NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 2) 16&17

~Book 2~ ????????1⃣6⃣
……………..“Kin shirya taimakon Mijinkine Munaya?”.
A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad’an lumshe idanu sannan na bud’e a kansa, muryata na rawa nace, “ni bansan komaiba. kuma
ina ganin a wajen Abie yakamata ka k’ara samun haske ai, tunda yanzu yana magana”.
Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d’aya ba?”.
Kaina na girgiza masa a sanyaye.
Ya murmusa, tareda d’ora hannunsa saman cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda zata zama uwar d’ana ko ‘yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k’anina. daga k’arshe ina rok’onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik’irarki a ma’auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana cikin had’ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak’iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad’in kar’a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN ‘DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d’ina ma a wahale take kasantuwa, dan haka nakeson gyara gobena da goben ‘ya’yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba”.
Nad’an muskuta domin gyara zamana, ina fad’in “shikenan, amma kabani lokacin please”.
“Nabaki”. yafad’a yana mik’ewa tsaye.
Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud’ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk’in kai, saidai idan baka fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai.
A gaba d’aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita karo dasu a d’akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d’in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d’aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d’in da yakeyi, motsin da d’an cikina yayine ya sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d’aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d’ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad’i, yace na sauka k’asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k’ara k’urewa saina d’auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.
Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d’azun yana lura da dukkan motsita ta camera d’in daya ajiye a d’akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk’ata ga Abbanta, dan Abba yak’i bashi kowacce k’ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk’ar muhimmanci a aikinsa.
Wayarsa tai ‘Yar k’ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak’on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak’on, yay hanzarin bud’ewa. (Galadima ya had’a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to).
_“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k’arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k’uda, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k’are a tsakaninmu, domin babu alak’a kuma kenan, kinga nima na samu ‘yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace”._
Babu shiri Galadima ya mik’e tsaye, jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad’annan yaran suka sani? kenan Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d’anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik’irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da ‘Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.
Baifi mintuna 15 ba da tura sak’on da Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d’insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d’aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d’agawa Munaya race, “Sweetheart kinga sak’ona kuwa?”.
“Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”.
“Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k’afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k’fur d’in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad’amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad’amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d’innan yake bani da gaske”.
Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace, “to ALLAH yabar k’auna dai, sweetheart”.
“ban ganeba, k’aunar mi zai bari?”.
“keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine”.
“Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok’eni ALLAH akan nafad’a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d’in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa”.
Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara kwanciyarta tana fad’in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara?”.
“kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k’aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k’ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa”.
“to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok’eshi inhar bashi bane kokin fad’a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik’e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k’asarnan”.
“Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad’a masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”.
“to shikenan, sai naji yanda kukayi kenan, Yaya unborn d’inmu?”.
“gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy, na k’agara ma ya fito na huta, kema Yaya namu da lafiyarki?”.
Cikin tsokana Munubiya tayi dariya, “aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”.
“wlhy na kula bakida man kai Munubiya, sai anjima”. Munaya tafad’a tana yanke wayar.
Galadima daga can yay wani k’asaitaccen murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai lumshe idanu.
????
????Galadima Kodai-kodai????
************
Muna gama waya da Munubiya na sakko k’asa, babu kowa gidan dagani sai su innarmu sai jakadiya, a falon k’asa na iskesu suna hira.
Jakadiya tace, “ranki ya dad’e kin fito?”.
Murmushi namata, ina fad’in “na fito jakadiya, ya k’ok’ari?”.
Tai ‘yar dariya tana cewa “kuke fama da k’ok’ari ai, ALLAH dai ya raba lafiya”.
Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta amsa tana tambayata ya jikin.
“da sauk’i” na fad’a kaina a k’asa, nace, “innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”.
“A’a sun fita ai shida Sauban tunda safe, zasuga likitansa daga nan sud’an zaga gari”.
“Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”.
Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”.
Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai birgeni yakeyi, babu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”.
“Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi sai nasa halayyar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya saibai canjaba kuma”.
Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi danake tayasu dashi kawai.
Mun dad’e a falon har su Abba suka dawo, masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cigaba da hira, tashi innarmu tayi tabi bayan Abba.
Sauban ya mik’e yana cewa zaije ya watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin haka natashi na nufi masaukin su innarmu.
Nakama handle d’in k’ofar zan murd’a tareda yunk’urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad’ama kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki, sannan inajinka kana sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k’ok’arin 6oyewa kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba Auwal, a tunanina yanzu munzama irin d’ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga lokacin da wani bak’in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma magana tsakaninka dashi cikin fushi”……
A rikice naji Abba ya katseta da fad’in Ai’sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak’in fatane shine yake tambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin tambayar mike faruwa ina baki amsa babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai d’inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da babu wata sauran matsala, ki sanarma Munaya ta sanar da mijinta gobe zamu koma kawai”.
“gobe kuma Abbansu?”..
A fusace yace “eh!”.
Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja baya daga jikin k’ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za’a bud’e k’ofar, tabbas akwai abinda Abbanmu ke 6oyewa da gaske, to wanene bak’in fatar da innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? dan tabbas na tarar Abba baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a’a kansane kawai ked’an ciwo.
Bansan na iso bedroom d’inmu ba saboda zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri saboda jin an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya rik’oni da k’yau yana fad’in “Nutsu mana”.
Da k’yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana cikin matsala, amma wani dalili ya hanashi fad’a, takai har inda yake jiyya ana bibiyar rayuwarsa kenan?.
Ido Galadima shidai ya zubamin, bai hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto da kaina jikinsa, jina a k’irjinsa saina fashe da sabon kuka, nanma k’ala bai ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata nayi shiru sannan ya d’agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik’e cikin tafin hannunsa, Kafin yay k’ok’arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k’asaitacciyar muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”.
Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yakemin, shima murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a saman ido.
Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya daina, bud’e idona nayi nad’an kallesa, ya d’agamin gira yana fad’in, “ya dai?”.
Cikin tunzuro baki nace, “babu komai”.
“To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay maganar yana sakin kumatuna’.
Binsa nayi da kallo, ganin zai fara k’ok’arin cire kaya, na mik’e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum k’ara girmama yakeyi, baya shakkar cire kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na fita na bashi waje.
Hannuna ya rik’o, na waro ido waje cikin mamaki.
“ina zaki?”. ya fad’a cikin tsare gida.
“ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan dawo ai”.
“toni dodone?”.
“A’a na fad’a ina ta6e baki”.
“to koma ki zauna ki kalli sadakinki”.
Idanu na waro masa waje da hangame baki.
Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d’aya. Ni daifa k’in kallonsa nayi, dan wlhy kunya nakeji sosai, dukda ‘yar shak’uwa ta shiga tsakaninmu hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar’a kawo masa raini. Yakan bani dariya sometimes, amma nima saina Basar saboda Jan aji.
Iska kawai naji a cikin kunnena, da sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata.
Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad’ata, muryarsa can k’asan mak’oshi yace, “miya sakaki kuka?”.
Salon da yay maganar ya sakani lumshe idanu saboda tsigar jikina data tashi.
Nace “kabari ka gama zan fad’a maka”.
“miyasa ba yanzu ba?”.
“ka saka riga to”.
Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi……..”
Saikuma yay shiru yak’i k’arasawa, hannuna na saka na rik’e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k’arasa mana, akwaini da mi?”.
“Humm” kawai ya fad’a yana sakina, yaja bathrobe d’insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k’ok’arin d’aure igiyar sannan na d’ago na kalleshi.
“To mikuma kike kallo?”. Ya fad’a cikin tsare gida.
Baki na ta6e ina fad’in, “miye abin kallon to?”.
Ya d’an fiddo ido sannan ya matsoni, “zona nuna miki”.
Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan haka na duk’e ina fad’in “wash ALLAH cikina”.
Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da hanzari yana tambayar lafiya?.
cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi ALLAH”.
rankwashina yayi aka yana cewa “ke d’inan ko”.
Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne zaisha wahala.
Ina zaune ya fito, na d’auke kaina tamkar ban ganshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d’akko ruwa da Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda yayi yunk’urin cire bathrobe d’in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa, ban damuba dan nasan halin kayana yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana kamar ba shiba, anjima kad’an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a Hospital, Mara dariya mara later r????.
K’afarsa d’aya ya d’ora kan d’aya yana shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, batareda ya ajiye kofinba ya maido dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”.
d’ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna fusata”.
“shine kika shigo kina kuka?”.
Na jinjina masa kai batareda nace komaiba.
Shima bai sake cewa komanba ya kauda idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona, “Munaayaa mukawo k’arshen 6oye-6oye mana”.
Kallonsa nima nayi, nace, “kamar ya?”.
“humm” yafad’a yana cije lips, mik’ewa yayi tsaye ya ajiye cup d’in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d’akin hannunsa goye a baya, nikam dai binsa kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta katsemin tunanina.
“Munaaya! Mikuka ta6a gani a d’akin Abba ke da ‘Yar uwarki?”.
Zumbur na mik’e dan mamaki, “yalla6ai a ina kasan wannan?”.
batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan haka fad’amin?”.
Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad’a maka bane matsalar, kuskuren muhallin fad’arne da kuma makomata”.
“bakida dukkan Matsala da wad’annan, idan bai danganceni ba zan d’auki matakin taimakon sirikina, makoma kuwa inada yak’inin kare martabar matata uwar d’ana ta kowanne hali”.
Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace, “matar Contract ko?”.
“Well Duk yanda kika fassara dai-daine, abinda na Sani kawai wannan maganar batada nasaba da waccan, dan haka kibar kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”.
“humm” kawai na fad’a na koma na zauna inda na tashi.
Idonsa a kaina ko k’yaftawa bayayi.
Na nisa sannan nafara fad’in,
_“Na tabbata tunkan ka k’ulla alak’a dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana fito, kamar yanda kasani mu ‘yan biyune hakan yasaka ba’a banbancemu ni da ‘yar uwata, sai dai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai hak’uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne, sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d’aga k’afa, inhar kaga nayi dogon zama da mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji matakan iya zama danine, basai amfad’a ba nima kaina nasan halayena na kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d’in da bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinmu yayi wani bak’o, matsalar da aka samu shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka hak’in tarbar wannan bak’o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._…………………..✍????
Mu had’u a page na gaba????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????_*
*_typing????_*
???? *_HASKE WRITERS ASSO….._*
*_♦RAINA KAMA…..!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
~Book 2~ ????1⃣7⃣
_………………“Da haushi na d’auki ruwan da innarmu ta bani na fita, saboda muna tsaka da kallon wani film daneke masifar sone, Munubiya dan kartaje kaiwa saita hau barcin k’arya. Tunda na shigo shegen mutumin nan ya tsura min idanu yana lasar baki, kai kace tsohon mayene yaga nama, a zafafe na dire tiren agabansa ko k’ararsa zatasa ya dawo hayyacinsa, amma wawannan yayi nisa, na buga tsaki a zuciyata zan fice, caraf ya kamo hannuna, ban dubi girmansa ba na dage na watsa masa mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar Abbanmu falon. Amma d’an iskan ganin Abbanmu da marin danai masa baisashi sakin hannunaba, saida Abba ya daka masa tsawa da fad’in “SD! wane irin iskancine wannan? a cikin gidana ka kama hannun ‘yata?!”. Abba na rufe baki ina kuma bashi mari na biyu, tunda naga alamar shi bunsurune. a wannan karon ya saki hannun nawa, saboda janyeni da Abba yazo yayi, Abba ya nunamin k’ofar fita, koda na fita saina la6e a corridor d’in shiga falon bak’in._
_A zafafe Abbanmu naji yana fad’in “SD ubanwa yabaka damar shigomin gida ne?”. sautin tafin bak’on na jiyo dan haka nai saurin lek’awa ta kafar labule, gani nai yana zagaye Abba yana dariya da tafi, cikin shak’iyanci yake cewa “Alhaji Auwal, Alhaji Auwal! dama kanada k’yawawan ‘yammata haka? Woow nice babie, idan na samu wannan ai ko rana bazata sake ganina ba, wlhy nasan zan kwashi rom………, mari Abba ya zuba masa a kumatu, yana nunashi da yatsa, a matuk’ar fusace yace, “wlhy idan ka kuma furtawa saina datse kazamin harshenka a falonnan, wawa kawai”. SD ya shafa kumatunsa sannan ya sumbaci hannun yana hurama Abba, “Kafa birgeni Alhaji Auwal, kai jarumi, ‘yarkama jaruma, kai inason irin haka mutumina uhhhhhhm mutccch”. ya k’are maganar da kuma kissing hannunsa. Banza Abba yamasa ya d’auke kai daga kallonsa yana fad’in “miya kawoka gidana?”._
_Alhaji Auwal kenan, kaima kasan dakaga SD kasan zancen, a wannan karon da albishir d’in k’arin farashi akan tayin baya nazo maka, sannan kuma damace a gareka ta k’arshe hakan, mun yanke shawarar baka naira milyan 500”. Abba yaja tsaki yana hararsa, “ka koma ka sanar ma iyayen gidan naka ina kan bakana, sannan Ku farka daga barcin da kukeyi, dan bazan ta6a badawa ba, kamar yanda ban ba da jiya ba, bazan bayar yauba, sannan gobe ma bazaku samuba, wannan kuma yazama first and last dazaka shigomin gida, inba haka ba ina mai tabbatar maka zaka aikata kuskuren da bayan bayanka ma saisunyi takaicin jin yanda zaka k’are”. “kwantar da hankalinka sarkin jarumai, tabbas zan tafi, bakuma zan sake dawowa ba balle nayi nadama Oga, ammafa bazan 6oye makaba, kana bani mamaki, kak’i bama Wanda akace ka bamawa, sannan kak’i saida mana mu masu buk’ata, shikuma wannan Abu ba tuwoba balle muyi tunanin zakacine, waikai mike damun kankane haka? ka zauna kanata rik’ema Wanda yarigada ya mutum amana, shikuma Wanda kakema tanadin bashida maraba da gawa, koda yake ashefa ga Galadiman Ku nan, koshi kakema tanadi?”. “wannan ba matsalarka bace”. Abba yafad’a cikin karsashi. “kumafa gaskiyarka wannan ba matsalata baceba, amma tabbas inada yak’inin kai zata zama taka matsalar maybe ma harda santaleliyar budurwar ‘yarka, lallai labarin k’yak’yk’yawa da ahalinta zai Shiga duniya kwanannan, nabarka lafiya, ka huta”._
Da sauri nabar wajen gudun karya fito ya ganni, nakoma cikin gida ina juya wad’annan zantuka na abbamu da bak’onsa, masu tsananin wahalar fassara, mi bak’on yake nema a wajen Abba dahar yake ik’irarin sun basa zunzurutun kud’i naira na gugar naira, d’ai-d’ai har miliyan d’ari biyar? Amma dukda yawansu Abba bai firgitaba balle mik’a wuya?, sannan wanene Galadima kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d’aya.
Munubiya data lura da halin danake cikin ta sakani gaba da tambayar, tun ina k’ok’arin 6oye mata Dan kar hankalinta itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma gani, harma Wanda na aikata.
Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama, nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani gaskiyar lamarin, amma mun kasa kama bak’in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d’arare saboda tsoron furucin mutuminnan.
a wata ranar talata da Abba zai dawo daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d’akinsa saboda kanta namata ciwo. muna tsaka da aikin sai muka tsinci wani file da yasha k’yak’yk’yawar adana a awani akwati dake cikin wardrobe d’in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake muka bud’e wannan file, a shafin farko mukaci karo da wani Abun daya kuma rikita tunaninmu”.
????????
*_Tabbataciyar wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik’a wannan sak’on amana ga Wanda ya cancanta, to na shaida muku da cika umarnina na ida nufina a garesu ‘ya’yana ko ‘yan uwana, inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan masarauta…………”._*
“iya nan rubutun ya tsaya, muka bud’e shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k’arashen zancensa, amma sai sunayen mutane muka gani a k’alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d’akin batare da mun Ankara ba, wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana fad’in “ku harkunkai girman da zakumin bincike a d’aki a matsayina na mahaifinku? mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe kuka koma la6e?”. haka Abba ya rikice gaba d’aya muma ya rikita mu, ya dinga zabga masifar dahar tajawo hankalin jama’ar gidanmu, indai tak’aice maka bayani har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d’in matuk’a, dukda hak’urin da muka bashi yak’i saurarenmu, ya d’au tsawon lokaci yana fushi damu kafin ya daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani fad’ar bak’ar magana ga manyan k’asarnan har ‘yan uwana na tayani. Sai kuma mukaji sunanka a bakin wani saurayi da ‘yammata biyu. Wannan ganinaka ne yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine Wanda muka ta6aji a furucin bak’on Abba?. ga kuma sunan masarauta da muka gani a rubutunsa, dukda bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid’inne.. Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza, sainaga bebekin Abba daya saka kansa had’ari akan Wanda shi baima damu da damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai”. (Kafayi hak’uri, gaskiyata nake fad’a, guntun murmushi kawai Galadima yamata baice uffanba) taci gaba da fad’in “Wannan ne dalilin yimaka tsak’i a asibiti, idan har baka mantaba, har dogarinka d’aya yataho da zummar d’aukar mataki amma ka dakatar dashi da fad’in ya barni”.
Galadima ya murmusa alamar bai mantaba.
Nace, “ka tuna kenan?”.
“Na tuna kwarai da gaske, dan bancika manta abuba saidai idan na d’aukeshi mara muhimmanci, amma a time d’in ai banga face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d’aya a lab da muka iskeku keda sisters d’inki, ni nama zata Ku ‘yan uku ne ai”.
“Umyim, amma a time d’in babuma Wanda zai d’auka Kasan da zamanmu a lab d’in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak’i amsawa sai d’aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d’in, dasu munu sukace kainema kabada jinin da za’a sakama feena ban yardaba”.
Baki Galadima ya d’an ta6e yana shafa kwantaccen sajensa, ya d’agamin gira d’aya yana fad’in “bazaki fahimta bane yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara?”.
Na d’an ya mutsa fuska ina fad’in bamai nisa bace, dan ko 2years cikakku baza’a k’ulla ba, Muna Exam d’in NECO nema, dan har results d’inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran ‘yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k’aramine ya biya namu, so munfara karatu dai babu dad’ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad d’insu Ayusher yamasa Yakuma sake bashi hak’uri. tundaga nan komai yazama Normal. Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a kwanaki kad’an na amince da tayin auren Contract d’in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda alak’a da amintar tawaba, akwai wani dalili daya shafi ahalina”.
Mik’ewa Galadima yayi yana salute d’ina, yace, “kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da d’abi’unki sai kika kauda hankalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR ‘DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sai dai inason Sanin minene alak’arku da Muftahu to?”.
“muftahu kuma? babu wata alak’a bayan wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai”.
Takowa yay zuwa inda yake zaune a da, ya koma saman kujerar ya zauna, “kin tabbatar babu alak’a ta kowane fanni?”.
“miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan?”.
Ya murmusa yana fad’in “kozaki gaji Abba ne?”.
Nace, “akan me?”.
“jaridanci mana, naga kin shahara wajen iya bincike”.
Mik’ewa nayi saboda k’afata tafara yaamm alamar jinina yana buk’atar motsawa, nafara d’an takawa. hannaye kawai ya hard’e a k’irji yana bina da kallo, saida nad’an zagaya d’akin kafin nabashi amsa da fad’in “yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
Kansa ya girgizamin kawai.
Nace, “humm nifa nan daka gani, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo”.
“really?”.
“baka buk’atar jayayya”.
Ya d’aga kafad’a yana ta6e baki, “hakane kuma”.
Sharesa nayi na zauna a bakin gadon danna d’an mik’e, a haka najawo filo na kwanta k’afafuna a k’asa.
Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman k’aramin table d’in gaban sofa, jinai kawai ya kama k’afata ya d’ora saman cinyarsa yana matsamin a hankali.
Da mamaki na d’ago kai na kallesa.
Ido d’aya ya kannemin yana d’an ta6e gefen bakinsa, ya maida kallonsa ga k’afar.
Sabon salo, na fad’a a raina. a fili kuma nace, “yalla6ai kaine……”
Bai bari na k’arasa ba yay saurin fad’in, “ba dole na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba”.
Harara na dalla masa ina janye k’afata, ya kalleni da mamaki, “ya haka? ko haushi kikajine?”.
“miye zai Sani jin haushin? saika bari idan yafito duniya ka matsa tashi k’afar”.
“oh ni Sameer naga ta kaina”.
“zama kaga ta k’afa bata kaiba, Sunan nakama bazaka iya fad’arshi da r ba”.
“oh nan kuma kika dawo?”.
Matsawa nayi baya saman gadon sosai batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani yunk’urawa zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d’a mai ido ba, yasa hannu ya rik’eni, “yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad’a dalla-dalla”.
“lah wasafa nake maka, kaga rigar wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka”.
“Ai kinga dai-dai kenan”. Yay maganar yana k’ok’arin kwance igiyar rigar.
Hannunsa nayi azamar rik’ewa ina marairaice face alamar yaji tausayina.
Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma k’ank’ame nasa nak’i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto gefena tareda sakani jikinsa ya rungume.
“Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji”.
Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena yace, “kedai fad’i gaskiya, ko kina son a…….”.
Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina kukan shagwa6a, ya shiga k’ok’arin cirewa amma nak’i bari, shi dariyama na bashi, irin wannan hak’ilo haka. duk yanda yaso na barsa k’i nayi, saida barci yafara fisgata hannun ya zame.
Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a fili ya furta “mai bakin tsiwa”. Ya k’are maganar da sumbatar goshinta yana gyaramata kwanciya a jikinsa.
Ya tsira mata idanu yana kallon yanda take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa maganganunta taketa cud’awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k’arama mara tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had’ari? ya sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune, k’afafunta yashiga mammatsa mata a hankali, aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad’an murmusa, yasan ko’a d’azun tanaso fa, amma iyayi yasata hanashi ya mata. Ya d’auki tsawon lokaci yana mammatsa mata jikinma gaba d’aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta dalla-dalla, daga k’arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d’akin sirrinsa, duk abinda tafad’a yasamu sabon file ya bud’e masa, baya wasa da evidence komai k’ank’artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad’e yana rubuce-rubucensa kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara searching gameda SD d’in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama baiyi tunanin fahimtarba, waya ya d’auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace, “Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD?”.
“SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina zuwa bani mintuna 30”.
“ok saina jika”.
Galadima Na yanke wayar ya nemo number d’in Abba da bakowa ya sani d’innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d’in ciki suka bayyana, d’aya bayan d’aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu yafi yawa, yad’an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d’auki mataki a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad’o masa, nutsuwa yay yana sarrafa Computer’s d’in cikin tsantsar kwarewa da gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan watarana zasu iya kira ko sak’o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a kunne.
Babu shiri ya d’auki waya ya kira daddy, bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace, “ai a kunne take koda yaushe, Change ma baya k’arewa nake kuma sakata, idankuma zan zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, amma ina zuwa dai”.
Galadima ya amsa da to, amma k’asan zuciyarsa tana mamaki. babu dad’ewa Abba ya sake kiransa, “Ashe Change ne ya k’are babu dad’ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata”.
“to Dady, Na gode sosai”.
Sunayin sallama da Dady Kiran Nuren Na shigowa, d’agawa yayi, Nuren yace, “inagafa brother hanya d’ayace dazata saka musan shi wanene SD d’in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket insha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu, zai amsa mana dukkan tambayarmu”.
“ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita bama wayo ta cikaba sosai, k’ila kafi samu cikin sauk’i a wajenta, abinda yasa Malam saminu baison fad’ar komai, babbar ‘yarsa cikin ‘ya’yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan idan ta haihu za’ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad’ar komai, dan karya lalata waccan alak’ar, dan tabbas yasan yana fad’a auren bazai yuwuba, to nima banason shiga hak’in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud’u kenan, amma shi yaron ya kawota nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d’aya zasu dawo Nigeria a d’aura musu aure sannan su dawo Dubai d’in, dan Alhaji balala baya son abinda zai 6ata record d’insa, kuma mamar yaronce ta Dage sai anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, dan haka mu bama Malam Saminu wannan damar”.
Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin mamaki yace, “duk ya akayi kasan wannan brother? ”.
galadima ya murmusa, yana fadin “Nuren kenan, to bara nayi copy d’in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo, nasha fad’a maka bada kwanji kawai ake yak’i ba, sai anhad’a da dabarun tunani dana nazari, so kad’an nafad’a maka daga abinda ya shafi Malam Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d’in da zakuyi maganar ka tabbatar ka had’a Communication dani ok?”.
“babu damuwa aljanin munaya”.
Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama rainashi, wai Aljanin Munaya, d’an iska zan kamaka ai.
Kashe komai yayi ya fito daga d’akin, bai koma cikiba saiya sakko k’asa, ya iske Sauban kad’ai a falo, shima shigowarsa kenan daga asibiti yake.
Galadima ya zauna yana fad’in “jirgi sarkin tashi daga ina?”.
Dariya sauban yayi, yace, “kai Yaya, nine kuma jirgin?”.
“Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi gameda zuwa bautar k’asarka Nigeria”.
Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu “yaya yanzu fa ca za’ayi saina koma 9ja har zaman 1year?”.
Hararsa Galadima yayi, “to zakayi anan k’asar ne?”.
“Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a manta da bautar k’asar kawai mana, nayi joining masters d’ina”.
K’aramin tsaki Galadima yayi, yay crossing k’afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida ya d’auki wasu mintuna sannan yace, “rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi zatoba, idan kace bazakayiba it’s better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani waje”.
Ganin ransa ya 6aci Sauban ya marairaice fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d’aga masa hannu, sannan yamasa nuni da k’ofa alamar ya fice masa.
Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad’ai.
Galadima ya girgiza kai kawai yana fad’in “ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema ba”.
Jakadiya data fito ta rissina tana fad’in “Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa”.
Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan saboda halaccin datake wa rayuwarsu, “yauwa jakadiya, ya gidan?”.
“lafiya lau Ranka ya dad’e, a shirya abinci ko?”.
Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai kuma ya maida ga jakadiya, “bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje”.
“to ALLAH ya dawo dakai lafiya”.
Hannu ya d’aga mata kawai sannan ya tashi ya fice. mashin ya hau yafita.
Abba dake can gefe a harabar gidan tsakanin wasu flowers yana hutawa ya sauke ajiyar zuciya, tundaga fitowar Galadima har hawansa mashin da fitarsa akan idonsane, rufe idanunsa yayi yacigaba da tunaninsa da tun d’azun yake zaune a wajen yanayi.
Asibiti Galadima ya nufa, yay kici6us da Aunty Mimi Na shirin tahowa gida ta huta, ta kalleshi da mamaki, “my k’ani dawowa kayi?”.
Gefen girarsa yad’an shafa da d’an yatsa d’aya, “eh , ina zakije k?”.
“gida zanje nad’anyi wasu abubuwa”.
“ok sai kin dawo”. yafad’a yana ida shigewa, ita kuma ta fice.
Momma Na zaune tana waya da papi, ya zauna d’aya a kujerun yana kallonta cikeda sha’awa, uba da ‘Yar sun birgeshi, juyawa yay ya kalli gadon Abie, barci yakeyi, har Momma ta gama wayar ison Galadima Na kan Abiensa ko k’yaftawa bayayi, shi kad’ai yasan mi zuciyarsa take sak’awa.
“Muh’d daga ina haka?”. Maganar Momma ta katse masa tunani.
Janye idonsa yayi daga kan abie ya maido ga Momma, “Daga gida Momma, har yanzu barcin Abie yakeyi?”.
“eh tunda ka Fita bai farkaba, mike faruwa naganka cikin damuwa?”.
Huci ya furzo daga bakinsa, zaiyi magana sai kuma yayi shiru.
“Nifa tsiyata dakai kenan Muh’d, Yaya Abu nacin ran mutum bazai iya fad’ama kowa a taimakeshi da shawara ko addu’a ba, kaga yanda jijiyar kanka ta tashi kuwa? Haba Muh’d Sameer d’ina, kaifa yanzu ubane, girmanka ya k’aru, aringa rage damuwarnan da miskilanci mana, ni ALLAH ma yasa ba haka kakema d’iyar tawaba?”.
“kai Momma”. ya fad’a amarairaice cikin ‘Yar shagwa6a.
Murmushi tayi tace “to fad’amin mike faruwa?”.
Yay d’an tsaki, “Ni ai Momma bammasan ta ina zan fara baneba”.
“kafara ta sama kawai”. Momma ta fad’a tana dariya.
Shima dariyar yayi kad’an sannan ya gyara zama, kuma maida muryarsa k’asa-k’asa yayi yana maganar ahankali, tsaf ya zayyanema Momma yanda sukayi da Munaya, ya d’ora da fad’in “Amma kinsan wani Abu kuwa Momma?”.
“a’a saina fad’a dear”.
“uhm gani nake kamar bakomai ta fad’a minba, ta 6oye wasu abubuwan dai kamar, saidai bansan dalilinta ba.
Momma ta jinjina kai tana murmushi, “To Muh’d mizai hana kacigaba da binta a hankali, nasan zata fad’ama sauranma, ni aganina kamar tana ganin kaima ka kasa yarda da itane shiyyasa tafad’i wasu tak’i fad’in wani, idan har ka yaba da hankalin matarka yakamata ka fara sakin jiki da ita wajen Neman shawararta da sakata cikin wasu al’amura naka Na tabbata itama zata fara fad’a maka nata”.
“gaskiya kika fad’a Momma, dan naga fa’idar hakan kwarai da gaske, zan kula insha ALLAH. ya addu’oin Abie akwai saura?”.
“saura kad’an, gashi bakuyi wasuba”.
“mai k’arfin yince tazama sai a hankali, daga barci sai barci take yini”.
“ALLAH Sarki d’iyata, ai tanama k’ok’ari, dama idan ciki ya fara tsufa hakane, ALLAH dai ya sauketa lafiya”.
“To amin Momma”.
Sun cigaba da ‘yan hirarrakinsu har zuwa lokacin da Abie ya farka………………✍????
*_inata gaisheku da yawa da yawa, comments naku Na sakani nishad’i over????????????????????????????????????????????_*.
I love you wijiga-wijiga sister’s????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????✋????