NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 11

BOOK 2

               PAGE 11
Dariya bariki tayi tare da fad’in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh ban son inga ya shiga wani hali, bazan iya jura ba, ina sonshi da yawa…..

Habib yace Toh fah, yau Ina ganin bariki….  Toh yanzu dai Mai kika yanke….??
Bariki tace abunda kuka fad’amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d’aura aurenmu aka kaini ranan zan fad’ama Yarima gaskiya…..
Habib shewa ya saki tare da fad’in Aiko ki tabbatar kin fad’a mishi tun Kafin ya shiga yaji ya shige zirif kaman bakin gate…..
Bariki duka takai ma habib iya karfinta tare da fad’in rafi ne ba gate ba
Habib ya ri’ke wajan da takai Mai duka yana fad’in na shiga uku zata kassarani…..  Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu ki takarkare iya karfinki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba……
Bariki tace andai yi Asara
Habib yace ke kikaga Asara bani ba
Umman bariki tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu sai su kaimu gaba….
Habib yace gaskiyanki domin naga matar can d’akin ta kusa daku Tana min wani kallo wanda ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci in cire kaya mu daku Dan ban son iskanci….
 Suna cikin haka Yarima ya kirata tare da fad’in baby come out Ina waje…..
Tashi tayi tana fad’in bari inje inga Yarima na.
Habib yace oh kunga salo a gayas….
Fita tayi tana fad’in kaji dashi…..
Motarshi ta nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud’e motar ta shigo ciki tare dayin sallama….
Amsawa yayi tare da fad’in my princess na gaji, tunanin driving nakeyi in zan koma Gida…..
Kallonshi tayi tare da fad’in ko in tu’ka ka, in kaika gida??
Yace dakin taimaka min kuwa
Dariya tayi tare da fad’in kaman dagaske….
Yace dagaske nake mana Kinga Idan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa….
Hannu tasa tare da rufe fuskanta tana dariya
Yarima kiran sunanta yayi da Zainab…..
Da sauri ta d’ago ta kalleshi domin jin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai muhimmanci…. Wanda yake bukatar natsuwanta
Yace d’azu kina son Yimin magana Ina jinki yanzu….
Murmushi tayi tare da fad’in Yarima a kullum Ina tsoran fad’a maka cewa ni dakai bamu dace ba, saboda kai ka fito gidan girma ni kuma ba y’ar kowa bace ina tsoran auranka domin gudun wulakanci irin na mas……
Da sauri yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad’in enough, dama duk wannan nonsense din kike son fad’amin shine kike d’agamin hankali?….. D’an tsaki yayi alaman jin haushi tare da kawar da kanshi gefe…..
Ganin ranshi ya baci yayi banza da ita, yasa ta d’ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri, ban San zakai fushi ba…..
Katseta yayi da fad’in Zainab  ban taba tunanin zaki dinga irin wannan tunanin ba…. And kina ma sona kuwa????…..
Da sauri ta kalleshi tare da fad’in Yarima baki bazai iya fad’in irin sonda nake maka ba, how I wish in bud’e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka…..  Yarima Ina Sonka yanda baka zato duk wani jini dake gudana a jikina yana gudana ne da Sonka I…..  Da sauri tayi shuru ganin yana kallonta…..
Jin tayi shuru yasa ya ru’ko mata hannu tare da fad’in Zainab are you sure akan abunda kika fad’a??
Kai ta d’aga Mai alaman eh
Wani irin murmushi ya saki cikin jin dad’i, tare da fad’in nace zan baki albishir d’azu right?
Tace eh
Hannunta ya saki tare da fad’in ina goran albishir din???
Dariya tayi tare da fad’in zan baka in naji albishir din
Dariya yayi tare da fad’in promise?
Tace yes I promise….
Yayi murmushi tare da fad’in mai martaba ya amince da maganan aurena dake….  But at first yace in Bari nan gaba tunda ban dad’e dayin aure ba…. Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra’ayi ba yace za’a turo gidanku ayi magana d’azu waziri yake fad’amin May be cikin week dinnan a turo……
Bariki gaba d’aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba d’aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai….
Ganin tayi shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad’in lafiya kuwa my princess? Kodai you are not happy ne dan za’a turo??
Da sauri tace a’a am so much happy tare da sakin murmushi….
Ganin ta saki jiki yasa Yarima jin dad’i sun dad’e suna fira sannan Yarima yace Zai tafi tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a ciki ba….
Amsa tayi tare da fad’in ngd
Hancinta yaja tare da fad’in sai munyi magana…..
Tace OK tare da fita tayi cikin gida,….  Tana shiga habib ya amsa ledan tare da fad’in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa nakeji tun safe babu abunda naci….
Su turare ne Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud’i a ciki….  Habib d’aukan kud’in yayi dubu d’aya d’aya bandir biyu, dubu d’ari biyu kenan…..  Yace Kai Yarima akwai kyautar girma….
Uwar bariki ta Karya tace ai gidan sarauta ya fito dole ya dinga kyautar girma…. Domin da suji kunya gwara dukiyarsu ta k’are….
Bariki kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad’in mai kuke cine Wai??
Ummanta tace abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya…
Bariki tace toh yanzu tunda nazo inyi sati d’aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib tayi tare da fad’in muje muyi cefane mu dawo……
****
Tsakanin haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da kalamai masu dad’i da kwantar da zuciya……  Sai dai abu d’aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar Hjy habiba ta yarda d’anta ya aureta ….. Sai dai haulat din tana ganin in bata yarda ba kaman ta nuna mata rashin adalci, and inma ta yarda ta auri d’an nata ya zasu dinga yima juna kallo……..
Farhan ne zaune a falo shida mahaifinshi domin yana kasar…..
Farhan ya kalli dad dinshi yace dad I find someone dat I wanted to marry……
Kallonshi mahaifin nashi yayi tare da fad’in farhan aure Bayan baka kammala karatu ba
Yace dad Ina final year ne, Ina son a fara magana b4 in Gama….
Dad din nashi ya kalleshi cikin son gudan d’an nashi yace why are u so rush to marry??
Yace dad just
Dad din yace ok but wacece yarinyar and Waye mahaifinta??
Farhan yace sunanta haulat mum tasan ta domin at tym Tana kwana gidan na……
Muryan hjy habiba sukaji tana fad’in karyanka Wlh koda zaka mutu bazan bari ka aureta ba, gwara ma kabar wannan maganan…..
Mijin hjy habiba ya kura mata ido tare da fad’in akan wani dalili??  Har kike kiran koda zai mutu bazaki Bari ya aureta ba?? Kin kuwa San abunda kike fad’a kuwa? D’an nawa kike ma fatan mutuwa??…..  Toh let me tell you Wlh Indai Inada rai kuma yana Sonta dole In tsaya mai…..
Tace ni kuma ban amince ba domin bai dace da ita ba….
Mijin nata yace habiba akan wani dalili? Miye rashin dacewan? Kallon farhan yayi tare da fad’in naji kaman kace yarinyar tana kwana a nan wani zubin….
Farhan yace eh dad
Kallon hjy habiba yayi tare da fad’in na tabbata inda yarinyar tana da aibu bazaki kawota gidan nan ta kwana ba, harki kasa fad’amin, domin naga Idan kikai ba’ki kina fad’amin but baki fad’amin wannan ba, ina son ki sani kaman farhan ya aureta ya Gama Indai Allah yasa matarshi ce babu yanda za kiyi…..
Hjy habiba tace ni kuma Indai har Ina numfashi kuma ni na haifeshi ban yarda ya aureta ba, kuma bazan taba yarda ya aureta ba….
Dad din farhan yace habiba Ina son ki fad’amin dalilin da yasa bakya son ya aureta??
Tace hakanan kawai ban son ya auri yarinyar
Dad din yace you are not serious….  Tare da kallon farhan yace inka kammala karatunka I promise zan tsaya maka har sai ka aureta….  Yana fad’in haka ya haura sama Fuuuuu tare da fad’in rabo dai yana kisa…..
Kallon farhan hjy habiba tayi cikin bacin rai tace wato ni ban isa bako?? Ka kyauta amma ba laifinka bane…. Itama fuuuu tayi sama
Farhan d’aga kafad’a yayi tare da fad’in whatever nidai Ina Sonta kuma tunda dad ya tsayamin banda damuwa….. Fita yayi yabar gidan
***
Yarima Aliyu ya fara aiki a asibitin shi, sannan an fara gina Mai filin da Mai martaba ya bashi, da yake filin k’ato ne ko wacce za’a Mata gefenta ginin gidan sama, da yake akwai kud’i an d’iba ma’aikata da yawa suna aikin domin Yarima yace nan da wata biyu ko uku yake son a Gama duka ginin…..
Yarima ya dawo gida yau ko wajan Zainab bai samu ya biya ba, kaman yanda Ya sabayi kullum, domin ya gaji, yana shiga cikin falo gimbiya zinatu ta taso Tana kuka tare da fad’in Yarima jita jitan da naji gaskiya ne???
Kallonta yayi sannan ya kauda kai gefe tare da fad’in fad’amin abunda kika ji coz am tired, I need to rest….
Cikin kuka mai sauti tace Yarima naji ance ginin mata biyu kakeyi zaka K’ara aure……
Yarima Aliyu murmushi yayi tare da fad’in gaskiya aka fad’a miki…..
Wani irin ihu ta saki mai kara tare da fad’in Wlh bazan yarda ba, ai wannan cin fuska ne yaushe ka auroni saboda rashin adalci ka Fara maganan k’arin aure, ko wata d’aya Banyi ba amma kake fad’amin zaka K’ara aure Wlh baka isa ba…..
Yarima Aliyu kallonta yake cikin bacin rai, domin ya tabbata ihun da takeyi kuyanginta suna ji…. Dan haka ya wuce ba tare daya kulata ba…..
Ganin haka tabi bayanshi Tana fad’in ai dole ka wuce wlh Yarima bazan yarda da rashin adalci ba har d’akinshi ta bishi tana surutai….
Yarima kam ko kallo bata isheshi ba, toilet ya fad’a Ya barta nan tana ta surutai kaman zararra
Bayan yayi wanka ya fito daka shi sai towel yana goge kanshi, tashi tayi ta nufeshi tare da rungume shi tana kuka tana fad’in Yarima dan Allah ka tausaya min bana son kishiya Yarima Ina kishin ka, maina rasa da kake kokarin K’ara aure, ko wata d’aya Banyi a gidan nan ba amma har kana maganan aure……  K’asa tayi tana kuka mai ban tausayi…..
Jikin Yarima Aliyu yayi sanyi tare da tausayinta….  Gimbiya dake k’asa tana kuka ganin kaman jikinshi yayi sanyi taji dad’i dan dama tasan za’ayi hakan…..
D’agota yayi tare da fad’in zinatu kiyi hakuri, ki d’auka komai kaddara ne, komai ya faru da bawa ki d’auka wannan auren da zan kara a matsayin kaddara…… 
Tureshi tayi tare dayin baya tace babu wani kaddara….  Karka kara cewa kaddara akwai abunda ba kaddara bane mutum shike sama kanshi…..  Duk namiji inya tashi aure saiya dinga amfani da wannan Kalman kaddara kaddara ban yarda da wannan kaddaran ba….
Yarima Aliyu yace baki da ilimi baki san addini ba, so banda time din in tsaya ina bata bakina wajan yi miki bayani……  Kaya ya fara kokarin sawa…..
 Ta Fara zunduma ihu tare da fad’in Wlh baka isa ba ,ni nafi karfin wulakanci, sai dai ka zaba cikin biyu koni ko wacce zaka aura…..  Ni Wlh bama laifinka bane na iyayenka ne da suka d’aure maka gindi kake son yin wannan rashin adalcin sune munafukai marasa tsoran Allah d…..   Tas ya sauke mata Mari da sai da yasa ta dawo cikin hayyacinta……
Ri’ke wajan tayi domin Marin ya shigeta Sosai…
Yarima Aliyu yace you cross your limit kije na sakeki saki d’aya bazan zauna da macen da zata zagi iyayena ba koda da wasa……
Gimbiya zinatu tace saki?? Yarima kasan Mai ka fad’a kuwa? Ka manta cewa babu saki tsakanin mu koda kuwa maina maka saika kamani da laifin Zi……
Yarima yace keep quiet, wannan ne dalilin daya baki daman kiyi min komai saboda bazan sakeki ba?ciki harda raina iyayena? U r wrong, al’ada ba addini bace,  you better leave this place tun Kafin in miki abunda za kiyi mamaki na Iletered ……. Tashin hankali???? Yarima Aliyu ya karya dokan masarauta koya zata kaya muje zuwa……..
plz masu min magana ta messenger kuyi hakuri ku daina saboda bani da messenger na goge facebook kawai gareni shima saboda posting ne, duk mai son magana dani yaje page dina yamin magana zan gani Inba mutum amsa, amma in a messenger ne zan gani babu daman bada amsa, dan na goge
MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button