NOVELSUncategorized

NAJEEB 5

            PAGE 5
Ibtisam kam dariya take, Koba komai zata so Granny tasa a d’aura ma wannan shegen Mai girman kan y’ar kauye kodan taga yanda zaiyi, ibtisam tace uhm Granny ai inaga Najeeb yana jiran ku zaba mishi mata ne, sai yasa har yanzu bai fito da Mata ba. 


Granny tayi shuru can tace hakane kam, zanyi magana da audullahi, zanje yola a duba mishi Mata wacce zata dinga koya mishi fulatanci. 

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Ibtisam dariya take Sosai cikin ranta, tare da ro’kan Allah yasa ayi mishi hakan. 

Granny tace toh ke ya Magananki da kabir? Ina fatan kin amince koh? 

Ibtisam tasan ta gama magana da kabir, dan haka tace na amince Granny Indai zaki ma Najeeb aure, amma ina son a fara nashi Kafin nawa, tunda Kinga ya girmeni Sosai, ban so In rigashi aure 

Granny cikin jin dad’i da murnan ibtisam ta yarda zatai aure tace karki damu, gobe ni dake zamu habuja din inga audullahi muyi magana.

Koda ummi ta dawo ta kira ibtisam, Bayan ibtisam tazo, ummi tace Waye yazo nemanki? 

Ibtisam tace ummi shine wanda ya rage mana hanya shekaran jiya, nan taba ummi labarin yanda suka had’u.

Ummi tace naga kaman ya baki, Leda, ban San amshe amshen kayan samari, Indai kin San ba auranshi zakiyi ba gwara ki sallameshi, ban son fitina 

A hankali tace toh ummi, tare da tashi ta fita 

Washe gari da safe ibtisam ta shirya ita da granny Wanda Abba bai San da tafiyar Granny ba, sai ganinta yayi da safe ita da ibtisam, yace mama zaki rakata garage ne? 

Tace miye kuma wani garan?

Yace ina nufin tasha. 

Tace wani rakiya? Tare da ita zamu, muje ka sauke mu tasha sai mu shiga mota 

Yace mama tare kuma zaku?

Tace eh ko saina tambayi izini ne, Kafin a barni inje inda nake so? 

Yace a’ah kiyi hakuri mama ba haka nake nufi ba, naga tun jiya baki ce zaki jeba sai yanzu.

D’aure fuska tayi tare da fad’in Ummaru zaka kaimu tasha ko mu tafi da kammu? 

Yace a’ah muje in saukeku, ummi ta basu kayan miya sukai ma mum tare dasu gurasa da sauransu, sannan ta musu Allah kiyaye hanya suka fita. 

Saida Abba ya biya ATM ya cira kud’i sannan sukai hanyar garage, inda ya d’aukan musu shatan mota su biyu, nan ya biya kud’in motan, sannan ya bama Granny kud’i itama ibtisam ya bata, saida suka wuce sannan ya shiga tashi motar ya wuce kasuwa.

Sai wajan 3 da wani abu suka isa Abuja, dai dai kofar gidan alh Abdullahi aka saukesu, inda suka nufi gate din gidan suka fara nocking, wani soja ne ya le’ko yana fad’in ‘who is that? Ibtisam tace mune cikin harshen turanci take bashi amsa. 

Granny tace Mai yace? Ibtisam tace tambaya yake su Waye?  Granny tace oh yanzu har sai an tambaya, kai dan ubanka zoka bud’e Uwar Mai gidan ce, 

Dai dai lokacin sojan ya bud’e karamin kofar gate din, inda mutum zai shiga Inba da mota bane.

Kallonsu yayi sannan yace wa kuke nema? 

Ibtisam ta bashi amsa da fad’in Munzo wajan matar gidan ne? 

Yace tasan da zuwanku? 

Ibtisam na k’okarin bashi amsa, Granny tace wai Mai yake cewa ne? 

Nan ibtisam ta fad’a mata, Granny ta kalleshi cikin jin haushin tambayar da yake musu, tace Kai Dallah bamu waje mu shige tare da k’okarin tusa kanta cikin gidan.

Sojan yayi sauri ya tareta tare da magana cikin gurbattaciyar hausan shi yace mama inane zaka? Ka kira ajiya sai in Barka ka ciga, lokaci d’aya kuma ya kalli ibtisam yace ki kira madam a waya in tace in barku saiku shiga. 

Granny kam in banda faman surfa bala’i tare da fad’in audullahi yasa Anci min zarafi yanzu in banda iskanci In za’a zo gidansa sai an kirasu a waya, har dani uwarsa. 

Ibtisam dake k’okarin kiran mum tace Granny dan Allah kiyi shuru, shifa wannan bai San ke maman uncle bace, inda ya sani Aida ya Bari kin shiga, kuma daka gani sabon zuwa ne, dan duk zuwan da nake ban taba ganinshi ba. 

Granny ta galla mata harara tare da fad’in Dallah ni kirata Ina jin fitsari kaman marata zata fashe 

Kiran mum tayi, bayan mum ta d’auka tace ibtisam Kun zone, Ashe da Granny kuka tawo, yanzu na gama waya da abbanki. 

Ibtisam tace Munzo muna Gate, ance mu kiraki.

Mi’ka ma Sojan wayarta tayi Mai tocilan, ya amsa tare da sakawa a kunne, naji yana fad’in ok ma, ok ma, lokaci d’aya kuma ya fara sorry ma, tare da kashe wayan ya mi’ka ma ibtisam, ya fara basu hakuri, cikin harshen turanci tare da cewa ibtisam taba granny hakuri bai San Maman oga bace.

Nan ibtisam ta fad’a ma Granny abunda yace, Granny ta kalleshi tare da fad’in Dallah bani waje, munafuki, da sauri ya matsa suka shiga, tun Kafin su k’arasa wata yarinya Doguwa chocolate colour kyakyawa ta rugo da gudu ta rungume ibtisam tare da fad’in oyoyo, lokaci d’aya kuma ta saki ibtisam ta rungume granny 

Granny tace Dallah sakeni karki Karya ni, saida kika gama rungume y’ar uwarki sannan zaki zo kaina. 

Ibtisam tace zarah Kinga kyaleta zomu shige 

Granny tace zanyi maganinku Wlh, yara duk sun girma Sun Fara tsufa amma babu aure, ji yanda zarah ta k’ara fashewa, nidai Amina wani laifi na muku babu maganan aure a tsarinku, kwafa tayi sannan ta shige ciki ta barsu nan tsaye suna murnan ganin juna, sun dad’e a nan Kafin suka shiga ciki inda suka tarar da mum a falo ita d’aya.

Ibtisam gaida mum tayi,  mum ta amsa cikin sakin fuska tare da fad’in ya hanya? 

Ibtisam tace Alhmdlh, sai dai rigiman Granny, duk ta isheni dariya suka saka, mum kana kallonta Kaga balarabiya sak ita NAJEEB ya d’auko sai dai wasu sukan ce farinta ya d’auko yafi kama da dad d’inshi wasu suce da ita yake Kama, mum in kaji hausarta saika d’auka ba Hausa takeyi ba dan in tanayi kaman tana larabci

Granny ce ta fito cikin tan’kamemen falon Tana gyara zani tare da fad’in ku komai naku daban dana mutane, Kun tashi kun ajiye mara mutunci a bakin gate. 

Zarah tace Kai granny maiya miki kuma? 

Tace ban sani ba, in banda wulakanci in za’a shigo gidan sai ace sai an kira a waya, in mutum baida Kati fah, ko in bashi da wayan gaba d’aya fah? 

Zarah tace saiya koma, Granny ko a addinance anaso in mutum zaizo wajanka ya Sanar dakai, bawai yazo kai tsaye ba K…. 

Granny tsaki taja tare da fad’in tunda bakwa son mutane ba, ai dole ki Kawo maganan addini..

Dariya suka saka, mum tace mama muje kuci abinci ku huta 

Granny tashi tayi aka nufi k’aton dinning table, harta zauna, lokaci d’aya kuma ta tashi tare da fad’in nifa wannan abubuwan ban cika sonshi ba, in mutum zaici abinci saiya wani zauna a kujera kaman Maye, ni kusa min in zauna a k’asa Inci 

Zarah da ibtisam babu abunda suke sai dariya 

Granny tace uwarku kuke ma dariya, akan Mai yasa za’a ce cin abinci sai an hau saman kujera maima kuke kiran kujeran Denis ne ko Mai ohon muku 

Zarah saboda dariya har dayin k’asa tace miye kuma Denis dan Allah granny kar kisa cikina ya fashe saboda dariya. Tsaki Granny taja tare da zama ta mi’ke k’afa a k’asa tana fad’in nidai ban hawa Denis din nan wlh 

Mum da itama take ta dariya k’asa k’asa ta Fara zuba ma Granny abinci, Bayan ta gama ta ajiye mata a k’asa inda ta zauna, Granny Fara cin abinci akayi ana mamula baki.

Bayan sun kammala, Granny tace audullahi bai dawo bane har yanzu? 

Mum tace tun dazu yace Sun sauka, Nasan yana gab da gida yanzu 

Tashi Granny tayi, tace ni bari in shiga in huta kafafuwana duk sunyi tsami, d’aki ta nufa 

Ibtisam taba mum tsaraban da Ummi ta bata, mum taji dad’i Sosai tana ta godiya, inda zarah taja ibtisam sukai d’akinta, wanda d’akin yayi mugun had’uwa, komai dake d’akin pink ne, sai rasi rasin blue kad’an, zama sukai akan gadon d’akin Mai shape din mota, zarah tace kin Fara shirin zuwan mu skul kuwa? 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button