NOVELSUncategorized

RABO AJALI 1

RABO AJALI…!

HAUWA A USMAN
       JIDDARH

Am back again Alhamdulillah Allah yayi min dawowa, na dawo muku da sabon labari na mai k’unshe da abubuwa da dama, Allah yasa zai nishad’antar daku ya kuma fad’ar daku


Ina k’ara mik’a sak’on gaisuwa da godiya ga masoya na masu bibiyar littattafai na a koyaushe, ina matuk’ar godiya sosai nagode da Addu’o’inku


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());



1⃣


LOKACI NE
Masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek’e masge kwarkwatar idanunsu, da san kwakwale damuwarsu, da sanya bak’in cikin su facewa, su kwamaso sink’i-sink’in dariya, annashuwa da sassanyan murmushi kan fuskarsu, su antayawa ruhinsu salama, su sanbad’awa zuciyarsu yalwa,  masu san farin ciki wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik’a, fasihiyar, mai san kasancewar ku cikin annuri, wacce ta saba kawo muku nagartattun litttattafanta masu dad’i, wacce ta kware wajen rubuta dad’ad’an labaru tun daga kan wanda ya k’unshi nadama, kuku,tausayi, cin amana, da nagartacciyar soyayya mai yalwa mai sanya tsoho ko tsuhuwa su tuna da jiya samartakarsu da ‘yan matancinsu ya motsa,
ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k’unshe da abubuwan mamaki, al’ajabi, kala-kala, wa’azantar da ban tausayi gami da sanya zuciya tsinkewa, wanda zai nishad’antar daku, ya d’ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa, LOKACI NE shine sunan littafin, wanda ZUWAIRAT UMMU MARYAM tayi bajakulin fasaharta da basirarta wajen antayo muku dashi, LOKACI NE 
zaku biyu naira d’ari biyu (200) kacal domin samun labarin da karantashi akan 200 kacal domin samun k’arin bayani sai ku tuntub’i wannan number +2348106102727

LOKACI NE
ZUWAIRAT UMMU MARYAM



Zundumemiyar mota k’irar Land Range Rover evoque 2020, 
tayi parking a harabar shoprite dake garin Abuja Nigeria,
a k’alla anyi wajen minti biyar da fakawar motar kafin cikin isa,
tak’ama, izza gwarjini da haiba matuk’in motar ya zuro santala-santalan kyawawan fararen k’afafunshi,
wanda suke cikin takalmin Berluti Oxford,
cikin nutsuwa ya zuro su waje,
an d’auki minti biyu zuwa uku kafin ya fito gaba d’ayanshi,
” masha Allah, shine abinda na iya furtawa ganin santalelen matashin saurayi,
mai cike da tsantsar haiba da kamala,
wanda da gani bazai wuce 25yrs a haife ba,
idanshi ya lumshi ya shak’i daddad’ar iskar duniya mai cike da nagarta,
sanye yake cikin sky blue na d’anyan farin men boyel material,
hannunshi sanye da expensive watch, takalminshi na world men, sai hular kanshi kalar takalminshi,
hannuwanshi zube cikin aljihun wondanshi,
 ya taka cikin takunshi mai tafiya da hankalin ma’abocin kallanshi,
zuwa d’aya b’angaren gaban motar fuskanshi cike da k’ayataccen murmushi,
ya sanya kyakkyawan hannunshi ya bud’e murfin motar,
had’i da mik’a hannunshi na dama ga wanda ke zaune cikin motar,
kyakkyawan hannu na gani na mace sanye da zubunan diamond,
ta d’ora saman hannunshi kana ta fito tana kallanshi ido cikin ido kyakkyawar fuskarta k’unshe da yalwataccen murmushi,
kai da ganin irin kallon da suke aikawa junansu ko ba’a fad’a maka ba,
kasan sun jima cikin tafkin so da k’aunar junansu, 
kasan suna matuk’ar son junansu,
hannunta ta sak’ala cikin nashi kana suka taka zuwa cikin shoprite d’in,
duk wanda yayi musu kallo d’aya sai yayi sha’awar k’ara yi musu kallo na biyu,
idan kuma kayi musu kallo na biyu sai kayi sha’awar dauwama kallan zak’ak’uran masoyan har abada.

B’angaren kayan kwalliya suka fara nufa still suna sak’ale da junansu,
tamkar wani zai kwace matashi, koya kwace masa ita,
yaran dake binsu da basket na zuba kaya shi kanshi mamakin zallar son da suke nunawa junansu yake,
sai da ta jidi kayan shafe-shafe da goge-goge,
san ranta kana suka nufi b’angaren k’ananan kaya da kayan bacci,
yadda kasan zasu bud’e shago haka take jidar kayan kamar ba gobe,
cikin so da k’auna ya kalle ta  da rikitattun idanuwanshi masu kama dana mashaya,
cikin zazzak’ar muryarshi mai kamar ana busa sarewa,
yace ” meye saura my Queen?

Murmushi tayi mishi cikin so ta kalle shi tace ” b’angaren kayan ka mana,
d’an sama yayi da idanshi kana ya mayar da kallanshi kanta yace ” what…!?

” Perfumes, ta bashi amsa,
” baki tab’a mantawa da duk abinda ya shafe ni my Queen,
” ko da mutuwa ce a kaina bazan tab’a manta koda sawun k’afar ba,
bayyi magana ba yaja hannunta suka wuce zuwa b’angaren turarurruka,
” wow…! look my Queen  new design Dior,
yayi maganar had’i da kallan b’angaren da take,
ganin bata nan yasa shi d’aga kanshi da sauri yana kallan wajen,
karaf idanshi ya sauka a kanta tana nufar wata budurwa dake kallanshi tana murmushi,
cikin tashin hankali ya zaro idanshi had’i da cewa ” ya Salam,
yana nufar da sauri had’i da kiran sunanta “NAJWAH….!,
bata ko juyo ba balle ta saurare shi ta nufi yarinyar da har lokacin idanta yana kan NEEHAL….!,
tuk’uk’in bak’in ciki da takaici ne suka k’ara rufe NAJWAH.  !,
 ganin yadda budurwa ta kafe NEEHAL…! da ido bata ko k’iftawa,
ta tattara dukkan hankali da nutsuwarta ga NEEHAL,
still tana murmushi, wanda shi Neehal d’in baima san tana yi ba,
in banda ganin Najwah ta nufe ta,
take BAK’IN KISHINTA….! ko ince KISHIN JAHILCIN NAJWAH,
ya motsa idanta yayi jajir kamar gauta, cikin zafin rai da tsantsar ruwan bala’in kishi ta isa ga budurwar,
bata tsaya b’ata lokaci ba ta kifawa yarinyar gigitattun marika,,
a firgice yarinyar ta sauke ajiyar zuciya dan babu zato ko tsammani sai jin saukar marin datayi,
dan hankalinta baya jikinta yana wajen kallan NEEHAL…!,
cikin takaicin halin bak’in kishin Najwah Neehal ya runtse idonshi da k’arfi ganin aikin gama ya riga ya gama,
” me nayi miki….!?

Cewar yarinyar dake dafe da kuncinta both side,
” au bama kisan abinda kikayi ba ko….!?

“Shegiya kwartuwa, wacce bata ramin kanta sai dai idan wani yayi ki shiga,
munafuka annamimiya mai kallan mazajen mutane,
Najwah tayi maganar tana huci da kerrrrma,
murmushi yarinyar tayi danta fahimci dalilin haukan Najwah,
tace ” wow dama kece ke da wancan Handsome an Classic guy d’in….!?

Zuciyar Najwah ta k’ara k’uluwa tazo har wuya,
yarinyar tace ”  oh…! akan haka kike wannan abun…!?

“Kodan banga laifinki ki ba, ko ni ke da kamarshi zan iyayin fiye da haka,
but I advice you, ki rage wannan jealously d’in naki tun kan ya kaiki ya baro ki,
dan ba’a yiwa namiji irin wannan haukan, 
in ko ba haka ba, rana d’aya zai kaiki Dawanau ya aje ki wallahi,
cikin zafin rai Najwah ta rufe yarinyar da duka idanta sun gama rufewa gaba d’aya,
ganin haka yasa jikin Neehal  na kerrrrma ya k’arasa wajen ya d’auki Najwah cak daga kan yarinyar,
fisge-fisge Najwah ta farayi tana k’ok’arin kwacewa daga hannun Neehal,
cak ya d’aga ta sama yana tafiya ya idanshi kan yarinyar yace ” we’re very sorry please…!,
” never mind handsome, yarinyar ta fad’a had’i da kashe mishi ido d’aya,
aiko kishi ya k’ara kama Najwah,
take numfashinta ya soma yin sama-sama saboda bala’in kishi,
cikin mota ya dannata kana ya zagaya ya shiga ya tashi motar yabar harabar wajen,
cikin takaici yayi shiru yana tuk’i, 
k’aramin d’an yatsanshi yasa a bakinshi yana d’an cizawa,
haka yake yi dama idan ranshi ya b’aci tun yana yaro,
 kallan Najwah yayi wacce dakyar take numfashi, na ‘yan mintuna kana ya kawar da kanshi gefe,
deep down yana mamakin masifaffen kishi irin na Najwah,
matuk’ar kana san ganin ruwan bala’i, tsagwaran tijara da zunzurutun rashin mutunci,
to ka motsa kishin Najwah akan MIJINTA NEEHAL,
yanzu idanta zai rufe ruf ta zama bata ji bata gani, ko waye kai, a kuma gaban kowa zata iyayin komai akan kishin MIJINTA,
tana da matuk’ar bala’e’en kishi.

Ajiyar zuciya kawai Neehal ke saukewa cikin b’acin ran halayen macen dayafi so da k’auna fiye da kowacce mace a fad’in duniya,
ya rasa yadda zanyi yayi controlling kishin Najwah,
tun abin baya damunshi abun harya fara mugun bashi tsoro yana d’aga mishi hankali,
dan babu damar ko cousin sister d’inshi ne su rab’e shi balle wata macen daban, 
har suka k’arasa gida bayyi mata magana ba,
yayinda har lokacin dakyar Najwah ke iya fitar da numfashi saboda tsabar bak’in kishi,
yana yin parking ya fita yabarta zaune nan cikin motar yayi shigewarshi cikin abinsa,
dan Neehal mutum ne mai taurin kai, kafiya, da bak’ar zuciya,
dukda yana da faram-faram da san mutune had’i da wasa da dariya,
amma kwata-kwata bai d’aukar raini da wulak’anci, haka duk sanda yake yiwa abu bai hanashi ya wagarar da abun,
jikin Najwah na kerrrrma ta bud’e motar ta fita tabi bayanshi da gudu,
a parlor ta iske shi ya kishingid’a saman sofa had’i da rufe lulu eyes d’inshi,
a hankali ta zauna saman cinyar shi cikin sanyin murya tace ” fushi kake yi dani…..!?

Bai ko motsa ba balle ya bud’e idonshi ya kallenta,
” I’m sorry my life…! 
still Neehal bai motsa ba, rikitaccen kuka Najwah ta sanya da k’arfi wanda yasa shi saurin bud’e idonshi,
dan harga Allah babu abinda Neehal yafi tsana a rayuwarshi irin kuka,
shi ko kukan yaro da wani daban can wanda bai sani ba, 
bai iya jurewa balle kukan abun so da k’aunarshi,
ita kanta sanin haka ne yasata saka mishi kukan dan tuni ta rik’e kukan a matsayin makaminta a wajen mijinta Neehal,
ido ya kafe ta dashi ganin yadda take kukan bil hakk’i da gaskiya,
k’ara volume kukan tayi ganin baida niyyar saukowa,
batare da yayi mata magana ba ya rungume ta,
had’i da shafa bayanta yana d’an bubbugawa alamar rarrashi,
” kayi hak’uri ban k’arawa…!
kamar bazayyi magana ba, sai kuma yace ” kullum haka kike cewa my happiness,
amma kink’i canjawa, abin nan yana masifar damuna, 
k’ink’i ki gane Neehal naki ne ke kad’ai har abada,
kanta ta gyara saman k’irjinshi had’i da zura hannunta ta rungume shi sosai,
cike da jin dad’in kalamanshi tace ” am sorry dear, wallahi matuk’ar naga wata mace tana kallanka sai na kasa daurewa na danne,
gaba d’aya ido na ya rufe, idan ko naga wata mace ta rab’e ka ji nake kamar na mutu,
dan numfashi na dakyar yake fita,
dan Allah ka zama nawa ni kad’ai karka raba min kanka da wata please,
ajiyar zuciya ya sauke kana yace ” nayi miki alk’awarin ni naki ne ke kad’ai har abada,
nayi miki alk’awarin bazan tab’a had’a soyayyarki da wata ‘ya mace ba har atashi duniya,
ke kad’ai ce a gidan Neehal, ke kad’ai ce matar Neehal, ke kad’ai ce a zuciyar Neehal daga ke kuma an rufe k’ofa babu k’ari,
” kayi alk’awari…!?

“Nayi alk’awari bazan tab’a yi miki kishiya ba har abada,
cikin tsantsar farin ciki ta shiga manna mishi kiss ta ko’ina,
” so please ki rage kishi, kima daina tab’a lokacin ki wajen yin fad’a da mata akan mijinki,
” thank you so much,….! tace tana dariya.

NEEHAL d’ane ga hamshak’in mai kud’i Alhaji BILAL LAGOSA,
Allah yayiwa Alhaji Bilal Lagosa tarin dukiya mai tarin yawa,
ya kasance fitaccen shahararran d’an kasuwa, wanda duniyar kasuwanci take damawa dashi,
a halin yanzu zan iya cewa kaf Africa babu tantirin d’an kasuwa kamar Alhaji Bilal Lagosa,
yana da matar aure d’aya tak mai suna TAHEERAH wacce sukayi auran soyayya,
suna da yara biyar maza biyu mata uku,
NAUFAL shine babban d’ansu, daga shi sai NEEHAL, shekara biyu ne tsakanin Naufal da Neehal,
 daga Nehal an dad’e ba’a k’ara haihuwa ba dan a k’alla anyi 15yrs kafin Allah ya sake bawa Hajiya Taheera ,
ciki ta haifi ‘yan biyu mata SUHAILA da SUHAIMA, shekararsu biyar aka haifi SUHAIRA wacce itace auta a halin yanzu Naufal yana da 27yrs, sai Neehal 25yrs, 
sai twins Suhaila da Suhaima masu 10yrs & auta mai 5yrs.

Lagosa Family, Family ne da yayi k’aurin suna a Nigeria wajen taimakon talakawa da marasa k’arfi,
wajen bada tallafi tun daga sutura, abinci, gidan zama, aikin yi, jarin sana’a, marasa lafiya, marayu, da masu buk’atar taimako,
kai harma da wad’anda basa da buk’atar taimako yi musu ake yi,
haka duk k’arfin buk’atar ka idan ka kawo musu bazaka tab’a tabarin wajen batare da sun share maka hawaye ba,
suna da kyakkyawar mu’amula da alak’a da mutane, 
sun samu shaida mai kyau kwarai da gaske a wajen al’umma,
 mutane sunsha rok’on Alhaji Bilal Lagosa daya fito siyasa,
sai yace shi ba d’an shiyasa bane shi d’an kasuwa ne,
suna zaune lafiya cikin farin ciki, walwala, so, k’auna da kulawar junansu,
basa tare da wata matsala dan gida ne gidan addini, an gina gidan kan tsarin da turbar addinin islama,
kowa yana gainin girman na gaba dashi suna mutunta juna, suna matuk’ar k’aunar junansu fiye da komai,
babu wanda yake k’aunar ganin d’an uwanshi cikin damuwa da k’uncin rayuwa,
suna bala’in bawa juna caring 100%,
suna da kyakkyawar alak’a ga junansu.

Alhaji Bilal Lagosa cikekken Babarbare ne d’an asalin garin Maiduguri Barno, har yau har gobe iyayenshi kakanin Neehal suna zaune  cikin garin Maiduguri a unguwar Shauri’s Place, 
haka ma suna da babban gida a Dambuwa road,
sai dai zama da yanayin kasuwanci ya maida Alhaji Bilal zama Abuja,
amma har yau har gobe duk wata hidima data tashi biki ko suna, ko wani taro a can suke yin kayansu,
amma Taheerah bafulatana ce Usul gaba da baya, haifaffiyar garin Adamawa ce,
itama har yau har gobe iyayenta suna garin Adamawa.

Neehal ya kasance mutum mai faram-faram da mutane,
yana da wasa da dariya ga san hira, shi ba muskili bane, dan yana da son magana, sai dai bai san raini kwata-kwata,
 yana da bak’ar zuciya da taurin kai had’i da kafiya,
mutum ne shi mai tsatstsauran ra’ayi, 
ta wani fannin kuma mai sauk’in kai da sauk’in hali,
duk irin son da Neehal ke yiwa abu bai hana shi yiwa abun rashin mutunci,
idan ya tab’a shi koya b’ata mishi rai,
 haka duk sanda yake yiwa abu yana iya wofintar da abun yayi kamar bai damu dashi ba,
so baya hana shi d’aukar mataki akan mutum,
kamar yadda yake faruwa tsakanin shi da Najwah muddin ta b’ata mishi rai,
bai dannewa sayya nuna mata dan ta koki gaba, saboda tsabar zuciyarshi,
Neehal kyakkyawa ne ajin farko, san kowa k’in wanda ya rasa,
duk da kasancewar shi Babarbare ya kasance fari tasss kamar zabiya,
dogo ne sanb’al, mai kwantaccen gashin kai, wanda ya gangaro zuwa fuskanshi yayi mishi k’awanya,
(saje), ya taru a hab’arshi yayi mishi kyau sosai, fuskarshi doguwa mai d’auke da d’an k’aramin baki,
da fararen hak’ora ajere cas-cas,
yana da dogon hanshi, da dara-daran fararen idanuwa,
masu kama dana mashaya, kwayar idanshi ash color ce, 
d’an gayu ne na k’arshe yana da tsafta sosai fiye da tunanin mai karatu,
bai tab’a yin amfani da abu sai expensive,
haka yana bala’in son k’amshi, 
shiyasa tasu tayi masifar zuwa d’aya da Najwah dan itama ‘yar gayu ce sosai,
yana da san tsafta da kwaliya gami da gayu,
itama Najwah kyakkyawar gaske ce ajin farko ta bugawa a jarida,
irin matannan ne full option, wato komai yaji.

Najwah ‘yace ga Ubayyu Auwal Nigerian General custom controller,
da mahaifiyarta mai suna Sakina,
tana da yayye maza uku HAKEEM, HALEEM, NASEEM,
sai k’anwarta wacce itace auta Nabeelah,
suma gidansu gidan tarbiyya ne, dukda wayewa da boko sun fi yawa,
sun kuma yi mugun tasiri a gidan, dan basu tsinana komai sai dai suci su kwanta kawai, sai yawan k’asashe bud’e ido,
da kallace-kallacen film, ko chart da using systems, gidan su basu da wata matsala suma,
tun Najwah na yarinya take da mugun kishi ta tsani yin abu iri d’aya da wani,
ko sisterta basu saka kaya iri d’aya, 
basu using komai iri d’aya kowa da nashi,
babban burinta a duniya ya zamana duk abinda ta mallaka ya zama nata ita kad’ai,
idan ko wani yayi mata amfani da abu, ko iyayensu suka siyo musu abu iri d’aya da Nabeelah,
babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan ta dinga kuka kenan tana burgina har sai an canja mata shi,
even makaranta tata daban da ‘yan gidansu, kai ko sutura Najwah ta saka taga wani da irinshi bata k’ara saka nata,
kasancewar mahaifiyarsu Hajiya Sakina ba mace ce mai san yawan magana ba,
yasa Najwah ta cigaba da tasowa a haka har girmanta ba kwab’a,
gwara ma yanzu da tayi aure Neehal yana kwab’arta yasa ta rage kishin abubuwa da dama amma banda kanshi,
dan yanzu tana iya saka kaya iri d’aya da wani, tana iya usinga abun wani ko ayi using nata,
haka tana iya yin abu iri d’aya da mutane.

Neehal da Najwah sunyi auren soyayya kuma auran gata,
makarantar secondary school d’insu d’aya acan suka had’u suka fara soyayya,
tana Jss1 yana SS3 kasancewar su ‘ya’yan masu kud’i kuma a private hospital hakan ba komai bane,
bayan ya gama secondary school yak’i tafiya turai karatu saboda Najwah,
babu yadda Alhaji Bilal bayyi dashi ba amma yak’i,
dayake Nigerian turkish yayi from nursery 1 to SS3 yasa aka samar mishi,
Nigerian Turkish Nile  University Abuja, ya karanci business administration,
lokacin Najwah tana Jss2,
Najwah na Ss1 Neehal yana level 2 akayi musu aure,
mahaukacin fitanan jahilin so Najwah ke yiwa Neehal,
wanda bata iya had’a sanda take mishi dana kowa,
akan Neehal tana iya rufe ido ta shatawa kowa rashin mutunci,
duk duniya kowa da kowa a yasan irin mugun son da Najwa ke yiwa Neehal,
haka kowa yasan bak’in kishinta.

Naufal ma yana da aure da matarshi UMAIRAH tare akayi bikinsu da Neehal,
yanzu 3yrs kenan da auransu Neehal ya gama karatunshi last month yanzu service kawai ya rage mishi,
haka ma Najwah ta gama secondary school,
Umaira ba ‘yar masu kud’i bace sosai iyayenta suna da dai-dai nasu rufin asirin,
‘yar garin Kano ne Bahaushiya usil,
itama ta gama karantunta a BUK,
kowa gidanshi daban ko unguwa basu had’a ba, suna zaman lafiya da juna sosai.

Kasancewar Umairah ta gama karatunta yasa Alhaji Bilal Lagosa,
ya dannak’a mata ragamar LAGOSA VILLAGERS HELPER,
k’ungiya ce da Alhaji Bilal ya k’irk’ireta dan shiga karkara da k’auyuka dan wayar musu dakai,
da kuma kai musu tallafi da taimako, har ma ana d’ebo ‘ya’yansu ana kai su makarantu,
zuwan Umairah cikin k’ungiyar ya k’arasa bunk’asata sosai,
suna shiga irin k’auyukan nan wad’anda even gwamnati bata san da zamansu ba,
balle tasan dasu, sosai ake kai musu taimakon abinci, sutura, da kayan amfani na yau da kullum,
har titi, nepa da Bohol anayi musu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button