NOVELSUncategorized

KWARATA 11

???? —— 11

            Tashi nayi na fito nayi alwallah, bamma kowa magana ba na koma d’akina… Kuma koda na gama sallah kwanciya na k’arayi dan inajin gajiya sosai ga kuma bacci.


      Amma k’iri k’iri baccin ga yak’i zuwa, hankalina da tunani na gaba d’aya ya tafi ina tunanin irin yanda Nana ta tozarta mijinta daren jiya a cikin bainannasi, miji da yake da daraja yake da matsayi yake da mutunci abin tattalawa idan Allah ya baka, ubangiji ya rataya ma Nana rigar arzik’i amma tana k’ok’arin yagata ta ratayawa kanta rigar wahala, idan har Nana ta fito daga gidan mutunci ko a gaban d’iyanta batayi wannan iskanci ba amma shine har ta fito tsakar gida kuma gidan ma na haya dan ta nunawa mutanen gidan cewa ita ta hana mijinta hak’k’inshi.

        Gaskiya abinda wasu matan sukeyi bai kamata ba, duk yanda akayi a zaman jiya aka rud’awa Nana tunani, ashe kuwa idan har zaki biye ma labarin “yan iskan mata babu ranar da hankalinki zai kwanta a gidan aure, su basuyi auren ba kuma su hana masu zaman auren suyi aurensu, sai su rud’aki da zance babu labarin k’arya a samu a kakkab’oki sai kin fito daga gidan mijin kizo kiga labari yasha banban…..

       Maganar Karima najiyo tana cewa jama’an gida ku fito majalissa d’inki duniya ta fara tattaruwa, ga A’ i nan ta taho da labari, Nana tace ai bama labari kad’ai tazo dashi ba naga ta shigo da leda duk “yanda akayi daren jiya anci kaza mu ta ragowa sauran, kaji jakka sai kace rainon mayu dan ubanta. 

       Hayaniyar matan gidan naji da alama kowa tayo waje, agogo na kalla naga duka 6:22am, gaskiya dai hakan bai kamata ba da zasu yadda dana basu shawara amma bara nima na fita wajen mu gani….

Nana na gani tana wanke fuskarta tare da cewa ai ilimi yafi sallah ita sallar bara a jingineta idan na gama d’aukar darasin nayi ta daga baya…..

       Kallonta nayi k’asa da sama amma banyi mata magana ba, duk yanda akayi Nana uwayenta jahilai ne, wata zuciyar tacemin karki zargi iyayenta Sultana wallahi kina iya ganin babu laifinsu d’a nawa kake ba tarbiya idan yaga ba idonka ya barbad’ar da ita yayi wanda yake so.

     Ina isa inda kowa yake na kalli A ` i, nace gaskiya ki daina yo mana sabko duk fa masu gidan basu fita ba kawai sai ki baro gidanku kizo ki hana mazajen wasu baccin safe ? Irin haka da kukeyi gaskiya bai kamata ba, kallon Nana nayi tare da ci gaba da cewa gaskiya kuma matan gidan nan kuna da naku laifi da kuna zamanku a wurin mazajenku baku fito ba babu wacce zata rik’a dako muku sammako ta hanaku samun ladar kwanciya a jikin mazajenku…..

      Nana zatayi magana A ‘ i tace barta in bata sani ba a fad’a mata, kallona tayi tare da cewa ke Sultana kinsan makaho idan yana kashi baisan ana kallonshi ba sai an tsokalo d’uwawunshi, munsan tal munsan sal abu d’aya yasa bazan gaya miki ko waye ubanki ba da rayuwar gidanku amma yau dana bud’e miki zani cikin kasuwa.

     Ke harma kina da bakin da zaki zo ki wani ce an hana mazan wasu bacci , ina kika san wannan keda uban naki ma ko gidan bai kwana….. Murmushi nayi ba tare dana nuna naji zafi akan tabo Babana da tayi ba nace…..

       Ai duk ubanda ya ganni yasan ubana zauna gida ne, ko bai kwana ba kinsan yayi k’ok’ari kuma ya fita hak’k’in mata tunda har ga sakamakon mu ya fito, duk namijin daya zauna gida ai soko ne tunda babu k’ashin zuciyar da zaisa ya fita neman abinda zai ba iyali, niko zuciyar ubana tsaye take wurin nema ya nemo aci asha kuma ko bai kwana gidan ba da safen idan ya dawo suma matan gidan zai basu hak’k’insu kinga kuwa dan bai kwana ba ai ba aibu bane ba tunda dai abinda suka aure shi danshi d’in ai yana basu bai hanasu ba.

      Saboda mata da yawa wannan abun dake kika raina su sunsan darajarshi, wasu matan kuwa zasu iya hak’uri da talaucin namiji amma wannan abin d’aya da kike magana akanshi basu yadda su rasashi ba, wata macen kuma mijinta ya daketa ya hanata abinci amma idan dai zai kwanta da ita ta samu gamsuwa zatayi hak’uri taci gaba da zama dashi a haka tasan arzik’i na Allah, amma wata ita ba shi take mawa ba rayuwarta da tunaninta ya tafi wurin tunanin neman duniya, kamar dai ni dake kinga ba abun ya fiddo mu ba kasuwanci muka d’auke shi, tou haka matan gidan nan suke su ma, da mazajensu masu kud’i ne ko sunyi wani abun wani sa d’aga k’afa dan duk yanda ka raina d’an tsintsu bakacin shi da gashi, namiji ya sakarwa mace ragamar gida ai dole ta koma mijin shi ya zama matar, amma duk da haka dai ki sani Allah ba ruwanshi da kin nemo kinba miji tunda hak’k’in cida da sha sutura da wurin zama lafiya da ilimantar wa duk saida ya d’auki alk’awarin zaiyi a gaban waliyyanki , 
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
     To tunda anyi auren kin gane bazai iya ba ai sai a raba auren ki huta amma bawai ki zauna kiyi ta yayar ma kanki zunibi ba, zaiyi wuya kiji mace taje gidansu takai k’arar mijinta yana basu abinci so d’aya a rana.

      Amma mafi yawancin mata namiji ya hanasu hak’k’insu ko baya gamsar dasu sai kinji sunyi tsegumi, aba k’awaye labari aba mak’ota labari aminiya da duk wanda kike hud’d’a dashi sirrin mijinki fallashshe ne, tou wa kikayi mawa ? 

       Nidai shawara ce idan ta muku zafi sai kuyi hak’uri, amma ya kamata ku rik’a sirrinta sirrin mazajenku domin dai wannan sirri ba abin yayad’awa bane shi yasa yake rufaffen sirri ko an shiga d’aki sai an rufe k’ofa….

     Tsoki Nana tayi tare da cewa mu idan zaki zauna kiji ki zauna idan bakiji ki k’ara gaba, Karima tace da Allah kyaleta tafi ma mill tsayuwa bamu fasa zancenmu, ke A ‘ i albishirinki ….! Saida A ` i ta harareni sannan tace goro,

Jiya fa Audu yaci ubanshi da gudu ya biyo Nana har tsakar gida, kallon Nana tayi tare da cewa kai jiya fa Nana tayi bala’i gidan nan , can naji gurnanin munafiki kamar an kwacewa mahaukaciya diyarta…..

      Ke Nana bada dai labari da kanki kinsan masu iya magana nacewa wak’a bakin mai ita tafi dad’i, mu na waje muka gani bamu kalli na d’aki ba.

       Tab’o ledar hannun A ` i tayi tare da cewa da Allah idan dai namu ne ki bamu mu cinye sai miyau na yake tsikewa, mik’a musu tayi “yan iska masu kama da maguna suka rarraba suka cinye, Nana na cewa dan Allah A ` i ki kawo min ice cream rabona da insha shi tun ina budurwa,

      Karima ta katse ta da cewa haba da Allah bamu labarin Audu ki daina wani zancen ice cream, lashe hannunta tayi sannan ta fara cewa, in fad’a muku tunda na ganshi ya shigo da leda nasan dole yana buk’ata…

    Ajiye ledar yayi a gefe na tare da cewa karfa kiyi bacci, inajin yace kar nayi bacci nasan tafiye yake da damuwarshi, saida na bari ya gama abinda yakeyi tsaf yazo ya hawo ta bayana yana wani shashshafoni na fara mutsirniya, cikin raunanniyar murya magana mai fitar da numfashin wahala yace kar muyi haka dake Nana yau kusan sati biyu kenan kina hanani hak’k’ina bakyajin tsoron fushin Allah ya sauka kanki ……?

        Aiko na b’ata rai nace gaka k’atoton wanda fushin Allah zai saukar mawa , ai idan dai har kaga ka kwanta dani tou wallahi sai ka biyani duk bashin da nake binka….. cikin rawar jiki ya fara k’ok’arin juyoni yana cewa kiyi hak’uri Nanata wallahi ba’ayimin biyan bashin ba, kuma banyi ciniki sosai ba yau abinda na samu gashi nan na biya na dafo miki indomie, tsoki nayi tare da cewa ai sai ka cinyeta ka kwanta kayi bacci.

     Haba Nana idan dai har kika ga anci ko ansha saida natsuwar ci, ina tare da babbar yunwar da abinci bazai gusar min da ita ba kin sa na zama wani susutacce na zama kamar wani tab’ab’b’e banda natsuwa bare kwanciyar hankali kiyi hak’uri don Allah yauma karki ce zaki hanani….

     Ai ban gama jin zancenshi ba na duro daga saman gado nayo waje….. Ni kuma naji tana wannan haukan shi kuma ya jata suka koma d’aki. Murmushi nayi tare da cewa kin burge Nana…. Tou me ya faru bayan kun koma d’akin ne ?

         Tunda na lura basa san gaskiya shi yasa nima zan biye musu mu zama riftattun gaba d’ayanmu, Nana tace ai koda ya maidar dani d’aki da k’arfin tsiya babu abinda na yadda ya shiga tsakani na dashi, yayi magiyar yayi nacin kuma ya jaraba ansa ta k’arfin tsiya amma ya gagare shi, dole ya hak’ura ya fita baima kwana gidan ba……

      Dariya nayi tare da cewa tou ina kike tunanin ya tafi Nana ? Yo can shi ta matse mawa koma gidan uban waye ya tafi bai dameni ba wallahi saiya biyani bashi na ko zaici gaba da kwanciya dani.

        A ` i  kuwa cewa tayi kwarai Nana karki sake ki yadda ko gidan haya kake zaune kud’in wata ya k’are idan baka biya ba no uziri tashinka akeyi, ya baki idan babu kullum yaita kwanan hak’uri, gaba d’aya suka bushe da dariya…… Banda ni da nabi Nana da kallon tausayi !!!

       Mijin Karima ne ya fito cikin kunya yana san ya shiga bayi amma kunya ta hanashi fitowa dan yanzu mun k’ara yawa, daya d’aga labule ya hangomu sai ya koma, k’arshe dai hak’ura yayi da wanka yasa rigarshi yabar gidan…..

      Fira akaci gaba dayi tunda muka zauna har zuwa yanzu babu macen data tashi koda wasa, ganin rashin aikin yin nasu bashi k’arewa yasa na tashi dan ina da wurin zuwa anyi firar dare dani idan banyi baccin wuri ba,

      Saida na share d’akina na gogeshi tass na kunna tsintsiyar k’amshi sannan na zuba ruwa naje nayi wanka, ina fitowa na shirya saida na gama shiri na sannan nasha ruwan tea ko biredi babu ina gamawa nayi ma mutanen gida sallama tare da rufe d’akina nayi gaba abuna…..

        A zaure na sauk’e nik’af ina na fice daga gidan tare da addu’ar yo babban kamu idan na fita, A ` i na gani tsaye da wani amma bansan ko waye ba, ni mamaki ma ya kamani dan bansan lokacin da A ` i ta fito daga gidan ba…

     Har zan wuce naji tace ina zuwa haka Hajiyata ? Yaye nik’af ina nayi tare da rage girman idona na dama nace farauta zanje kinsan sai ka gane girman gida kake sanin ta inda zaka fara shara…. Murmushi A ` i tayi tare da matsowa kusa dani ta d’an rik’o k’uguna da hannu d’aya, sannan tayi min wani irin kallo wanda ni bansan abinda yake nufi ba……

         Saida ta wani yi k’asa da murya sannan tace da ganinki zakiyi tunon asiri amma ina gargad’inki da ki rik’awa bakin linzami ta k’arasa maganar tare dayin murmushi, bud’e idanuwa nayi dukansu wanda idan har na d’an ragesu na bud’esu lokaci d’aya nasan ina k’ara kyau kuma mutane sunsha fad’amin haka.

      Kallonta nayi da duka idanuwana sannan nace dama tunda kike kin tab’a ganin mazinacin da yayi sirri ? Miya had’a karuwa da sirri dama ? Ai da amana da kunya da sirri da gaskiya duk karuwa bata dasu, kunya tana tasowa ne daga b’oye tsiraici tou ban b’oyeshi ba zan bud’ashi wa duk wani mai kud’i ya gani, kinga nan rashin kunya ta fito, daga inda babu kunya kinga babu imani duk mutumin da baida imani kuma bashi tare da rahmar Allah, ina bud’ewa ga maza, namiji kad’ai ya isa ya gani yasha kuma ya tab’a dan haka sakarmin k’ugu daga yau karki kuskura ki sake tab’amin jiki, idan har na baki sha’awa tou ki zama namiji kizo da dubu dari shidda sai in baki duk abinda kike gani a jikina ya burgeki, na k’arasa maganar tare da sauke hannunta a jikina….

Kallona A ` i tayi tare da cewa ai duk saurin anguwar zoma ta bari a haihu ? Duk saurinki kin bari kiji uzirin da nazo dashi….. Bud’e k’ofofin hancina nayi sannan nace ai tunda har aka tanaji aikin ungozance ansa haihu tana zuwa kinga kuwa duk daren dad’ewa amfaninta zaizo. Tou ni bana jira idan na gani saina tanka na dakatar dake ne tun kafin cikin ya samu bare kisa ran ansar haihuwar….

      Na sanki cikinki da waje, duk macen dake gidan nan nasanta kuma tun ranar da na kwana na gama karatun halin kowa, kwalwa ta gane inda mutum ya dosa Allah ya bani amma bai bani kwalwar gane rubutu da karatu ba, ina iya gaya miki duk macen dake lesbian a cikin gidan nan , kuma ina gane duk macen da namiji ya kwanta da ita ba tare da na sani ba, ki kiyayeni ina da had’ari ne mai girma domin nima kaina tsoron kaina nake, ki fita idona tun kafin inyi miki terere…….

     Shiru A ` i , tayi ta kasa magana….. Murmushi nayi tare da dafa kafad’arta nace yawwa kisan wani abu gaskiya ni bana gaba da mutum ina so abun nan ya tsaya iya mu biyu, zan wuce ki gaishe min da mijin Nana kuma bazan bata labari ba , ina fad’in haka nayi gaba abuna…..

        Cin amana da rana k’iri k’iri wannan fa shine an raka zomo rami an dawo…. A ` i takai Nana ta barota gashi kuma tana tare da mijinta, kila ma jiya da yayi zuciya da Nana wurin A ` i ya tafi ya kwana, tabbas ma can yaje tana nan tana haukan banza mijinta yaje ya siyo ma k’atuwar banza kaza taci ta rago musu….

        Zuciya ta ce tace Sultana kiji tsoron Allah zato zunibi, tsoki nayi tare da cewa wannan ai ba zato bane abinda yake filin Allah kowa yana gani dandai kawai gaskiya bata fad’uwa, sudai suka sani amma idan tayi tsami kowa yaji.

      Napep na tare na fad’a mishi inda zanje, ciniki mukayi na shiga yaja muka tafi. Yau babu inda zan sauke zango sai wurin Alhaji mai gidan “yanci, wato inda Umar yakai ni da farko ban shiga ba na dawo, dalilina na haka kuwa yanzu zakuji…….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button