NOVELSUncategorized

QANIN MIJI 1

QANIN MIJI
Daga alqalamin marubuciyar zamani????
MARYAM A.I GITAL
@ Meerahgee pure moment of life writers???????? 
SADAUKARWA GA JININANE REAL FANS, MUCH LUV GUYS????
1

 Kusan awa ɗaya da minti talatin ta shafe a gaban mirror bayan fitowarta daga wanka tana tsantsara shahararriyar kwalyarta duk na tarɓar habibin nata, wato sahibul qalb ɗinta Fa’eez, wanda yake kan hanyarsa ta dawowa daga germany domin zuwan da yayi qasar shigo da wasu kayayyakin da suke da buqata a ma’aikatarsu 
Fareedah yarinyace matashiyar zamani, son kowa qin wanda ya rasa, mace ce iya mace domin kuwa ta mallaki duk wani kayan yaqin da zata iya farauce zuciyar duk wani lafiyayyen ɗa namijin da ya ɗora idanunsa a kanta, ta haɗu ta ko ina kuma sai aka yi sa’a ta san me take yi, wato mai tsabtace ta qarshe da kuma son qyalli da qamshi, ga uwa uba kamun kai, ta fuskar addini ma ba a barta a baya ba, duk da dai ance mutum tara yake, bai cika goma ba
Kana ɗora idanu akan fareedah zaka gane zallar hutu a kan fatarta da jin daɗi, alamun babu wani abu da ta nema ta rasa a rayuwarta, saidai abin ba daga nan take ba wai an danne bodari ta ka
Akwai wani babban qalubale a cikin rayuwar fareedah da kullum yake addabar zuciyarta da nutsuwarta, wanda yake hanata gamsuwa da fahimtar ainahin ni’imar da take ciki a matsayin cikakkiyar ni’ima, bal ma wani lokacin takan tsawaita kuka da shiga damuwa akan marqabun na rayuwar da take ciki
Toh fa masu karatu sai mu bi fareedah domin gano matsalar, ni dai a tunanina ai an wuce gurin tunda akwai kayan kwalyar da za a iya yin fiye da awa anayi, ko kuwa readers????
 Cikin tsadaddiya mat ta ke mint green wacce aka yi wa ɗinkin zamani, irin ɗinki ɗiban albarkan nan, amma ita a gareta na ɗeban ladane tunda tayi ne dan mijinta, riga da sikirt ne da suka kamata tsamtsam, rabin bayan rigar duk a waje yake, ya bayyana rabin fatar bayanta mai matuqar sheqi yayin da gaban rigar ma ya bayyana saman nonuwanta da cika da batsewarsu a waje, sikirt ɗin kuma duk wasu halittunta ta ‘ya mace sun bayyana kansu  zamzam tamkar an ɗinka ne da jikinta, ɗan kwalin nan kuwa an masa ɗauri  irin wanda ake kira da dani zaka maigida?, shi ta baza, kai abin faɗi kawai mashaa Allah tabarakallah indai akan fareedah ne, domin an wuce gurin, macece ta kece raini
Ta gama fesa turarukanta kenan ta jiyo kamar qarar shigowar mota harabar gidan, hakan yasa tayi saurin zuwa jikin window ta zuge labulen kaɗan ta leqa, kasancewar ta san hafeez qaninsane zai je ɗaukoshi daga airport da motarshi yasa tana hango motar hafeez ɗin taji wani irin daɗi da farinciki sun mamaye zuciyarta, dan Allah ya sani tana matuqar qaunar mijinta, babu abinda ta fi so tamkar ganinta ga ta ga shi, tana tsananin muradin zama da mijinta a koda yaushe cikin irin rayuwar da zuciyarta take hararo mata kullum
Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta haske kyakkyawar fuskarta da murmushi mai ratsa zuciya sannan ta sake labulen ta ɗage yatsun hannunta sama ta murza wani haɗaɗɗen zobe mai masifar kyau da sheqi da yake yatsarta manuniya ta sumbata sannan ta fara taku tamkar ɗawisu tayi hanyar fita daga ɗakin nata
Adana motar hafeez yayi da kyau sannan ya fito ya je ya buɗe wa yayan nasa qofa wato fa’eez, tare da masa bismillah fuskarsa ɗauke da murmushi
Da bismillah a bakinsa ya fito cikin shiga ta alfarma, wata haɗaɗɗiyar dakakkiyar  shadda ya sanya ruwan zuma a jikinsa wacce aka baza mata zare coffee colour, hular kansa da takalmansa duk coffee colour ne masu matuqar kuɗi, domin fa’eez ɗan gayene na nunawa a taron sallah, ga son qamshi tamkar Ammar ɗin Elham????
Daidaituwar qafafunsa akan qasa ba daɗewa ya ɗago hanunsa mai ɗaure da agogon rolex ya duba time yayin da hafeez yake qoqarin rufe qofar motar bayan ya ɗauko masa mr boss ɗinsa a bayan motar (briefcase)
“na kusa makara hafeez, ni ban ga saurin jirgin nan ba” cewar fa’eez cikin haɗe fuska da rashin walwala
Hafeez yana murmushi yace “an gode Allah dai tunda gashi ka iso gida lafiya yayah”
Wani kallo ya bi hafeez da shi sannan ya ɗauke kai yana cewa
“a sallah kawai kullum sau biyar nake gode ma Allah”
Dariya hafeez yayi ya sosa qeya yace “afuwa yayana”
Sannan ya dafe wa yayan nasa baya ganin ya fara tafiya cikin tafiyarsa ta qasaita duk da sauri yake yi
Da sallama ya shigo falon yayin da fareedah ta haɗa amsa sallamar da oyoyo, da gudu ta je ta rungume kayanta tsamtsam tana cewa
“oyoyo my handsome” cikin wata iriyar murya mai cike da kirsa da kisisina
Maimakon ya appreciating ɗinta ya tayata su enjoying moment ɗin, sai ma ya ɗagota daga rungumar da ta masa ya ɗan sake fuskarsa kaɗan ya cire hular kansa ya miqa mata tare da juyawa ya kalli hafeez da yake tsaye yana kallonsu cikin wani irin yanayi ɓoyayye yace
“ka ban 15m zan shirya in fito ka kaini office, ka kira maxwell kace ya haɗa min zama da su cikin gaggawa, ina zuwa yanzu”
Yana gama faɗin haka ya raɓa gefen fareedah ya wuceta ya shige cikin gidan
Daga fareedah har hafeez bin bayansa suka yi da kallo yayin da idanuwan fareedan suka ciko da qwallah, muryar hafeez ne ya dawo da ita daga duniyar da take yayin da ta ji yana cewa
“matar kin haɗu wallahi, gaskiya ke wankakkiyace ta qarshe, samun irinki ribace da ba za a iya qirgawa ba, kullum ina taya yayana murnar samunki, ina ma nima in dace, maganar gaskiya kin yi kyau, kuma daman ke kyakkyawace, tsaya in miki hoto pls”
Mai da qwallar idanunta tayi ta watsa masa haɗaɗɗun idanunta farare yayin da shima ya kafeta da idanu yana murmushi
Yaqe tayi tace “hafeez ba ka gajiya da tsokana, ka gama dube dubenka ba zaka samu kamata ba sai qasa dani, mummuna ma”
Hmmm yace tare da yin murmushi yace “Allah ko”?
“sosai” sannan ta ɗora da cewa “ban briefcase ɗin ka gani in yi sauri in tafi gurin mijina kar yayi fushi”
Taɓe baki yayi yace “wato ma mijinki,? hmmm, zo muyi selfie ki wuce ki turo minshi ko inyi tafiyata”
Dariya tayi tace “toh ai ba ni zaka yi wa burga da bulanci ba”
Bai amsa maganar ba sai ma ciro wayarsa da yayi daga aljihunsa ya matso jikinta tare da haɗa kansu ya fara  ɗaukarsu a hoto yana yi yana canza style ɗin tsayuwarsu, sun haɗa kai suna murmushi zasu ɗauki na qarshen dan har ta nemi damuwarta ta rasa sai ga fa’eez ya fito cikin suit jajaye yayin da ta cikin ta kasance baqa siɗik ya kallesu ya ɗauke kai sannan yace
“ku ba kwa rabo da shiriritar banza, ina ta jiranki ke kuma kin tsaya a nan kuna ta shirme, ko me za ku yi da hoto ohonku, mts ku dai baku san muhimmancin lokaci ba”
Sai da hafeez ya ɗauki hoton kafin ya kalli yayansa yana murmushi yace
“ina yin hakan ne in na yaba da kwalyar matar, kai ma yaya ya kamata ka yaba, ka tsaya in ɗaukeku ko guda ɗaya”
Yatsina fuska faeez yayi kamar ya ga abin qyama yace “wa?, ni?, caɓ, kai ma ba ka da aikin yine, ka zo mu wuce in kana da time” yana gama faɗin hakan ya wucesu ya fice abinsa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button