗar maganganu babu daɗi , ita kuma wannan yarinya ta wani kama hanya ta biyoni bayan itama na ganta maza sai rumgumarta suke ,

Ai banma san na cire belt na zaneta ba ina cikin wani fushin ke kuma kika zo , ƙara riƙeni yayi sosai a jikinshi hawayenshi ya ɗigo a saman wuyana ya sassauta murya yace dan Allah An mata idan kika kirani ban ɗauka ba ki daina zuwa wurina kuma ki daina kiyi ta kirana idan kin kira sau ɗaya ban ɗauka ba kinji ko ? Nace tou haƙuri ya bani saida ya tabbatar na samu natsuwa ya gogemin hawayen fuskarta nima ya umarceni da in goge mishi nashi da hannushi yayi min nuni goge mishi nayi tare da shafa gemunshi najashi dan yana burgeni , murmushi yayi mai kyau tare da gogamin gemun a fuskata , a kasanlance na sake komawa jikinshi na kwanta , dariya yayi cewa jeki zanzo gobe insha Allah , dakel na iya fita daga cikin motar na wuce ciki kamar wacce bata da lakka a jikinta , cike da tausayin Sultana su Dikko suka bar gidan….

     Bayan Dikko ya gama ci musu uwa motarshi ya hau yai tafiyarshi , haka akayi ta ibar mutane ana tafiya dasu asibiti , Momy bata faɗawa Dady ba amma dan sharrin mata aka samu wacce ta sulalewa Dady waya ta fesa mishi komai , shima daya tashi bai kira Momy ba ya kira Dikko bayan sun gaisa yace Babana duk abinda kakeyi ka barshi zuwa jibi ka sameni , wato kaga bana nan shine kake duk abinda kaga dama ko ? Na taho ganin likita ban dai tsira ba saidai ka kasheni hankalin ka zai kwanta ? To ka taho ka sameni zuwa jibi na baka yana faɗin haka ya kashe wayarshi.

      Tunda na shigo ɗakina nake tunanin wannan wace yarinya ce ? Bansan mutanen su Hafsa ba amma naji a raina inasan sanin yarinyar da Dikko yayi ma kuka saboda tausayin ta , kuma inasan nasan dalilinta na shiga karuwanci , Dikko yana da tausayi amma baida mutunci ko kaɗan da wannan tausayin nashi Allah ya kamamin zuciyarshi akan abinda yayi min a baya , tabbas ina san sanin ya rayuwarsu Amisty take yanzu , ina san sanin a wane hali Ummu Affan take matar auren da nayi silar zuwanta bariki , ina san sanin abinda yasa matar Baban Babana ta korasu daga gidan mahaifinsu , ina san sanin labarin Aunty Suwaiba , ina san karatu kuma ina san Dikko sannan ina san sanin abinda ya kashe matarshi ko da gaske tsafetan yayi ?…. Kuma gaba ɗaya sai nayi babu wanda zan fasa a ciki ! 

    Sai kuma rashin lafiyar Dikko da abinda yake sashi cusa ɓacin rai a cikin farin ciki wani , tabbas saiya faɗamin meya jawo mishi wannan lalurar da fushin wani yake shafar wani…

     Asibiti mai kyau aka kai su Al ‘ Ameen duk wanda Dikko ya daka babu wanda baima rauni ba , ya gota wasu ya karya wasu Al ‘ Ameen duk yafi kowa shan wahala dan har safiyar yau bai dawo ba , amma likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu wurin ceto rayuwarshi…

        Duk azabar dake damun Bello bata barshi ya zauna a asibiti ba guduwa yayi domin ya kudiri ganin bayan Sultana , dan haka yabar asibiti ya koma gida ,

     Da sauri ya fito daga toilet yasha wanka a gaggauce ya saka kayanshi bayan ya shafa mai ya wanke jikinshi da ruwan turaruka dan yanzu yake so ya wuce akwai abinda zaiyi Abuja kafin yabar nigeria , cike da kissa ta shigo ɗauke da kofi ta haɗoma Dikko tea data barbaɗeshi da garin maganin da Al ‘ Ameen ya kawo mata , cike da kwarkwarewa tace my excellency kasha wannan kafin ka tafi , da sauri ya ansa ya ajiye a saman madubi yana ɗaura agogo bayan ya gama ya saka takalminshi wurin ɗaukar wayarshi kofin ya biyoshi ya faɗo ƙasa ya watse , cikin kyarmar jiki Jiddah ta dafa goshi tace bara in kawo maka wani , kallo ɗaya Dikko yayi mata yai murmushi yace haka nake ni da zaran gishiri yayi yawa abunsha ko abinci ɓarewa yakeyi haka rayuwata take tunda safe kina so ki ɗuramin masifa babu gaira babu dalili , yana faɗin haka yayi gaba ,

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());      Ko wurin Sultana bai biya ba kuma bai kirata ba haka kuma baije gidansu ba danyi ma Momy sallama suka kama hanya daga shi sai Ashiru…

     Bayan la’asar Yazeed yazo ciki muka shiga suka gaisa da Kaka aka kawo mishi ɗan abun taɓawa bai taɓa komai ba muka shiga firar duniya , ya daɗe sai gab magrib ya tafi bayan na faɗa mishi zanje daura gobe idan Allah ya kaimu yace zaizo ya akaini , yayi hauka da kuɗi wa duk wani ma’aikaci dake gidan itama Kaka ya bata kuɗi masu yawan gaske , ni kuma wasu irin jikkuna yasa aka shigo min dasu masu ɗauke da kaya iri daban ² kuma nima ya bani kuɗi gaba ɗaya ma’aikatan gidan maganar Yazeed sukeyi da irin kuɗin daya bada , tou wai me hakan yake nufi……..?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button