KWARATA 48

???? —— 48
Ni naja motar muka tafi Mamy kuma tana gefe na tana waya , dama ta shigo tanayin abunta kuma har yanzu bata gama ba , hanya na iba ɗoɗar saboda ta nunamin hanyar da zanbi da hannunta ta kuma nunamin kawai in tafi miƙe kar in kwanta ,
Munyi tafiya mai nisan gaske sannan Mamy ta gama waya , sawa tayi nayi parking ta anshi tuƙin motar mukaci gaba da tafiya har muka iso inda muka zo Mamy bata sake magana ba ,
Get in gidan buɗe yake dan haka muma muka samu damar antayawa daga ciki , tun kafin Mamy tayi parking Allah ya nunamin Al ‘ Ameen , haka nan naji gabana ya yanke ya faɗi gaba ɗaya sai guyawuna sukayi sanyi nama kasa fitowa daga cikin motar , ni kaɗai nasan Al ‘Ameen Mamy bata sanshi ba , sannan kuma numbershi da ta saka a whatsapp inshi ba shine ba Dikko ne ,
Dogon nazari na shiga to me ya kawo Al ‘ Ameen wurin nan kuma ?Tunani nayi sosai firata da Mamy ta daren jiya ta dawo min , to duk yadda akayi yarinyar da mukayi faɗa da ita kenan tana da alaƙa da Al ‘ Ameen ? Na shiga tunani sosai amma na kasa fahimtar ya abun yake ,
Mamy kuma fita tayi daga motar tabar harabar gidan ta koma ƙofar gida , bayan wani lokaci kuma ta dawo ita da wata matashiyar yarinya shekarunta da kamanunta duk bana iya ganewa saboda ta saka niƙaf ta lulluɓe fuskata , ciki suka wuce ta barni zaune a mota kamar mage na dakon tsuntsu ,
Shiru² babu Mamy ba labarinta , ni kuwa sai sassada kai nake ƙasa dan bana so Al ‘ Ameen ya ganni , gashi ina so na fita nima na shiga amma dole banda yadda zanyi saboda Al ‘ Ameen zaune yake kuma baida alamar tashi ,
Har su Mamy suka gaji da daɗewarsu suka fito , yarinya bata shigo motarmu ba ficewa tayi Mamy kuma ta shigo mota taja muka tafi , saida mukayi nisa nace mata wai mutumin dake zaune a wurin nan shi kuma waye ? Ko gadi aka sashi ne ? Mamy tace ƙanin matar Baban yarinyar ne , jinjina kaina nayi sannan nace tou wace ce da niƙaf kuma ? Tace “yar uwarki ce da kika ce na farauto ,
Nace Hamida ? Tace ɗiyar ƙanin Babanki ce , dariya nayi sosai nace tsakaninki da Allah tace wallahi kuwa , tou ya akayi kika farauto ta da wuri haka ?
Mamy tace wallahi ina zaune gidana Allah ya kawo minsu ita da ƙanwata , ashe ita ɗiyar ƙanin baban naki aure zatayi ? Mamy ta tambayeni nace mata Eh Safiyya ce zatayi aure , Mamy tace to ai kinsan “yan matan zamani sun saka kansu ƙarya basa haƙuri da abinda iyayensu sukayi musu , basa da gashin wance sai suce dole zasuyi kitso irin nata ,
Ƙanwata tacemin tana naima wa ƙawarta aiki a ƙarƙashi na , na taimaka wannan ƙawarta ce zatayi aure iyayenta basuyi mata wani abun kirki ba na kayan ɗaki , shine ta kawota wurina ko zan taimaka na ɗauketa aiki ita kawai talabinjin in bango da kayan sautin ta take so ta siya sai labulaye masu tsada ta gyara palon ta dan bata so ƙawayenta su raina mata gidan aurenta ,
Saina tambaye su bikin kwana nawa ya rage ? Shine tacemin wata 3 nace tou yarinya banda abinki wata3 taya zaki samu kuɗin da zaki sayi talabinjin in bango da kayan sautinta ? Kona ɗaukeki aiki na baki kuɗi da yawa a wata baifi na baki albashin 3k ba , kinga 3k sau wata3 ya kama 9k ba talabinjin ba ko labule bazai siya miki ba ,
Tacemin haka ne , tou bayan nayi bincike naji daga inda ta fito kuma naga kina nemansu da karuwanci ruwa ajallo yasa nayi mata tayin karuwanci bayan munyi ciniki dashi baban ƙawar faɗan taki akan zai bayar da dubu hamsin , nayi ² ya ƙara wani abu akai umm lusarin a haka ya tsaya , bayan mun gama ciniki dashi ya kafe kai da fata haka zai bayar ,
Kodai yane tunda na samu an farketa shikenan kinga ta tsaya zaman jiran talabinjin dan ubanta saidai kawai taji a salansa tamin hauka akan na bata kuɗi ga vidio na ɗauko ta ƙarasa maganar tana dariya , nima dariyar nayi tare da cewa yaro inya iya ruwa ai bai iya laka ba , dariya Mamy tayi sosai tare da tambayata meye ruwan kuma miye lakar ? Nace zancen sai wanda ya kwana a bakin gabi…. Mamy tace ina ne gabi kuma ? Nace wata matattara ce ta karuwai dake can wajen gari !
Haka dai mukayi ta taɓa fira har muka iso ƙofar gidanmu , bayan Mamy tayi parking ta fara kiran wayar Maman budurwar Dikko da mukayi faɗa da ita wacce bayan an ɗauki wayar naji Mamy tana cewa da Allah Momy ko Mardiyya tana kusa ne ? Eh tana nan Mardiyya kizo anyi miki waya ,
Tazo ta anshi wayar , bayan gaisuwa Mamy tace mata kin gane ɗiyar ɗan caca wacce kukayi faɗa da ita a motar saurayinki akan haryar ku ta zuwa Abuja ? Wacce bayan kunyi faɗan tayi zuciya ta barku a hanya ta samu mota ta dawo katsina kin tuna har kikace mata jahila daƙiƙiya kidahuma jaka kin tunota ? Tace Eh na ganeta ya akayi ne ? Mamy tace yawwa dama cewa tayi ki riƙe wayar Mamanki a hannu ki duba ta whatsapp zata turo miki saƙon ta tashi daga jahila ta koma ma… Da sauri na anshi wayar daga hannun Mamy nace.
Mai ilimi barka da tsakiyar rana , barka dai ta amsa a daƙile , nace suna na SULTANA ALIYU MUHAMMAD BINNA… ina miki albishir da mummunan gani , salona ne yin albishir da mummuna ga abokin gaba sai kuma nayi albishiri da kyakkyawa ga masoyina , idan baki manta ba a waccan ranar nace mutuwa kaɗai zaki ki huta da ganin baƙin cikina , tou yanzu muka fara ki fara yininki da wannan anjima ma zan turo miki na kwanciya bacci kisha kallo lafiya…… Gashi nan zuwa , ki gani ke ɗaya idan uwarki ta buƙaci gani itama ki bata ta gani muna da maganin ciwon zuciya na hausa idan kina buƙata kallon Mamy nayi tare dayin dariya nace masu magani kasuwa ta buɗe ….
Ina faɗin haka na kashe wayar , Mamy kuma ta ansa ta tura vidion data ɗauko kuma hada Safiyya a cikin hoton tana ta kwarara ihu saboda azaba yayin da Baban Mardiyya ke kwarara wani irin gurnani kamar kura tayo kamu , na raka vidion da voice note cewa mi yasa ya faɗa ruwa bai iya iyo ba ?
Dariya mukayi dukanmu , saida muka tabbatar an buɗe saƙon kuma ya ɗauki lokacin da ya isa Mardiyya ta gama gani sannan naba Mamy Umarni data goge shi daga wayar mamanta , wato ta saka delete 4 everyone , bayan an goge duka hada voice note in da nayi nasa Mamy ta rubuta cewa ta kawo kuɗi masu yawa sai mu goge idan kuma ba haka ba ta tara a tashar yanar giza gizo.
Bayan mun gama nayi sallama da Mamy na wuce gida akan sai mun haɗu gobe idan Allah ya kaimu , tace Allah ya kaimu lafiya , a gajiye na shiga gida dan haka ruwa na watsa kawai nayi sallar la’asar na kwanta ina hutawa.
A ɓangaren Ummu Affan da Maman Sadiq kuwa fitarsu suka yanke shawara cewa idan na kaisu so ɗaya bazasu sake tafiya dani ba dan abinda suka fahimta zan riƙa ci musu aljihu , ma’ana idan aka basu zan riƙa ragewa ni inci da yawa su abasu kaɗai , ummm kuji ɗan adam butulu ,
Yayin da Maman Sadiq ke bayar da shawara cewa suyi wayau muna zuwa su lallaɓa su anshi lambar shugaban ƙungiyar sai suce masa idan ana taro ko yana nemansu karya kira Sultana ya nemesu kai tsaye , Ummu Affan tace gaskiya haka ne , dan kinga idan aka bamu dubu ɗari zata saka rai a cikin kuɗin ta, ga, tunda itace ta haɗani dashi zata jira na bata wani abu a cikin kuɗin , Maman Sadiq tace haka ne , ai tana nuna mana hanya mun gama da banzar , haka dai suka yanke shawarar su ,
Bayan sun rabu kuma kowa ya yanke shawarar saiya koro abokin tafiyarshi dan kowa yaci shi ɗaya , yayin da Maman Sadiq take tunani idan gwamnati ta bada mai da sabulu da magi da rigunan siyasa da ake rabawa zatayi samayya fiye da tunanin mai tunani ,
Itama a ɓangaren Ummu Affan haka ne dan har ta kasafa dubu ɗari yadda zata kaya mata tun kafin akai inda za’aje har sun yada Sultana a gefe , Ummu Affan ma tana tunanin yadda zata yada Maman Sadiq yayin da itama Maman Sadiq in take tunanin yadda zata kora Ummu Affan taci ita ɗaya ba tare data samu mai tayata ba.
Washe gari kuwa tun 7:22am Ummu Affan ta bayyana a gidanmu , tasha wanka ta ɗauko jagira irin ta zamani sai baɗa ƙamshi takeyi anci jaka da takalmi masu kyau ta ida rufe wankan da wani irin tsadajjen gyale tayi kyau fa abunta ,
Tana zuwa ta ganni ban shirya ba , tacemin da Allah muje kafin wacce mayyar tazo , nace tun yanzu ? Tace Eh na samu na ajiye yaran a maƙota muje mu dawo , nace tou ki bari itama Maman Sadiq in tazo basai mu tafi tare ba ? Tace nidai karmu jirata da Allah ki tashi mu tafi , nace tou yanzu gwamna ma kanshi ai bai tashi bacci ba , tace haba ai da a jiraka gara kai ka jira , dan Allah ki tashi mu tafi , nace kai gaskiya ni ko shara banyi ba , kuma ban wanka ba , tace jeki kiyi wankan ni kuma sai in tattara miki ɗakin kafin ki fito , nace to amma mi yasa bakya so aje da Maman Sadiq , na tambayeta ? Danni dama bana so aje da ita ,
Ummu Affan tace kinsan mutanenmu da baƙin ciki sai kaja mutum inuwa ƙarshe kuma yakai ka rana , nace tou ba aminiyarki bace ba ? Tace wa ni ? Ta nuna kanta sannan taci gaba da cewa ba aminiyata bace ba kawai dai muna gaisawa cikin anguwa , nace tou ina kika cewa mijinki zakije da wannan safiyar ?
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Saida tayi murmushi tace tambaya kamar “yar jarida , ce masa nayi ƙawata bata lafiya za’a tafi da ita asibitin zariya zanje na dubata kafin su tafi , nace to misali idan mukaje bamu samu ganin gwamna ba fa sai akace gwamna abubuwa sun mishi yawa mu dawo gobe tou sai muka dawo idan zaki fita goben sai mijinki yace baza ki fita ba tou ya zakayi ?
Tace ina ai dabara ma bazata ƙare ba , idan yace bazan je ba nasan hanyar da zan biyo masa , nace Allah ya taimaka ina faɗin haka nayi waje dan inje inyi wanka , kafin in fito wankan ta share ɗakin tas ta goge shi ta shinfiɗamin zani a katifa , ina fito na shirya a gaggauce ko kalaci banyi ba muka bar gidan kafin Maman Sadiq tazo.
A napep muka je gidan Mamy , a ƙofar gida muka same ta cikin motar wani namiji ga kuma wanda ta nunamin da sunan mijinta yana zaune saman dakali yana kallon ikon Allah , gaisawa mukayi dashi na umarci Ummu Affan da ta shiga ciki na nuna mata gidan tare da cewa shiga muna zuwa ,
Tana shiga ni kuma nayi wurin Mamy muka gaisa na gaishe da baƙon nata , bayan mun gama gaisawa Mamy tacemin in shigo mana , baya na buɗe na shiga bayan na zauna muka ƙara gaisawa ,
Shiru na wani lokaci sannan Mamy tace Sultana ga mutumin ki yaga mutuniyarshi kalli iskanci da yakeyi leƙo ta nan ki gani , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ni basai na gani ba , tace dan girman Allah leƙo kiga yadda bironshi ki rubutu babu takarda , dariya nayi sosai nace nidai bana san gani , Mamy tace haba so ɗaya fa zaki gani kawai , nace ba komai idan ya rubuta a takardar zan gani danni bana gane rubutu bisa iska ,
Dariya akayi gaba ɗaya , bayan wani lokaci kuma mukaci gaba da maganganu dai na sakin layi , bayan an gama mutumin ya tambayeni yadda mukayi da sabuwar sheƙar tashi , na goga mishi bayani duk yadda mukayi da su Ummu Affan hada Maman Sadiq duk ban ɓoye masa ba !
Yace babu damuwa ba hamsin za’a bata ba dubu ɗari zan bata yanzu sai ince mata gwamna yaje Abuja sai jibi zai dawo , kinga tana dawowa jibin ke Mamy sai ki bamu aron ɗaki mintuna 30 sun ishemu sau ɗaya kaɗai zan sa mata hannu kuma in bata kuɗi daga nan da kanta zataci gaba da zuwa ana mata singing ,
Shiru nayi sukaci gaba da firansu da Mamy , bayan wani lokaci kuma ya juyo yace Sultana kirata na sallameta tafiya zanyi na ansa da to tare da fita daga motar na nufi cikin gidan babu jimawa muka dawo tare da Ummu Affan bayan sun gaisa yace mata gwamna yaje Abuja wurin shugaban ƙasa amma zai dawo jibi idan Allah yasa muna da rayuwa , tace tou Allah ya dawo mana dashi lafiya…
Ya ansa da amin tare da karkacewa ya fiddo bandir in “yan ɗari biyar² masu zafi ya bawa Ummu Affan da kwalin sabuwar waya yace kuma da akwai layi a ciki , ruɗewa tayi ta duƙe har ƙasa tana zabgaga mishi godiya tare da cewa Alhaji kasa min lambar ka a ciki ? Yace zan kiraki zuwa gobe yadda mukayi da gwamna zan faɗa miki , godiya tayi sosai kamar zata faɗa mishi sai ƙara godewa take godiya irin ta maroƙa ,
Wani irin kallo ya bita dashi yana lashe loɓonshi na ƙasa mai nuni da zan kashe wuta dake , Mamy kuwa fitowa tayi daga mota mukayi mishi sallama bayan muma yayi mana wanka da ruwan naira ya tafi ya barmu da ɗaurewa da ruwan godiya ,
Ai Ummu Affan kuwa cewa tayi bazata koma cikin gida ba lokacin da Mamy tace mu shiga ciki , juyin duniya nayi mu koma ciki tacemin tabar yaranta suna jiranta gida zata tafi , babu ko tayin kuɗin bare ta jira taji munce ko mun ƙoshi , haka ta saɓe abunta tabarmu da kuɗinta da wayarta tai tafiyarta , mu kuma muka koma gidan Mamy , gaba ɗayanmu a palo muka zauna inda Mamy take cemin Al ‘ Ameen ya kirata ya zageta fess dan Mardiyya ta kirashi ta faɗa mishi babu daɗi yace duk sai yaci uwarmu dagani har ke kuma ya faɗawa mai gida abinda mukayi ma matarshi kuma shi mai gidan yace duk sai an tattaremu an ɗauremu , ni kuma jin haka yasa na kira wannan mutumin na faɗa mishi tunda naga yana cikin gwamnati shima.
Nace to yanzu ya ake ciki ? Mamy tace sai munemi mafita , nace shi Alhajin ya yace miki ? Mamy tace yace mu jira idan anyi ƙararmu zai ɗaukar mana lauya , idanuwa na zaro nace wane irin lauya kuma na shiga 14 nidai gaskiya bana san huɗɗa da koto ƙarshe akai mutum gidan yari ni banda wanda ya tsayamin , kawai saina fashe da kuka , Mamy tace haba Sultana tou miye abun kuka muna fa da bakinmu ki barshi ya yanko sammacin kiga yadda alƙalin zaiyi idan yaga lafiyayun katifu ,
Cikin kuka nace shikenan kullum mai makon katifa tahau saman gado sai gado yai ta hawan katifa nidai na shiga 3 , Mamy tacemin da Allah ke banza ce ki kwantar da hankali babu abinda zai faru domin na sake kiran yarinyar nayi mata baraza na da zan saki vidion a social media idan Al ‘ Ameen ya sake magana kuma ta kama kanta sosai ,
Dakel dai Mamy ta lallashe ni ta kwantarmin da hankalina ta sake bani ƙwarin guiwa , a gidanta na yini saida nayi sallah isha’e ta kawo ni gida ,
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya , yanzu tsawon watanni 3 kenan da kafa su Ummu Affan da Maman Sadiq a ƙungiya kuma tun daga ranar dana kaita bata sake bi takaina ba , yanzu tama ƙwace sosai wuta kawai takeyi abunta a cikin anguwa ,
Mijinta kuma tuni ta wanke ta bashi dan tunda ya taso ya fara hayagaga ta kwantar da banza da asiri , Maman Sadiq itama tuni an mata register amma bata ƙarƙashin ƙungiyata tana ƙarƙashin ƙungiyar su Amisty ne ,
Safiyya kuwa ɗiyar Baba ƙarami ciki gareta , gashi biki yazo Mamy ta hana talabijin bare labulaye , fitina sukayi ta rashin lissafi akan rashin talabijin da labulaye , ga rashin lafiya ya taso ta gaba tun Safiyya tana boyewa har abu ya fara damunta dan haka ta faɗawa Mamy cewa bata lafiya wata 3 bata ga jinin al’ada ba , kai tsaye Mamy tace ciki gareki sai kawai kije ki zago bedi ki saɓa kisha ,
Safiyya kuwa ta gaji da ɓoye ²ta rasa ina zata soka rayuwarta gashi Mamy bata , bata sahihiyar mafita ba , dan haka kawai ta haƙura ta faɗawa mahaifiyarta komai bata ɓoye mata ba , da Mamy da mahaifiyar Safiya akaci gaba da musayar harshe tsakanin Mamy da Uwar Safiyya , tashin hankali naƙin ƙari , ni ko kada Mamy ta faɗamin cewa nayi ai ba danneta akayi ta ƙarfi aka ƙwata ba lokacin da Alhaji yake bata tana ta tanɗewa tare da wa suka tanɗene ? Taje can taji da abunta sakaran banza tunda bata iya shan gishiri ba ,
Ƙarshen film in dai mahaifiyar Safiyya zama akayi aka sasanta suka fuskanci juna ita da Mamy daga ƙarshe dai a asibiti aka wanke cikin tass , ta tashi babu talabijin ba labulaye babu budurci kuma babu albashin kuɗin aikin da alhaji yayi , bayan wanke ciki da sati biyu aka ɗaurawa Safiyya aure , kwanata biyu a gidan miji ya korota tare dayi mata shegen duka rashin samunta da baiyi ba a matsayin budurwa , itama daga nan ta yanki nata tikitin na shiga sahun jerin Kwarata… kuma buƙata na ya biya.
Rayuwa mukeyi dai tsakanin ni dasu Amisty kowa naji haushin kowa , har yanzu ban sake ganinta da Babana ba , ta sake faɗaɗa ƙungiyarta da manyan mata masuji da duniya kuma duk matan aure sunfi yawa a cikinta domin yanzu kasuwar sutafi ja ba’a neman “yan mata kuma bata zawarawa akeyi ba matan auren dai ,
Ƙungiyar Amisty ta samu karɓuwa fiye da tunanin mai tunani ta samu kuɗi ta goge ta zama lafiyayyar hajiya , nima kuma inata bakin ƙoƙarina wurin ganin na kafa tawa ƙungiyar amma wallahi taƙiya daga ni sai Mamy a ƙungiyarmu , itama Ummu Affan ta kafa tata tana bada hayar matan aure ko a hanya ta ganni batamin magana saboda tana ganin tafi ƙarfina , al’amirin duniya ya fara bani mamaki dan haka na fara sanyi da rayuwata.
Mazan kuma nabi su² amma da an fara ciniki dai kalmar ɗaya ce 1k gani ni kuma haɗama gareni bana iya iba kaɗan sai in kantamo dubu ɗaruruwa , zuwa wannan lokaci kuma al’amura sunjamin baya sosai tun ba’ayi nisa ba duniyar ta ajiyeni bani ake yayi ba lokacin ba nawa bane na wasu ne , kenan tun kafin na ajiye bariki tana neman ta ajiyeni , dan har alaji su Amisty sunyi gaba dashi !
Ina cikin wannan tararrabi Allah ya kawomin wani zazzafan matashi maiji da kanshi ga kuɗi ga gayu amma matsala ɗaya wallahi mummuna ne ,
Naji daɗin zuwanshi kuma mun antaya soyayya shi ya wankoni daga talauci yayi ta yayyafin ya cidar hadarin naira da anyi tsawa saidai kiga yana ɓarin naira , cikin ƙanƙanin lokaci nima na farfaɗo na fara dawowa hajiyata ,
Naci gaba yanzu har hotel nake kwana amma matsalar ɗaya abunda na fuskata bayada alƙamin rubutu , kullum haka zanje in kwanta salaf in taso babu wani ɗan shafe² ko ɗan lashe ² ko ɗan tsotse² idan kuma na tashi tafiya haka zai bani kuɗi masu sa mutum ya kasa gano hanyar gidansu , abun a dameni dan haka na tambayeshi nace shin wai kai bakajin kanajin sha’awata ? Saidai yayi dariya yace yana da sha’awa in kwantar da hankali ranar hawa na zuwa ,
Ina kwance ina bacci a saman gadon hotel nayi guda² ina sararawa abuna idanuwana a rufe amma ba bacci nake ba , a tunaninshi nayi bacci dan haka ya tashi saf² ya fita daga bedroom in , wallahi haka nan naji tsikar jikina ta tashi jarr hankalina ta tashi ƙararrawa ta doka hayani ta riƙa tashi cikin kaina , da sauri na sauko daga saman gadon nayi bakin ƙofa ,
Da sanɗo na shiga palon ya bada baya yana waya cikin harshen turanci , hakanan na tsargu dan haka zuciyata tace kiyi masa vidio ko recording kamar yadda kika saba wannan da ganinshi baida gaskiya , da sauri na latso recording na fara ɗauka saida ya gama wayar tas sannan ya juyo da wata irin siffa mai ban tsoro dasa firgici tunda nake duniya ba taɓa ganin irin siffar ba , dakewa nayi banji tsoro ba kuma ban firgita ba naci gaba da addu’a nima na tsareshi da ido ,
A hankali siffarshi ta dawo siffarshi da nasanshi da ita , murmushi yayi yace ke matar aure ce ? Na girgiza kai da a , a , yace tou ki wuce daga yau karki sake dawomin matan aure muke nema , murmushi nayi tare da cewa ngode kuma na barka lafiya , ina faɗin haka nayi gaba abuna ko ciki ban koma ba bare na ɗauko gyalena , saida na fita daga ɗakin na ruɗe na firgice na kwarara wani irin ihu mai tada hankali ,