KWARATA 9

???? —— 9
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, itace kad’ai abinda Dikko yake ta maimaitawa a cikin wannan tsalelen dare,
Juyi yakeyi sosai a saman gado sai kace macen da ciwon ciki ya taso ta gaba, kifa kanshi yayi a saman lallausan bargon dake kusa da kanshi ya goge hawayen dake bi masa idanuwa.
Allah na tuba…, ya fad’a a bayyane tare da gyara kwanciyar shi, girgiza kanshi yayi , yayin da zuciyarshi da kwakwalwar shi suka hasko mishi abinda yayi ma Sultana, a hankali ya lumshe idanuwanshi na tsawon lokaci sannan ya fad’a a bayyane baiwar Allah baki dace mahaifi ba,
Sai kuma Allah ya jefoki a rayuwar Dikko yayin da nake nemanki, kika zo a daidai lokacin da na d’auki hud’ubar shaidan , Allah ya baki hak’uri kinji, ya k’arasa maganar tare da bud’e idanuwanshi duka da sukayi jajir saboda kuka……..
Ko ina kike ? Me kike yi yanzu ? Wane irin bak’in ciki kikeji idan kika tuna dani ? Ki zama mai yafiya a rayuwarki, manta da Dikko ki fuskanci rayuwa, ina nan ke kuma ina ki ke …..?
Ina gidan karuwai,…. Ina shiga d’akina na mayar da k’ofa na rufe, ya zama lallai na gano waye mamallakin wannan gidan, sannan idan har na karb’i dubu d’ari a hannun wancan garan me ya kamata nayi da ita ne ? Ansar kud’in sune wahala Sultana anso su tuk’una idan suka zo hannu ba’a rasa abinda za’ayi ba, wannan shine shawarar da zuciyata ta fad’amin.
Ajiyar zuciya na sauke tare da hayewa saman “yar k’aramar katifata na kwanta bacci.
Da safe ina tashi sallah asuba nayi, na dad’e ina zaune a saman abin sallah ina addu’o’i na neman tsari d’aukaka farin jini da kuma k’war jini a harkar bariki.
Sai 7:00am na tashi daga saman abin sallah, toilet na shiga nayi wanka, ina fitowa na shirya a gaggauce domin akwai inda nake so naje.
Ina gama shirina na fito sanye cikin hijabina, sai nik’af dana dabkakawa fuskata, ina rufe d’akina mai kirana da irin sunan da Dikko yake kirana yazo.
A k’ofar d’aki muka gaisa daga gaisuwa ban sake masa magana ba naci gaba da rufe d’akina.
An mata ina zakije haka da safe ? Ban kalleshi ba nace zanje wurinka ne dama, murmushi yayi tare da cewa kuma gashi nima nazo wurinki yake nan .?
Babu wani damuwa zamu iya maganarmu anan, mudai shiga daga ciki zaifi ko ? Ya fad’a yana kallo na, gyara tsayuwata nayi tare da cewa kayi hak’uri gaskiya na fito bazan koma ba, yana k’ok’arin bud’e bakinshi yayi magana nace kayi hak’uri da Allah bana san magana tayi tsayo na wuce, ina k’ok’arin tafiya yace d’an tsaya kiji mana.
Tsayuwa nayi ba tare dana juyo ba, am dama cewa zanyi idan kina da hali anjima zamuje wurin Alhaji yace yana san ganin ki, ba tare dana juyo ba nace wane Alhaji ne ? Mai gidan nan, na bashi labarinki shi kuma ya matsa saiya ganki.
Saida nayi shiru na wani lokaci sannan nace wurin k’arfe nawa zamu je kenan ? Yanzu ma dan zaki fita da munje saboda ba’a gida ya kwana ba yana nan bayan gidan nan yana tare da bak’i da sukazo wurinshi manyan alhazawa ne masu kud’i da suka ansa sunansu a kud’i, d’an mugun murmushi nayi a cikin nik’af ina sannan nace tou kai ya maganar kud’in da zaka bani ne ? Suna cikon mota muje, murmushin zalinci nayi irin wanda naga mugu Dikko yanayi sannan nayi gaba abuna ya biyo bayana.
Cikin motarshi ya d’aukeni, muna shiga cikin motar na yaye nik’af ina tare da kallonshi sannan nace niko na tambaye ka mana ? Tambayarni mana ya fad’a a daidai lokacin daya fara tafiya da mota.
Shiru nayi ban sake magana ba, shine ya gaji da shirun yace kinyi shiru kuma ! Ey zan tambaye ka amma ba yanzu ba dan na d’auka ne baka san tambaya da surutu ne kamar yanda nima bana so, amma tunda ka bani izini zan rik’a tambayarka a duk lokacin da tambayar yazo min, amma dai ya sunan ka …?
Murmushi yayi sannan yace suna na Umar, gyara zama na nayi tare da cewa me yasa Babanku yasa maka suna Umar ne ? Dariya yayi sosai tare da cewa sunan ubangidan shi ne,
Zaici gaba da rattafo min bayani na dakatar dashi ta hanyar cewa barmin bayanin haka nan zan tambayeka wani lokaci, babu gardama ya kame bakinshi ta hanyar yin shiru….
Har muka isa bakin get in gidan babu wanda ya sake magana daga ni harshi, horn yayi mai gadi ya bud’e mana muka shiga, gida ne had’ad’d’en gida na “yan gayu yasha ado da shuke shuke na filawowi, daga gefe kuma wasu irin lafiyayun dawakai ne tsabtatacci kuma k’osashshi aka d’aure sai tattabaru masu kyau wanda suke sauka k’asa lokaci lokaci su kuma tashi sama firrr lokaci lokaci….
Gaskiya dokunan sun burgeni sun kuma bani sha’awa, amma dana tuna da Dikko yana san doki yana k’aunar doki a rayuwarshi sai kawai naji dawakan nan sun fita a raina, saima zuciyata ta fara tunanin taya zanyi in kashe su, domin na tuna cewa Dikko ya fad’a cewa yana san doki ko ba nashi bane, lallai ni kuma na tsani dawakai.. Muje Umar ya fad’a da yaga banda alamar fita daga cikin motar.
Fitowa nayi tare da cewa Umar waye yake kiwon dokuna ? Wallahi na uban gidan Alhaji ne, ya bani amsa ne a lokacin da muka fara tafiya, tou shi Alhajin duk kud’inshi kenan yana da ubangida shima ? Na tambayi Umar, Umar yace Eh mana ai ubangidan nashi shine duk wata k’aryarshi, shine ya d’aure masa k’ugu shi ya tsaya masa saida ya tabbatar Alhaji ya zauna saman k’afafuwanshi , gaskiya mutumin kirki ne sosai, da yana harkar mata na tabbata idan na had’aki dashi yarinya kin warke, bake ba talauci, ke bake ba kaf zuri’arku da talauci ya k’are.
Maganar Umar ta k’are ne a daidai lokacin da muka shiga palon gidan, k’aton palo ne mai girman gaske, sai wata irin dakekiyar tv tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin tv mai girmanta ba, ko da yake ma ina naje ina na sani a wannan lokaci ? Saifa gidansu Dikko shima naga tashi tv n babba ce amma banda natsuwar gane wacce tafi girma,
Bin palon nayi da kallo, d’an rumtse idona nayi na bud’e tare da k’ara d’ora idanuwana a saman hotunan dake palon, tabbas idan ban manta fuskar Dikko ba wannan shine Dikko, mutumin dana tsana nake san ganin bayanshi komin daren dad’ewa, dan ina sayen gida wa Babana Dikko shine mutum na farko da zan fara sabautawa rayuwa a duniya……
Muje suna ciki, Umar ya fad’a tare da katse mun tunani na, sauke nik’af ina nayi na rufe fuskata sannan nace mu koma gida, zai tambayeni dalili nace kawai mu koma zamuyi magana dakai daga baya. Haba Sultana har mun shigo wuri zaki ce mu koma…. Kallon Umar nayi sannan nace tunda nazo da kaina ai kasan zan sake dawowa ko ? Ina fad’in haka nayi gaba abuna……
Ina fitowa idanuwana suka cika da hawaye, tun ranar da Dikko ya ajiyeni a k’ofar gidanmu ban sake tunaninshi ba sai ranar da Umar ya kirani da An mata, ban sanka Dikko na tsani duk sunan daya fara daga kalmar D insha Allah ni zan zama ajalinka….. Kuma ta hanyar da kabi ka azabtar dani to nima ta hanyar zanbi in rama abinda kamin, yanda ka somar dani ni kuma saina kasheka…. Babana yaci darajar mahaifi na ne shi, zan tara masa dukiya ta hanyar karuwanci zaici yaci bulus amma wallahi kai Dikko bakaci banza ba…..
Fitowar Umar yasa na saita kaina, na bud’e mota na shiga domin ya bud’emin ita tun lokacin daya fito, zakuji dalilin da yasa na fasa shiga ciki, Umar kad’ai yasan fuskata kuma yau ya zamar min wajibi nabar gidan karuwai domin wannan kwanakin sune kwanakin dana iba zanyi a gidan karuwai, na ga abinda nake so na gani, naji na kuma gani nima zanyi gaba dan nima in dogara da kaina.
Muna fitowa yayi hanyar gida nace dakata ajiyeni nan, ina zakije ne ? Ya tambayeni , ban bashi amsar tambayarshi ba nace masa ga makullin d’akina kasa a gyara man, bani kud’in nan zanje in had’o makaman yak’i…..
Miye makaman yak’i kuma ? Ba tare dana kalleshi ba nace ai kasan ba’a shiga gida dole saida sallama, gida ba shara ai baya dad’in zama, na ciki bai san akwai na waje ba idan baya kwankwasa ba, to haka bazai yuwu ba wani yaci abinci yace kai yaci mawa, kaidai bani kud’i kaji idan na dawo zan baka bayani,
Kud’in ya d’auko ya bani, bayan na ansa nace samu wuri ka rubuta min number ka idan zan dawo zan kiraka kazo ka taho dani, yo ina wayarki ne ? Banda waya amma ka rubuta min zan samu aro na kiraka, rubuta min yayi a jikin takarda ya mik’omin, ansa nayi na fita daga motar tare da cewa sai munyi waya…
Saida na daina hango Umar sannan nima na ibi tawa hanyar na shiga duniya……,
Tafiya nayi mai tsayi ba tare da sanin inda zanje ba sannan na tsaya wani shago na samu aron waya, lambar Umar na basu nace da Allah su saka a waya su kirashi, ansa mai shagon yayi yasa lambar ya kira, babu wani b’ata lokaci aka sadani da Umar…
Sultana ce, na fad’a a lokacin da Umar yace hello, Oh kin gama ne ? Ya tambayeni, maimakon na bashi ansa saina kece da dariya kamar hauka sabon kamu….. Meya faru ne ? Inji Umar, saida na gaji da dariya dan kaina sannan nace darasi.
Yau na tabbatar ni bariki ta fini tabbas na tafi na barka, wannan makullin d’akin daka bani ne shine na dawo muku da kayanku, amma zan baka sak’o a wurin Dikko tunda kasanshi , ka fad’a mishi cewa Sultana tace zasu gauraya…….. Ina fad’in haka na yanke wayar na mayar da ita ga mamallakinta nayi gaba abuna….
Wata irin zufa ta ketowa Umar mai makon salati sai ashariya, ya fara luk’ak’a zagi tare dayo waje da gudu, yana cewa amma lallai yarinyar nan ni zata danfara, wato wani bazaici abinci yace kai yaci ma ba, wato nine abinci itace bakin ni zakici ki gudu ? Kuma har kike wani cewa mai gida Dikko zaki gauraya dashi ? Kai wallahi idan na yadda shege ne ni, kuma yanzu zan kira Dikkon zaki ci kutumar ubanki, kici dubu d’ari zanci miliyan daga jikinki.
Jikinshi na kyarma ya fara kiran wayar Dikko har ta tsinke bai d’auka ba, k’ara kiranshi yayi bai d’auka ba, ci gaba yayi da kiran wayar babu k’ak’k’autawa, saida ya kira Dikko yakai sau goma sannan miskilin ya d’auka wayar…..
Ya akayi ne ? Shine tambayar da Dikko yayi ma Umar, cikin tausasa lafuzzan shi yace ranka ya dad’e kasan wata yarinya Sultana….. ? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un Dikko ya fad’a a ranshi lokacin da aka ambaci sunan Sultana,
Me ya faru ne ? Dikko ya tambaya ? Umar yaci gaba da cewa ranka ya dad’e yarinyar nan “yar damfara ce, tazo nan gidan “yanci ne , gidan karuwai suke cewa gidan “yanci, dan idan aka kira karuwai d’in haka abun babu dad’in ji. Shi yasa su gogaggin “yan bariki suke kiran gidan da gidan “yanci.
Wata irin zufa ta tsatstsafowa Dikko amma yayi shiru yana sauraren Umar, ranka ya dad’e kwananta hud’u a gidan “yanci shine yau ashe ta shirya guduwa ta raina min hankali ta ansar min kud’i dubu d’ari akan zata bani tukuici, { zasuyi iskanci } shine ta gudu, wai kuma saboda ta d’aukeni sakarai wai tayomin waya in fad’a maka wai zata gauraya dakai.
Saida Dikko ya goge zufa sannan yace yanzu kayi hak’uri zan biyaka kud’inka, ai ranka ya dad’e ni ba kud’in bane yafi damuna mummunar maganar data fad’a a kanka ne, bayan zata gauraya dani tace maka wani abu ? A , a batace komai ba, amma ina ruwanta dakai ? Tana da dalilinta na fad’in zata gauraya dani, ka fita harkar yarinyar nan zan tura maka kud’inka karka ma sake kace zaka sake tashin wata magana kuma karka sake ka nemeta ,
Umar yace mai gida zafa ta gaura dakai ? Ka kuwa san abinda gauraya take nufi ? Dikko yace ta gaurayo dani d’in ina ruwanka ? Kaine tace zata gaura ko ni ? Shiru Umar yayi, tsoki Dikko yayi da niyar kashe waya, Umar yace ranka ya dad’e nidai idan kaine zaka biya kud’in nan na yafe maka su, Dikko yace ita zaka yafewa bani ba tunda ni banci maka ba, taci albarkacinka na yafe mata, na gode shine abinda Dikko ya fad’a tare da kashe wayarshi.
Miye tsakanin Dikko da Yarinyar nan ? Shine tambayar da Umar yakewa kanshi wanda ya rasa mai bashi amsar tambayar, tou yaushe mai gida ya fara harkar mata ne ? Dariya yayi tare da cewa shegiya duniya mata bala’e ne wato duk musulinci mutum da kawaicinshi babu uztaz babu mahaukaci kowa dai yasan darajar ku, ai dole nake yafe dubu d’ari nasan wasu miliyoyi ne zan ansa, inama zanga yarinyar nan da na tambayeta miye tsakaninta da Dikko.
Mi yasa zakiyi haka ? Me zaki tsinta a harkar karuwanci banda wahala ? Me kike so ne ? Me kika rasa ? Kud’i ba damuwa na bane da zan ganki da na wadaki da dukiya har sai kin rik’ajin kyankyan kud’i, k’amshisu ma idan kikaji saiya rik’a tayar miki da zuciya, ke kuma duniyar kike so ? Jinjina kanshi yayi tare da cewa Allah yasa miki natsuwa ki dawo daga rakiyar shaidan. Allah ya had’ani dake Sultana in baki hak’uri in kuma nemi yafiyarki,
Mutane sunamin bahaguwar fahimta, yanda kike kallona ba haka nake ba, kuna min wani tunani na daban bayan ba haka Dikko yake ba,
Duk abinda ya faru tsakani na dake wallahi ina ganinshi ne kamar wasa, banso haka ba, bansan ya akayi nima na koma kamar wani sakarai ba wallahi, Allah ya tsareki fad’awa halaka, idan har kika fad’a harkar karuwanci na cuci rayuwata da zuri’ata da banma fara tunanin auren ba.
Farin ciki kamar in tashi sama yau gani ga naira dubu d’ari, kud’i suna da dad’i gaskiya da farko dai saina ci kaza, sannan na gano wani abu d’aya da maza suke so a tattare da mata, suna san k’osashshiyar mace, suna san tsaftatacciyar mace, suna san mace mai aji suna san mace ma’abociya k’amshi macen data iya soyayya da tattali, ina zan nufa yanzu ? …….