NOVELSUncategorized

KWARATA 50

???? —— 50

         Cike da farin ciki ya juyo , amma me ? Sai yaga Jiddah tsaye ta zarge hannuwan ta , wayoyinshi ya ɗauka sannan ya tunkaro ta dan ta hanyar da zaibi ya wuce ta tsaya , cike da kissa tace haba Yaya daga dawowa kuma ina zakaje haka da daren nan ? Inda raina yake so zanje , haba Yaya gaskiya haka an shiga haƙƙina , kallon raini wayau yayi mata tare da cewa a haba ? Umm gaskiya
ina so mu kwanta mu huta duk gajiyar jirgi tana damuna , ta ƙarasa maganar tare da san kwanciya a jikinshi , zamewa yayi da sauri ya karkata ya fice daga ɗakin.

       Ni kuma bayan nayi sallah isha’e tunanin duniya yazo ya tokaremin zuciya , ikon Allah wato ita rayuwa haka take , Mamy bata taɓa tunanin mutuwa ba kwata ² a “yan wa’annen lokuta , hawaye ya gangaromin daga cikin idona nace shikenan anyi zamaninta an gama , duk saɓawa ubangiji da tayi saboda samun duniya kuma Allahn ya yaddar mata ta samu kuma ta tara , amma ta tafi ta barshi domin ansa kiran mahaliccin ta , 

      Me ake ma haɗama a duniyar ? Bayan babu wanda yazo dashi kuma babu wanda zai tafi da komai , anan aka samu kuma anan za’a tafi a barshi , haba mata meke ruɗarmu a cikin duniya ?

    “Yar uwa ko kunyi yar jejeniya da mala’ikan mutuwa ga lokacin da zaizo miki ? To kisani mutuwa bata sallama bata jira sai kin gama sharholiyarki wallahi zata iya riskarki a duk yanayin da kike ciki , ba ruwanta da kina aikata alheri ko akasin haka , ya ubangiji ka karɓi rayuwarmu muna masu aikata alkhairi ka sada mu da aljannar ka dan darajar fiyayyen halitta S. A. W , am3n.

    Gadai Mamy nan an tafi neman duniyar amma an haɗu da mala’ekan mutuwa a hanya , kai ubangiji kasa muyi kyakkyawan ƙarshe , ko waye ma ya haɗa Mamy da wannan ibilishin ?

      Ƙarar wayata naji a gefena a firgice na juya inda take na miƙa hannuna na ɗauko , lambar Dikko naga ta bayyana a saman screen in wayata , ajiyar zuciya na sauke da sauri na ɗauki wayar tare da miƙewa tsaye na karata a kunnena ,

     Sai sauke wani irin wahaltaccen numfashi nakeyi mai nuni da nasha wahala , cikin muryarshi maisa natsuwa yace har kin fara bacci ne ? Kukana ya ƙara kwacewa ban bashi ansar tambayar shi ba nace shine ka tafi ka barni…. ?

       Murmushi yayi mai sauti cikin murya mai kashe jiki yace in dawo ne ? Da sauri nace Eh , dariyar mugunta yayi yace An mata taji a jikinta tou fito gani nan ƙofar gida , da gaske ? Na tambayeshi sai kin fito zaki tabbatar da haka , da sauri ya ajiye wayata nayi waje da gudu ,

    Dikko yana tsaye ya jingina da mota ya rungume hannayenshi a guje na isa inda yake tsaye da niyar in rungumeshi , a wayance ya matsa daga saitina ni kuma na ɗan sassauta gudu na saboda na iso ina ganin ya kauce nima na basar na rumgumi mota ,

      Kauda kanshi yayi gefe tare da cewa ya kike ? Nima juya mishi baya nayi ina wasa da ƙasa da babban ɗan yatsana na ƙafa nace aini dana san kaine ma da ban fito ba , buɗe mota yayi ya shiga yana cewa ai dan nasan dama idan nine baza ki fito ba shi yasa nace miki ga Dikkonki ya dawo , ya ƙarasa maganar a daidai lokacin da yake zama a mota , 

      Juyowa nayi dan a tunani na tafiya zaiyi , murmushi yayi yace ba tafiya zanyi ba banajin daɗin tsayuwar ne shigo mu tafi , da sauri na zagaya na buɗe mota na kame a gaba , ina rufe murfin motar ya taka motar muka shiga gidan dawakan shi ,

      Kusa da motar daya bani yayi parking , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙe sitiyarin da duka hannayen shi biyu yayi miƙa cikin yanayin gajiya tare dayin hamma yace An mata na gaji wallahi yayi maganar cikin murya mai ladaftar da zuciya ,

        Murmushi nayi amma banyi magana ba , dan idan inajin muryar Dikko sai inji tawa wata iri shi yasa ban cika magana a gabanshi ba , wayarshi ke ringing dan haka ya ɗauketa daga gefenshi daya ajiye yana cewa tou fa , karkace kaina nayi ina kallon fuskar shi yayin da hasken wayar ya haskaka fuskarshi dan duba mai kiranshi waya ,

      Ɗan kallo yayi mai kyau yayin da idanuwan shi ke duba daga saman wayar zuwa ƙasa , zai ɗauka yace nifa bana san kallo da yawa , ki daina kallona haka nan tunda bakya so na , a dai² lokacin daya ɗauki wayar yana cewa inajin ka ,

      Tou haka yace kuma ? A , a gaskiya bana kusa kawai kuje idan na dawo Ashiru zai tattaro minsu , ba komai fa kawai kaje abunka , to yayi kyau , ya kashe wayarshi ,

    Bayan ya gama wayar ya juyo ya fuskance ni sosai yace An mata mi yasa kika bar mota tayi datti bakya hawanta ? Nace haka nan , hmm tunda bakyasan Dikko motar da ya baki ma bata burgeki ko ? Nace tana burgeni mana kuma ai nahau ta ma , Dikko yace haba An mata ai da kin hau wannan motar da naji a jikina , zansa a wanketa a daren nan ko baki so na ki hau motar nan don Allah inji daɗi kuma ko bakida inda zakije gobe kiɗan hau ta ,

    Nace tou , yace yawwa ngode sosai , bayan wani lokaci kuma ya sake kallona yace An mata wai dan Allah mi yasa kike da kunne ƙashi ? Mi yasa bakyajin magana ? Nace me kuma nayi yanzu ? Bama kisan abinda kikayi ba ko ? Nace Eh , jinjina kanshi yayi yace yanzu ina amfanin irin rayuwar da kika koyama kanki don Allah ? Kullum baki da aiki sai ɗaukar tsiraicin mutane ,

     Idan an taroki nan sai ki koma nan kina rayuwa kamar baki da kwalwa a kanki , shiru nayi banyi magana ba , cikin ɓacin rai yace ki kiyayeni ranar da nima zan miki tsirara in miki irin abinda kike ma mutane , bana san ɓacin raina akan ki saboda fushi na baida kyau idan har nace zanyi miki hukunci dai² da irin abinda kike aikatawa lafiyayen duka ɗaya zan miki ki mutu , cike da ɓacin rai nace tou ni yanzu waye kuma nayi ma vidio ,

         Ƙanƙance idanuwa yayi yace Baban Mardiyya dama shine baƙin cikin da kike cewa zaki dasa mata a zuciya ? Ki bari bana so , nace tou , sake maimaitawa yayi cewa bana so ׳ idan kuma kuma kika sake zakiji babu daɗi , nace tou , 

      Hararata yayi cikin salon so , yace to me kuma akayi miki kikayi kuka naga fuskarki duk sai a hankali , ban bashi ansa ba na canja maganar da tambayarshi wanda ya faɗa mishi nayi ma Baban Mardiyya vidio ? Cikin lallausar murya yace babu ruwanki da wanda ya faɗamin idan nace bana san abu kawai ki bari idan baki so mu ɓata , a ɗan zuciye nace tunda baza ka faɗamin ba bari in tafiyata , hannuna ya riƙo yace yi haƙuri An mata , tou faɗamin , yace ni bana san ɓacin ranki Al ‘Ameen ne ya faɗamin , gaskiya An mata Al ‘ Ameen bai jitu dake ba kullum burinshi ya nemo aibunki ya faɗa a gidanmu duk da kince bakya so na ina so ki zama mai mutunci a idon “yan uwana da kuma iyayena kinga idan aka tashi bada labari cewa za’ayi ƙawar Dikko bata da hali mai kyau ni kuma kinga ai bazanji daɗi ba ko ? A kunyace nace Eh , yace tou da Allah ki baryin abu mara kyau duk ki barbaɗawa “yan baƙin ciki yaji a ido ya ƙarasa maganar yana kashe min ido ɗaya na dama , nace tou ,

    Tada motar yayi yana cewa bari in ajiyeki haka nan kar ace kin ɓace , a dai² lokacin daya fara tafiya a hankali , yau da natsuwa yakeyin tuƙi yana ƙara jamin kunne na daina shiga sabgar kowa nayi rayuwata ni ɗaya idan banji bari ba kuma zanji hoho a jikina , a ƙofar gida ya ajiyeni yana cemin idan Allah ya kaimu gobe zai dawo , nace tou Allah ya kaimu ya kuma hutar da gajiya , ya ansa da amin ni kuma nayi cikin gida da gudu , murmushi yayi ya wuce cikin farin ciki ,

Yau zuciyarshi ta ƙara tabbatar mishi da akwai soyayyar shi a zuciyar An mata tunda har tasan idan ya daɗe bai zo ba idan yazo zata zo da gudu ta rumgume shi , kuma yace ko tana so ya dawo tace Eh , babu abinda ya kawo haka idan ba soyayya ba , yau kam yana cikin farin ciki.

      Washe gari sai 9:30am na fita daga gida domin zuwa wurin jana’izar Aunty Mamy dan naji ance 10:00am za’ayi mata sallah domin kaita gidanta na gaskiya , doguwar hijabi nasa mai hannu ta saukar min har ƙasa mai ruwan jinin kare , dake ina da haske sosai sai hijabin ta matuƙar martabamin fuskata , babu abinda na shafa domin yau ranar ta jimami ce , makullin mota na ɗauka nayi gaba abuna ,

      Ina fita naga su Amisty suma sunsha nasu hijaben cikin mota suna tahowa , ganin zan shiga gidan dokuna yasa Amisty tayi parking dan ganin abinda zanyi , a natse na shiga da jakata a hannuna saboda riƙon wayoyin zaimin yawa a hannu ,

       A gidan na iske Dikko da kayan training jikinshi ya cire takalma rufaffi ya jiye a gefenshi ya naɗe kafafuwan wandonshi , silifas ne a ƙafarshi ɗorowo { Yellow } masha Allah shine abinda na furta lokacin da na kalli ƙafarshi , hutu dajin daɗi ya tabbata a gareta har wani hurhurun haske takeyi tsabar tasha madara ta ƙoshi “yar gayun ƙafa da ko mai ba’a shafa mata sabar hutawa , ga wani gargasa ya sauko saman ƙwaurinshi “yan yatsunshi masu kyau dan dani keda ƙafafuwan shi babu abinda zaijamin saka wasu takalmi idan ba irin silifas in daya saka a ƙafarshi ba domin yafa burge ,

       Yana gani na ya tashi tsaye ya tare da ɗauko takalman daya ajiye a gefenshi ya tun karo inda nake yana cewa ina zaki tunda asuba haka ? Nace rasuwa akayi , Allahu Akbar Allah Allah ya sawaƙe , nace ba rashin lafiya ba mutuwa , yace Ey ai na sani ina nema ma ahalin gawar sauƙi ne , Allah ya kiyaye hanya nace amin , biyoni yayi bai sake magana ba shima ya nufi wurin motarshi ya buɗe but in mota ya watsa takalman ya rufe ya shiga motarshi nima na shiga wacce ya bani wanda yau itace ranar farko da zan fita da ita ,

      Tasha wanki tayi kalar ɗaukar hankali , saida na shiga harna sauko daga inda na ajiyeta shima ya sauko yana cewa mintuna 15 na baki ki dawo , tsayawa nayi nace ya kuma minti 15 sai kace kai ka aikeni ? Ban aikeki ba amma wallahi kika wuce lokacin da nace saina ɓata miki rai za’a faɗamin lokacin da kika dawo ai , haba wai mi yasa kake yin haka ne ? Ki wuce lokacin da nace miki sai kiga dalili , cikin hayani nace aure na kakeyi da zaka tsaramin yadda zanyi rayuwata ne ?

Murmushi yayi ba tare daya kalleni ba yace ai da ina aurenki babu abinda zaisa na barki kije gaisuwar wacce aka kwakwale ma ido tirr ya ɓata baki tare da ficewa ya barni cikin mota kamar sakarai.

        Da sauri na kalli agogo naga 10:19am , kenan zan dawo gida 10:34 ? Gashi kuma har naci minti 1 , ina da sauran minti 14 yaushe naje har nayi musu ta’aziyya na dawo ? Tsoki nayi kamar kar naje wata zuciyar tace kije kawai kina ɓata lokaci ,

        Da gudu na fito daga gidan kamar zan tashi sama , su Amisty suka rufowa motar baya dan a tunaninsu Dikko ne a ciki , lokacin da suka fito bakin titi tuni na ɓace musu ko ƙurata basa gani , hanyar da motar tabi ta wuce suka gaza gano ta ina motar tabi ta wuce ,

      Da nasan haka hawan motar nan zai jawomin tashin hankali wallahi da ban hauta ba , ni kuma na hauta ne kawai dan Dikko yayi farin ciki saboda tayi wata huɗu da “yan kwanaki da bani ita amma ban taɓa hawanta na fita sai yau ,

      Ina isa ƙofar soro har an dawo daga kai Mamy dandazon mutane kamar ƙasa gaskiya Mamy tayi jama’a a hankali na shiga mutane suka riƙa darewa suna bani hanya duk wanda ya kauce saiya bi motar da kallo kowa ya ƙagara yaga Dikko ya fito dan nace muku lokacin daya siyo motar anyi ihunta a gari duk garin katsina wannan motar Dikko kaɗai keda ita ,

      Daga Qerau zuwa ƙofar soro minti biyu kacal ya kaini shima dan nabi a hankali dan motar tana da tafiya sosai , nabar gida 10:20 , na iso ƙofar soro 10:22 harda parking da nayi , manyan mutane suka fara yayyaɓe motar dan cikawa Dikko sheda ba’a iya gane waye a motar saboda gilashin motar duhu gareshi , wa za’a gani ta fito daga motar ? Ɗiyar ɗan caca ,

     Tunda na fito kallo ya koma sama a dai² lokacin dasu Amisty suka iso , banbi takan kowa ba na ɗauki jakata na wuce jama’a suka bini da kallo yayin da surutu ya fara tashi ƙasa² danni taron mutane baya hanani tafiya kuma bai ruɗani bai firgitani haka kuma yawansu basa gigitani kuma banayin tafiya inji kamar zan harɗe na faɗi ,saida nakai gaf da zan shiga gidan Mamy naga Bello , kallona yayi ƙasa da sama yace wai Sultana ce haka bakya ko gane mutane ? Murmushi nayi tare da cewa ya za’ayi lafiya ta kasa gane mai bata damuwa ? Magana ce na faɗa masa ina faɗin haka na shige abuna na barshi da dogon nazari ,

         Gidan mutuwar sai koke ² akeyi yayin da tabarmin zamar gaisuwar suka rarraba kashi ² , dangin Mamy da tasu , sai dangin mijinta makota sai kuma wasu lafiyayun karuwai suma sunyi nasu mazauni , ahalinta na farawa ta’aziyya sannan “ya “yanta , sai dangin mijinta , ko inda karuwan suke ban kalla na miƙe zan fita wata mata tacemin nan zaki zauna ke ?

     A dai² lokacin dasu Amisty suka shigo gidan , miƙewa nayi banyi mata magana ba , tace ke Sultana take ko wa ? Ta tambaya , aka ce mata Sultana , tace nan ne mazaunin mu , juyawa nayi da niyar feƙe mata uwa saidai banda isashshen lokaci dan ina so nayiwa mijin Mamy ta’aziyya , ina ƙoƙarin fita matar ta biyoni ta cakumoni ta baya tana cewa akace ina zakije ? Baki ga inda karuwai suke zaman gaisuwar su ba ? Ban mata magana ba na fiddo wayata daga cikin jakata nace ki duba zaki ga an rubuta Sultana itace lambar wayata ,

       Kallona tayi sosai kuma kome tayi tunani Oho sai ta sakarmin hijabi ba tare data anshi wayar ba , ɗan gajeren murmushi nayi da gefen bakina na juya na fito ba tare dana sake mata magana ba , a ƙofar gida nayi ma mijin Mamy ta’aziyya da “ya “yanta maza Bello kuma sai kallona yake , murmushi nayi mishi na miƙe shima ban mishi magana ba ,

       Tunda na fito daga barandar ƙofar gidan Mamy ake nunani nice nazo a motar Dikko ,  wasu kuma na cewa ni karuwa ce amma meya haɗashi dani bayan baya harkar mata , wasu kuma na cewa ɗiyar ɗan cacar nan ne shege mashayin giya ya haifo wannan kyakkyawar , wani yace ai yarinyar shegiya ce tana burgeni domin tanayin karuwancin cikin tako ne , kowa dai da abinda yake faɗa akaina abundai babu daɗin saurare ,

        Murmushi mai ciwo nayi yayin dana tunkari mota ta , wato shi karuwanci babban tambari ne da baya gogewa har “ya “ya da jikoki kayi ƙoƙari ka zama na gari domin gori akan karuwanci ciwo gareshi yau mutane da sun san zasu taɓani su kwana lafiya inajin dasai sunci ubana kafin na fito , mota na shiga na karce duk wanda bai ga zuwa na saida yaga fita ta ,

      Wuta ² na iso anguwarmu , a ƙofar gida naga motar shi , lokacin 10:33am kai tsaye inda na ɗauko motar na maida ta , lokacin dana fito ban sameshi ba kenan yazo da kanshi yaga lokacin da zan dawo ? Da sauri na wuce cikin gida dan inada abinda zanyi ,

       Wuri ɗaya naje da mota amma yau gari magana ta kawai akeyi wata karuwa take tare da ɗan gwamna ta gama dashi ta tsafeshi har ya bata motar daya siyo ta miliyoyin kuɗi , duk inda ka saƙa a gari Sultana ɗiyar ɗan caca kafin wani lokaci kuma hotuna na sun fara yawo a social media da motar dana hau ɗiyar ɗan cacan da yafi ko wane ɗan caca sa’ar rayuwa ,

      Al ‘ Ameen kuwa tuni yaje ya samu mahaifiyar Dikko ya faɗa mata halin da ake ciki dan yaga Dady yayi sanyi , Momy kuwa tayi zafi har ta wuce tafasashshen ruwa , matar Dikko data zo gaisheta itama ta cika ta kawo wuya , tace ma Al ‘ Ameen ya bari Dikko ya tafi a kamo Sultana zata ƙagi azabar da zata bata , Al ‘ Ameen yace ai ko yanzu ina iya kawota , Momy tace kudai bari yabar katsina dan koni baya so kamar yadda yake san mayyar yarinyar nan ,


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


        Wane dalili yasa Dikko ya matsamin nahau motar daya bani yau ? Tabbas dan yasan za’ayi magana ne kuma haka yake so dama kowa yasan ina tare dashi shima yana tare dani dan idan babu wata alaƙa dani dashi mai girma me zai haɗani da motar shi…. ?

        Yau kuma idan akwai wanda yafi Jiddah baƙin ciki bai wuce Momy ba kuma sun tanadin shaglin partyn wulaƙanta ni , Jiddah bata ƙara jin takaici ba saidai Dikko ya tura Ashiru ya maida ita gida , tace bata komawa , koda Ashiru ya faɗawa Dikko tace bata komawa cewa yayi ya barta idan ta gaji ta koma da kanta ,

     Tunda naje gidan rasuwa ban sake komawa Dikko ya hanani , sai yau sadakar 3 yace inje amma yau mintuna 10 ya bani , Umar ya aiko ya kawomin kuɗi in bada sadaka idan naje , kuma har yanzu yana gari bai tafi ba saboda kullum rana muna tare , 

       Ina ta shiri zan fita saiga Ummu Affan wai tazo min gaisuwa , bayan ta gama ta’aziyyar tacemin ashe kuma sai kikayi mota ? Murmushi nayi ban bata ansa ba naci gaba huɗɗar gabana kenan ba gaisuwar ta kawota ba dan kawai taji labarin mota , saida na gama shirina kaf nace tou zan rufe ɗakin , tace tou bari in tafi idan kika dawo na dawo , fita tayi nima na fita na rufe ɗakin .

      Ina fita naga Baba zaune a tsakar gida duk yayi wani kalar ban tausayi , nace Baba baka lafiya ne ? Kallona yayi yace wallahi Mamana gabana keta faɗuwa , nace miya faru ne ? Yace nidai nayi miki alƙawari nabar caca har abadan duniya nace Eh Baba , yace tun daga ranar da mukayi maganar dake da na saka motarki a caca wallahi ban sake zuwa koda wurin caca ba haka duk abokai na bana tare dasu tun ranar ban sake shan giya ba haka kuma ban sake neman mata ba ,

     Nace to yanzu meya faru ne ? Yace abun ya dameni ne tun ranar da nayi wannan maganar idan na kwanta bacci sai inga wani mutum tsaye a gabana yana cewa idan baka koma caca ba ajalinka ne zaici gaba da fuskantar ka , ka koma caca kaci gaba da neman mata kasha giya idan ba haka ba zamuyi maka kisan wulaƙanci domin zaka lalatamin duk wani tsari na ,

     Shine nace bazan koma ba , jiya itace rana ta ƙarshe daya bani kuma yace yau idan banje gidan caca ba wallahi kasheni zaiyi , murmushi nayi nace Baba kenan wannan ai duk shirmen bacci ne , yace Mamana ba shirme bane da gaske ne dan har sunanki naji an kira a mafarkin yace shine ya toshe miki rayuwa wai ya rufe ƙwalwarki a bakin mataccen kwaɗo , dariya nayi sosai nace ji wani magana Babana ni na tafi saina dawo ,

       Saida na fita daga anguwarmu zuciyata ta fara tabbatarmin da ba shirme bane , maganar Baba abin dubawa ce da tunani iri ² na isa gidan rayuwa , ban jima ba na fito bayan na basu kuɗin da Dikko ya bani duka ban rage komai ba ,

      Jiki a sanyaye na dawo gida ban samu Baba ba , dan haka na shiga ɗakina kaina sai juyawa yakeyi , wayata na ɗauka na kira Dikko kaf na rattafa mishi abinda Babana ya faɗamin , yace baya nan yaje kano amma idan yayi magrib zai taho in Allah ya yadda , nace tou don Allah daka dawo kazo wurina , yace insha Allah An mata ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkairi , nace tom saida ya kwantarmin da hankalina sannan ya kashe wayar ,

       Ina gama waya da Dikko wayar Mamy ta fara kuka , da sauri na ɗauki wayar ba tare dana san mai kirana ba , ina ɗauka nace Hello , mai magana a waya tace Mamy na samu duk bayanan da kike buƙata , kila bata san Aunty Mamy ta rasu ba , akwai wani kwaɗɗo da aka rufe gawarshi a kwalbar lemu kuma gawar kwaɗon saida aka zuba kwata a cikinta , akwai bokan dake gyara aikin kullum amma yace abu ya warware komai zai iya faruwa tunda har Binna ya fita a caca ,

       Anyi ƙoƙarin juya al’ƙamin tsafi ya sauka akan yarinyar da kike magana bokan yace sai ta tsallake sallar isha’e da asuba idan har batayi su ba tana dai cikin tsarki ba jinin al’ada ba itace zata maye gurbin ubanta , yarinyar tana da addu’a gaskiya kuma bata wasa da sallah , kiyi sauri yanzun nan suka kira Binna zasu kashe shi…. Kwalbar da akayi asiri gata a hannuna , amma kiyi gaggawar zuwa gidan…….. Ihun matar naji ina ta hello ׳ amma cikin wahaltacciyar murya tace kiyi gaggawa zuwa bayan gidan caca acan za’a kashe Binna ni kuma zanci da sauran….

       A firgice na fara kiran wayar Dikko amma sai akacemin a kashe take , wayar Babana na fara kira sai ringing take amma ba ‘a ɗauka , wayyoni Allahna na sake faɗawa wata rayuwar , me yasa Dikko ya kashe wayarshi ? Su waye suka kirashi ya fita ? Me akayi ma wacce nake magana da ita a waya ? Wayyo Allahna rayuwa me yasa zakiyimin haka ne …..⁉ ????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button