NOVELSUncategorized
RAGGON MIJI 46-50

4⃣6⃣
*another page for you rukayya haroun(maman nour)* *and erminatou*
Ummi tace “gaskiya alhaji bazan kai diyata gidan kishiya ba “
Abba yace “haba asiya be kamata kina magana irin haka ba, ita ai ba budurwa bace jawara ce kinga mawuyacine tasamu saurayi, dan Allah kibarta tunda tanasonshi karki sage mata gwiwai “
Ummi tace “ni ban iya kishi ba bare ita hakanan kaje aimaka wani mugun abun kana zamanka lpya “
Abba yace “shikenan tunda zancen kikeso bari nabaki wuri inkingama mitar kikawomin fura ta “
Ya tashi yabata wuri, ummi tace “shikenan se inki magana, yanzun intayi auren ko nima hankali na ba kwanciya zeba bare ita, tunda taji tagani shikenan Amman dole na dage mata da gyara na musamman in inaso tai daraja ”
Ta tashi ta nufi dakin abba,
Faseelat nashiga daki ta haye gado ta kunna data cikin farin ciki,
Messages nagama shigowa tabude na maman amira wanda yanzu ta meda number ta da my anty , ta bude message nata “wai antyn amira kinmanta danine?ko duk zawarcinne ya boyeki?har munyi tafiya mundawo, in bazaki zoba kibani address naki zanzo ni saboda yarki ta matsamin “
Faseelat tai dariya ta tura mata “zanzo insha Allah zuwa jibi de nima ina missing naku “
Tafita tashiga contact na fahad ta turamishi “masoyi naji dadin kyautar ka, Allah yakara maka budi ya kareka daga sharrin makiya, kanata kara kyau miye sirrin ne?”
Ta turamishi tana murmushi ta kashe datar se barci,
Da laasar fahad ya kirata suka kara shan vedio call sannan sukai sallama,
Se dare ta samu tabude data bayan sunyi bankwana da habibinta, ta shiga message din maman amira “????????????????????????thank se kinzo inanan ina zuba eyes”
Faseelat ta tura mata “don’t mind”
Tafita alokacin fahad ya turomata reply kamar haka “amin cutie karki damu da kyauta da namiki bakomai bane danko raina kikeso zanbaki, kinason kisan sirrin?”
Faseelat tace “thanks eh inaso inji “
Cikin zolaya yace “aisha ce sirrin tana kula da service dina duk lokacin dana bukata ana bani “
Faseelat ta tura mishi “???? To yayi kyau ,tunda ta isheka me zakai dani “?
Yace “I’m joking fa naga kinhau I just test you kinga kema kishinne dake zuwa zakuyi kuyita hadamin zafi “
Faseelat tace “aini bazanyi kishi da anty ba “
Yace “hmmm Allah yasa, gobe inanan zuwa fa, don kullum zanzo sekin gaji dani “
Tace “ai bazan gaji ba kazo yanzu ma “
Yace “kina tsoron nawa da rana ma yaaka kare? “
Tai murmushi ganin ya sauya zancen tace” good night sleep well ????“
Yanagani yayi murmushi ya cigaba da aikinshi.
Da safe abba yaje yasamu baba babba akan maganar fahad yace zesa amishi bincike akansa,
Da marece faseelat taci gayu sosai tasaka kayan da ya siyomata, tafito ummi tace” kinyi kyau gaskiya ina zuwa halan? “
faseelat tace “fahad ne yace yana kan hanya “
Ummi tace “to waike bazaki ce yarika shigowa ba kullum fira a mota? “
Faseelat tace “to ummi zanmasa magana “
ummi tace “kibada asiyomiki dan juice mana kitafi mashi dashi yadansha “
faseelat tace “to bari nabawa Mubarak “
Ummi tace “sekinfa dage yarinya, don ba khalil bane wannan awaye yake kuma yanada mata “
Faseelat tace “nasani ummi bari naje “
Ta juya ummi tabita da kallo rigar duk tafito mata da shape dukda tanada fadi, kuma faseelat dan mayafin rigar kawai ta yafa,
Karfe 5 yazo ya mata waya tafito, be fito daga mota ba ta cikin glass yake karemata kallo, harta zo tabude marfin motar ta shiga,
Yaja numfashi ya sauke ta kalleshi tana turo baki,
Ya lumshe ido ya bude yace “cutie wannan kwalliyar fa?”
Tace “i did it just for you “tana marmara ido cike da jan hankali,
Yayi murmushi yanabinta da ido yace “thank you I’m happy, kinyi kyau sosai “
Tace “thanks ga ruwa”
ta mika mai water melon juice yana kallon kwalin yace “ni bazansha ba sede kibani a baki “
Ta bata fuska tana hararanshi yace “abinda aisha keyi kenan komi yimin take taimin wanka, tasmin kaya, ta bani abinci abaki, amma ke just kiban drink yagagara “
Ta harareshi tace “kabari kaga muyi auren ba wanka ba har goyonka ma zanrika yi “ya kyalkyace da dariya yace “sure? “
Ta daga mai kai yace “to fara tundaga yau mana mugani inda gaskene”
Ta tunzuro baki gaba tace “open ur mouth”
ya wage baki yana jiran tafara bashi,
Tai dariya ta bude marfin ta dora mishi kwalin abaki, ya dage yayita kwankwada, tai sauri zata janye caraf ya rike hannun alamun ta cigaba da bashi,
Ta dora mai yayi ta sha ta fiddo ido tana kallonshi tasss ya shanye yana meda numfashi ,tana mamaki ta sadda robar Kasa bakomi ciki ta dago tace “amma yau anty batai maku girki ba ko? “
yayi dariya yana goge bakinshi da handkerchief yace “yau nidakaina nashiga kitchen, bawani yunwa nakeji ba jindadin juice dinne yasa na shanye shi duka, kinsan duk abinda ya fito daga gunki dole yayi dadi “
Ya kashe mata ido daya,
Ta rufe fuska tana dariya,
ya dauko waya yace “kigyara nai miki pic, badani zaaiba bare kice danna samu na tabaki ne “
tace “OK, amma zamuyi da kai a wayata “
Ya saki murmushi yanajin dadi,
Ta dan fiddo ido ta matse baki ya dauketa, pic din yayi mugun kyau kalar rigarta purple da baki ,
shiru be dagoba yanata kallon bakinta da ta matse kamar zatai kisss,
Tana kallonshi tace “muyi atare mana “
cikin rashin sanin abinda yake yace “wait for me “
Ta turo baki ta matsa ta leka wayar yayi zooming bakinta yanata kallo ta fashe da dariya,
yayi sauri ya dago cikin dawowa tunani,
tana nunashi da yatsa tana dariya tace “Allah kacika jaraba dubi duk yadda idanunka suka koma “
Yayi murmushi ya jingina da seat ya juya ya kalleta yace “kamar kinsani kima shirya “
Ta canza maganar da matsawa kusa dashi ta dauke su pic,
Tana dauka shiko hankalin nakanta tana samu tadauka ta matsa tana dubawa tace “yayi kyau sosai, kasan wani abu zan dorashi a status da insta “
Yayi murmushi yace “idan kuma bakisaka ba ni zan saka akan nawa “
Ta rufe baki “rufani kasayani ban shirya abinda zancewa anty ba, gobe ma zanzo ganin yata anty ma tace tayi missing dina “
yace “gobe munada special guest kenan Allah yakaimu “
Tace “amin bari natafi se munyi waya”
Yace “ammmmm”ya fiddo 1000 rafas biyu daga gaban motor ya mika mata yace “kibawa yara “
Ta girgiza kai tana murmushi tace,”bana son kudinka kai nikeso”
Yaji dadin maganarta ya lumshe ido ya bude kafin yace wani abu tabude tafita tana mai murmushin dauke numfashi,
ya rumtse ido gam yanajin yadda zuciyarshi ke harbawa saboda tsananin sonta,
sannan ya bude yana kallonta har ta shiga gida, seda ya dau 10 mnt sannan ya tada mota ya tafi,
Yana kan hanya yamata transfer na 500,000,
faseelat mamaki ya cikata da tagani tanata tambayar kanta koshi bejin wuyar fidda kudine oho, ta nunawa ummi, ummi tace
“duk kan gyaranki zasu kare ai”
faseelat tai dariya
Next day tunda wuri faseelat tagama aikinta tatafi super market, ta kwashi kayan kitson yara danginsu beads ,robber band,robar kitso ,Brazil wool dasauransu sannan taje wurin kayan wasan yara,
Wata big teddy me kyau ta baby ta burgeta ta dauka taje tabada ATM suka cire kudinsu kusan 50 thousands teddyn yakama tana dauke daita ta hau napep zuwa gidansu Aisha,
Me napep na ajiyeta ta biya tai knocking ta gaida baba tsoho ta shiga,
Amira na wurin wasanta ta hango faseelat da gudu taje ta rungumeta,
Faseelat na dariya tace”daughter I really miss you “
Amira tai dariya tanakai hannu kan teddy faseelat tabata tace “dama nakine gashinan “ta mika mata amira ta rungume babyn,
Faseelat tace “ina anty? “
Amira hankalinta na kan teddy dukda tana da wadanda suka fisu setaga wannan tafi mata tace “she’s inside “
faseelat tace “OK zo mushiga ciki “ta jawota suna tafiya tana kallon kitson kanta da yadan tsufa,
Suka tsaya bakin kofa faseelat ta danna door bell shiru takara dannawa seda akai 15 mnt sannan aisha tazo tabude tana murmushi tace “maraba da anty “tana kallon kayan jikinta,
Faseelat ta shigo tana murmushi,
faseelat ta gaida aisha, ta amsa tana mata kallon up and down tace “a, a! Jawara kinfaso gari kinga yadda kika kara kyau kuwa? “tana dariya
Faseelat tace “anty bawani kyau kina zaulayata ne “
Maman amira tace “Allah kinsauya gaskiya bazawarinki na kula dake “
Faseelat tai dariya tace “anty very soon de zanyi aure nahuta da kirana jawara da kike “
Aisha tace “Allah yakaimu muna murna ai, saboda mune kirjin biki “
faseelat tai murmushi,
Aisha ta mike “baride nakawomiki drinks, inkoma ciki daddyn amira nanan, bacci ma muke kika tadamu “
Faseelat tace “ok”
Aisha tatafi kawo mata drinks ita kuma ta bude jaka ta fiddo kayan kitson amira ta dauki wasu da zatai amfani ta ajiye sauran ta ajesu a kasa, tafara wa amira tsifa,
aisha nadawowa tagansu tace “yau ranar ta amira ce kenan naga harda katuwar teddy aka siyomata “
Faseelat tace “eh dan ita nazo “
aisha tace “to Nagode “ta ajiye mata ta haura sama,
Seda tagama mata tsifa ta danzuba drink tasha, ta daga kai tana kallon benen jin aisha shiru, wani malolo yatsaya mata a makoshi ta daure ta farawa amira Twisting,
Irin manyan nan ne masu guda ukku shaf shaf tagama mata aisha shiru bata fito ba, abun yabata mamaki kusan 1hr,
Cikin dabara ta kalli amira tace “kitsonki yayi kyau jeki gwadowa mommy “
Amira ta gudu tana taka step,
Ba jimawa segasu sunfito Aisha rike da hannun fahad shi kuma ya dauki amira yana tambayarta wa ya mata kitso dan besan faseelat bace har tazo,
Har suka sauko falo ahaka faseelat tunkan bene take kallonsu tanajin haushi,
Fahad na dago ido yaga faseelat,
Tayi kyau tana sanye cikin milk hijab da brown atamfa ya dan dauke ido daga kallonta,
Aisha tace “yaya kaga teddyn da faseelat ta siyowa amira nan gashi harda kitso tai mata “
Faseelat cikin jin haushi tace “inayini “
yace “lpy thanks for your care for our child “
Tai banza dashi ya juya yacewa Aisha “sena dawo “
Ta matsa tai masa kisss a cheek tace “take care of yourself”
Faseelat ta cika tai famm yana satar kallon faseelat ya fita,
aisha tazo ta zauna tajawo amira tana duba kitson tace “gaskiya kinyi kokari har kingama cikin sauri kiyi hakuri nabarki ke daya wlh se yanzu mukai wanka tundazu muna kwance “
Faseelat tace “badamuwa “tana yamutsa fuska tace “tafiya ma zanyi “
aisha tace “tunyanzu kitsaya mudanyi fira mana “
Wayar faseelat tahau ruri ta ciro ta duba taga fahad ne batare data dauka ba ta kalli Aisha tace “jirana akeyi dama nacika alkawari ne kawai “
Aisha tace “to shikenan Nagode kwarai faseelat Allah yabarki da masoyinki naga yanaji dake har iPhone 8s kike riko yanzu “faseelat tai yake,
Aisha tace “bari nakawomiki tsarabarki “
Faseelat tace “dan Allah anty kibarta ina sauri “
aisha tai dariya tace “aikuwa har gida zan kawomiki wasu English dress ne masu kyau nasiyomki naga zasuyi kyau da jikinki dan Allah kima bari nakawomiki daukosu kawai zan yi “
Faseelat tace “tom”
Aisha ta juya faseelat taja tsoki,
Can zuwa aishar ta dawo da ledar ta amsa tai godiya shaf shaf ta fita daga gidan,
Tana fita taga motar fahad awaje tana sauri tai gaba yabi bayanta da motar,
haryakai setin ta ya rage glass yace “kishigo in kaiki “
Tai banza takara sauri,
Yakara binta yana cewa “meyafaru ne wai? Kishigo mutafi “
Takarayin gaba, cikn fushi yakashe motar yafito yabita yajawo hannunta tana ta kokarin kwacewa ya sakata motar yaja yabar unguwar,
Faseelat ta duke tafashe da kuka me cinrai,
kujimin iko seta hanashi soyewa da matarshi ????
team faseelat de ????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*SHALELE????????♀*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
4⃣7⃣
Yana tuki yana jiyowa yana kallonta saboda mamakin abinda yasakata kukan kawai yake,
Ta cigaba da kuka tana sheshsheka, cikin jin ciwon kukunnata ya gangara gefen titi yatsaya, ya kifa kai jikin sitiyarin motar zuciyarshi na zafi,
Faseelat batabar kukan ba don wani mugun kishi takeji yanda suka fito tareda aisha says it all sunacan suna soyewarsu ne,
Ya dago yana kallonta cikin jin haushi yace “wai me yafaru ne?hakanan sekita kuka ninasan banmiki komi ba, kifadamin mekikewa kuka “
Ta cigaba da kukanta tana rage volume din,
Ya matsa ya dago fuskarta yana kallonta,
Bata kalleshiba ta cigaba da zubda hawaye,
Yana nazarinta yace “cutie kifadamin damuwarki plsss banajin dadin kukanki “cikin rarrashi,
Ta daga ido ta kalleshi tana ajiyar heart tace “bakome kaina ne ke ciwo “
Ya girgizakai kawai yafara share mata hawayenta da hannunshi sannan yace “kishi ko cutie?”
Taki cewa komi ya kwantar da kanta kan kafadarshi ya jinginar da kanshi jikin seat din motar ya rumtse ido zuciyarshi na harbawa dasauri,
Bayan 3mnt tanata ajiyar heart tadena kukan cikin jin tausayin kanshi yace “faseelat meyasa zakimin haka? yakamata ace kina boye kishinki kefa kikace min bazaki kishi da aisha ba yanzu me kike? Aisha ce fa ,aisharki haba for god sake ni yazan da rayuwata, faseelat akwai kalubale da yawa akaina, kullum cikin tunani nake taina zamfara fadawa aisha wannan batun, momy zata amince koko?ga shawarki data addabeni inason aurenki nankusa na rasa taina zanfara komi ya jagulemin hakanan kike ganina Amman ni nasan me nake ciki, yanzu bazaki temakamin ba ?ki kwantar da hankalinki kicire kishinnan ko nasamu kwanciyar hankalin yin abunda yakamata, saboda inkina fushi dani wlh duk tunani akanki yake tafiya “
faseelat ta daga kanta daga kafadarshi tanajin tasayinshi ta saka hannunta cikin nashi ta damke ya bude ido yana kallonta,
Tace “kayi hakuri plsss bazan sake ba”
Yana ta kallonta yace “yanzu haka zamuyi auren faseelat? I’m not going to take you to somewhere agida daya zaku zauna ya kenan, I want to build a peaceful family,idan kina haka yazaku zauna lpya keda aisha? Itama fa bansan ya zata dauki abun ba fa “
Faseelat tai fuskar tausayi tace “I’m really sorry nadena kishinka are you happy now? “
Ya juyar da kai yace “I’m not, ai bacewa nai kidena kishina ba, cewa nai ki rage ai u have to hide it now “
Ta cire hannunta daga nashi tace “naji nabari, kuma badole naji ciwo ba, nazo kunbarni a palo kuna ciki kuna…… Sannan kunfito harwani kisss zatai maka dan iskanci “
Yayi murmushin takaici yace “to miye aisha cefa maman amira “yaida yana dariya,
Ta harareshi tace “nasan kunayi basekafada minba ai”
Yayi murmushi ze kamo hannunta ta janye tace “kakaini gida ni “
yayi murmushi “ke yarinya kincika wayau time dinda kinason kiji dadin hannu na keda kanki kika rikoni nikuma in inaso seki hana? “
tai murmushi ta rufe fuska tace “kuskure ne akasamu “
Yayi dariya yana tada mota yace “inason irin kuskuren nan,”
yana hawan titi yace “bari muje na kaiki kidanyo shopping ko se nakaiki gida “
Tace “nide kakaini gida kawai banison shopping din “
Yace “I insisted “
Tai shiru yana tuki har suka isa big mall yayi parking ya fita ya budemata tafito suka shiga ciki,
Duk yadda yaso tadauki abunda takeso taki, sede shi yazabar mata kayan makeup da different perfumes dasu kayan tea ,
Yaje yayi payment suka fito suka kama hanyar gida, sunata labari kamar ba yanzu tagama kuka ba,
Suna zuwa kofar gidansu ya tsaya ya kashe motar ya kalleta yace “kigaidamin da kowa se nazo gobe “
Tace “tam Nagode hubby Allah yabiya maka bukatunka na alheri “
Ya lumshe ido ya bude yace “inason adduarki kicigaba damin addua “
Tace “karka damu ahakan bakomai bane akan wacce nakema aduk salla ta”
Yace “thanks Allah ya amsa “
Tai murmushi tafita,
Ya bude back seat din ya dauko ledojin yaji da nauyi yace “muje narage miki aiki banso ki expanding “yana dariya,
Tamai harara irinta masoya ta juya sunatafiya tare har bakin kofar gidan ya mika mata yace “bye”
Ta daga mishi kai kawai ta shiga, yana juyowa abba naiso wa akan mashin,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Fahad ya dakata har abba ya sauko ya zukunna har kasa ya gaidashi,
Abba ya amsa yana kallonshi, sannan fahad ya tashi ya tafi,
Bayan abba yashiga gida suna daki da ummi yace “anyi bincike kan yaronnan”
Ummi tace “to lpy de ko? “
Ya girgizakai yace “akwai matsala gaskiya ,wato shi mahaifiyarshi sun rabu da babanshi da dadewa kuma ba rabuwar arziki ba, shi yataso ne awurin matar babanshi, lokacin da babanshi na raye yahana mahaifiyar shi koda ganinshi saboda wulakanta yaron da tayi lokacin tana neman Saki, yanzu da yamutu tanata bibiyar yaron ya yafemata yaki ,saboda ancusa mishi kiyayyarta,yafison matar babannashi akan mamanshi sannan diyar ita matar babanshi yake aure, kinga akwai matsala kenan ace mutum na fushi da uwa, kuma yana tareda diyar ita wadda yakeso kinga faseelat zatasha wuya ne, kuma bazata hada kanta da kishiyartan ba tunda sunfi mu hali ganinake abun zezo da matsala, nima dazun alhaji ke fadamin Amman yace wannan duk ba matsala bace tunda suna iya sasantawa da ita mamanshin nangaba “
ummi tace “a, a gaskiya ni dama banason gidan kishiyarnan, bare ita wannan da yaruwarshi ce ,wlh da maganar da zanmaka ince kungama binciken ace yaturo dan naga ita faseelat ta haukace kanshi yanzu ma daga zuwa unguwa ta dawo da nikinikin kaya yasiyo mata “
Abba yace “Allah sarki ainima mungaisa yanzu har Kasa ya zukunna ya gaisheni “
ummi tace “ai yanzu sede ta hakura don abunnan bazeyiwuba”
faseelat dake bakin kofar daki kan tabarma tana kwance duk tanajin abunda ake wufff tatashi ta shiga dakin abba ta durkushe gabanshi tana zubar da hawaye tace “dan Allah abba karku rabani dashi, wlh inasonshi ni aganina shi abun tausayi ne, ansa mishi tsanar mamanshi kuma bayada wanda ze nuna mai gaskiya, dan Allah abba kayarda in aure shi kodan na temaka mishi “
Daga ummi har abba sukai kasake suna kallonta saboda mamaki, itako she don’t care batamasan kunya ayanayin da take ciki ba ,
abba yace “faseelat karfa ai abunnan azo ana danasanin yinshi”
ta girgiza kai “insha Allah abba baabunda ze faru “
Ummi hannunta kan baki tana zaro ido tace “kajimin ikon Allah dama kina labe kinajinmu kenan, kuma yanzu faseelat tunda kinfara soyayya kin tattara kunya kin aje gefe kina ta zuba rashin kunya, bama agabana ba hargaban abbanku ko? “
Faseelat ta girgiza kai “ummi dan Allah kubari na aureshi “
ummi tace “ahaf tunda kinji kingani ai shikenan Allah yasa alheri iyakar abunda zamu ce kenan “
Abba yana kallon faseelat yace “tashi kije “ta tashi tafita,
Ya kalli ummi yace”mutayata da addua kawai Allah yasa hakan ne alheri”
hannun ummi kan gemu tana mamaki tace “amin ya Allah” tana kadakai dan mamaki,
akan hanya fahad se tunanin yadda yaga gidansu faseelat yake duk da ginin cement ne amma ya tsufa, acikin ranshi yake shawarar canzamusu gida daga cikin gidajenshi,
Se marece ya koma gida, kodayaje aisha batanan tafita, yakada kai kurum dama da mommy takirata inde baya gida tafiyarta kawai takeyi sede ya samu batanan,
Se dare ta dawo amira ahannu tana bacci ,yana cikin balcony ya taso ya amsheta suka shiga ciki se akan hanyar shiga takecewa “mommy ce takirani anty kulsum ta haihu shine muka tafi tundazu muna asibity se yanzu muka dawo ,ta samu baby boy “
Yanata tafiya yace “Allah yaraya “tace “amin”
Tunda tashiga take ta kai kawo tai wanka ta shige salloli,
shiko yana saman bed yajawo computer dinshi yana aiki, yana cikin aikin faseelat ta turomishi pic Data dauka da dayan color da yasiya mata ,ya bude pic din yana kallo rigar is maroon irin robar nan ce irin kayansu na yan can tabi jikinta sosai ta mata dasss kamar dan ita aka yisu ga pic din andauketa from head to toe ta dan juya kadan wanda har hips nata ana gani,
ya kure pic din da kallo yanajin many emotions, yana tunanin kila dan takarasa shi ta turomishi pic din,
Yanata kallon pic din bako kyaftawa gabadaya ya rikice hannunshi biyu adunkule akasan habarshi,
Har Aisha tagama sallolinta taje gaban mirror ta shafa perrfumes dinta tasaka rigar baccinta da wando ta juyo tana kallonshi taga baaikin yakeba tunani ma yake, yadda taga yakure system din da ido dukda bata cika bin aikinshiba amma yasa ta zagaya ta bayanshi tai tsaye tana kallon computer din,
Abinda idonta yagani ne ya tada mata hankali gabanta ya rika harbawa fat fat!!!
Jikinta yadau rawa koina tafara ja da baya tana jawo numfashi da karfi,
Jin nishi nishi yasa fahad ya juya yaga aisha nata kyarma tana ja baya,
Cikin tsoro ya mike yana kallonta ,
Har takai karshen bango tanajinta jikin bango ta zukunna ta dora hannu biyu tafasa tsuwwar da fahad besan lokacin da yakai wurinta ba yariko ta yana “sorry Aisha take it easy please “
Jikinta na cigaba da rawa cikin rarrabuwar harshe tace “fa..fa….see…. Lat…. Ce….. Fa……A…com. ..pu.. Ter…dinKa…. KaKe….. Kallon….pic……nata “tadora hannu abaki tana fiddo ido,
Ya rumtse ido ya zukunna gabanta yahade hannu biyu yace “kiyi hakuri Aisha ki saurareni “
Itako kojinshi batayi tana ta tariyo maganganun faseelat, “harna fara son wani daban , anty soon de zanyi aure nima nahuta dakirana jawara da kike “sune maganganun datake ta tariyowa, that means tun tanada aure suke tare, kuma shine Wanda zata aura.
ya jawota jikinshi yana fadin “listen to me aisha “
Tai kukan kura ta tunkude fahad daga jikinta tai waje da gudu tana kuka , yabita yana kiran “Aisha wait plss kitsaya karkifita dare ne “
Koda yafita har tabar gidn ko takalma babu bare dankwali,
Kusan karfe 10:40 tana fita tasamu mashin ta haye tana kuka da rawar jiki tafada mai yakaita malali quarters ,
mashin na ajiyeta ta dira tafara buga gate din gidansu da karfi tana kuka,
megadi yazo yabude da katuwar gorar shi ahannu,
Tabanka aguje ta shiga cikin gidan,
Me mashin ko kotsayawa amsar kudi beba yajuya, don ya tausaya mata
Kannenta biyu na kallo Tawuce su dagudu tafada dakin mommy, mommy na zaune tana waya kan bed aisha tafada jikinta,
Jikinta na rawa tace “mommy mommy kitemakamin faseelat ta cuceni zata auremin miji… ……”
tohwa ana wata ga wata ????????♀
inga ruwan comments woooo ????????????????????
Shalele takuce fans????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY SHALELE*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4⃣8⃣
*dedicated to firdausi, F????????kinsanme? Inasonki sister????, kina sona kinga ko dole naso ki hausawa na cewa kaso me sonka,shiyasa nakamu over, fans kutayani son firdausi don nima inasonta, tadamu Dani matuka da zanwuce 9am bana online seta kira taji ko lpya nake, I love you F????????,my masoyiya*
Mommy tarika kallonta hankali tashe takamo fuskarta tace “ban fahimta ba, ki kwantar da hankali sosai kimin bayani”
Tana sheshsheka tace “mommy yaya aure zeyi kuma kawata ce, wlh faseelat ta cuceni ban cancanci haka daga gareta ba”
Momy tafara tafi tana salati tace “nashiga ukku ni faiza, yanzu yazanyi ne? Ke dan ubanki har wata kawa kikasamu wadda bansaniba? “
Ta daga kai tana kuka tana jijjiga mommy tace “dan Allah mommy kice karyayi aurennan wlh zuciyata bugawa zatayi, nide nashiga ukkuna faseelat ta gama da rayuwata “
Mommy tace “keda harkina da guarantee kan kawa? da har zaki saki jiki daita? To yanzu gashinan de kinaso kijamin asara inyi renon banza, nasaki jiki zansamu kudi Amman kinjawomin tsiya, kafin mahaifin fahad ya rasu ya mallaka mishi gidaje da filaye da gonaki da bansan adadinsuba, su ramlat su ukku bazasu samu rabin gadonshi ba shiyasa nasamu nahadaki dashi kinga komi de nawa ne akarshe Amman kinyi sakaci zekawo wata ta ragemin lissafi “
Aisha tace “mommy kihanashi plsss wlh bazan iya sharing dinshi ba da wata “
Mommy tace “aiko sede ki hakuri sanin kanki ne nariga nasaba mishi da goyon bayanshi akan komi, yanzu innace aa to matsala zaasamu saboda yana iya bijiremin gwara na yarda din yafi “
aisha tafasa kuwwa tadora hannu saman kai mommy ta jawota tana rarrashi tace “ki kwantar da hankalinki diyata baabinda ze faru a aurennan kede kirika bin shawarata sannan kirika fadamin duk abinda ake ciki “
Aisha ta cigaba da kuka mommy nata rarrashi tace “dole ki hadiye kishinnan ki nuna mishi kinason abunnan kinga zeji dadi yakara sonki kuma ko tazo ki kauda kai ga alamuransu seki zauna lpya, inkika yi haka se yakara ganin girmanki fiyeda da “
tana kuka tace “mommy wlh bazan iyaba ni ina kishin mijina sosai bazan iya dannewa ba “
Mommy tace “to hauka zaki tayi duk kisure mishi, ?kowane namiji fa inde zaiyi aurennan seyayi doki, kuma yanada damar auren mata hudu in yaso, kita hauka yadena sonki bahaka kikesoba, kinade gani yanda nazauna da babanshi komi atafin hannuna “
Takara volume na kuka “wlh faseelat setayi danasani inta auri mijina “
Mommy tace “aure kam kamar anyi angama ne, kedai kinyi kuskure, yanda mazannan sukai karanci bare naki da kowa zeso kikabari har tasanshi, kiyi hakuri kinji nasan kome zanyi akai “
aisha takara volume itafa inba auren akace anfasa ba bazataji dadi ba,mommy nata bada baki Amman ina,
Jiki sanyaye fahad yakoma cikin gida yana shiga amira tazo ta rungume tana kuka tana kiran mommy ya dauketa yana rarrashi ya dauko Key yasaka riga suka nufi gidan mommy tunkan hanya amira tai barci, shiko yanata sakesake,
Yana zuwa yayi parking ya sabi amira awuya suka nufi ciki
Yana shiga su sadee suka tashi sukai saman bene da gudu don sunajin kukan aisha su azatonsu ko jibgarta yayi ,
Bedamuba ya kwantar da amira kan kujera yana sauraron kukan aisha daga sama,
Ya kama hanyar benen cikin sanyin jiki, dama yasan bazaa kwashe da kyau ba,
Mommy nata bata shawarwari koji batayi tanata kuka ya shigo dakin, yana kallon fuskar mommy yaga yanayinta ya zauna gefen gadon yafara magana “dan Allah mommy kiyi hakuri bazan kara aurennan bane don inci mutuncin aisha ba, inason yarinyar ne kawai”
Mommy fuska a sake amma deep down tanajin zafi tace “rabu daita dana ai kai mijin mata hudune, ni nagoyi bayanka kaje kayi aurenka karka biyewa Aisha kishine ya rufe mata ido “
Yayi shiru cikin jin nauyi zaaiwa diyarta kishiya Amman bata damu ba ya kalli aisha ya sadda kai kasa,
Mommy tace “gobe nidakai na zanje naiwa kawunka magana ayi komi in time akawo maka matarka “
Yayi shiru bece komiba sede yana jinjina irin son da mommy ke mishi, ya matsa ya rungumo aisha jikinshi yana cewa “kiyi hakuri Aisha, zanyi aure ne kawai amma ketadabance kinada special place in my heart, ki kwantar da hankalinki plss honey”
Mommy na zaune na kallo shiyasa aisha bata fizge ba daga rikon da yamata,
Tana ta kuka taji hannun mommy ta tsunkuleta ta dago ta kalleta mommy tai mata alamun tai shiru da ido,
Aisha tadan rage kukan, mommy tace “kutashi kutafi Allah yamaku albarka diyana, kiyi hakuri aisha kishi jihadin mata ne se andaure “
Ya mike tana jikinshi yace “seda safe mommy “
Mommy tace “ka kara bata hakuri plsss ka kuma hakuri daita har ta sakko “
Yace “Nagode mommy “yanajin sonta da kaunarta yaja aisha sukafita,
Ya dauki amira suka tafi gida,
Aisha naganin amfito takara saka kuka hannuwa biyu saman kai tanayi tana dumumuwa “ni nabani na lalace ni aisha, wayyo Allah na ancuceni an ci amanata “
yana tuki sede yajuya kai ya kalleta yana mamakinta wasu dumuwan dashi takeyi sam bata bashi haushi ba har suka karasa gida,
Yana parking tabude ta banka cikin gida da gudu, ya girgiza kai ya dauko amira ya medata dakinta ya kulle yafito ya shiga dakin aishar,
Ya sameta tana ta wurgar da pillows tana hauka, cikin rarrashi ya rikota cikin kwantar da murya yace “Aisha plss stop all this kar kanki yayi ciwo, faseelat ba kowa bace in zan kwatanta ta dake, inasonki sosai Aisha kuma u knew it ki yi hakuri nasan namiki laifi plss pardon me my love “
Yazo ze kaimata kiss ta kwace daga rikonshi tana kuka tace “ni zakuciwa amana? Ni faseelat zataiwa haka after all I did to her? “
Taja tsokii tai wurin mirror tabude Jakarta ta fiddo waya, yana tsaye yana kallonta ta dannawa faseelat kira hannuwa na rawa,
Wajen 1am ne faseelat tayi barci bata kashe wayar ta ba kiran aisha ya shigo, cikin magagin bacci ta lalubo wayar takara akunne,
ganin andauka aisha tafara balai tace “marar mutunci marar amana faseelat ni zaki ciwa amana? Kirasa wanda zakiso se mijina? Dan kina diyar akuya ko azatona ke diyar arziki ce ashe bansaniba da katuwar karuwa nake tare kinci amanata kuma wlh bazan barki haka ba, kishigo cikin gidan se naci kutumar uwarki jakka yar iska “
Faseelat tuni ta wartsake tafara kuka cikin kukan take cewa”anty dan Allah kitsaya ki saurareni kiji me zance “
Aisha tace “bakida hankali da kike tunanin zan tsaya in saurareki karuwar banza karuwar wofi me bin mazan mutane… “
Kafin taida maganar fahad da kejin kalmar karuwar nan kamar ana zuba mishi wuta ya fige wayar yanajin kamar ya kai mata mari,
Ta riko hannunshi cikin kwaratsi take cewa “kabani waya ta kabani wayata in kara zagin shegiyar can, yanzu daddyn amira ni zakaiwa kishiya? Nice fa aisharka ur honey “
yazo ze rikota tai kasan bene tana kuka ya zauna dabass kan bed ya dafe kai da hannu biyu saboda tsananin sara mishi da yake,
Faseelat najin aisha takashe wayar tafashe da kuka me karfi, ummi da jin maganar faseelat tafito tai tsaye jikin window tanajin abinda aishar ke cewa,
ummi ta tura dakin tashiga tace “ke dama kinsan matarshi ne? “
Faseelat ta daga kai tace “eh inazuwa gidanta “
Ummi tace “amma baki kyauta ba faseelat ai wannan cin amana ne, yakuna tare daita kuma kizo ki auremata miji baki kyautaba gaskiya “
Faseelat cikin jan numfashi tace”ni aganina kowa da yadda Allah yatsara haduwarshi da wani, nita sanadiyarta ne Allah yasa nasanshi be kamata tayimin irin wannan wulakancin ba, saboda banida niyyar cutar daita ko na aure shi, inaganin girmanta bazan manta alherin da tamin ba”
ummi dake tsaye gefen bed tace “to Allah ya kyauta, tundade kinji kingani aishikenan amma kinde fara fahimtar yaki zakijeyi kenan, ita kuma bewar allannan kisamu bayan kwana biyu kikirata kibata hakuri in Allah yasa tayi shikenan, “
faseelat ta daga kai tana kuka, ummi namata kallon tausayi saboda batasan me diyarta zata tarar ba tace “kidena kuka ki kwanta seda safe munyi maganar “
Faseelat ta koma ta kwanta amma takasa bacci tanata tunani ta yanke shawarar gobe taje tabawa aisha hakuri su dedeta,
Duk yadda fahad yaso ya bawa Aisha hakuri taki hakura a karshe ya barta falon tanata wurge wurge ya shiga dakin amira ya kwanta ya jawota jikinshi, tunani be barshi bacci ba yana ta tunanin ita faseelat ya take ciki yanzu,
Se asuba bayan yayi salla bacci ya daukeshi itako aisha tana gama salla ta dawo falo ta zauna har tagaji da kukan sede azabar zafin da zuciyarta ke mata ta mikar da kafa tadan kwanta itama bacci ya dauketa amma ba me dadi ba,
Tun asubar farko faseelat tafito tana aiki ko tarage jin damuwa amma ina hankalinta yaki kwanciya tanata tunanin miake ciki yanzu,
Ummi na dakin abba dan befita da wuri ba,
Faseelat tai wanka tasaka doguwar rigarta orange color tasaka farin hijab ta duba wayarta karfe 9 dede ,batare da ta fadawa ummi ba tai wufff tabar gidan tanufi gidan aisha,
Aisha cikin dan gajeren baccinta taji karar door bell tana yamutsa fuska taje ta bude ,
Ganin faseelat tsaye tai mutuwar tsaye tanajin kamar ta shakota ta daba mata wuka kotaji daman abinda takeji,
Ganin tayi tsaye tana kallonta faseelat ta kutsa kai ciki tana tunanin kila su dedeta, ta zukunna gaban aisha kanta Kasa tace “anty nasan ni me laifi ce agunki dan Allah kiyi hakuri bansan taina zan fara fadamiki bane tuntuni cewar muna soyayya da mijinki…..”
Bata bari takara saba cikin tsawa tace “keeee dan uwarki harkin isa kifadamin kina soyayya da mijina, karuwar banza kawai wato tunda kikaganshi kika like masa ko? To ki san dasanin nidake har abada wlh nayi danasanin saninki a cikin rayuwata “
Faseelat tafara hawaye tace “anty kitsaya ki saurareni plsss “
Aisha tace “kimaza kibarmin gida wlh kafin inci ubanki “
Faseelat ta dago zatai magana aisha ta rufeta da bugu ta koina, jikake fas! tab!duf!duf ,
Jin Azaba faseelat tafara ihu, cikin barci yaji ihu, ya farka zaune yakasa kunne inyaji da kyau muryar faseelat ce ,yace “oh my God “ya fita dasauri,
Tunkan bene ya leko yaga yadda aisha tahaye faseelat tana jibga ya kwatsa tsawa “keeeee aisha”
Koji batayi tana ta jibgar faseelat cikin sauri ya sauko daga kan benen ya janye aisha ya dauketa da mari a duka kumatunta, jikake tasss! Tassss,
Aisha ta dafe duka kumatun da hannu biyu tana kallonshi dan saura kirisss ta kife awurin,
Cikin sauri ya tada faseelat tana ta kuka ya rungumota jikinshi yana………
*inajin dadin comments naku jiya anyi ruwan comments godiya lodi lodi, nima inasonku masoyana*????????
Wani sabon salo har team aisha ke da kwai yanzu ????????
Team fahad ????
Team faseelat ????
team khalil bodari????
Team Aisha ????
Yayin team team ake saura team hajiya da team jamila ????
luv u always my fans dake koina ????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
4⃣9⃣
*dedicated to those lovable group’s*????????
*RAGGON MIJI FANS*
*RAGGON MIJI FANS 2*
*RAGGON MIJI FANS 3*
*UMMYN YUSRAH NOVELS GROUP*
*MUKARU DA JUNA BY MOMYN SAUBAN*
*NOVELS ZAFAFA BY DR FATEE*
*MY FORUM GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*
*MOMMY’S NOVELS GROUP BY SHALELE*
*THIS PAGE IS ALL YOURS FRIEND’S ACIGABA DA COMMENTS KAWAI*⛹????♀
*MANZON ALLAH (S. A. W) YACE :-lalle Allah ya rubuta kishi akan mata, da jihadi akan maza wadda tai hakuri acikinsu tana da lada kwatankwacin wanda yayi shahada.*
Yanajin wani irin ciwo a zuciyarshi, jintana ta kuka ya dagota yafara duba jikinta duk yayi ja abunka da farar fata ga gashinta duk Aisha ta yamutse shi cikin jin tausayi yakara rungumeta yana shafa bayanta,
Kwata kwata kuka yaki zuwa ma aisha tazuba mishi ido tana ta kallonshi ganin yadda ya kwakume faseelat kamar ze medata ciki yasa ta sauke hannuwa daga kumatunta tai hanyar kitchen da gudu ko seconds goma baaiba ta fito da sharbebiyar wuka ahannu tai kukan kura zata sokawa faseelat a baya, fahad yayi sauri ya rike kaifin,
Aisha tafara jujjuya wukar tanaso ta kwace ta sokawa faseelat shi kuma ya rike kuma still yana rungume da faseelat daketa kuka,
Dandanan jini yafara diga Kasa kan farar hijab din faseelat, ganin jininshi yana zuba amma yaki sakin wukar Aisha ta saki wukar ta dora hannuwa biyu akunne ta kwara baki ta saki kuka tai saman bene da gudun tsiya,
Fahad ya Saki wukar tafadi kasa ya bude tafin hannunshi yana kallon yankan da ke jiki,
Faseelat ta zare jikinta tana kallonshi cikin tausayi ta duka ta dauki kallabinta dinta ta kama hannun fahad tana nannada mishi tana kuka, shi ko kallon fuskarta kawai yake yana ganin wautar ta na zuwa gidan a yanzu,
Suna haka aisha tafito tana kuka sabe da amira awuya tafita tabar gidan, duk sukabita da ido,
Seda tafita faseelat ta medo kallonta gareshi tana sheshsheka tace “I’m sorry bansan haka anty take ba nazata zata saurareni ne dana sani banzo ba “
Ya riko fuskarta da hannu biyu yana kallon cikin idanunta yace “aisha zata iyayin fin haka, karki sake irin gangancinnan cutie yanzu da bani nanfa? Wlh aisha har kashe ki tana iyayi saboda gabadaya ta haukace,”
Ya riko jikinta “jibo yadda taimiki da jiki”
Faseelat takara zubo da hawaye dan ta jibgu ba karya ,
Ta riko hannunshi tana fadin “it’s hurting ko? “ta kalleshi cikin jin tausayi,
Ya rungumota jikinshi yana kwantar mata da gashin kanta yace “it’s not idan nahadashi da zafin dukanki da Aisha tayi “
ta kwantar da kai kan kafadarshi tana hawaye,
Yana ta shafa gashin kanta tai breaking hug din tace “zan tafi gida “
Ya jawo hijab dinta da take dauke da drops na jininshi yasaka mata, sannan ya kalli jikinshi daga shi se boxer ya dago ido yace “bari na dauko key na kaiki “
Ya juya ya haye bene few minutes ya dawo cikin jallabiya da keys a hannu ya kamo hannunta suka fito daga cikin gidan ya bude mata motor ta shiga ya zagaya yaja sukabar gidan ,shide baba tsoho yanata kallon ikon Allah yadda yaketa ganin Aisha na ficewa da kuka yasan akwai matsala,
Suna kan hanya yana tuki da hannu daya hannunshi daya kan cinyar faseelat, tunda suka fito take ta kara zubda hawaye,
Ya kalleta ya meda kai kan titi yace “kiyi hakuri cutie ki dena kuka ,Aisha bata isa ta hanani aurenki ba inasonki sosai fiyeda yadda zaki harsaso, ki kwantar da hankalinki aisha zata sauko insha Allah “
Faseelat zuciyarta zafi kawai take yadda Aisha ta wulakantata ga zafin yankan da taiwa fahad da takeji kamar ita akaiwa,
Ta Kalli hannunshi dake kan cinyarta
Tasa hannu ta rufe fuska jin kukan da ya taho mata tafarayi tana jan numfashi,
Fahad ya dauke hannun daga kanta ya shafi kanshi zuwa sajenshi ya fitar da iska me zafi daga cikin bakinshi gabadaya Sun caza mishi kai yace “cutie ya kikeso nayi ne? Yanzu kina ganin zan bari kitafi gida kina kukannan? Kiyi hakuri plsss”
Ta daga kai ta jawo hijab dinta tafara share hawayen dake zubomata tana sharewa wasu na zubowa,
Ya girgixa kai ,har suka kawo kofar gidansu, Ta bude zata fita yace “kode nakaiki asibity ne ko akwai inda ke miki ciwo? “
ta girgiza kai cikin muryar kuka tace “thank you “ta bude tafita ta shiga gida dasauri,
Yakara murmuxa gashin kanshi kanshi na zafi sannan ya tada motar ya nufi gidan mommy,
Faseelat dasauri ta shiga gida ummi da tundazun ta duba bataga faseelat ba ta ga wulgin faseelat dasauri tafito daga dakin abban tabi bayan faseelat da kallo kayan jikinta a cumumuye ga jini saman kan hijab din zuwa kasan hijab din,
Hankalinta ya tashi tabi bayan faseelat, lokacin faseelat ta yaye hijab din tahaye can karshen gado ta hade kai da gwiwa tana kuka,
Ummi ta shigo dakin tana kallon gashin kanta cumimiye tace “kee daga ina kike “
Faseelat ta dago tana raba ido tafara nazarin me zatacewa ummi,
ummi tace “dan ubanki ba magana nake miki ba? “
Faseelat ta fara yarfa hannuwa tana kuka,
cikin zafin rai ummi ta haye kan gadon ta shakarota cikin tsawa take cewa “bazaki fadamin ba ne dan ubanki daga ina kike? “
Abba yafito daga daki jin kakari da fadan ummi yayi sauri ya shiga dakin ummi ganin ta shakare faseelat yayi sauri ya je ya janye faseelat din yana kallon ummi yace “haba asiya kibari mana aibata haka zaki tambaye ta ina tajeba “
Ummi tace “alhaji yarinyarnan harta san takwasa taje wurin saurayi? Yaga ma tumurmusarta ta dawo tana kuka, jibi hijab dinta “ummi tajawo hijab din tana nunamasa tace “duk jinine jiki wlh faseelat ta iskance tunda har taiya bashi kanta kafin aure “
Faseelat ta dago tana zare ido jin abinda ummi ke cewa,
abba cikin mutuwar jiki yakebin faseelat da kallo duk ta harmutse,
ummi tace “nikam nagaji alhaji dan Allah kasamu yaronnan kace ya turo tunkan ta jawo mana abun kunya”
Abba bece komi ba yabar dakin ummi tazo zata kawowa faseelat bugu faseelat ta kauce tana zare ido tace “wlh ummi banyi komi ba, naje bawa anti hakuri ne, shine ta yankeshi a hannu amma wlh baai komi ba “
Ummi cikin rashin yarda tace “gafara can da Allah ni zakiwa karya, ko ni makauniya ce? ke kikasani dan wlh ko aurenki yayi bazaki wata daraja ba sakarai kawai yo miki so hauka ne da zaki je kibashi kanki, kin kyautawa kanki ai “
Fuuu tabar dakin faseelat ta fashe da kuka ta jawo pillow ta danne kanta dashi ta cigaba dayi,
ummi nafita bataga abba ba har yabar gidan takoma dakinta ta buga tagumi zuciyarta na zafi, tundazu maganar da sukeyi da abba akan faseelat ne don yaji abinda yafaru jiya Sunata neman mafita sega sabuwa ta billo,
Aisha nashiga cikin gida takara sakin kuwwa da mommy dasu ramlat sukayo waje, sadiya tai sauri ta amshi amira daga hannunta,
Aisha ta rungume mommy tana kuka,
Mommy tace “wato Aisha bazaki bi shawarata ba ko? Yanzu mi yakawoki da safennan?”
Aisha na kuka tace “faseelat dince wai tazo bani hakuri shine nahauta da duka ina cikin dukanta shine yazo ya mareni shine na dauko wuka zan soka mata shine yarike da hannunshi duk yaji ciwo ahannun “
Hjy tace “wato de bakijin magana ta kenan ko? yanzu da kin kasheta fa? Kema ba barinki zaaiba, nace kiyi hakuri kibar lura da abubuwansu kinki, inaji miki tsoron ya sake ki dan masu irin wannan haukan da saki suke karewa, kinga shikenan se ita wasila take kowa tasami yadda take so”
Aisha tace “wlh bataisa ta rabani dashi ba “ta cigaba da kuka,
Ramlat dake gefe tace “kinyi dede anty gwara da kika ci ubanta da kyau “
Mommy ta banka mata harara tace “tashi kiban wuri “
Ramlat tatashi tabar wurin dama sadiya bata zauna wurinba tunda ta amshi amira ta wuce daita ciki ta kimtsata,
Mommy ta medo hankalinta kan Aisha taja ta tazaunar daita kan cushion tace “haba Aisha inafada miki abinda yakamata kiyi kina kaucewa, kiyi hakuri kibari ayi auren karkimanta fahad a tafin hannuna yake ya daukeni tamkar uwa, ba abinda waccan zata fiki awurinshi inde zakibi shawarata “
Aisha takara saka kuka mommy nata ban baki amma taki denawa,
Seda fahad yafara zuwa hospital akai mishi dressing sannan ya taho gidan mommy,
Yana shigowa ya gansu main pallow yaude fuskar mommy ba walwala dan taji zafi da ya mari diyarta akan wata,
Yazo ya zauna gefen kujera Aisha ta dago ido tana kallon hanninshi da bandage ta cigaba da kuka kanta kan cinyar mommy,
fahad yace “Aisha kiyi hakuri kizo mutafi gida banso na dakekiba “
Aisha batace komi ba mommy na kallonshi tace “inaganin kabarta anan ta danyi kwana biyu tadan samu natsuwa sannan se ta koma don naga duk tafita hayyacinta, kayi hakuri daita da duk abinda zatayi anan gaba, nide namata duk nasihata taki ji “
Fahad gabanshi ya fadi don be tunanin zeiya 2days batare da matarshi ba wannan nema yasa yake tafiya daita duk inda zashi,
Cikin rarrashi yace “Aisha kiyi hakuri mukoma gida, kinsan bazan iya kwana nikadaiba “
Ta dago fuska ta watsa mishi harara ta meda kai kan cinyar mommy,
Mommy ta canza maganar tace “dama inadawowa daga gidan kawunku se gata ai naso nakiraka tazo ta hargitsamin lissafi, naje nasameshi munyi magana yace kaje kuyi maganar kasameshi a office “
Aisha tatashi ta haye bene dagudu jin abinda mommy tace
Fahad Yace “Nagode mommy bari naje nasameshi “
Ya tashi yafita yaja motar zuwa gidan kawunshi rabiu,
Yana fita mommy taja tsoki, tace “dole fa intashi tsaye kar abinda na raina yazo yafi Karfina “
Fahad har cikin office din alhaji rabiu ya shiga ya zauna suka gaisa alhaji rabiu yace “danbaba mommynka tazo mun da maganar kanaso ka kara aure, naji dadi sosai ka girma kazama babban mutum ai karin aure sunna ce kuma mutum nakara girma,sede bata fadamin gidansu yarinyar ba nace ta turoka muyi maganar”
fahad yayi murmushi yace “Daddy sunanta faseelat gidansu a kofar durbi yake bazawara ce babanta sunanshi alhaji maaruf “
Alhaji rabiu yayi dariya yace “ai zawarawannan ma sunfi hankali da dadin shaani yanzu yaushe ka ke ganin zanje na musu maganar mommynka tace bataso bikin yafi wata amma inaso naji ta bakinka “
Fahad yayi dariya yasan kawunshi dama da barkwanci yace “yau nikeso inde akwai damar hakan, kuma su zasu zabi tym sede banson komi daga garesu kuma inaso ayi komi kamar auren budurwa “
alhaji yayi dariyar manya yace “to maganar kudi fa? “
fahad yace “zan rubuta maka chek kaje kacire yanzu de kafara zuwa tukun, anjima zan kawomaka kudin “
Alhaji yace “to yayi Danbaba Allah yasa ayi damu “
Fahad yace “amin se nazo anjiman ya tashi yafita “
Shiko abba gidan baba babba yawuce dan suyi shawara dan bayayin komi seda shawarar shi,
bayan an mashi iso ya shiga alhaji yace “lpya kake naganka somehow kamar kana cikin damuwa “
Abba yace “tunda safe asiya tazo takecemin bataga faseelat ba se yanzunnan gata tadawo jikinta duk jini wai taje wurin yaron sunyi lalata inaga, ni tundazunma muna ciki muna tattaunawa da ita akan batun saboda jiya matar yaran takira ita faseelat taci mata mutunci d daddare har mungama yanke shawarar tirsasata ta rabu dashi sega wannan abun “
baba babba yace “subhanallahi ashsha abu be dadi ba “
abba yace “shine nayi shawarar fadama yaron ya fito amma yakace? “
Baba babba yace “hakane dede ayi mishi magana yafito inda gaske yake, tunda gashi har yayi mata fyade, tunda ai tataba aure this means dakarfi ya kwata “
abba yace “to Allah masani nima abun ya dauremin kai amma tunda tana sonshi zanmasa magana yafito ayi musu auren suje can su cinye kansu tunda da kafarta tabar gida ai “
Baba babba yana jimami yace “Allah ya kyauta “suka cigaba da labari, sannan sukai sallama abba yawuce wurin kasuwancinshi.
Kafin sha biyu zazzabi da ciwon kai me zafi ya rufe faseelat, ummi Takoma dakin da niyyar takara cin ubanta ta sameta cikin bedshit dukunkune taja tsoki tafita tana ta maganganu ita kadai ta dora bagaruwa da karamfani da dankumasu da ganyen magarya saman wuta ta dahu sosai ta tace ta cika uwar robar wanka takai toilet tazo ta yaye zanin gadon da faseelat ta rufa dashi tace “kitashi ki tube muje nagasa miki jiki in Iskanci dadi ne gobe seki kara zuwa sakarai wadda batasan ciwon kanta ba, “
Faseelat dakyar jikinta yayi tsami ta mike zaune tafara jijjiga kai, zataiwa ummi magana,
Ummi tace “karki cemin komi anan kitashi ki abinda nace “
faseelat ta sunkuyar da kai cikin tausayin kanta ta tashi ta daura zane tana dafa bango zata fara tafiya ummi ta kamata tajata har cikin toilet ta zame mata zane cikin bacin rai tace wa faseelat ta shiga ciki,
Faseelat tafara matso kwalla ganin yadda ruwan ke suraci,
Ummi ta daka mata tsawa jiki na bari ta shige ta zauna ciki tanata cije lebo Tana rumtse ido saboda zafi.
Bayan wani lokaci
Ummi tajawo karamin towel ta rika tsomashi tana mammatsa wa faseelat jiki tanayi tana mata fada hawayen azaba yarika wankowa daga idon faseelat .
Team faseelat kuje ku fadawa ummi ba abun bane tukunna ????
all teams ana tare ????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELENKU)*????????
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
5⃣0⃣
*????????ashe haka soyake shiga zuciya yake,yasamu wurin fake cireshi wuya yake ????????????araina kena rike ,kimance komi kirike, koina kin mallake, nakine amshi kirike????this page is for you lady my habibaty Nagode da alherin da kikamin Allah yakara budi, thanks once again lady*
*Dedicated to lady*????????
Ummi nagama gasa mata taja tsoki tace “shasha kawai seki tashi ki wankan abinda kukai kizo ki amshi magani “
Tafita tabar mata toilet din, faseelat ta rufe ido da hannu daya tana kuka, ranta na mugun baci idan ummi taimata mummunan zato ,bare na yau da har abba seda yaji, ta share hawayenta tafito tai wanka saboda ruwan da ummi tai mata gashi sunyi duhu dan haka tasaka soso da sabulu ta wanke jikinta ta fito ta koma daki tasamu tasaka vest ta koma ta kwanta,
Wajen 2:00 ummi ta dawo da abinci da paracetamol and ibuprofen tana kallon ta tace “kitashi kisha magani seki koma ki kwantan”
Faseelat ta tashi zaune tana yamutsa fuska tai spoons biyu na jelop din pasta din ta dauki maganin tasha, duk ummi na tsaye na kallonta ta koma ta kwanta,
Ummi tadade tsaye tana kallonta sannan ta dauki plate din tafita,
Karfe 3:00 abba ya dawo, bayan ummi takawomishi abinci yaci yake bata labarin yadda sukayi da baba babba,
Ummi tace “ai gwara dakamishi maganar dan faseelat tayi nisa inajin yadda takeson yaran nan koni bataso haka “
Ana haka akaiwa abba sallama ya tashi ya fita, ganin sabuwar fuska dabe taba ganiba sukai musabaha da alhaji rabiu,
Sannan alhaji rabiu yace “nasan baka sanniba nine kanin mahaifin fahad yaron dake neman yar wajenka, nazo ne neman izini muzo neman aurenta “
abba yace”to alhamdulillah sede banine madaurin aurenta ba, don haka zan baka number din yayana shi medaura mata auren se kuyi magana dashi”
Alhaji rabiu yace “to masha Allahu badamuwa “
abba yabashi number din baba babba tareda yimishi kwatancen gidanshi,
Alhaji rabiu gidan baba babba yawuce sukai kicibus kofar gida dede shi kuma ze fita, bayan Sun gaisa yafadi abinda yakawoshi, baba babba yace “bamatsala zakuiya turowa amma zuwa gobe don zan danyi tafiya zuwa niger,”
Alhaji rabiu yace “alhamdulillah haka ma yayi insha Allah munanan zuwa goben”
Baba babba yace,”Allah yakaimu lpya “
Alhaji rabiu yace “da karfe nawa zamuzo?”
baba babba yace “zuwa de 10 to above”
Alhaji rabiu yayi godiya ya tafi,
Fahad bayan ya bar wurin alhaji yawuce gida ya kimtsa yafita aiki, zuwa 3 ya dawo tunda ya shigo gidan yaji gidan ba dadi, yanata kallon falon da yanzu amira nanan na wasa, tunanin Aisha yafado mai da yanzu tazo ta tarbeshi ,ya samu kujera ya zauna ya fiddo waya ya kira Aisha tana ta ringing taki dagawa, har ta tsinke ya ja tsoki besan haka aisharshi take ba sedaga jiya zuwa yau,
Ya tashi ya haye sama ya watsa ruwa yayi sallah, ya shiga kitchen ya hada ruwan tea ya dawo dashi ahannu da snack ya zauna yana ci yana latsa waya ya shiga gallery ya latso pics din faseelat yana binsu one by one yana kallo besan meyasa ba ko kallon pic dinta kadai yayi seyaji yana samun natsuwa sosai,
Aje tea din yayi dukda bawani abu yaci ba rabonshi ma da abinci tunjiya amma yakasa shan tea din saboda rashin kwanciyar hankali,
Yayi dialing number faseelat yanabin screen din da kallo yaji tana kashe abun yabashi mamaki jin wayarta kashe ya tashi yakoma bedroom yana aiki da system dinshi yaji yanajin bacci ya kwanta ,yana baccinshi har 4:30 sannan yatashi yana duba agogo yayi sauri ya tashi ya shiga shaf shaf yayo alwala ya dawo ya kabbara salla ,
aisha ko tasha kuka har tagaji, mommy de batako leko taba tunda batajin magana ta shareta,
ramlat tashigo dakin tazauna gefen Aisha tace “anty maganar da mommy ke fadamiki fa gaskiya ne, yanzu an waye kishi da kissa ake baa fitowa aita haukannan nide kinmun dede da kika jibgi shegiya Amman tunda kin rage zafi seki hakura kinga har mommy tayi fushi tafita har karki ,kiyi yadda tace kurum tun kafin asamu matsala dan kinga fayanzu har marinki yayi akanta nangaba Allah abinda yafi mari ze miki, kirika daurewa de hakanan”
Aisha tana kallonta tace “yanzunnan yaya har seya iya kwana da wata baniba ?”
Ramlat tace “namiji nefa, cabb bare yaya da dama can beda wata kunya sosai, kinagani agabanmu se ya rungumoki ko yamiki kiss fa ,aikede ai shaani kawai “
Ramlat tacigaba da dorawa Aisha darasi, tana budurwa amma ba makircin da bata iyaba don tafi aisha wayau,
Har marece fahad nata trying number faseelat amma bata shiga duk se hankalinshi ya tashi ya rasa me zeyi,
Itakuma faseelat jikinta ne yayi tsanani dan amai tarika yi ma daga baya, ummi duk ta rude ta dawo jinyarta,
Da daddare fahad yaje gidan alhaji suka zauna alhaji yafada mishi yadda sukayi yace “yanzu de in Allah yakaimu gobe zamuje nida su alhaji yunus “
Fahad yace “Nagode daddy ga kudin nama cirosu daga banki one million kudin neman auren se 200,0000 taka “
Alhaji yace “to godiya nake insha Allah goben zan nemeka idan mundawo “
fahad yatashi yafita cikin farin ciki, koda yakoma gida yata kiran faseelat amma akashe itako wayar har ta mutu saboda rashin caji da bata saka ba,, ya hakura ya dena kiran yanajin ba dadi dan yariga ya saba da jin muryarta, ya danyi aiki a computer shi ya kwanta da niyyar gobe zeje gidansu faseelat tunda wuri ko hankalinshi ya kwanta, yadade da kwanciya amma yakasa barci, gabadaya desire ta hanashi baccin he’s missing Aisha yanata juye juye har kusan 2 nadare yatashi ya jawo laptop dinshi ya cigaba da aiki saboda ta dauke mai hankali,
Wan safe da karfe 10:30 su alhaji rabiu su ukku sukaje nemawa fahad auren faseelat, baba babba ya karramasu sosai sannan suka mika mishi kudin a leda 1 million cifff, batare da alhaji yasan adadin kudinba yace “faseelat deba budurwa bace don haka base kunkara ba kanku wahala ba munbashi ita idan kun shirya nan da 1 month ma seayi biki “
Alhaji rabiu fuska a sake yace “shi yaron yace bayason amata komi zeyi duk wata hidima, inde babu damuwa alhaji munason a ragoshi ya koma 3wks “
Alhaji babba yace “ba matsala mu ashirye muke Allah yakaimu nanda 3wks din Amman muma iyaye zamuyi mata abunda yakamata ace munyi”
Su alhaji sukayi godiya aka rufe taro da addua aka tashi bayan ansaka rana nanda 3 wks,
fahad ko se 10 yatashi ya kimtsa cikin sauri ya kama hanyar gidansu faseelat yana kan hanya ne alhaji rabiu ya kirashi danhaka ya juyar da motar zuwa gidan kawunnashi,
Yana zuwa yakirashi alhajin ya fito a harabar gidanshi, suna kan resting chair alhaji yace “to alhsmdulillah yanzu de faseelat ta zama taka, munje munyi magana da iyayenta sunbaka ita kuma sunsaka ranar aurenku nanda 3wks”
Fahad ya rumtse ido yanajin mugun dadi na ratsa dukkan gabar jikinshi, ya bude ido ya Saki kayataccen murmushinda besan yayi ba ya kamo hannun alhaji yace “Nagode daddy I’m very proud of you ,naji dadin wannan labari sosai da sosai “
Ya saki hannunshi ya fara shafar sumar kanshi da ya saba,
alhaji yace “badamuwa danbaba, yanzu seku fara shiryeshirye kafin lokacin “
fahad yayi zumbur ya tashi tsaye yanzu ba abunda yake son gani sama da faseelat yafada mata wannan gud news din, ya kalli alhaji yace “daddy zantafi semunyi waya thanks you so much”
alhaji yayi murmushi ganin irin farin cikin da fahad ke ciki yace “welcome son “
fahad ya juya ya fita daga gidan ya shiga mota ya kama hanyar zuwa gidansu faseelat cikin farin ciki.
Yana zuwa ya bude mota ya fito don samun yaronda ze tura yakira mishi ita don haryau wayarta kashe take,
Sega Mubarak yafito daga gidan fahad yayi sauri ya rufe motar ya karasa kofar gidan yacewa Mubarak yakira masa faseelat,
Mubarak yace “yaya batajin dadi tunjiya bata lpy “
Fahad ya zaro ido ya dafe kai yasan bakomi yaja ba se dukan da Aisha ta mata, ya dafa Mubarak yace “tana gidan ne? “
Mubarak yace “eh dazun suka dawo daga asibity “
Fahad yace “to kashiga kacewa ummi fahad zeshigo gaidata kaji? “
Mubarak ya gyada kai ya juya cikin gidan, fahad ya fitarda iska daga baki ya cusa hannaye cikin aljihun wandon,
Mubarak yashiga ummi na cikn aikinta na yau da kullum Mubarak yafada mata abinda fahad yace ,ummi tace “to jira karka fita bari na saka hijab na kimtsa waccan tukunna, aibawani gaidani dayazoyi faseelat de yazo gani yazo duba barnar da yayi “
Ta juya ta shiga daki ta sako hijab dinta ta shiga dakin faseelat tana barci ko hijab da suka dawo daga hospital bata cireba ta kwanta,
ummi tafita tacewa Mubarak “jekace ya shigo “
Mubarak yafita har lokacin fahad na tsaye yace mishi ya shigo, fahad ya taka zuwa cikin gidan ,
Da sallama ya shiga ummi tafito ta amsa ta masa iso zuwa dakinta, tana kara kallon kyawunshi ya shiga ya zauna akasa ya tankwashe kafa daya dayar kuma ya tsaidata cikin sanyin murya yace “ina wuni”tareda sunkuyar da kai,
Ummi tace”lpya lau ya iyali? “
Yace “alhamdulilah ya me jiki? “
ummi tace “dasauki “
Yace “Allah yakara sawwakewa, ayi hakuri ummi haukansu ne na mata bana kusa lokacin da abun yafaru “
Ummi na kallon hannunshi dake nannade da bandage tace “ai bakomi Allah ya kyauta gaba “
Cikin jin nauyi yace “zaniya ganin faseelat din? “
Ummi tace “eh bismillah “tatashi ta fita,
ya tashi yabi bayanta,
Ummi ta shiga dakin faseelat ta dan bubbuga gefen gadon faseelat ta bude idanunta da sukai ja ta kalli ummi, ummi tace “ga fahad nan ze shigo ku gaisa “
Ummi na rufe baki fahad ya shigo dakin faseelat tafara kallonshi daga Kasa zuwa sama tana akwancen yana sanye da white shirt da golden trouser,
shima kallonta yake tunda ya shigo room din fuskarta kadai yake iya kallo duk tayi ja saboda kuka da yar ramar datayi daga jiya zuwa yau,
Ummi na gefe, fahad ya tsaya daga nesa yana kallon faseelat baruwanshi da ummi da takafa ta tsare yace “cutie ya jiki? “
Tadan Saki murmushi kawai yace “I’m sorry “
ta lumshe ido tabude alamun OK,
ganin ga ummi tsaye yace “ina wayarki I have call you several times “
murya dishe tace “banida chargy “
yace “alright Allah yabaki lpya “
yacewa ummi “Allah yabata lpy “
Ummi tace “amin “
Ya juya yafita,yana fita ummi tace “Ashe de faseelat bakida hankali wani lokaci idan kikai abu se inga kamar kece yar farin, inba rashin wayau ba ki kwasa ki tafi gidan ta dankina sakarai? To Allah yatemakeki dan wlh inda nice ko fuskarki bazata ganu ba “
Faseelat lumshe ido kawai tayi, kashi biyar na ciwonta ya tafi taga habibinta da kuma gaskiyar da ummi ta gano,
fahad nashiga mota ya dauko power ban ya ba Mubarak yakaiwa faseelat tareda bashi 2000, Mubarak ya amsa ya shiga cikin gidan,
Yashiga dakin faseelat ummi nata surutu ya mikawa faseelat power ban din, Ta mike zaune dasauri kamar ba Marar lpy ba ta dauko wayarta ta jona chargy, ummi tace “hmmmm Allah ya kyauta “tatashi tabar dakin saboda takaici,
Faseelat takoma ta kwanta bayan ta saka chargyn danba warkewa simul tayi ba,
Fahad bebar kofar gidanba ya dauki wayarshi yakira daya daga cikin yaran dake aiki a plaza dinshi yace mishi yana bukatar engine good quality kuma ai masa full tank, da 2 cartoons of peak milk ,2 cartoons of maltina kwalin holandia ya fadawa yaron address din gidnsu faseelat,
sannan ya tada mota yana tuki Ahankali yana ta tunanin faseelat ya kama hanyar gidan mommy.