KWARATA 53

*KWARATA*
???? —— 53
*_ƊAN MACE…! Sabon abinci yafi ɗumame daɗi ???? na zaune makahon duniya , wasan kokowa bana gurgu bane hanzarta ki nemi naki karki sake ki bari a baki labari , tsohon hannu ce tuni ta shahara wannan marubiciya kuwa itace HAWWA MUH’D USMAN {{ real smasher }} ina tayaki murnar fara sabon littafinki ubangiji yasa yadda kika fara lafiya ki gama lafiya ,
Am3n…_*
Cikin tashin hankali Ashiru ya fara kiran wayar Momy dan ya sanar da ita halin da mai gidanshi yake ciki , koda ya faɗa mata cewa tayi ko nazo ba abinda zan mishi dan maganinshi yana hannunshi ka nema ka zuba mishi a bakinshi ,
Kallon Dikko yayi yace Hajiya wannan ba irin waccan ciwon bane ba , tsoki tayi tare da kashe wayarta tana masifa cewa ni mutuwarshi bata wani hanani nayi rayuwata dan wanda ya mutu shi jin daɗi ya ƙare mawa danni a halin yanzu banda wani abinda ya isa ya tashi hankali na , mijina kawai zai kwanta ya mutu in tashi hankali ba Dikko ba ,
Ƙanwar shi daya zane jiya tace Momy miye ? Cike da masifa tace Dikko ne kinsan shi idan bai ɓatawa mutane rai ba hankalinshi baya kwanciya ni yanzu bazai sake tayarmin da hankali ba saidai ya tada ma ubanshi danni na gaji da iskanci shi , tunda na haifi Dikko duniya ya hanani in zauna lafiya dan yaga bana so ya shiga damuwa shi yasa duk hanyar da yasan zaibi ya tadamin hankali yasanta ,
Meya sameshi yanzu kuma Momy ? Ta tambayi mahaifiyarta cikin damuwa , tashi Momy tayi daga palon tana cewa koma miya sameshi cansu ta dama ba abinda ya dameni , ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah duk dukan da Dikko yayi mata jiya ta manta dashi ta ɗauki wayarta ta fara kiranshi , Ashiru ya ɗauka tace ina Yaya ? Ashiru yace baida lafiya ,
Bashi waya mana , cikin damuwa yace ai baya iya magana , kamar ya baya iya magana ne ? Tayi maganar cikin tsawa , shiru Ashiru yayi tare da kashe wayar , wayyo Yaya…… Momy Yaya fa baya magana kuma an faɗa miki zakice ba ruwanki ? Daga ciki Momy tace ba ruwan nawa ke mai ruwa sai kije kiyi.
Cike da tausayin ɗan uwanta ta fara kiran wayar Dady amma bai ɗauka ba ta kirashi yakai ×3 baya ɗauka kawai ta tura mishi text Yaya bashi lafiya !
Ashiru kuwa ya ɗako magani ya zuba² amma kamar ana zubashi a ƙasa Dikko ya ɗauke gaba ɗaya sai hawaye dake gangarowa daga gefen idonshi , cike da tausayi Ashiru yabi mai gidanshi da kallo yana tunanin tou wane irin sirrin ne yakeyi da Sultana da yace Allah kaɗai yasan tsakaninsu yace babu wanda yasan abinda ke tsakaninsu daga shi sai ita sai Allah , wannan wane irin sirri ne mai ƙarfi haka……?
A wannan hali Dady yazo ya samu Dikko , fuskarshi ɗauke da damuwa yace ma Ashiru ya koma palo , fita Ashirun yayi Dady yabi Dikko da kallo bayan wani lokaci ya saka hannunshi a aljihu ya ɗauko wani garin magani ya shaƙa mishi a hanci tari Dikko yai tayi yana atishawa , saida ya ɗauki wani lokaci yana tari da atishawa sannan ya dawo dai².
Cikin natsuwa Dady ya kalleshi yace Babana kana neman dai ka kasheni ko ? Ka hanani in zauna lafiya kullum jini na a saman akaifa ko wadataccen bacci bana samu kullum zuciyata a takure take banda walwala bare kwanciyar hankali wannan fitinar daka tsiro da ita ba kanka kake wahalarwa da ba , ni kake ba wahala duk duniya baka da jigon daya wuceni idan har ka bari wani abu ya sameni ko na mutu taka ta ƙare ,
Cike da ladabi yace kayi haƙuri na bari , Dady yace kai zan ba haƙuri , Dikko yace insha Allah bazan sake ba , Dady yace da ka taimaki rayuwata , saida ya tabbatar Dikko ya dawo hayyacin shi sosai ya tafi tare da jaddada mishi ya daina fushi da tunani tunda yasan baida cikakiyar lafiya , kuma yaje gida da daddare yana nemanshi , da kanshi yayi ma Dady rakiya har wurin mota saida ya tafi sannan ya dawo palo wurin Ashiru ya kwanta.
Ni kuma ɗaki na koma na cire wayata daga jirgi na fara kiran wayar Dikko , duk kiran da nake mishi yana gani yaƙi ɗauka dan yayi alƙawari cewa sai nazo da ƙafafuwana na sameshi idan dai ya furta zaiyi ko zai mutu saiya yayi , tun ina kiranshi yana basarwa ƙarshe sai ya riƙa rejecting , nima na daskare naci gaba da kiranshi bayan wani lokaci ma kashe wayarshi yayi gaba ɗaya ,
Murmushi nayi maicin rai a bayyane nace ni zaka wulaƙanta ina kiranka ka kashe min waya nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba na ƙarasa maganar tare da maida wayata a jirgi.
Ranshi a ɓace ya kalli Ashiru yace zanyi tafiya zakaje ? Dariyar jin daɗi yayi tare da cewa mai gida zanje mana amma kace baza ka sake zuwa ko ina ba sai Sultana tazo , hmmm manta da An mata Dikko ya bashi ansa…
Saida na ƙara yin kuka sosai sannan na sake cire wayata daga jirgi na ƙara kiran Dikko , har yanzu wayar a kashe take ci gaba nayi da kira har matar da ake jiran zuwanta ta iso amma Yaya DK bai buɗa waya ba , yayi fushi dani yayi tafiyarshi London ya manta dani ,
Sultana ….! Aka kira suna na daga palo da sauri na tashi na fita ba tare dana ansa kiran ba , gaishe da matar nayi bayan na samu wuri na zauna , ansawa tayi cikin sakin fuska tace sannu baiwar Allah , murmushi nayi mai ciwo dan yanzu duk duniya banda damuwar da tafi rashin Dikko a tare dani…
Auntyn da tazo dani tace Yaya kinga kwalbar nan kallo ɗaya tama kwalbar ta kauda idonta tare da neman tsari daga azaluman mutane a wurin ubangiji , abin babu kyan gani gwanin tashin zuciya da tashin hankali , Auntyn da tazo dani tace tare da ita za’a tafi ne ? Yayar ta tace a , a cewa yayi kawai na anso kwalbar na kai mishi , Aunty tace gata nan , kwalbar matar ta ɗauka tare da cewa saina dawo zuwa jibin insha Allah , godiya Aunty tayi sosai wa “yar uwar ta , ita kuma ta tafi tana mai addu’a ubangiji ya yanke wahala.
A daddafe nayi kwana ukku , ga ciwon mutuwar mahaifina dake nuƙurƙusar min zuciya , ga maraicin Dikko dake damuna gashi banda abokin fira kuma gidan ba’a fita gashi ni ban saba da Auntyn da tazo dani ba , abubuwa dai duk sun dameni na rasa inda zan saka raina naji sanyi , duk alƙawarin da nayi bazan sake kiran Dikko ba na kasa kullum saina kirashi kuma har yanzu wayarshi ya rufeta.
Al’ Ameen da yakai Jiddah ƙin dawowa yayi wai sai ranar da zata dawo zasu taho tare , haɗuwa sukayi sukaci gaba da gulmar Sultana yayin da Al ‘ Ameen ke cewa ai Sultana asiri tayi ma mai gida ta gama dashi danshi tunda yake duniya ma bai taɓa ganin mai gida yana shiga sabgar mace ba sai akan yarinyar nan , tayi mishi asiri na gani kasheni , idan dai kina san zaman lafiya ki miƙe tsaye ki fitsare ƙafafuwanki.
Jiddah tace aini bansan ta ina zan fara ba , Al ‘ Ameen yace ina da malami a zaria zan kaiki amma karki fara neman mai gida dan ɓannar kuɗinki zakiyi saboda yana da addu’a sosai , banda toshewar basira irin na Jiddah yanzun nan Al ‘ Ameen ya gaya mata cewa Sultana ta nemi Dikko da asiri fa , amma ita yace mata kar ta nemi Dikko da asiri wai ɓannar kuɗinta zatayi , yaci gaba da cewa saidai ita yarinyar a firgitata a saka mata shakkun mai gida a zuciyarta , idan ta ganshi tayi kamar taga cici , Jiddah tace tou haka yayi yaushe zamu je ?
Al ‘ Ameen yace bara inyi waya dashi saiya fitar mana lokaci da kanshi , Jiddah tace ngode Al ‘ Ameen da Allah ya haɗani dakai da na shiga gararin rayuwa , tayi godiya sosai shima ya gode tare da fitowa daga palonta ,
Bayan ya fito yayi dariya yace sakarar banza zan kaiki malam yayi ta ɗirka miki asirin da ke da kanki zakice mai gida ya sakeki , ina ansar taimako ina kaiwa Mardiyya insha Allahu sai mai gidana ya auri Mardiyya zuri’armur zasu fita daban yarinyar “yar uwata ta samu sa’ar rayuwa , ita kuma Sultana zamu goge labarin mai gida daga zuciyarta , shi kuma mai gida soyayyar da yake ma Sultana sai a juya sunan Mardiyya a kan soyayyar da yake ma Sultana , sai ya koma san Mardiyya wannan shine mafita , Yeeee wannan shawara tayi , yayi “yar rawa tare da taɓawa cikin farin ciki.
*_London_*
Dakel ya juya kwanciyar shi cikin yanayin gajiya idanuwan shi a rufe , miƙa yayi sosai yace An mata , saida ya gyara kwanciya yace duk ki gama yarintarki da duk abinda kika ga dama insha Allahu duk duniya baki da miji saini , buɗe idonshi yayi a hankali yaci gaba da cewa ni wallahi tausayi kike bani dana tuno na tattara fushi na da ƙarfina na sauke a kanki sai tausayinki ya kamani , tsoki yayi tare da saukowa daga saman gado yana cewa banso ranar tazo a haka ba , amma ya na iya yadda ubangiji ya tsara kenan.
Toilet ya shiga bai wani daɗe ba ya wanko bakinshi da fuskarshi ya fito , Ashiru ne ya shigo cikin bedroom in ya miƙawa mai gidanshi waya wai Jiddah tana kira , ansa Dikko yayi ya kara wayar a kunnenshi tare da cewa inajinki ,
Cikin soyayya da gogewar kalamai tace haƙuri na kira in bada ranka ya daɗe , sai yanzu na gane nayi kuskure kishinka ne ya rufemin ido har na aikata abinda bakaji daɗi ba , amma ka gafarceni insha Allah haka bazai sake faruwa ba kayi haƙuri don Allah , waye ya faɗa miki bana nan ne ? Cike da ladabi tace Momy ta kira Hajiya tace kayi rashin lafiya , sai tace zata zo ta ganka shine Momy tace baka nan amma zata turo mata number ka ni kuma data turo saina ɗauka in bada haƙuri.
Ajiyar zuciya Dikko ya sauke shima cikin kulawa yace ba komai ya wuce , tou Yaya zan koma dan Allah , a , a , haba Yaya ka rufamin asiri don girman Allah ka barni na koma , Dikko yace keyy….. Jiddah tace Allah baka lafiya yasa kaffara ne , yayi kyau ya ƙarasa tare da kashe wayarshi.
Kallon Ashiru yayi bayan ya gama wayar ya nuna mishi hanyar fita da hannunshi , da sauri Ashiru ya fita shi kuma yaci gaba da tunanin An mata……
Kwance nake saman gado na ƙurawa wayata ido dan yanzu na cireta a jirgi kwata² ina tsammanin kiran Dikko ko wane lokaci , Yayar Aunty ce ta shigo dan sun daɗe suna kirana banji ba hankali ya tafi tunanin Dikko , dan na kalli hotonshi dake cikin wayar Aunty Mamy wanda Al ‘ Ameen yasa a d p inshi Aunty kuma ta ajiye hoton a ma’ajiyar hotunan cikin wayarta , nasha kuka har na gode Allah dan idan zan kalli hoton shi so goma sai nayi kuka sau adadin kallon da nake ma hoton.
Dafani tayi na dawo a firgice tare da goge hawayen idona ina sauke ajiyar zuciya , murmushi tayi mai haɗe da cewa sannu , nima murmushin nayi na sauko daga saman gadon na gaisheta , ansawa tayi cikin sakin fuska tace muje tayi gaba nabi bayanta ,
A palo , Auntyn da tazo dani ce a saman keken guragun ta , sai Yayar Aunty sai wani babban mutum yasha rawani zubinshi dai irin na malam zaure ne , duƙusawa nayi na gaishe su cikin ladabi , cike da kulawa ya ansa tare da cewa sannu baiwar Allah , nace yawwa,
Shi kuma yaci gaba da cewa cikin hukuncin ubangiji abinda ya faru shekaru da dama da suka wuce Allah ya bada iko cikin hukuncin sa da yaddarsa ya warwareshi , bamu yi ƙoƙarin bincike ba saidai nayi amfani da bayanin da Hajiya Suwaiba tayimin ya nuna Auntyn da tazo dani yaci gaba da cewa.
Hajiya Mamy kafin ta rasu tace duk musabbabin abinda ya janyo wannan rikici da tashin hankali da jefe² duk sanadin ɗaukar budurcin matar Bello ne wanda shi Binna yayi a matsayin ɗaukar fansar abinda akayi ma yarinyar da ya zauna gidansu ,
Wannan dalili yasa shi Bello ya ƙwallafi marigayi Binna a zuciyarshi wannan itace ƙiyayyar dake tsakaninsu , kafin haka kuwa abinda ya shigo da Bello a rayuwar Binna shi ɗan uwan Binna wanda suke Baba ɗaya shine ya turo Bello a rayuwar Binna bayan mahaifiyarshi ta haɗa tuggun da mahaifinshi ya korashi daga gida ,
Taga ya tafi bai lalace ba shine ta tashi hankali su kuma “ya “yanta suka taimaka mata wurin ganin sun cika mata muradin ta na ganin Binna ya lalace dashi da ɗan uwanshi kuma babu abinda sukayi mata haka kuma mahaifiyarsu Binna batayi mata komai ba , da sukaji labari su Binna sun samu gidan aiki da ake kula dasu , shine suka nemi hanyar lalatashi wannan dalilin yasa suka tura Bello ya shigo rayuwarshi ya shanmace shi da sihiri ya samu damar afkashi a wasan caca kuma suka fidda ma Binna tunanin waiwayar gida , ana cikin haka ne kuma Bello ya lalatawa yarinyar gidan dashi Binna yake zaune rayuwa sai aka korasu , Bello kuma yajasu suka zama suna ƙarƙashin ikonshi har Allah yasa shi Bello yayi aure Binna ya ɗauki budurcin matarshi a daren ranar da ango zai shiga ɗaki.
Daga nan sukayi faɗa na tashin hankali suka rabu , bayan rabuwarsu ne “yan uwan Binna suka tura Bello akan kar ya sake ya yadda ya nemi Binna ya bashi haƙuri idan ya dawo rayuwarshi shima ya ɗauki fansa akan kaff ahalinshi ,
Haka yabi kaf ahalin Binna yaci gaba da jifarsu , amma saiya lura hankalin Binna baya kansu bai kuma damu da lalacewarsu ba , yaci gaba dai bai daina ba har Allah ya kawoki kuma mahaifinki ya ci buri akanki kuma yaso kiyi ilimi mai zurfi ganin Binna dai ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora miki yasa Bello ya juya akalar tsafinsa akanki shine yaje yayi wannan tsibbacin nasa wanda kuma ubangiji ya kawo ƙarshenshi da izininshi da yaddarshi kuma an warwareshi , ga magunguna nan Hajiya zata faɗa miki yadda zakiyi amfani dasu.
Gyara zama nayi na kalli Hajiya Suwaiba nace Aunty da kika kirani kince an tafi a kashe Babana su waye suka tafi kashe shi ? Kuma ke me kikeyi a wurin lokacin da kikemin waya me yasa kikayi ihu bayan ke kuma na ganki baki da ƙafafuwa ya akayi kika je wurin……….?
Cike da damuwa tace bani bace kikayi waya dani , yadda kika ga wannan kwalba da wannan waya da na kiraki da ita ina kwance a saman gadon asibiti Allah ya kawo min matar da kikayi waya da ita batamin bayanin komai ba tadai bani wayarta tacemin amana ce aka bata kuma itama ta bani amana , tabbas tamin maganar Mamy idan baki manta ba da kika zo asibiti ai kinji nace miki ina Mamyn take ? Bansan Mamy ba amma matar ta nunamin hoton Mamy a cikin wayarta ,
Wannan bawan Allah kuma da kike gani itace tace in duba cikin wayar ta zanga lamba an rubuta malam ɗayyu inyi ƙoƙari na nemeshi shine zai kawo karshen matsalarki domin tamishi bayanin komai , ni banda ƙafafuwa shi yasa na kira “yar uwata bayan ni nayi waya dashi malam ɗayyu ya faɗa mana mazauninshi shine na tura Yayata takai mishi kwalbar ,
Idona cike da hawaye nace shin ina ita matar data baki wayarta da kwalbar nan take ? Aunty Suwaiba tace bansan inda take ba domin tana saƙamin a cikin bargon da nake lulluɓe dashi naga wasu mutane sun shigo suna nemanta ita kuma tabi ta wata hanya ta fice , ba’a sallameni ba gudun bi baya yasa nima na baro asibitin dan bana san rayuwata ta sake komawa cikin matsala.
Kai ׳ innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , Allah ngode maka ubangiji ya bayyani min duk masumin wannan bita da ƙulli , an kashe Aunty Mamy , an kashe Babana ita kuma wannan tana raye ko tana mace oho ? Ya zamar min dole nabar gidan baiwar Allah nan da bata san sake mayar da rayuwata a damuwa ita kuma meya faru da nata rayuwar ?
Kallon malam ɗayyu nayi tare da cewa shin ko kasan inda gidansu Babana yake ne ? Yace yasan gidan a katsina yake ƙofar marusa , nace kai a wane gari kake ne ? Yace katsina yake , miƙewa nayi tsaye tare dayi ma Aunty Suwaiba godiya na koma ciki na tattaro wayoyina ina dawowa palo nace ma malam ɗayyu muje katsina.
Miƙewa yayi tare da tattara magungunan daya zo min dasu yayi gaba , ni kuma na duƙa a gaban keken guragun ta nace Aunty ngode sosai zan tafi amma zan dawo domin ina sha’awar jin wace irin rayuwa ce kikayi ta baya wacce har baki so ki sake komawa cikinta , miƙewa nayi tare dayi ma Yayarta sallama na fice daga palon ina kewar mutanen kirki irinsu Aunty Suwaiba amma tabbas akwai dawowa bayan kowa ya ajiyewa kowa lambarshi a cikin wayarshi……
Ƙarfe 7:43pm acikin garin katsina tayi mana wanda malam ɗayyu shine ya jawo motar tun daga daura har zuwa cikin birnin garin katsina , kai tsaye ƙofar gidan su Babana muka tsaya , ina ƙoƙarin fita daga motar naga Baban Hafsa ya fito , kallonshi nayi sosai yayin da Bello ke biye bayanshi , kallon malam ɗayyu nayi nace lallai² nan gidansu Babana ? Yace shakka babu wannan shine .
Dogon nazari na tafi anya Baban Hafsa yasan ni ɗiyar ɗan uwanshi ce kuwa ? Da babu Bello dana sauka nayi masa magana na gani ko zai ganeni ? Kenan wannan shine dalilin da yasa Mamy tace da Binna yasan wace ce Hafsa a wurinshi da ya haɗiye zuciya ya mutu , a bayyane nace ummm tare da taɓe bakina naci gaba da cewa ƙaddara da ajali ba’a kauce musu tou amma kuma meke tsakanin Hafsa Amisty da Babana ? Wannan ansa banda mai bani ita itama.
Daga gidan su Baba gidan Baba Ƙarami muka nufa na nuna masa zan zauna ne zuwa wani lokaci amma saboda tsabar shi butule ne ya manta da irin karamci wanda mahaifina yayi mishi ya shafawa idonshi kwallin rashin mutunci yayi min wulaƙanci na ƙarshe tare damin gori karuwar banza karuwar wofi wacce ubanki ya mutu a gidan caca.
Kallon Baba Ƙarami nayi ƙasa da sama nace aiko caca ta gama maka komai tunda harya ciyo gida ya baka kake zaune dan na tabbata da “yan uwana sunsan wannan magana wallahi da sai sun ƙwace gidan nan sunce na magada ne , kuma da kake cewa ya mutu a wasan caca kai kaga yadda taka ƙarshen tazo maka ne ? Kuma da kacemin karuwa inda na gode Allah tambarin ba a kaina kaɗai yake ba kaima kana da taka karuwar zaune a gida.
Cikin hayani yace ni ban haifi karuwa ba kuma bazan haifeta ba har abadan duniya idanma nasan ina da karuwa a gidana saina kashe ta ko an faɗa miki ni lusarin ubana ne ? Nace shima uban nawa ba lusaranci ya janyo mishi haka ba ƙaddara ce kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddara , haka kuma shiriya ba iyawar kowa bace ba daga Allah ne kuma na rantse da Allah idan baka barni na zauna gidan nan ba saina nemo “yan gidanmu sun anshi gidan ubansu tunda ba takadda ya rubuta ya baka shi daga duniya har lahira ba ,
Matanshi suka sako baki wallahi bazan zauna musu gida ba na lalata musu tarbiyar “ya “ya inji maman safiya , kallonta nayi nace aike taki ta daɗe da lalacewa ko kina tunanin bansan komai ba ? Naci gaba da cewa ƙofar soro , asibitin da akayi komai ke hatta gidan da aka samo tukuicin da niƙaf taje , da sauri Safiya ta tashi tayi cikin ɗaki , uwarta ko ta kama bakinta bata sake magana ba gudun kar in tona mata asiri a gaban kishiyoyi ,
Tunda abokan zama sukaji haka kowa ta fara ɗakinta zan zauna sarai na gane dan suji labarin abinda Safiya tayi amma sam nace ɗakinsu Safiya zan zauna , uwar Safiya kuwa bata sake magana ba shima Baba Ƙarami ɗaureren azumin magana ya ɗauka , waje na koma wurin malam ɗayyu na anso magunguna na bayan yamin bayani duk yadda zanyi amfani dasu , godiya nayi masa na anshi lambar wayarshi tare da cewa saina shigo.
Satina biyu a gidan Baba Ƙarami na kammala kaf magungunan da Malam Ɗayyi ya bani , natsuwa ta shigo cikin kaina tsoron Allah da gudun duniya ya dawo amma kaf iskancin da kuka sani yana nan ɗibge akaina saidai idan ba’a latsomin wurin ba ,
Ranar dana cika sati biyu cif ranar na ɗagawa Baba ƙarami hankali saiya maidani makaranta , yace min baida kuɗi nace aiko ni ba’a gayamin babu duk inda zai samo kuɗi saiya samosu ya maidani makaranta , yacemin wallahi baida inda zai samosu , dole na haƙura amma na yanke zan kira Alaji in jaraba sa’a na gani ko an dace amma kafin nan zan koma islamiya in fara hadda.
Da daddare na tambayi Baba Ƙarami ƙarfe nawa yake rufe gida ? Yace min ƙarfe 10 idan har goma ta wuce koda minti ɗaya ne saidai mutum ya kwana waje , nace tou babu damuwa , saida nayi alwallah sallar isha’e na kira Alaji nayi masa kwatancen gidan Baba ƙarami nace mu haɗu dashi yanzu da Allah ina san ganinshi yace yana zuwa.