NOVELSUncategorized
DOCTOR NA’IM 13

Page1⃣3⃣
Tsaye take tana ta faman kissima yadda zata bullowa lamarin gidan. Duk ta inda tabi ba nassara, gashi zuwan ummin husna ta ruguza kaso 70 bisa dari na plan dinta, lallai kuwa zama bai zama nata ba, don in batayi d gsk ba tanaji tana gani mitsiyaci zai zamo surukinta
Ita d take fatan muslihu ya mallaki companin A’A wata rana kuma sai kawai ta buge da aurar d y’arta ga mitsiyaci kamar na’im Wanda kanin abban shine komanshi lallai kuwa da sake
Mikewa tayi kamar wadda aka zabura. Part din yaran gidan ta nufa
A karo n Hudu kenan data taba jefa kafarta bangaren, ma’aikatan gidan suka dinga zubewa kwasar gaisuwa,
Da sallama ta shiga falon sun kewaye ummi da tun zuwanta ta dawo nan ta tare don daman ita zuwan ba don kowa tayi shi ba sai don amaren, don tasan halin sakeena babu abinda zata tsinana musu hk zata dauke su ta kaisu gidan miji ba wani dan gyara.
Suka amsa mata sallamar cike d ladabi suka soma gaisheta. Ta amsa musu cikin sakin fuska
Ummi n ganinta tace kin ganni nan nida y’ay’a na muna ta shirye shiryenmu. Sakeena tayi dariya “ai gara Ku shishshirya don lokaci yana ta dada matsowa nima nayi mgn d wata kawata zatayi musu halawa, Amman sai bikin ya rage saura sati daya sannan
Ummi ta dan zaro ido????alamun mamakin maganganun n sakeena kafun tace” wane irin halawa kuma? Ai ni na riga nayiwa wata chadiyan magana tun zuwana, zatayi musu dilke da sauran gyararraki. Sakeena sai kace wata ta da, amare ne fah
Murmushin yake mum sakeena tayi don daman ba wani halawa da tayi mgn, borin kunya ne kawai
Mikewa sukayi don bawa iyayen nasu guri. Mum sakeena ta samu guri ta zauna tana sauraron yadda ummi take ta faman shirya yadda bikin zai kasance, da kuma sauran abubuwa daya kamata ayi
Ita dai ta saki baki tana kallon yadda bil hakki take ta rattaba bayanai. Lallai matar nan d gsk take, aikuwa xaki gane kuskuranki don in bakiyi wasa ba sai dai husna ta auri na’im ammn ba yata ba (nidai kam nace sakeena kibi sannu ????)
Mikewa tayi don duk hirar ta gundureta sai wani bayani take akan wani mishan din auren d muddin tana raye baxata taba bari ayishiba
Wayar siyama ta kira tace ta sameta a falonta
Aikuwa tana xuwa ta balbale ta da fada, wato keeee siyama bazaki taba yin hnkl ba koh? Kullum ina nusar dake inda nakeson ki dosa ammn kina gocewa koh? Ynx akan auran na’im din kike wannan rawar kafar? Toh wllh da sake, in ma zaki shiga taitayinki ki farga kisan inda dare yy miki
Siyama datayi shiru tana sauraron mahaifiyar tata ta rausayar dakai cike da ladabi tace “Mumm plzz u have to understand me, ki fahimceni mum. Wllh ni bazan iya kallon dad na watsa mishi kura a ido ba. Ki lura sosai mum shi dayake ba dolenshiba yayi biyayyah ga umarninshi, ammn kuma ni danake matsayin yarshi ta cikin shi na kiyi mishi biyayyah? Ta soma girgixa kai duniya ma bazata barni ba “
Iyyyeeeh! ???? lallai siyama, au wato saini da kika raina zaki kalli tsabar idona ki fadawa hk? Shin wai na’im din d kike duk wannan abun akanshi shin yama taba miki kallon arziki da kike wannan abun a kanshi hk?
Ta sake rausayar da kai “mum meyasa har ynx kinki ki gane abinda nake son ki gane ne?, akwai qualities dayawa a tattare da shi wanda sai anyi d gsk xa’a samu masu kwatankwacinshi, nima sai ynx na fara karantar hk. Kudi basune komai na rayuwaba, akwai abubuwa dayawa Wanda suke gaba d kudi, na’im mutum ne yasan kanshi mum ni ynx n riga na saddak’ar
Sakeena ta soma yiwa yar tata kallon mmk kafun ta soma mgn ” siyama Me kike tunanin zancewa Hajiya fatuuu? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, ehhh! Lallai duniya taxo karshe, zamanin da ake bamu tarihi ya kusan to,
Mum kiyi hkr? Enough jeki kawai
Siyama ta futa jikinta a salube tana tunanin hali irin n mahaifiyar tata lallai Wanda yy nisa bayajin kira
Na’im yana zaune a office dinshi, yayi zurfi cikin duniyar tunani Sam bai Ankara da shigowar mujaheed dinba, sai daya dafa shoulder dinshi sannan ta farga ya dawo haiyacinshi
Mujaheed ya zuba mishi ido yana nazarinshi na Dan lokaci “wai kuwa kaga yadda ka koma cikin kwana kin nan? Gsky ka saura rawa kanka dayawan tunanin nan in baso kk ka haddasawa kanka wata larurar ba
Na’im ya dafe kanshi yace “bazaka gane bane mujaheed kwana cikin nan ina cikin matsala har n rasa yadda zanyi da rayuwata
Mujaheed yayi dan murmushi yace “Matsalarka, zurfin cikin ka yayi yawa na’im. Nasha fada maka ba komai ake ajiyewa a ciki ba, wani abun yafi karfin ka barshi a ranka
Na’im yy dan murmushi mai ciwo tabbas gskyr ka mujaheed, ba komai ake ajiye a ciki ba kamar yadda shi cikin badon tuwo a ka yishi ba. Sai dai ni Matsala ta bb amfanin fadarta don babu me yimin maganinta sai Allah
Mujaheed yace hk ne saika dage da addu’ah kamar yadda nasan ka ma’abocin addu’o’i
Sun danyi shiru akayi knocking kwan kwan
Mujaheed ya bada zini ” yes shigo”
Alhaji mahmuda ya shigo bakinshi dauke da sallama
Na’im da mujaheed suka hada baki wajen amsa masa sallamar tashi
Jikinshi duk a sanyaye yake. Sukayi mishi nuni d gurin zama have a sit
Alhaji Mahmud ya samu guri ya zauna. Bayan sun gaisa yadanyi shiru kamar yana tsoron abinda zai fadan
Chan dai ya nisa yasoma mgn”doctor na’im gani na sake dawowa a gareka a karo na uku ina mai Neman taimakonka akan rayuwar Dana affan Wanda shi kadai ne Dan dana mallaka nake kuma yi mishi son da bb abinda nakeso sama dashi”
Na’im ya numfasa yasoma mgn dashi kai tsaye “kamar yadda dai na fada maka tun farko zan taimaki affan ne kadae idan har zai amsa laifin shi nayiwa raheelat fyade a ranar biyhday party dinshi da sukayi inviting dinta shi da abokananshi
Alhaji Mahmud ya sake sauke dogon numfashi yana goge zufa da handkacief dinshi. Yana mamakin yadda yaron yake bala’in yi mishi kwarjini. gashi karamin yaro dan cikin shi ammn yana ta wahalar dasu akan abin da bai taka kara ya karya ba
Lallai in yanason lafiyar Dan nashi yazama dole ya futo da ainahin gskyr maganar d yake boyewa tsawon lokaci, in ba HK ba kuma xai rasa yar guntuwar damar data rage mishi
Kuyi hkr da wannan doctor na’im (aa) fans
Har kullum baxan gaji da dangwala muku ba love u oll????????????????