NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 2) 28&29

   ~Book 2~ ????????28
…………A yanda Na kula har yanzu bayajin dad’in jikinsa, dan komai a d’an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damuwa nima,

Na cire Abdurraheem Na kwantar, sannan Na mik’e zuwa garesa, durk’usawa nayi Na d’ora hannayena akan gwiwarsa, “yalla6ai lafiya?”.

       Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk’ura na mik’e da nufin barin masa d’akinma duka.
     Hannuna ya rik’o, na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d’ago motsa ba.
    Na cije lips ina had’iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y’ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidane mukanyi hira koyayane, amma shifa magana ma idan bai ra’ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk’iba, Momma ta had’ani da aiki, a watannin baya kad’an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya Momma take tunanin zan iya canja Galadima? murd’ad’d’en mutumne shi mai wahalar sha’ani, ga tsantsar mulki da k’asaita da suka zama jinin jikinsa, s………
        Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad’awa danayi jikinsa, shikuma yay baya ya fad’a kan gadon, kad’an ya rage mu danne Amaturrahman, yad’an kauce kad’an yana sauke ajiyar zuciya.
      Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.
   Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k’irjinsa yana d’an buga bayana da d’ayan hannun, zanyi magana ya d’ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.
      Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na danne wajen sannan na d’ora kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips.. 
     Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d’in k’ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk’ura zan tashi ya maidani.
      Munkai mintuna 7 sannan ya zameni ya kwantar ya mik’e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad’ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk’ar d’aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid’a abin salla, domin rama sallolin da suka riskesa yana barci.
       6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y’an uwansa, tunani nai ko yanayin nasa barcin kenan shikuma, saboda wahalar da suka sha,
      d’aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina. 
      Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi kuka, aidai sa jira na fito mu gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.
        Sallamar da akeyi na amsa da k’yar, sannan na bada izinin shigowa,   cikin bayina ne guda biyu, zubewa k’asa sukayi suna gaisheni.
        Cikin girmamawa d’aya tace, “dama ance mu gani idan kin fitone”.
    Nace, “Hummm”.
   Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik’ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.
      Kusan mintuna 5 saiga Samha ta shigo, ta durk’usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d’ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k’arfin hali ina tashi zaune.
     Muryarta da alamun tasha kuka itama tace, “Aunty Uncle Sam na kiranki”.
     Kai na jinjina mata kawai, na tashi gaba d’aya na d’auki mayafi muka tafi tare.
    Koda mukaje k’ofar falon bata Shigaba, nikad’ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d’aya.
          
A falo na iskeshi cikin doguwar kujera a kwance, ya kifa yaron d’aya a k’irjinsa Wanda nake k’yautata zaton Abdurraheem ne, wayace manne a kunnensa, amma a hankali yake magana koni danake tsaye cikin falon banaji, na kalli abincin da aka jere a tsakar falon ina zama a kujera.
      Bai dad’eba ya kammala wayar, idonsa dake jajir har yanzu ya d’ago yad’an kalleni, jijiyar kansa dukta tashi rud’u-rud’u. saida yad’an lumshe idanu kafin ya motsa la66ansa ahankali yace, “kici abinci inji inno”.
     Dukda maganar taban haushi haka na danne, wato inji inno ma ba injishi ba ko?. Sakkowa nayi k’asan lallausan carpet d’in, d’aya bayan d’aya na bubbud’e kulolin da kwanikan, a rai na ina tunanin ina zamu kai wanna abincin haka?.
    Tashi nayi zuwa ga show glass d’in dake falon, wadda aka jera mugs and glass cups, mug d’aya na d’akko, naje wajen wanke hannu dake a wajen dinning, Wanda babu tebirin cin abincin ba’a sakaba, bansan dalinsa nak’in sakawarba, wanko mug d’in nayi na had’o kayan tea a ciki dake a wajen show glass d’in suma, na zubo ruwan zafi daga dispenser na dawo, yana kwance yanda na barsa, yanzuma garda su lumshe idanu yanata shafa kan yaron zuwa bayansa.
    Na kallesa a d’arare Dan yaune karan farko dazan aikata hakan, komi yake buk’ata yakan yi da kansa, ko ruwa wannan inhar bana manta ba bai ta6a cewa na d’auka masaba, sometimes ma sai idan yasaka Samha ko Sauban su masa Abu saini na tashi nayi idan naga rashin dacewar hakan, amma dai dakansa yace Munaya yimin kaza, gaskiya bai ta6aba. muryata na rawa nace, “bismillah”.
     Shiru kamar bazai bud’e idonsa ba saikuma ya bud’e d’aya yad’an kalleni ya kauda kansa. cikin k’asaitar nan tasa yace, “miyasa?”.
     “miyasa kuma?”. ‘nakuma maimaita maganar ina k’ok’arin janye hannuna’.
      Carab ya rik’e hannun nawa, ni tsoroma ya bani, na kalli hannunsa da nawan ga mug cikeda ruwan zafi yanata turiri, kuma zafin yana ta6amin gwiwar yatsuna, idonsa a lumshe har yanzu, idona harya fara tara kwalla, nayi alk’awarin koda hannun zai toye gaba d’aya bazan tanka masaba, ai yasan abinda yake dai-dai da akasin haka.
      Saida mukayi 1minute a haka kafin ya maido face d’insa inda nake yana kallona, ya d’age gira d’aya yana fad’in “da zafi ne?”.
        Humm lallai Galadima akwai rainin wayo, na fad’a a zuciyata, janye idona nayi daga kansa na maida kan Abdurraheem dahar yanzu yake kwance a bisa cikinsa.
     Ya yamutse fuska yana sakin hannun, cikin basarwa yace, “inason jarumta”.
     Had’iye kukan dake k’ok’arin tahomin nayi, na ajiye Mug d’in na cigaba da zuba masa farfesu a k’aramin bowl batareda nayi koda tariba.
      Tashi yay zaune yana jije lips, yayinda hannunsa ke rik’e da yaron, d’ayan kuma ya dafe saitin zuciyarsa, a wahalce yake fisgo numfashi kafin ya fesoshi, tun kuma d’azu na lura da hakan, kalmar zafi daya fad’amin na shiga fassarawa, har na fahimci da manufa ya fad’a, hakanne ya Sani murmusawa batareda na d’agoba ina zuba masa farfesun nace, “tabbas duk zafi sunansa zafi, amma akan samu banbance-banbance wajen banbancesu, wani zafin a gangar jiki muke jinsa, wani ko tawani sashen jikin ake samunsa, wani zuciya, wani rayuwarma gaba d’aya Ce ke tsintar kan a zafi, saidai babu zafi mafi rad’ad’i daya kai na Mutuwa, idan da zamuyi nazari zamu fahimci rayuwa tana a tsare ne mataki-mataki, sannan iri d’ayace ga kowanne launin halitta na mutum ko aljan ko dabba, Dan mukan tainci kanmune akusan mizani d’aya, dukda ubangiji ya banbantamu ta halitta da ayyuka da tunani ko nace kaifin basira, ko’a jinsi launi biyune, akwai namiji akwai mace, dukkan rayuwa takan farane da mafari yalla6ai” na d’ago ina sake mik’a masa mug d’in tea d’in again, a mamakina a yanzu saiya kar6a, na lashi lips d’ina na k’asa ina gyara zama sosai da maida hankalina wajen juya kunun dana zuba a cup da tsokali, cikin nisawa nacigaba da fad’in, “mafarin rayuwa shine dasuwar bawa a cikin mahaifiya, mukanyi wannan rayuwarne a cikin halin su wanene mu? daga nan sai matakin haihuwa, shigowa duniya a bisa bigiren wane ahali muka kasance, dukkan ahalin daka Sani sunada matsalarsu, saidai tawasu tafi tawasu zafi, daga ranka ka iso filin gwagwarmaya wato duniya, shikenan littafinka dayazama rubutacce tun a cikin mahaifiya saiya fara aiki, mala’iku masu kula da fitar numfashi su dasa alk’alaminsu, masu kula da abinci suma haka, masu kula da ruwa ma haka, masu kula da magana ma haka, masu kula da kallo ma haka, masu kula da ji ma haka, masu kula da duk wani motsinka ma haka, tafiya, zama, kwanciya dadai sauransu, kowa ana haihuwarsa tsaftatatccene, iyaye suke fara juya akalar rayuwa, walau mai k’yau ko sa6aninta, (kaga kenan akwai hisabi tsakanin iyaye da y’ay’a ma kenan?) daga nan rayuwa zata cigaba da yad’o kamar d’an duma, tun ana maka, harka koma koya, harka fara iyawa da kanka, harma ka kware ka koyama wani, (wanne ka iya? ko ka koya? yarage ruwanka) duk Wanda kaga an masa a farko to tabbas za’a k’ara masa a k’arshe, kodai silar tsufa, ko ciwo, kokuma iftila’in rayuwa, kokuma na k’arshe shine hidimar gawarka, a dukkanin dunk’ulalliyar rayuwar da kowanne bawa yakanyi zakaga cike take da k’alubale masu zuwa da zafi kala-kala, yalla6ai kasan mike taushe wannan rad’ad’in zafin kuwa?”. nayi maganar ina d’ago ido na kallesa. A mamakina sainaga ya girgiza min kansa. na murmusa ina janye idona daga kansa na maida ga kofin tea d’in ina masa alamar yasha mana.
    Yamutse fuska yay irin kalar tausayinnan.
    Nima sainayi kwal-kwal da ido kamar zanyi kuka, na had’e hannayena waje d’aya alamar rok’o????????..
     Lips d’insa yad’an ciza kafin yafara shan tea d’in. Nayi salute nashi ina masa jinjina????????.
     Basarwa yayi, nima saina kad’a ido ina tunzura baki gaba, sannan nacigaba da fad’in, “Abinda ke taushe wannan rad’ad’in zafin shine *_HAK’URI_*. hak’uri muhimmun sinadarine dake jagorantar garkuwar jiki ta kowacce launin halittar jiki na  d’an Adam, walau a fili take ko a 6oye take, saidai babban makarinsa da taskar adanashi shine *_ZUCIYA!_* a duk lokacinda k’arfin zuciya ya raunana to zaka samu madarar hak’uri ta salwanta, idan zafi yanata yawa babu wannan hak’urin bugu d’aya take duk wani ma’adani na cikinta saiya tarwatse, saikaga an rasa ayyukan jiki dana ruhi, shikenan wane yazama labari. daga lokacin da rad’ad’in fitar rai ya kusanci bawa dukkan mala’ikunan da suka kasance tare dakai a randa kazo duniya saisu fara janyewa daga gareka, wani bawan kafin ranar mutuwarsa zakaga ya daina cin abinci, hakan na nufin mala’ikan dake kula da abinci ka yagama aikinsa, domin ya zagaye duniya kaf duk yawan abincin dake cikin ta babu rabonka koda kwayan gero ne, ka gama cinyewa, wani kafin ranar Mutuwa ya daina shan ruwa, aikin mala’ikan dake kula da ruwa shanka yagama k’arewa kenan, duk yawan koramu da tafkuna na duniya bakada sauran rabo na ruwa, ka shanye naka, wani kafin Mutuwa ya daina magana, mala’ikan dake kula da furucinka yagama aikinsa, babu sauran wata kalma data rage harshenka ya furta, wani kafin Mutuwa ya daina ji, mala’ikan dake kula da jinsa ya gama aikinsa, babu wata kalma data rage kunnensa zaiji, wani kafin Mutuwa ya daina gani, mala’ikan dake kula da ganinsa ya gama aikinsa, kwayar idonsa bazata sake kallon wani abuba, wani kafin Mutuwa ya daina tafiya, mala’ikan dake kula da tafiyarsa ya gama aikinsa, haka-haka wad’annan mala’ikun zasuyita ja baya suma barinka, har yarage sai mai kula da fitar numfashi kawai, daga ranar da UBANGIJI yace yana buk’atar ganinka shikenan takuma k’are, sai rundinar mala’iku su had’u su takewa kwamandan mala’ikan d’aukar rai baya, idan kai mutumin kirkine fararen mala’ikune, idan na banzane mala’iku masu azaba zasu take masa baya, sauran al’amari kuma sai Wanda ya haliccemu yasan ya zata kasance????. zakasha mamaki idanfa nace maka duk wannan zafin k’aramin zafine acikin kashi-kashin na abinda ya shafi haluttu, shi wannan zafin ana kiransa zafin na za6in kai, kokuma zafi na a haka tsarin yazo, ma’ana kaine ka had’ama kanka wannan zafin, kokuma wanine ya had’a makashi. Abu na biyu shine zafi na rad’ad’in Mutuwa, dolene kowa saiya d’an d’anashi, walau kafiri ko Musulmi, saidai akwai banbance-banbance na awanne tsari ka koma ga ALLAH, ba wannan zafinne kawai ke jiran d’an Adam ba, akwai zafin na *_BARZAHU_* shi ake kira kwanciyar kabari, mika tanada, mi zaka tarar shine abin tambayar, wannan kam ALLAH ne mafi sanin wad’anda zasu d’and’ana wannan zafin (ALLAH ka datar damu????)”.
      Akan la66a Galadima ya amsa da amin, Munaya ta share hawayenta, ta cigaba da fad’in sai zafi mai gaba d’aya, shine na makoma, *_WUTA KO ALJANNA_*, yalla6ai wad’annan jimullar zafin ga d’an Adam tilas ne, na cikin rayuwa shine zafin da zaka iya controlling nashi ta hanyar hak’uri, to Ashe bai kamata ka tasirantar da wannan zafin ya cigaba da k’onaka ba, musamman idan zakayi dubi dawasu ni’imomin da ALLAH yamaka a cikin wannan zafin, ka kasance mai yawan hak’uri saikaga kanka cikin masu yawan riba, wlhy ta wannan hanyarne kawai zaka zama mai *_NASARA_* akan mak’iya ni……….”.
           Maganata ta katse saboda knocking d’in k’ofar da akayi, kallon juna mukayi ni da shi, yay wani luuu da idanunsa ya lumshesu, hakanne  ya sakani bada izinin shigowa kawai batare da na jira amsa daga garesa ba.
      Sarkin k’ofane ya shigo, ya zube yana gaishe mu, nice kawai na amsa, boss kam hannu kawai ya iya d’aga masa, yay mana ya jiki again, nanma nice nakuma amsa shi, cikeda girmamawa yace, “ranki ya dad’e yalla6ai harun ne ke buk’atar iso”.
     Saida gabana ya fad’i, na had’iye wani yawu mai kauri ina kallon galadima dayay biris damu yanata shafa kan d’ansa, bud’e idonsa jajaye yayi akan Sarkin k’ofa, ya jinjina masa kai alamar ya shigo dashi.
     Kallonsa nayi tamkar zanyi magana saikuma nai shiru, a raina ina mamakin wannan munafukin dami yazo kuma?….. ban kai k’arshen zancen zucin ba Harun yay sallama, nid’ince dai na amsa cikin danne zuciya da fushina.
    Ya zauna fuskarsa d’auke da murmushi.
    Nima saina saki tawa ina fad’in, “barka da hantsi ranka ya dad’e”.
      “Barka dai gimbiyarmu, ya jikin ki dana yalla6ai?”.
     Na kalli Galadima dayay shiru kansan jingine da kujera ido a rufe, “da sauk’i”,  na fad’a ina mik’ewa na koma saman kujera, dan bazan ta6a barin falonba sainaji uwarmi ya kawosa.
     Ya amsa da “masha ALLAH, ALLAH ya kiyaye gaba ya k’ara lafiya”.
      “humm” na fad’a ina amsawa da “Amin dai”.
  
       Hankalinsa ya maida ga Galadima, “Sameer ya jikin?”.
     Bud’e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d’in hannunsa a teble d’in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yana taunar lips.
     Banga alamar damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa.
       Saidai idonsa k’uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d’in yana barci, mik’ewa yay yana fad’in, “my son zo mu gaisa ko?”.
     Ganin haka nima nayi azamar mik’ewa nakai ga Galadima kafin shi ya isa, na d’auke Abdurraheem d’in ina fad’in “ai barcima yake ranka ya dad’e”.
     Ba Harun ba hatta da Galadima saida yaymin kallon mamaki, nakoyi cid’in-cid’in da fuska yandama bazaice nabama Harun d’inba.
     Baki ya bud’e kamar zaice wani Abu saikuma yay shiru yana kauda kansa daga kallona, nima saina ta6e baki ina barin falon da harar Harun ta gefen ido.
    Gaban Harun ya fad’i, mi yarinyarnan take nufi?……
      Kafin ya lalubo amsar ya tsinkayi maganar galadima yana cewa, “sorry Harun, kasan har yanzu a tsorace take, duk wani motsinsu akan idontane”.
      Murmushin basarwa harun yayi, yace, “ai dolene hakan ranka ya dad’e, abinne akwai tsoratarwa, wlhy jiya tashin hankalinnan ne yasaka azababben ciwon kai rufeni, shiyyasa ko ganina ba’ayiba, yanzu police d’in ina suka samosu?”.
      “humm” Galadima ya fad’a cikin tsananin taune lips da k’unar zuciya, ya bud’e baki a hankali zaiyi magana nida ke bayansu basu saniba nai saurin tareshi da fad’in “a hannun wasu munafukaine ranka ya dad’e, ai koni daza’a bani baiwar nan da aka kama da yaran wlhy saina tsoma kanta cikin drum d’in ruwa harsaita daina Numfashi zan barta, kafin sannan kuma nagamajin labarin Wanda ya sakata, amma shi my boss ai a station suka zauna har aka kawo yaran, badasu akaje farautarba”.
       Tsuramin ido Galadima yayi cikin tsagwaron mamaki, miyasa to zanzo na kasa na tsare dukkan wani motsin Harun d’in? ya kula satar yaran tana Neman ta6a tunaninta takasa banbance Wanda zata zarga, ai Harun yawuce ya 6oye masa wani sirri na sashen rayuwarsa, tun da babu abinda bai saniba na baya, saidai abinda ba’a rasaba kam, danne ransa yayi ya nuna hakane, yabari har Harun d’in ya tafi sannan yaji dalilinta.
      Ina kallon Sassanyar ajiyar zuciya da Harun ya sauke a 6oye, sannan yace, “ai police d’in sun cancanci Babar k’yauta, shiyyasama na shirya musu ita, sunyi aiki irinnan jaruman masu tsaro”.
      “hakane wlhy ranka ya dad’e ”. Na fad’a cikin murmushi.
     Dukfa yanda Harun yaso bugar cikin Galadima yaji yanda abun yake, na kafa na tsare, dayayi tambaya nike bashi amsa, saiya d’auka kodan Galadima bashida lafiyarne shiyyasa bai iya amsawa, tun da tunda ya shigo baice k’ala ba, kuma yasan yanayin ciwonsa, a baya ma shikan bashi taimako, baidai tsinci komai ba yay mana sallama ya fita, da k’udirin anjima ma zai dawo ne.
      A sace na raka bayansa da harara, sannan na kalli Galadima na basar, dukda kallon tuhuma dayake jifana dashi kuwa.
       Wani farfesun na sake zuba masa na mik’a masa.
    Batare da ya kar6aba cikin k’ank’ance idon bala’i yace, “mikikayi haka? kinsan waye Harun a wajena?”.
       Kaina na girgiza masa.
       Yaja tagwayen tsaki yana hararata, “halan satar yaranki yafara shafar tunaninki ne? kina tunanin akwai abinda Harun zai iya gazaji daga sirrina?”.
      Na d’an ta6e baki ina jawo teble d’in gabansa, na d’ora bowl d’in dana zuba farfesun, baki ya bud’e kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. nima bance uffanba na ajiye masa sannan na koma k’asa Na zauna na zuba sabon kunu nahau sha.
      Kwafa yayi, yace, kinma maidani d’an iska ko?”.
       “Hummm” na fad’a kawai, naimasa kallo d’aya “yalla6ai wani karatun akan barsane a yanda yazo, sai idan lokacin fasaarashi yayi amasa fashin bak’i, nasan darajar alak’ata dakai batakai koda rabin tsakaninka da Harun ba, domin ni alak’ar wucin gadice ta had’amu, k’iris ma ya rage ta k’are, saidai inason nabama y’ay’ana kamar yanda ka fad’a kariya koda sau d’ayane a rayuwarsu kafin na barsu, dan haka maida wuk’arka a kube, lokacin zareta baiyiba, sometimes kalmar Mahangi da mai hange takanyi kamanceceniya, dan bakowa ke iya rarrabata wajen fasaara ba, amma kalmomine duka masu harshen damo, wani k’alubalen saida tunanin mai zurfi, wata k’oramar ruwan mutanen dake zagaye da ita sukanyi imani bazata balle harta cisu ba, saboda sun yarda sud’in masuntane da kullum suke rayuwa cikin wannan k’oramar, abin mamaki saikaga wataran an wayi gari da mutanen da muhalansu duk wannan ruwan ya had’iyesu, abinda basu ganeba bakowacce irin alak’a bace ake kulla amana da ita, wani farin idan yashiga cikin fari banbance k’arkonsa saidai ALLAH”.
     Tashi nayi nai shigewata bedroom d’insa.
     A fusace shima ya mik’e zai bini, kad’an yarage ya zubda farfesun dana ajiye masa, ALLAH dai ya kiyaye ya shallakesa ya wuce.
     Hucin mutum kawai naji a bayana, hakan yasani waigowa da sauri, hannu ya dunk’ule zai kaimin naushi, nai azamar fad’awa saman gadon ina zaro ido waje, a lallai Abu ya girmama, nikuma miye nawa da zai sauke fushinsa a kaina? nai maganar a zuciyata.
      Janye hannunsa yayi yana ciza lips d’in sa da k’arfi, idonsa dukya kuma rinewa, ya dunk’ule hannun ya daki d’ayan dashi, muryarsa har rawa take yace, “Miyasa zaki kuma hargitsan tunani ne? Minene laifin Harun shikuma? kuna nufin duk Wanda na yarda dashi shine mak’iyina? Kai impossible wlhy, Munaya wakikema aiki a kaina? ya rankwafo kaina, kaikace cinyeni d’anya zaiyi, saikace zaki yaga bandar nama, da k’arfi yace, “bazaki sanarmin ba saina k’arar da numfashinki ne waishin Ubanwa ke fad’a miki wad’annan maganganun da kike d’aureni dasu a ko yaushe?!!!”. Ya k’are maganar cikin tsananin tsawa da k’araji.
     Ba k’aramin firgita nayiba, badan karnayi k’arya ba danace har wutar bala’i Nagano a idonsa tana ci, wannan bawa akwai zuciyar tsiya, idan zai zama jami’in tsaro da k’asarmu ta amfanu da yawa………
     Da k’arfi ya girgizani, saboda ganin saboda rainin wayo tunanima na tafi……….
      A firgice nace “yi hak’uri zauna zan fad’a maka”. na fad’i hakanne dan kawai ina ganin itace mafitar dazan nema ya fasa had’iyeni. a mamakina kuwa saiya tashin ya zauna yana dafe k’irji hawaye nabin kumatunsa.
     Tsantsar tausayinsa ce ta kamani, na tashi na d’akko ruwa na dawo kusa dashi na zauna, addu’oi na shiga tofawa a ruwan, yana zaune dafe da kansa, da alama kuka ma yakeyi, dan ajiyar zuciyar da yakeyi ta yawaita.
         Saida na gama na dafa ka fad’arsa, tamkar bazai d’agoba saikuma ya  kalleni, ruwan addu’ar na basa, babu musu ya kar6a ya shanye, duk da baima san mita bashiba, idanma poison ne  dai gara ma yasha ya mutu ya huta.
     Mintunansa biyu zuwa uku dasha yafara sauke ajiyar zuciya mai k’arfin gaske, saiya zame kuma ya kwanta, kafin kacemi barci ya saceshi a haka.
     nima ajiyar zuciyar nayi ina girgiza kai da share hawayen dake silalomin, ina rok’on ALLAH ya kawoma wannan bawan nasa sauk’i da rangwame cikin gaggawa da  warwarewar al’amura.
    Dagashi har yaran tausayi suke bani, nayi zurfi a tunani wayarsa tayi ring, kamar zan share saikuma Na tuna maybe Momma ce, tashi nayi zuwa inda wayar take, aikam dai itace, nayi picking jiki a sanyaye, dan tunanina kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y’ar raharta ma tace, “Muh’d duk hidimar sunance haka?”.
      “Uhm Momma bashi bane nice”.
      “a’a d’iyata kece?”.
     “eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie?”.
      “Alhmdllh d’iyata, ya k’arfin jikinki kema? ina yaran?”.
     Gabana ya fad’i, Na had’iye wani yawu da k’yar, cikin in ina nace, “lafiyar kowa k’alau Momma, shima y… yana barcine”.
      Dagacan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace, “humm d’iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin?”.
     Na had’iye yawu dak’yar, “kiyi hak’uri Momma, ki gafarcemu”.
      “Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh’d yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak’on mak’iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k’arshen komai, na yarda dake 100% Munaya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k’uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad’a miki tun farko karki ta6ama Muh’d sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad’a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh’d yabar duniya bazanyi bak’in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad’anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba’aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d’inmu Na k’arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda yafaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya”. Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad’in “ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k’autata kar6ar Abu mai wahala  (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y’ay’anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y’an uwansa,  nusar dashi abinda duk baki gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d’aya shine mafi had’ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak’uri nasan bak’yajin dad’in zama da Muh’d ko kad’an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane kansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa”.
     Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci k’arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd’ad’d’e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halinsa saika zuna dashi, Mara hak’uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak’anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu saisun tashi inhar d’aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki.
   
********************
       Har akayi la’asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d’insu suna can an kaima papi su tun d’azun.
      Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan.
 
*******************
         Bayan la’asar kad’an Galadima ya farka, ganin shi kad’aine a d’akin ya tashi zaune bakinsa d’auke da addu’ar tashi barci, jin k’irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d’azun, saidai abinda ba’a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala.
     Sallan zuhur da la’asar ya rama, tareda addu’ar neman sauk’i akan wannan lamari da samun k’arfin zuciya, dolene saiyayi yak’i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna baifi 2 ba saigasu inno.
     Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci,  sunsan Munaya kuma tana d’akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad’ad’a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d’ai-d’ai.
    Inno ta mangari kansa tana fad’in “ja’iri baka sanmu bane halan?”.
        Hannunta ya rik’e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k’asaita yace, “Inno wai ina zakuje ne?”.
       “inda muka fito mana”. Inno tafad’a tana zama kujerar kusa dashi.
       “saikace wad’anda ake kora?”.
      “A’a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka”.
      “To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun gode sosai da sosai”.
         “Amin” inno tafad’a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu’oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata.
     Yace, “mom hada ke wai?”.
      “eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tunda ALLAH ya iyakance komai cikin sauk’i, nanda y’an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakamata dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai”.
     Kansa ya jinjina mata alamar amsawa.
     A gurguje sukad’an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba masa takumace yamata alk’awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d’auke da y’an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya, (nace, “aiki jaa kenan, inba dariyar k’udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad’e baka ganiba Uncle triplets????).
  
      Galadima ma madai yatsansa d’aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina kansa da kujera, maganganun Munaya na d’azun kawai yake nazari dalla-dalla.
      Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki.
    Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?. Tace, “yana 6angaren Ummu hasheem”.
     Baice komaiba, itama ta k’araso ta d’auki Ammaurrahman data rik’e yatsansa gam tak’i saki.. 
     d’agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman.
     Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud’awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba.
        ********
Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d’in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek’a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akash Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren.
    Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, doctors zasu kuma duba lafiyarsu.
★★★★★★
     Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k’arasa d’akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k’aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, babu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa.
     Harun yace, “haba dai, wannan y’ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand’an bincika yarannan danni na lurama kamar ba wad’anda muka saka bane sukayi aikinnan?”.
       “sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had’a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan sunyi luff ne sai k’ura ta natsa su fito”.
     “ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k’asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa”.. 
        “karka damu zamu sauke masa shine ai”……………????
????abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya  kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai????????.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*????????????
*_typing????_*
 ???? *_HASKE WRITERS ASSO….._*
           *_RAINA KAMA…..!!_*
                  _(Kaga gayya)_
              *_Bilyn Abdull ce????????_*
   ~Book 2~ ????????29
…………..Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d’akin kan katifa tace, “ranki ya dad’e lafiya kuwa?”.
       Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad’an murmusa, “uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta”.
      “eh lallai hakan yanada k’yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d’ayaba”.
    “aiba shi kad’ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi ”.
     A to hakan yayi.
  Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita.
       Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine?”.
       Nayi murmushi, “yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy”.
       Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina.
     Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d’auke da Qur’an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad’in yanda na sameshi, Addu’a da karatun Qur’an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d’an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d’auki Qur’an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa).
      Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d’ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur’an d’in ya ajiye, ya cire medical glasses d’insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad’an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo.
     Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d’an nesa dashi kad’an.
       Ya lashe le6ensa da cizarsa kad’an yana hard’e hannayensa a k’irji.
      Muryata can k’asan mak’oshi nace, “yaya jikin?”.
      Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace, “Munaya!?”.
      “Na’am”. Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d’aya saboda ya tsareni da nasa.
      Huci yad’an furzar, ya cire hannayensa daga k’irji yana gyara zama, “Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d’azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok’o nake miki na k’arshe akan ki fad’amin abinda kika sani, ni d’an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad’i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad’ai a kuma ke6antaccen waje” yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad’in “Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k’uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k’afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito, domin idan kinganni a lokacin da nake karatu da koyan sana’oi bazaki ta6a kawo ni jinin sarauta baneba, ko d’an wani, nayi gwagwarmaya sosai irin wadda d’a Mara gata yakeyi, badan mahaifiyata bata sona bane ta tsaya tsayin daka wajen ganin na horu kona nemi na kaina, hikimarta itace nazama jarumi mai yawan juriya, nakuma kwato mana y’ancinmu a lokacinda ya dace, duk wannan fad’i tashin da kikaga inayi wlhy badan nayi mulki baneba kamar yanda su suke tunani, Burina kawai nasan miyasa aka durk’usarmin da mahaifi? Tabbas ni jinin sarautane gaba da baya, kuma yana yawo a cikin jinina, amma rashin kwanciyar hankalin dake cikin sarauta baya birgeni, kallon kitse kawai akema rogo, ayau inason Kituna kema kin haifi yaranda sun rigada sun shigo cikin wannan harmutsi, tunda tazama jininsu, ki fad’amin kodan mu gyaramusu gobensu su rayu cikin salama koda bama numfashine, nasan hakanan bazakima Harun abinda kikai masa d’azunba saboda son zuciya kawai, please miyasa kika hanashi d’aukar Abdurraheem ne? Miyasa kikak’i barina na fad’a masa gaskiyar abinda ya faru?”.
     Shiru nayi nakasa cewa komai, sai faman had’iye abinda ya tsayamin a mak’oshi nakeyi, Dan bansan yanda zai kalli abunba koya fahimceshi, babu Abu mafi saka rud’u irin cin amanar makusanci, gashi dai a Ransa shifa ba k’aunarka yakeba, amma kulum yafi kowa kusanci da kai, da Nuna girmama alak’ar tsakaninku. (ALLAH ka Shiga tsakaninmu da duk wani Wanda yake tare damu a matsayin fuka biyu, Dan yanzu abinda yafi komai yawaita kenan a rayuwar d’an adam☹????).
      Cikin katsemun tunani Yace, “please my friend say Something mana”.
      Kaina na jinjina masa, cikin nutsuwa nafara masa bayani, Dan yau nayi alk’awarin sanar masa komai, koda zai samu wani haske akan lamarin, shima yasamu nutsuwa a rayuwarsa.
          
     “Tabbas kamar yanda kake zargi aiki nakema wani, saidai fahimtar wanene d’in shine mai wahala, na fad’a maka tun farko a dalilin bak’on Abbanmu naji wani yankin matsalasa da bai ta6a sanarma waniba a ahalinsa, a lokacin da wancan abin yafaru Abba yak’i fad’ama kowa dalilin fishinsa a kanmu, dakuma abinda muka masa, hakanne yasaka innarmu zuwa tasamu baba mai kanwa abokin kakanmu na k’ut da k’ut ta sanar masa fushin da mahaifinmu keyi damu, ankuma bashi hak’uri yak’i sauraren kowa, gashi ba dad’in zama takejiba cikin matan gidanmu, wannan Abu daya faru sai sukejin dad’i damata arashi da habaici, harma damu kanmu. baba mai kanwa yace taje zai masa magana, bayannan bamusan misuka tattaunaba. Sai da bayan komai ya lafa harma mun fara karatu sai sanata halluru ya buk’aci abbanmu yabama y’ay’ansa biyu auren yara cikin yaransa, sunzo gidanmu har suka nuna mune za6insu, a lokacin tabbas naji a raina Sa’eed yamin sosai a rai…..”
    Galadima ya tsuk’e fuska yana taune lips dajan k’aramin tsaki.
    ‘Dagowa nayi nad’an kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayiba, nima sharewa nayi na cigaba, “bamusan miya faruba sukace Zarah da siyama sukeso, wannan Abu ya 6atama Abbanmu rai, dan aganinsa anyi wani abune domin k’untatama mahaifiyarmu, hakkane yasashi zuwa ya sanarma Baba mai kanwa, dama duk dai wani Abu dazai taso gidanmu shine ake sanarmawa, yayi sasanci koya tsawatar, koda kuwa innro ce. bayan Abbanmu yaje da kwana d’aya, sai innarmu ta aikemu wajensa muka kaimasa goro da y’ar sayayyar da takan masa lokaci-lokaci, saboda yamusu hallaci a rayuwa a yanda take bamu labari, shiyyasa a kullum take d’aukarsa uba”.
      Mun iske baba mai kanwa a d’akinsa na zaure kamar ko yaushe, muka gaidashi cikin girmamawa da tsokanarsa a matsayinsa na kaka, shima ya tsokanemu tareda sakamana albarka kamar yanda ya saba, saiya murmusa tareda gyaran murya, hakanne yasaka muka nutsu dan fahimtar magana mai muhimmanci zaiyi, ya nisa cikin dattako na tsufa ya fara fad’in___”.
      _“yarana kuyi hak’uri da damuwar da kuka tsinci kanku a ciki, wadda tunkafin Ku mahaifiyarku a ciki take, amma nasan watan watarana kuda ita duksai kunci ribar wannan hak’urin, karkuyi bak’inciki akan hanaku wannan auren da akayi na y’ay’an halluru, dama can sud’in ba mazajenku baneba, hasalima aurensu ba alkairi baneba”._.   
      “A razane duk muka kallesa baki bud’e”.
     Yayi murmushinsu na manya, _“abin ya baku mamaki ko? Humm ba abin mamaki baneba, yau zan fad’a muku wani sirrin dabaku saniba, domin ina hango wani tarin alkairi tattare da rayuwarku, inakuma ji ajikina kune wad’anda zaku fidda mahaifinku daga wata sark’ak’iya daya Shiga a dalilin taimako tun kafin a haifeku. Alhaji halluru da wata manufa ya nema ma y’ay’ansa auren d’iyan mahaifinku, amma Shifa na fuskanci bai fahimci hakanba, sabo da ya aminta da amintar dake tsakaninsu ta tsawon shekaru. Alhaji halluru yanason shiga jikin mahaifinku ne sosai danya kar6ama iyayen gidansa wani sirri dake hannun Auwalu, ina k’yautata zaton shine kukaji wani Abu a ciki, shi kansa Auwalu baisan minene a ciki ba, domin kuwa bashi akai amana ya Isar dashi ga Wanda yadace, kuma baita6a yunk’urin ya duba ba ya barsa a yanda aka bashi. Kuyi hak’uri akwai wasu k’alubale dake tunkaro rayuwarku, kuma yanada tsananin sark’ak’iya,  saidai insha ALLAH zan baku dikkan gudunmawa inhar ALLAH yabani tsawon ran kaiwa wannan lokacin, Ku dage da yawan sadaka kudai da mik’a lamuranku ga ALLAH mai kowa da da sirrin komai, ALLAH kuma ya cigaba da tsareku.”_
      “duk cikin tsantsar damuwa muka amsa masa da amin, haka muka baro gidan jikinmu duk a sanyaye, dan har innarmu tata bincikarmu a lokacin, sai muka fake da ciwon mara. sati biyu da faruwar wannan lamari sai Munubiya tafara min k’orafin yawaita  mafarkin wani bawan ALLAH, kullum takan gansa ne a cikin dokar daji zagaye da wasu irin halittu masu ban tsoro suna kaimasa hari zasu halakashi, yakanyi k’ok’arin kare kansa amma saiya gaza, idan yanemi taimakonta kuma bata zuwa, saboda tsoro suke bata. Duk sanda tafad’amin wannan mafarki sainace bata addu’a ne, shaid’anune kawai. haka taita jera wannan mafarki kullum dare, kuma da gari ya waye bazata fasa fad’aminba, tundai abin na damunmu har muka watsar muka cigaba da harkokinmu. Ranar kuma sai nima nayi mafarkin makamancin na Munubiya, saidai nikuma na shige ina taya wannan mutumin kare kansa ga wad’annan halittun kamar yanda ya buk’ata, na jigata sosai dan harnatashi jikina duk yayi week, nima ban 6oyema Munubiya komaiba na sanar mata, abin yabata mamaki, kuma tundaga sannan nima na cigaba da mafarkin, kullum kuma ina taimakon wannan mutumin dako fuskarsa ban ta6a ganiba, itako Munubiya takan cemin saidai ta tsaya kallonsa daga nesa yana bata tausayi, kuma yana shan nuna mata tazo ta taimakesa, amma saitak’i ta nok’e kafad’a. nikam a nawa mafarkin duk lokacin da ya nuna na taimakesa nakanje nashiga muyita fama da wad’annan halittu, ita Munubiya tana ganin fuskarsa, amma da zaran ta tashi, saita manta, niko ban ta6a ganin fuskarsa ba ko sau d’aya. Muna cikin halin wannan mafarki ne aka shiga bikin salla, tabbas randa muka had’u dakai a asibiti sainaita jin haushinka akan dalilin da ni kaina nasan bai isa daliliba, (dan kawai ina maka kallon mai girman kai bai kamata naji haushinka ba, tunda bawai hud’ace ta had’amuba, banikuma da tabbacin akanka abbanmu ke a had’ari), saidai had’uwarmu ta filin idi tasha banban data asibiti, dan a filin idi tsoro-tsoro mai gauraye da mamakinka ne suka zaunemin a zuciya, bayan kabani wayarka kabar wajen inata mamaki da juyata da tambayar kaina kaid’in wanene? Sai wata murya ta bani amsa da cewar *Galadima!* saidai koda na waigo banga kowaba sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya, na dad’e soaai wannan al’amiri bai bar rainaba, a haka muka shiga shagalin bikin y’an gidanmu, harda kuma su siyama, anan ne muka had’u da Fu’ad, harga ALLAH bansan wanene Fu’ad ba, bankuma San daga wace tawagar ango ya fitoba, amma amamakin kaina lokaci d’aya na aminta dashi, dukda kasancewata mutum mai masifar tsarta, cikin kwana d’aya kacal na saki jiki dashi, dukda ban amsa masa Cewar na kar6i soyayyarsa ba, daga ni harsu Ayusher bansan miya shiga kanmu ba muka yarda ya kaimu birnin gayu plaza ba, dukda kowannenmu ransa akwai fargaba, musamman ni danakeji kamar akwai wani gagarumin Abu dake tunkaro rayuwata. hardai muka shiga muka fito abinda ya faru ya faru a tsorace nake. fitowar wannan jarida a washegari yasaka dukkan wani ahalinmu a rud’ani, Wanda bansan yazan musalta makashi ka fahimtaba, lokaci d’aya da akazo bincikar wacece a cikinmu na amsa, dan jinai bazan iya bari Munubiya ta amsa laifinba, saboda tanada hak’uri, amma tanada tsauri Wanda nikad’ai da mahaifiyarmu muka San wannan tsaurin nata, dan sometimes takanyi mugunta amma tayi tamkar ba ita baceba, kai tsayema sai’a zargeni ita ba’ayi tunanin zata iyaba….”
          Galadima ya katseta da fad’in, “kina nufin bakece kika kusa fad’iwaba a plaza?”.
     Nad’an murmusa ina gyaran mayafina dake zamowa saboda kayan sunada santsi, “tabbas bani baceba yalla6ai, Munubiya ce, tausayi. Y’ar uwata yasani kar6ar laifin. Bayan wannan Abu ya faru nanma kowa yata fushi damu musamman Abbanmu, haryace saina nemo miji cikin 2weeks kacal, wannan ya d’agamin hankali, dan nikam kaf samarina babu Wanda yamin, amma sainaga kamar zan iya auren Fu’ad, wannan dalilin yasani kiransa bisa shawarar su feena, amma saiya toshe sukkan hanyar dazamu iya yin magana. bansan yazan misalta maka halin dana tsinci kaina a tsakaninba, naji natsani Fu’ad matuk’a, a wannan time d’inma na cigaba da wancan mafarkin, amma yazomin dawani sabon salo, sannan ita kuma Munubiya ta daina, mafarkin ya canjane zuwa salon da mutumin kanyi yunk’urin ta6ani, amma nakan hanashi damar hakan ta hanyar ja baya da masa gargad’i, shikuma saiya ringa rok’ona da cemin karna masa haka, ni fitilarsa ce. Har sannan kuma still bana ganin fuskarsa, abubuwa da yawa sun had’u sun dagulemin, dukna fige na fice hayyacina. A lokacin da baba mai kanwa yaje dubani asibiti bayan maganar aurenmu da haidar ta rushe saiyake magana cikin murmushi, k’asa-k’asa kuma ta yanda wani bazai jimu ba”.
         _“Ki kwantar da hankalinki Hussaina, har yanzu dai mijinki bai kai ga zuwaba, kuma bayan wannan ko 10 zasu k’ara zuwa saisun barki, dan akwai k’alubale a gabanki kafin kisamu nutsatstsiyar rayuwa._”
       “Da mamaki na kallesa, amma saiyak’i bani damar neman k’arin bayanin komai a wajemsa. Bayan na warke nadawo gida kuka saka aka saceni kaida Muftahu, na koma gida mangariba ta rufa a ranar, ashe wai baba mai kanwa yaga sanda na shiga gida a firgice, sai’a washe gari ya aiko a kirani, innarmu da Munubiya sunyi mamakin kiran, dan cayay Hussaina taje, (shi dama baya kiranmu Munubiya da Munaya, sai Hassana da Hussaina). Haka na saka hijjab naje, a yau baiyi wasan daya sabayi da niba, kai tsaye yafara maganarsa”.
       _“Hussaina jiya daga ina kika dawo a firgice?”._
        “A tsorace na kallesa, dan lallai tsohonnan yafara bani tsoro, dama tun muna yara mukanji ana cewa tsoronsa akeji, saidai bamusan manufar tsoronba, murmushi yayi yana gyara zama da cigaba da gyaran wasu takarsu Dana tarar yanayi, yace___”.
      _“karkiji tsoro, nimai taimakonki ne gwargwadon abinda ALLAH yabani ikon sani, dan haka ki fad’amin gaskiya_”.
      “dak’yar na iya had’iye yawu, sannan na fad’a masa abinda yafaru tsakanina daku. Murmuahi yay mai matuk’ar sauti, wanda ya bayyana fararen hak’oransa da basu wuce goma sha ba da suka rage, wad’anda a kullum zaka sameshi da ashuwaki yana d’abbak’a sunna, yace___”.
          _“Hussaina ni bazance ki amince ko karki aminceba, saidai nabaki dama kije ki duk’ufa rok’on ALLAH, a cikin kwana ki biyu rak ALLAH zai nuna miki mafita da abinda zai zama alkairi a gareki, sannan karki sanarma Hasaanar ki, danna kula bazata amince ba tacikin sauk’i, tashi kije”._
        “A wannan ranarma haka baba mai kanwa ya sakani cikin rud’ani, nazo dukna hana kaina nutsuwa da kwanciyar hankali, saidai nabi shawararsa ta mik’a kukana ga Ubangijin al’arshi, dan shine gatana kuma fitilata, a kwana na biyu kuwa saiga dalilin dayasani amincewa da buk’atarka ya faru, na amince maka badan hankali na ya kwantaba. tunda kuma lokacin baba mai kanwa bai kuma min maganar data shafi auren ba, harma na d’auka duk mafarki nayi, har maganar da mukayi d’in dakai. Saida ana gobe d’aurin aurenmu da safe na fita yin wani Abu na gamu da baba mai kanwa, shine yace na biyoshi gida. Mun Isa gida a d’akin zaurensa, yabani wasu abubuwa dabansan mineneba na sha, sannan yabani turare kashi biyu, yace ni 1 Munubiya 1, yace____”
         _“Hussaina kimin wata alfarma mana?”._
       “A sanyaye nace kabani Umarni akwai baba. Yay murmushi da fad’in___”.
      _“ALLAH ya yimiki Albarka Hussaina, ina tausayinki ta wani fannin, ta wani fannin kuma murna nake tayaki, duk abinda nake hasashe a kanki nasan zaki iya, dan kinfi y’ar uwarki wayo, ni dake zamu had’a kaine wajen fidda mahaifinku a sark’ak’iya, su a gangancinsu sun tozarta kune domin tunzura mahaifinku da karyar masa da zuciya, amma basusan Ubangiji mai hikima baneba, yafisu sanin akan abinda su bai basu damar saniba, kiyi hak’uri inata miki magana a cirkud’e, zaki fahimci komai anan gaba kema, alfarmar da zakimin shine dukkan abinda kikaci karo dashi a rayuwar aurenki ki sanar min shi, insha ALLAH Zan miki fashin bak’i gwargwadon abinda na fahimtar nikuma, maganar zaman aurenku da yanda kuka ginashi kuma ya rage naku bayan warwarewar komai, wannan ba hurumina baneba, tashi kije, daga nan dai zamu dinga tayaku da du’ai”._
      “Dukda banida tabbacin mijin dazan aura wannan magana tashi tamin nauyi da wahalar fasaara, da y’an gidanku suka kai lefena kuma saina kuma tsintar kaina a rud’ani da firgici, ban kuma fita daga wannan firgicinba har aka kawoni wannan masarautar. Saka pills da Muftahu yayi mana shine k’alubale na farko dana fara cin karo dashi Wanda nake k’yautata zaton baba mai kanwa ya hangomin, hakanne kuma ya sakani tada hankali  nace nafasa auren, dan a zatona kun had’a bakine da Muftahu, amma sai maganar tafiya India ta datse dukkan hanzarina, ko kad’an banyi yunk’urin sanarma baba mai kanwa wannan batunba, dan aganina baya cikin abinda shima zaiso Sani. Idan baka mantaba a lokacin da ka kaini sallama gida da kuma gidansu Munubiya ka barni a can?”.
        Kansa ya jinjina mata idonsa a lumahe ya jingina da gado, kai kace ba saurarenna yakeba barci yakeyi.
     Ajiyar zuciya na sauke, na cigaba da fad’in “Aunty Salamah tazo gidan ta sameni ai, saboda Munubiya ta sanar mata zaka tafi dani, wannan itace damar farko dana samu na rok’onta yimin bincike akan Muftahu da Saleem yaronka na plaza, (abinda yasa Saleem yashiga Layin zargina saboda randa abinnan ya faru bayan fitowarmu shikuma naga ya fito daga tsakanin wasu motoci a firgice, dayake a time d’in bamusan mizai faruba ban kawo komai a rainaba sai washe gari, danayi bincike a kansa saina gane yaronkane na shago kuma amintacce) daga ita har Munubiya a lokacin basusan dalilina nason amin bincikenba, saidaga baya Munubiya ta fiskanci komai, dayake tanada kaifin basira, amma batasan tsakanina da baba mai kanwa ba. mun tafi India nabar Aunty salamah da wannan aikin”.
         Knocking k’ofa da akayine ya saka Munaya yin shiru bata cigaba ba, na kalli Galadima da har yanzu idonsa a lumshe, batareda ya bud’eba yabada izinin shigowa, yasan dai bazai wuce Sauban ba.
      Samha ce ta shigo, ta risina tana gaidashi, sannan tace, “Aunty Amaturrahman ta tashi itada Abduraheem”.
     Yunk’urawa nayi zan mik’e galadima ya katseni ta hanyar fad’in “jeki kawosu”.
     Na kallesa da mamaki, yayinda Samha ta fice abinta, “amma yalla6ai darefa yayi, mubari mu k’arasa zuwa gobe mana?”.
      “uhm-uhm”. Kawai ya fad’a.
     Shiru nayi nakasa cewa uffan, har Samha da Sauban suka shigo d’auke da yaran duka uku, kar6ar Abdurraheem nayi, dan yaron tausayi yake bani saboda rashin kuzarinsa (karku manta har Yanzu Munaya batasan yaron yanada irin ciwon mahaifinsa ba), su kuma Sauran ya kar6esu. Sauban da Samha suka fice sudai suna tunanin wannan zaman nasu, komi suke tattaunawa oho.
     Bayan fitarsu a cikin gyale na fara shayar da yaron, Galadima dai baice dani uffanba, sai kallon yaransa kawai yakeyi, na cigaba da fad’in “Abu na biyu dana fara cin karo dashi shine ganin Abie a halin daya tsinci kansa, wannan lamari ya d’aga hankali na, amma a lokacin banida wayar kiran baba mai kanwa na sanar masa, ina tsoron na saka a wayarka kuma ka gano wataran, sai kuma tarihin masarautar nan da Momma ta bani…….”
      Cikeda mamaki Galadima ya kalleta, dak’yar ya bud’e baki cikin yamutse fuska yace, “Momma!?”.
       Nace, “eh lallai Momma da kanta, dukkan rayuwar dakasha ta gwagwarmaya ta sanar min, tundaga yarinta zuwa girmanka, ta sanarmin hakanne danna lura da abinda ban saniba a masarautar, kar wani yayi amfani dani wajen cutar dakai. Bayan nan babu dad’ewa kabani waya, daga nan nasamu damar sanarma baba mai kanwa sirrinan guda biyu, ciwon Abie da tarinku. shine yabani dukkan addu’oin da maganin daza’a nema arink’ama Abie, kuma Alhmdllh munakan ganin haske. daga nan kuma na cigaba da samun haske game da dukkan Motsin Muftahu, amma kuma babu wani abinda bai daceba ko cin amana tattare dashi, damukaga mun shiga kokwanto saimuka saka Sarkin Mota da Saleem suka sace manashi a randa kaje d’akkomu a airport ni da Sauban lokacin da Abba yay accident ”.
        “ya salam! Kina nufin kece?”.
       Murmushi na masa, nace, “kwarai nice, hakan shine kawai mafita agareka damu kanmu, dan satar nashi ya zame mana haske, aunty salamah taje masa a amatsayin d’aya daga cikin matan Abie, ta hakanne kuma muka ji sunan Harun a bakinsa. daga nan muka sakama Harun ayar tambaya, su Ameer suka cigaba da bibiyar Harun d’in, kayi hak’uri ka gafarceni da abinda zan fad’a yalla6ai”. ‘nai maganar ina kwantar da Abdurraheem na d’auki Amaturrahman dake cinyarsa, itama na fara shayar da ita.
       “ki fad’i komi ke bakinki, na shirya kar6arsa da makamin HAK’URI”.
      Murmushi nayi cikin nisawa, “yalla6ai akwai sirrin dabaka saniba Wanda ya banbanta Muftahu da Harun, Muftahu shine masoyinka na gaskiya, Harun kuwa akwai manufar ra6arka tattare dashi, yasan kuma komai game da satar yarannan, akwai dalililai masu yawan gaske dazan iya kare kaina dasu, amma nabaka dama kayi wannan binciken da kanka. Sannan k’arin bayanin dazan maka shine, mak’iyane zagaye dakai, sannan kowanne akwai manufar sa a kanka, abinda yasa suka taru maka da yawa akwai k’iyayyar mahaifanka data dawo kanka a yanzu, wasu saboda tsoron ta6argazar dasuka aikatane basason kayi mulki ka yak’esu, wasu y’ay’ansu sukemawa, wasu iyayensu ne, wasu kuwa kansune, dukkuma akan inhar kahau mulki zaka iya canja komai da hukunta kowane ya sakasu wannan k’iyayyar a gareka, a yanzu dai kanada Avedance guda hud’u zuwa biyar a hannu, na farko sune wad’anda ka kama da yaran nan, yakamata kasan wanene ya saka su kafin kasan dalilin sasun, na biyu Harun, yakamata kasan miyasa yake tad’eka bayan ka yarda dashi Yakuma San airrinka, na Uku shine Saleem, dolene a wannan karon kasan wanene ya sakashi aikin tsaida CCTV cameras a waccan ranar, na hud’u shine SD minene had’insa da mahaifina, na biyar shine Fu’ad wanene ya sakashi kaimu birnin gayu a waccan ranar, sai Malam saminu driver Alhaji balala dan akwai abinda ya Sani tabbas, hakama farhat ku sake bata tsaro sosai, dan mahaifinta zai kawo kansa gareka cikin sauk’i saboda k’aunar dasuke mata, Sauran kuma zuwa nan gaba zan baka haske a kansu,  wad’annan dai ka gaggauta sanin abinda suka Sani a cikin kwanaki biyunnan kacal, dan mak’iya bazasu zauna kallonka ba suma, sunacan suna had’a kayan yak’i. zanje na kwanta, saboda yakamata zuwa gobe mu fara shirye-shiryen komawa gida bisa al’adar haihuwar Fari, yau Munubiya tana can ma ita”.
          Ido kawai ya tsura min yakasa koda motsi, na d’auki Amaturrahman Na Goya, sannan Abdurrahman da Abdurraheem kuma a hannu nayi ficewata. Sauran bayani na k’ok’arin mahaifiyarsa Momma kuwa bazan fad’a masa yanzuba, sai komai ya lafa, saboda suna tattarene da sirrikan dasuka shafeni wad’anda bazan ta6a yarda ya sansuba…………….????
     *Kudai k’ara hak’uri dani, nasan a zak’e kuke da sonjin Galadima ya fara caskale, komai a sannu-sannu ne, dama ba tufk’ar keda wahala ba warwarar, babu abinda yakai k’arshen Novel da saka ciwonkai irin k’arshe, musamman ma mai sark’ak’iya, idan kuka cigaba da hak’urin bina kamar yaune komai zai k’are, shiyyasa nakebi daki-daki yanda kuma zaku gamsu cikin sauk’i.*
_lallai Comments naku nasakani nishad’i, musamman addu’oin Ku gareni ni da mahaifina????, harma nakan Gaza sanin yanda zan nuna muku jin dad’ina, amma ina kallon kowa wlhy, saidai idan bana cikin group d’in kuwa, ALLAH yabar zuminci, ina yinku irin Trillion’s d’innan, I love you all wujiga-wujiga wlhy????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button